Breaking News

Tayi Min kankanta 13


13*

 

Bayan Mahaifin Hammad ya ɗaukeshi zuwa nema masa magani a ƙasar rasha,anci baƙar wahala kamin asamu kansa ya dawo seti.
Cikin nasara akai masa aykin ido ya samu sauƙi,watanni bakwai suka kwashe a ƙasar sannan ya warware suka dawo gida nigeria.

Koda wasa Hammad be taɓa faɗawa kowa abinda ya ayƙatawa ƴarfillo ba,sede kullum cikin nemanta yake,be taɓa gajiyawa,sadaka sallah da addua cikin yi ike.

Jameel sojojin agajin gaggawane suka tsamoshi aruwan daya faÉ—a,taimakon gaggawa suka bashi,nunfashinshi yadawo,oxygen suka sa masa sannan akasashi a mota zuwa babban asibitin sojoji dake kaduna.

Cikin nasara akai masa ayki aka cire bullet din da aka harbeshin.yasha jinya kan yasamu ya warke,shiyasa yana warkewa ya ajiye aykin soja.

Tare sukai karatu da amininsa a turai fanni É—aya,shiyasa jameel ya koma inda yafi wayau.

Hammad hospital asibitine da mahaifin Hammad ya gina masa tun yana turai karatu,azuwan yana dawowa seya fara ayki,amma fafur Hammad yace soja zashi beson asibitin.

Haka Mahaifinsa ya haƙura,aka rufe asibitin,badan yana so ba sedan ba yadda zeyi.shiyasa da jameel yabar aykin sojan ya miƙa masa asibitin domin yaci gaba da kulawa dashi.

Hammad sunan yasamo asaline daga wani abokinsa bature,da be iya faÉ—in Muhammad ba se dai yace Hammad,mutuncin dake tsakaninxa dashine yasa Muhammad maida sunan nickname É—insa,sabida kar ya mance dashi,

Asalinsu Æ´an gombe ne amma yanzu a abuja suke zaune,sabida harkar kasuwancin mahaifinsa.

*Cigaban labari*

Shawarar da jameel ya basa tasa yasamu sassauci dan haka yanzu ya rage damuwa aransa,amma zullumin be bar shi ba.

Yau dandazon mutane suka shaida auransa da Zahra,ko ina kaduba jama’ar annabi ne,Hammad hannunsa har ciwo yafara sabida gaisawa da mutane.

Taro be watse ba se wajen magriba,a gajiye ya shiga É“angarenshi bayan ya raka su jameel,wanka yayi sannan yazura kayan baccinshi ya nemi kan doguwar kujera ya É—an kishingiÉ—a.

Amarya Zahra ko kamar wata balarabiya dan kyau,dan surayya ƙanwar hammad wacce ta iso jiya da dare daga malesia inda take karatu itace ta tsantsarawa amarya kwalliya ta ƙin ƙarawa.

ko ina ta gifta mutane se yaba ta akeyi,sabida taron mata ma cika gidan yayi ,yayi danƙam,da mutane.

Bata samu sakewa ba seda taro ya watse,a waya Hammad ya kira mummy yace a shagwaÉ“e”mummy jinjirinki fa yunwa yakeji,rabona da abinci tun safe,kisamamin abinda zanci,”

“subhanallahi,me yasa kazauna da yunwa irin haka,kai meyasa baka jin magana ne”mummy ta faÉ—i cike da damuwa.

“mummy muna cikin mutanene”yafaÉ—i a marairaice.

“bari insa akawo ma abinci yanzu katabbatar kuma kaci”tana kaiwa nan ta kashe wayar.

Kitchen ta nufa,cikin saa ko tasamu zahra da surayya suna girka abinda zasu ci,indomie ce suke dafawa amma kowa da raayinsa,na zahra da manja da busasshen kifi,na surayya kuma mangyaÉ—a ne domin soya indomie tayi da kwai.

Suna ganin mummy,duka suka rusuna suna gaisheta,murmushi tayi ta amsa sannan tace tana kallon girkin na zahra”yauwa zahra maza ki juye abincin in ya Æ™arasa kije ki kaiwa,yayanku yunwa yakeji ki hanzarta kinji,nasan baze iya cinyewa ba,kema ba ci ne dake ba duka ze isheku.”amsawa zahra tayi da cewa “to mummy bari in kai masan”tana kaiwa nan ta juya ta fice daga kitchen É—in taje ta É—auko hijabinta,ta É—ora kan doguwar rigar baccin dake jikinta,ta dawo kitchen É—in ta juye abincin a plate me kyau tasa cokali,sannan ta kifa wani plate É—in asama,ta fito ta nufi sashin nashi.

Da sallamarta ta tura Æ™ofar É—akin,zaune yake yanzu yana waya da jameel yana sake masa bangajiya,shigowarta tasa ya kashe wayar ya maida hankali kanta.a sanyaye ta zo gabanshi da abincin,tsugunawa tayi gab da Æ™afarsa,tace”barka da dare,ga abinci inji mummy”ta faÉ—i tana miÆ™a masa abincin.

Amsar abincin yayi ya ajiye a gefensa, sannan yace “bani ruwa a fridge”batare daya kalleta ba.
Miƙewa tayi da hanzari taje ta ɗauko ruwan,ta dawo ta tsuguna ta miƙa masa.

Amsa yayi sannan yace”miÆ™o min É—ayan wayata akan gado seki tafi”miÆ™ewa tayi da hanzari ta nufi cikin bedroom É—in nasa.

Zahra iyayen tsabta,tana shiga tasamu komai na É—akin a hargitse,hatta kayan daya cire zube suke kan gadon be É—auke ba.

Hijab ɗin jikinta ta cire ta rataye akan ƙofa,sannan ta shiga aykin da baa sata ba wato gyaran ɗakin nasa.

Komai seda ta tabbatar ta ajiye shi a mazuninsa,ta É—auko wani zanin gadon ta sauya masa ta gyara tsarin ajiye fulullukan,sannan ta isa kan mudubi ta fara gyara kan mudubin shima,dan komai ya hargitsa shi.

Hammad wanda tun É—azu yagama cinye abincin da mummy tace baze cinyeba,zaune yake zaman jiran ta kawo mashi wayar amma yajita shuru kamar an shuka dusa.
Miƙewa yayi ya nufi cikin ɗakin dan yaga ko me ya hanata dawowa falon.

Mamakine ya kamashi ganin ɗakin nasa agyare tsab ga wani niimtaccen ƙamshi, dake tashi,,ita kuma hakimar tana gaban mudubi tana gyara turarukansa.

A hankali ya taka yazo bayanta ya tsaya hannayensa zube cikin aljihun wandonsa,kallonta yake ta mudubi,gashin kanta ya zubo ya rufe mata fuska sabida duƙawar da tayi.

Bayan ta kammala,ta juyo da sauri zata bar gurin,ayko se tsintar kanta tayi a ƙirjin Hammad,ƙoƙarin faɗuwa take,da sauri yasa hannu ɗaya ya tarota ta dawo ƙirjin nashi.

Sunkuyar da kai tayi kunyar duniya tabi ta isheta,se sosa bayan kunne takeyi.

“ina wayar tawa?”ya tambaya a Æ™asetance.

Ganin beda niyyar sakinta ne yasa ta fara miƙa hannu bayansa,tanaso ta ɗauko wayar akan gadon da ta ajiye.

Hannunta be kai ba,hakanne yasa ta yunƙura da ƙarfi domin ta ɗauko masa,ayko baya Sukayi su duka da ita suka faɗa kan gadon hammad a ƙasa ita kuma asamansa ɗare ɗare.

A kunyace ta É—ago ido tana gyara gashin kanta,ta saci kallonshi,shima ita yake kallo,a hankali ta zame ajikinshi ta sauka da sauri tayi falon dan ta É—auki abincin daya rage taje taci itama.dan yunwa takeji.

Muje zuwa

 

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 
*TAYI MIN ƘANƘANTA*


*Zahra Surbajo*

*Marasa lafiyanmu Allah kabasu lafiya,masu ciki Allah ka saukesu lafiya,Allah kazaunar da kowa agidan auranta lafiya,Ameen*

No comments