Breaking News

Tayi Min kankanta 20


20*

 

Wasa-wasa tsawon sati guda kenan,likitoci na tsaye kan hammad amma ko alamun farkowa bashi da ita,
Hankalin iyayensa dana zahra yayi matuƙar tashi,ko kaɗan basu cikim natsuwa.

Duk yadda mummy tayi da zahra kam ta koma gida ƙi tayi,ko wanka bata zuwa gidan tayo sede tayi a asibitin akawo mata kaya ta sauya.

Koda su daddy suka tambayeta me ya haddasa masa ciwon,ce musu tayi faÉ—a sukayi da abokinsa jameel,sosai su daddy sukayi mamakin afkuwar hakan a tsakaninsu,

Daddy jameel ya nema a waya,dan jin abinda ya haÉ—asu,cikin girmamawa jameel yace”daddy wannan saÉ“anine yashigo da rashin fahimta,da taimakon shaiÉ—an,kar ku sa kanku aciki mu mukayi faÉ—anmu kuma da kanmu zamu shirya”ya faÉ—i cikin girmamawa.

“to amma jameel ga fa shi abokin naka a asibiti rai a hannun Allah,tun ranar da kukayi faÉ—an yake a sume a asibiti,baka ganin akwai buÆ™atar mu shigo ciki dan É—inke É“atakar da ta shigo tsakaninku?”

“Daddy bansan bashi da lafiya ba,amma zanzo in dubashi bana garine nima tun ranar ina lagos,”jameel ya faÉ—i cike da tausayawa abokin nasa,tabbas yasan hammad farin sani,masoyinshi ne na haÆ™iÆ™a,dole ze shiga wani hali aduk ranar daya gano gaskiya,duk yadda yaso yayi fushi da hammad É—in baze iya ba.sabida shima yana matuÆ™ar Æ™aunarsa,kuma ko shine hakan ta faru abinda zeyi kenan.

A cikin sati na biyu ne hammad ya farka gaba ɗaya ya rame yayi baƙi ya fice hayyacinshi.yazama abun tausayi.

A hankali ya kai dubansa gefen da zahra take tsaye tana share hawaye,a hankali ya miƙa mata hannu alamun tazo gunshi,ba musu ta taka a hankali ta isa gareshi.

Janyota yayi batare daya ji kunyar su mummy ba ya haɗeta da ƙirjinshi ya rungumeta yana hawaye.

Su mummy ficewa sukayi daga É—akin,sabida ya basu kunya.É—ago kanta tayi a Æ™irjinshi tana share masa hawayen tace cikin shagwaÉ“a”yaya kayi haÆ™uri karkayi fushi damu,don Allah ka samu lafiya banason ganinka baka da lfy”ta Æ™arasa maganar cikin kuka.

Ƙara rungumeta yayi ajikinshi yana ci gaba da zubar da hawayen,ya kasa magana.tsawo mintuna talatin ya kwashe rungume da ita,turo ƙofar da akayine da sallama yasa yakai dubansa gun me shigowar,

jameel ne.

Wata matsananciyar kunya ce ta kama hammad,maida kansa yayi ya kwanta,sannan ya lumshe idonsa ya juya baya.

Sosai jameel ya karanci aminin nasa,yasan kunyarshi ce tasa yayi hakan dan haka ajiye kayan hannunsa yayi sannan ya ƙarasa gunshi.

Cakumo rigarsa yayi yace”É—an iska mara mutunci,har da wani dukana rannan,to wlh baka daki banza ba zuwa nayi in rama”yana kaiwa nan shima ya shiga kirÉ“arsa,ta yadda yasan baze cutar dashi ba.

A galabaice Hammad ya buÉ—e idonsa,ya haÉ—a hannayensa gida biyu hawaye na bin idonsa,alamun tuba ga jameel É—in.

Shima jameel É—in hawaye yakeyi,da zafin nama ya janyo hammad É—in jikinshi ya rungumeshi,shima rungumeshi yayi dukansu hawaye sukeyi.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:  *TAYI MIN ƘANƘANTA*


*Zahra Surbajo*

No comments