Breaking News

Cheaters Club 3

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_ 



#ROMANCE


#FICTION

#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER


BY

 _SURAYYAHMS_

 _Watsap only 08060712446_ 


⏯️3️⃣

Gefe meenal ta koma dan tsabar kukan dataci har tana jan hancinta hawaye masu yawa da dumi sam suka ki tsayawa acikin kwayar idanunta sai zubowa bisa kan kyakyawar fuskarta sukeyi yuu kamar an kunnasu, hannunta na rawa sosai ta kara wayar a kunnenta muryanta mai cike da shessheka ta dada sauke shi can kasa kasa snn tace  "Hello, mumy.."?


Daga dayan bangaren mahaifyarta ne mai suna hajiya nadiya talba da bugu daya ta shako sautin kuka a muryan yartata hankli tashe tace

"Amina.. Amina lfya kuwa kike kuka wai meke faruwa ne naji muryanki haka? Hows the weding going hope dai ba wani matsala bace?..


Kamar jira Meenal take hajya ta gama rufe baki nan ta sake wasu sabbin hawaye masu yawan da dumi ta runtse idonta tanamai cewa wayyo Allah na mumy na shiga uku..


Hajy tace Kin shiga uku kuma?..shiru meenal tay bata amsata ba banda boyayar sheshekarta datakeyi ahankli bakajin sautin komi, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, hajya nadiyar tace Sann ta dora dacewa "toh meya faru? Wani abune ya sameki ko halisan?


Meenal na kuka a hankli tace "A'a...sann ta kuma cewa eh. Mum kaina a kulle yake nide nayi abunda ya dameni.


Da sauri cikin katseta Hajya tace menene. Wai Me kikayi?


Kuka marar sauti sosai meenal takeyi hjya na jinta ayayinda hanklinta ke dada tashi sai batace mata komi ba.


Da kyar meenal din ta iya tsagaitawa bayan dedeta nitsuwarta ta danyi shiru cikin sauke sarkafaffen ajiyar zuciya ta soma cewa "Mummy wallh wata yar matsala akasa mu, auren halisa is not holding anymore..zach yaki zuwa yace wai ya fasa aurenta wai bazai iya auren mace irinta ba.


Cike da tsananin mamaki hajya nadiya ta dafe kirji tanamai cewa..what? Meenal Me kikace?..wai wata halisar, kina nufin auren da kuka zuba milliyoyin kudi kuka shiryashi shine akafasa din?hmmmm Lallai tab di jam,toh akan wani dalili.


Hawaye fall idon  Meenal tace mummy ki tsaya kiji. Nan ta hau bata labarin yadda akayi batare da ta tsakuro mata nata kalar fargaban ba tukuna.


Hajia nagama jin bayanin ta tace toh Hmm Allah ya kyauta cikin sauke ajiyar zuciya take famar jinjinawa..


Shiru meenal tay a brain dinta tana kan tunanin yadda zata soma bullowa mahaifyarta da maganan da sukayi da zach.


Ita kuwa hajy nadia ta cika fam dan Aynzu janjan zcya da meenal kekanyi shiyake ɓata mata ranta sosai dan Bakaramin son yarta takeyi ba. Irin mummunar soyayyar nan ne takema yarta meenal wanda da bata iya kallon aibunta.


Hausawa nacewa ɗa na kowa ne amma banda wajen hajya nadiya, iyanzu kukan da meenal takeyi shine babban damuwarta cos she dont really give a shit akan matsalar kowacce yarinya. 


Ajiyar xuciya ta sauke tuna cewa inbadan son ran aminan bama da hala  bazata taba amsar halisa ta zauna gidanta dachan  harta rayu alakarsu takai haka girma ba, dan aranta gani kawai take kamar halisa is unlucky in her life, mummunar qaddarori ne kawai ke tafe da kaskantacen rayuwarta tun tana yar karama,. Wani tukikin tsaki taja acikim ranta Sai can Snn ta kuma cewa a masife "toh ke amina wai meye naki aciki ne da kiketa wann uban kukar sai kace an miki mutuwa eeehh,...

Ynxu Ciwon xuciya zaki dorawa kanki dan kawai yaron nan zach yace bazai aure halisa ba?


Meenal tace haba mummy zach fa bai kyauta ma halisa ba. On her wedding day, Is This fair?muntara mutane na alfarma mun kashe kudi mun bata lkcin mu, yanzu da wani irin ido halisa zata kallesu bare har ta samu gwarin gwaiwar gaya musu cewa zach yace ya fasa aurenta?


Karamin Tsaki hajy nadiya taja snn tace hmmm,..But Things like that are bound to happen this way meenal.

yo ai qaddararta kenan.

ni dama jikina tuntuni yabani wallh auren nan da wuyane yayu. Masu kudin nan basu fiye auren yaran da basuda asali ba..i mean, halisa's life and standard is nothing to write home about ke kanki kinsan yanayin kazantar data tashi aciki. 


She was a street girl har rawar kan karfen nan na karuwai tay a club danta ci abinci, snn ke zaki iya tantance mazan da suka taɓa kwana da itane? har ciki ma kawunta ta tay kikacemin..to wani hamshakin me kudin ne da iyayensa sukace masa jeka zaka gani zai aureta? Ku kun fiye tsawwalawa.


Baki bude Meenal ta tsaya sam takasa cewa komi saijin hajiya nadiya take datake famar rero bayanai..


Tace masu kudi suna neman mace ce mai kyaun asali koda batada kyan fuska sai kiga ta auru awajensu,wacce dai batayi rayuwa irin nasu halisa ba..kyabe baki tay, hnmmm"toh tunda wnn abu yafaru ai hakuri zakuyi ku rungumi na Annabi... kuyi masa adalci shima just imagine him bcming a presidential aspirant one day yo ai iya past din matarsa ma kadai ya isa ya jawo masa wata musibar arayuwarsa.


Meenal ta jinjina kai tare da sauke ajiyar zuciya jin yadda mum dinta take maganar babu dandanin tausayi babu tausasawa ayanayinta sam sam.


Idonta a lumshe cikin ragwabewar murya tace

"Mumy ta ina lefin halisa ya fito acikin wann lamarin..she' have never even choose this life for herself..bataso amma  kamawa dole yayi..mum kiyi tunani nima dana taso cikin gata da daula inda ace Allah yaga dama zai iya daukeku duka kamar yadda ya dauke iyayen halisa, nima kuma zan iya fadawa cikin rayuwar kazantar dayafi nata muni.


Cikin katseta da sauri a hayayyake hajya tace ke Dakata min Amina,wann maganan ya isa haka Allah ma ya tsagaita mana irin wannan mummunar qaddarar, "tuff da baqin yawu, kar inkuma jin kinyi makanki wann mummunan fata shashasha kawai!..ke Allah ya rufa miki asiri ashe kinan nan kinata neman wa kanki fitina..


Meenal tace mumy toh ai gaskiya ne. Kofa tausayi halisa bata baki ba, sai famar kushe komi kike as if her feelings is not valid a wann yanayin data tsinci kanta aciki.


Hajya nadia tace Hmm Toh tunda kince haka shikenan.. zach bai kyauta ba..amma shin kinsan dalilinsa nayin mata haka..naji kince min dake kukayi magana menene asalin dalilin dayasa yace miki ya fasa auren nasan dai da wani abu akasa ruwa ai baya tsami banza.


Meenal nataro hawayenta jikinta a sanyaye tace Mummmy, dats why am telling u is not alwys halisa's fault at all dan zach baisan komi game da rayuwarta na baya ba.


hajya tace Toh dama akan rayuwarta na bayan kenan ya fasa aurenta?


Wani Shiru Meenal' tay saida tadan sace juya baya kadan data lura da kamar hanklin shemau nakan wayarta saita sauke ajiyar zuciya, sann tace "Eh mummy akan hakan ne..amma fa mani kawai ya fada sabida dani muka yi magana irin haka dashi kwanan nan.


Hajya tace ban fahimceki ba..


Wani ajiyar zcyar meenal ta sauke snn tace mum Dama ranar ne muna dan hirar virginity a office dinsa da mukaje tare da halisan then she left us alone for some minutes inata tsokananshi akan yabi kawata ahankli, shine sai yace min shi ai bai taba aikata premarital sex ba, he is a virgin..sede ince halisa ce zata bishi a slow ..so, daga nan dai sai nafara masa hira, and i told him about halisa past life. 


Hajiya tace kamar me da me kenan kika gaya masa har haka ?


Shiru meenal tay tana dan dube dube duk tsoro yabi ya cikata dan gani take kamar hala shemau zata iya jiyota ga hjya ta matsu tanason itama taji


Da kyar ta iya budan baki tay magana kasa kasa dan saida hjya ta kasa kunne sosai kafun nan tasoma jiyota da kyau


Tace "Mum kawai de na gaya masa komi da komi ne..like..saitayi shiru alaman tanajin nauyin maganan abaknta..



Hajya tace ehn ehen inajinki meenalin mama


Dada kankance muryanta tay tace nide na faffada masa cewa tay talla tun tana karama kuma maza suka budata, kawunta ma yasha kwana da ita, kuma har yamata ciki ta xubar. Sai naga zach yaji tausayinta sosai,shine na kara gaya masa cewa ai da halisa tazo lagos club club take bi tana kwana kuma tana musu aikin goge goge dan abata na cin abinci kuma ba irin mazan da basu kwana da ita ba, cos u knw Dats how she pays her schl fees kafin nan ta dawo zama a gidanmu. I also told him dat..


Cikin katseta Hajiya ta dafe kai tace wow, Dat was soo foolish of you Amina. Gaskya baki kyauta ba..Ke Me yakaiki gaya masa haka ina ruwanki da sirrikan ta Amina? Abunda Allah ya riga ya lullube kece zaki ce sai kin bankado fili anan kam Kinyi ganganci wallhi!! Irin wann sirrin ba a gaya ma namiji sede in mugunta kikayi niyyar mata.


Ahankli Tace mum kawai nayi tunanin ai yakamata ace yasani ne. Ta turo baki gaba" Ko ba haka ba? I tot it wasnt a big deal ai..bansan zai dau abun da zafi haka ba.. tafadi maganan ba har cikin ranta ba.


Cikin sauke ajiyar zuciya mai nauyi hajiya tace Subhanllah amina kice ke dai kikayi kutunkutun kika hana yuwar auren kawarki da zach kuma nasan kina da dalilin yin mata hakan wallah sede inki boyemin.


Cike da yanayin damuwa a muryanta tace mum nide abinda ya faru ya riga ya faru ders no going back ni damuwata shinene yanzu me zanyi..am soo scared wallah, Ni Kaina duk ya kulle banason guilt yasani na gayawa halisa gaskiya ynxu zata iyacewa naci amanarta sauran kawayen ma zasu iya ganin lefina suce nice munafuka. Mumy am soo scared dan Allah ya zanyi. Ko de in je in fada musu kawai ince musu i tot it wudnt be a big a deal hala zasu fahimce ni. 


Cikin katseta da sauri hjy nadia tace hmm Amina lallai kanki na rawa..toh Ahirrrrr dinki da fadin mata, Are u really that mad? Kina tunanin zasu taɓa fahimtar ki acikin ruwan sanyi ne..this is gonna be a war girl cos u didnt just break a marrige you broke a whole beautiful relship.


Yarinyar nan halisa tun da ta fara neman nakanta bata taɓa bude zucyarta tay soyayya da kowa ba se zach din na Ke kanki nasan tsantsar soyayyar da suke yawan nunawa junansu agaban duniya na taɓa maki zuciya. Mata da hassada da kishi hmm? Tunda burinki ya cika...toh wallh Kada ki kuskura ki fada musu, shinkina hauka ne amina, to ki kame bakinki kiyi gum kamar kin binne gawa a kogi,yo kika sani ko zucya ya debeta ma ta kasheki u think u can fool anyone with ur silly excuse ko mtsww,..irin wann maganar ai tamkar wutar daji ce,inya kama bishiya daya to tabbass sauran bishiyoyin duk sai sun hadu sun kone, karda kisoma kunna wutar fitinar da bakisan inda zai tsaya ba,kinaji na ko? 


Gyada kai kawai meenal takeyi bata iya cewa komi ba sai sauke ajiyan zuciya datake faman yi jin maganar mahaifyrtan na dada bata gwarin gwiwar sanin yadda zata bullowa abun.


Shiru tyi Tanajin Hajya nakan mata magana cikin jadaddawa "Amina kada kice komi kuma kar ki aikata kome Just wait for my arrival inna dawo daga dubai zamu san ya za'ayi da wann maganan kinji auta na.


Jiki a sanyaye tace toh mumy. Nagode..harkin sa hanklina ya kwanta ure the best muaah i love u.


Murmushi hajiya ta sake najin dadi snnn tace yawwa Toh maza jeki karma suga kin jima kina waya su tuhumeki tunda bawai kin fada ma shemaun abunda kuka tattauna da zach din bane sai Kinemi wani abuna na daban ki gaya musu amma banda gaskiyar kinji .


Meenal Tace toh mumy.


Nan da nan suka datse wayar ,Meenal saida taci minti biyar cikin neman makanta nitsuwa da dedetuwar hankli kafin nan ta saka himman karasowa wajen shema'u.


Ahankli Meenal take takowa hawayen dake fuskarta sundan rage sauka sakamakon kiyasi da lissafe lissafe dake gudana a brain dinta na tunanin karyan da zatayi domin ta rufawa kanta asiri, dan saidai mum dinta ta fayyace mata  hakan snn itama ta gane cewa fadar gaskiya iyanzu bazai ficce ta ba sabida kowa acikinsu ransa a harzuke yake itakanta amarya halisa already bata cikin hayyacinta bare ta fahimce wani abu, dan haka fadin gaskiyar sam bazai haifar musu da ɗa mai ido a yanzu ba.


Tahowa take ahankli kamar bata da laka tana dan sarrafa maganganun da zata fada musu a kwakwalrta, ayayinda take daf da cimma shema'u tana daga idanuwanta sama caraf sai ga hadiza ta faso a rikice,abayanta vicky ce itama ta taho cikin sauri har kafafunta na hardewa.


Kusan dada rudewa tayi ganin dukansu sun hallara a rikice da alaman shemau har ta tura musu text ta gaya musu abunda ake ciki


Isowarsu wajen shemau yay dede da karasowar meenal din dake kkrin dedeta komi aranta cikin gaggautawa da sauri dan kar gaskiyarta yay saurin bayyana.


Hadiza na tsayawa hawaye masu zafi suka tsinko mata akan fuskrta jikinta na wani irin kyarma na bacin rai.


Cike da dauriya Vicky tacewa shemau da meenal muna bukatar bayani meye ke faruwa please what is going on girls..shema'u ban fahimce sakonki ba meyasa kikace auren nan bazai yu ba..what is goin on..


meenal talba? Shemau marafa. Both of u shud answer us now!!!


A dan hatsale hadiza tace u guys shud just say it out loud mana...i knw

He cant make it, he is london right..?i saw his location in dat email.


Vicky ce batasan komi ba jin hakan ya fito daga bakin hadiza yasa ta juyo a hujajan ta dube hadizar a tsananin mamaknce tanamai cewa "what did u say?..kikace bayama kasar ko kunnena ne ya dena jin magana dakyau


Shema'u tace yes vick..zach yana london..he dumped  halisa in the church waiting for him, while he is over der doing business... off couse.


Cikin sauri Meenal tace haba mana ya isa haka shema'u ,Karda ki gaya musu maganan nan ata wani siga dazai kara hatsala su mana. Muryan kuka ta saka, snn tace We are all in pain right now.. amma yakamata muyi amfani da hankalin mu wajen neman mafita.. we need to find a way of taking halisa out of this place...away from this messy weding nightmare dat zach created for her..


Hadiza dats soo hurt and emotional, dama tafi kowa rauni acikinsu abu dan kadan ne ke daga mata hanklinta sosai, nan ta kara fashewa da kuka mai ciwo dan wani irin tausayin halisa taji har cikn ranta yana tsagawa, atake shemau ta rungumeta sosai tana rarrashinta.


Vicky ta tsaya cak hawayenta na zubowa ta cije bakinta acikin yanayin baqin ciki silently take kuke batayi yunkurin tarewa ba.


Banda saka kanta a matsayin halisa babu abunda takeyi acikin kwakwalta dan kuwa tasan bakowane zai iya daukar irin qaddarar rayuwar halisa a zcyarsa ba.


Meenal yakamata ki gaya mana abunda bastard din can yace..shema'u ta tuhumeta.


Vicky dake tsaye waje guda bacin rai yasaka duk jikinta yadau ɓari sai yanzu ta share hawayenta snn tace

"Yes Tell us .


Nannauyr ajiyar zuciya meenal ta sauke snn tace..nide munyi magana dashi amma ni bai gaya min wani dalili na fasa auren ba. Zach just woke up and decided dat he can't be with halisa anymore...cemin yay wai yayi tunani yagane cewa halisa bata dace da rayuwarsa ba shiyasa kawai ya fasa aurenta...


"And How dare him.

Vicky ta faɗa da kakkaursar murya kuma a mugun raunane har tana missing step zata zube kasa meenal din tay saurin rikota jikinta na rawa. Tace Kajimin wani rainin hankli da rainon wayo.


Sabbin Hawaye ne suka sauka idanun vicky tay saurin sharewa taja gefe a fixge cikin bacin rai tana ziriya ahankli cos her heart is beating too fast da bacin rai sam batason ciwon asthman ta ya tashi anan.


"Wato Bata dace da rayuwarsa ba, amma sai aranar aurensu ne ya sanda hakan..Hadiza ce ta fadi hakan tanakan kkrin share hawayenta dake kin dena zubowa mata dan maganganun meenal din ya mugun zuwa mata a sama sama kamar wani almara.


Cikin kyabe baki Shema'u tace hmmm Shiyasa arayuwata bantaba yarda da namiji mai kudi kuma gentle shiru shiru me claiming perfect guy ba,cos in reality  they are the baddest, the most cruel ones..mugaye ne na inna naha..so what sort of emotional damage is this for god sake..Wallahi yakamata muyi wani abu akansa mudaukar wa halisa mummunan mataki..he cant go scot free..


Meenal tace "enough!! Iya abunda zai faru ya riga ya faru shema..girls, yanxu ba lkcin yin huci da jin haushi bane, lkcine da zamu san nayi akan halisa. Sai ta fara kuka alamar irin susan cewa itafa tausayin halisan ne kawai ya gama ragwabar mata da zcyarta sosai


Da kyar Vicky ta dedeta nitsuwarta snn tajuyo fskarta a mugun dore kamr an dauke wuta tace "ure right, hannu tasa ta share hawayenta kaf snn tace girls ya zamuyi da halisa..ga tulun mutane acikin church Did u think we shud tell halisa the truth just yet?.Ko muje mu daukota mukaita gida inyaso mu bawa mutane hakuri muce an daga auren.


shemau tace yes..lets act fast, no matter what we cant tell halisa the truth sai mun fitar da ita anan.


Tana gama rufe baki abazata sukaji muryan halisar abayansu a ragwabe tanamai cewa "what truth?..


A razane duka suka juyo kusan atare dan basuyi tsammanin zata fito nemansu har waje ba.


A gaggauce hadiza ta boye fuskarta abayan shemau ta hau share hawayenta meenal ma tay sauri duk suka goge idonsu itade halisa tanata kallonsu kamar wata zararriya


Wani irin Shurune ya dauke wajen cikin su an rasa wanda zai bude baki ya soma mata magana .


Dukknsu kallonta sukayi kowacce ta kasa motsawa itama kallon nasu ta tsayayi ayayinda take rike da jelar gown dinta idanuwanta cike da damuwa da tashin hankli hade da rudanin ganin du ahaka marar miisaltuwa...


Jikinta na rawa ta karaso wajensu tana tafiya hankli tanamai kuresu da idanu dan ta karance expression din datake gani a fuskokinsu.


Tana isowa daf ta dube idon meenal kai tsaye..

Muryanta a sanyaye tace

"Meenal, what truth?.


Shiru meenal din tay kanta na kallon kasa sam taki ta haɗe ido da halisar dan itakadai tasan irin bugawar da zuciyarta yakeyi a dede wann lkcin da guilt na sanin cewa itace sila.


A dan rude Halisa ta sake gown din nata kasa jelarsa ya bazu snn ta fara ja da baya a ragwabe kuma ahankli tanayi tana dan duban fuskokinsu duka, gani tayi cikinsu daga mai kawar da kai gefe sai me sunkuyar da nashi can kasa jikin vicky kuwa rawa jikinta yake har yanzu,wani runtse ido halisa tay dan already aranta tasan wani abu mummuna ne ya faru da ita.


cikin murya mai cike da tashin hankli tace "shiru zakumin bazaku fadamin ba?..


Shema'u tay kamar zata bude baki cikin sauri meenal ta mata alama akan tayi shiru aka bar halisa da binsu da kallo


Daga nan inda take tsaye tana hawaye ta dubi hadiza da idanunta ya kawo ruwa alaman tana cikin yanayin rauni tasan itace kawai zata iya fallasa abun cikin sauki nan ta soma rokonta tana hawaye sosai tace "Hadiza dan Girman Allah Dan darajar mahaifyarki ki gayamin meke faruwa..


Hawayen Hadiza  tuni ya sauko zirrrr,numfashi taja zatay magana vicky ta rikota tanamai ce mata no adiza. Snn ta juya tace Halisa pls calm down okay.


A masife tace NO!! "Dont tell me to calm down vicky just tell me what is going on"..ku fadamin mana,..meye haka kuke min? A rikice cikin kuka mai cike da rauni da kuma razana ta fada numfashinta na hawa sama sosai yana sauƙa dakyar.


Da wani irin sauri kuma a ragwabe meenal ta karaso wajenta ta dafo kafadunta a sigar lallashi 

Tanamai cewa "halisa zamu gaya miki..but i need you to calm down.


Kallon meenal din tay snn Tace but am calm..oh u think am not calm? Na zauna tun safe ina jiranshi da weding gown a church har kusan karfe sha biyu da rabi saura baizo ba and u still think am not calm..wani irin kwantar da hanklina da hakuri kuke son nayi. Nide Kawai ku fadamin meyene banason iskanci.


Masifa tahau musu amma da Meenal ta fara kuka sosai sai kuma taji tsoro me tsanani ya kuma lullubeta...


duk dama tana cikin halin fushi mai tsanani da zach amma tunani daya takeyi aranta gamedashi..gani take kamar wani abune ya sameshi na hatsari ko mutuwa ko kuma wata yar matsalace ya tsaresa a wani waje.


Kallon meenal ta dingayi tanata kuka batasan da cewa guilty consience ne kawai yake kwaranya acikin zuciyarta ba..


Tana daga idanunta sama sai kuma taga sauran kawayen nata suma sunakan share nasu hawayen jikin su duk yay sanyi. Wani irin bufff bufff taji zuciyarta na harbawa kamr this minute zai dauke cakk 


akan hannun vicky dake rawa sosai idanunta ya kuma sauka take taji Wani sanyi ya lullumeta ta juyo a kangare ta dube meenal dake daf da ita tana kuka, muryanta a kakkarye tace mmmm mee...meee..menal, mmmmmmmmeenal

"Is zach dead??? Ya mutu ne..did he die??tun meenal bata amsa ba ta fasa ihu cikin birkicewa da zaucewar hankali nan ta cakumota tana ta  jijjigata a rikice tanacewa please tell me mutuwa yay? Meenal bata iya cewa komi ba sai kukan da takeyi duk tsoro ya cikata ta ciki, Da sauri sauran kawayen sukazo suka rirrikesu.


Lkcin kowa na cikin wani yanayin da basu iya danne baqincikinsu ba


Halisa tana shirin yankewa ta fadi kasa vicky ta rikota dan rikice musutayi gaba daya zata suma duk tunaninta mutuwa zach yay kawai shiyasa ake boye mata


Ganin haka yasa Hadiza tasa kuka mai dan karfi acikin rudani ta dubesu duka snn tace in babu wanda zai fada mata nide zan gaya mata ta huta da wann azaban


Da sauri Meenal ta dago kai "tace a'a hadiza..dani mukayi magana da zach dan haka zaifi dacewa halisa taji komi daga bakina.


Jin hakan ya dawo da halisa hayyacinta kadan nan ta miƙe tsaye ajikin vicky da shemau dasu suka rirriketa dan babu karfi ajikinta ko kadan.


Bakinta na rawa tace ohj thank god meenal kin yi magana da zach? Where is he..what happen.


Meenal din ce ta karaso daf kusa da ita snn ta riko hannunta suna masu kallon juna..


kame kame goma da ashirin sai da tayi acikin zuciyarta dan kallon kwayar idanunta da halisa takeyi gwanin ban tausayo yasaka taji aranta kamar bata kyauta mata ba.


bayan ta gamsar da ita cewa zach na raye nan tafara mata bayanin abunda ya wakana a  wayarsu da sukayi dashi.


Sede nan ma Iya abunda ta gayawa sauran kawayen shine ta kuma gayawa halisa cewa zach yace yay tunani yaga bazai iya auren mace irinta ba.


Wayann kalmomi da meenal' tace mata zach ya furta saida halisa ta memetashi a brain dinta bila adadin tanata neman yuwar dalilinsu da kuma mafarinsu dan tasan dai zach baisanta da wani mugun hali ba, iyaka ace yasanta ne a matsayin mace mai kamun kai mai neman nakanta mai kuma kudin kanta, sann tana da kyau tana da aji tana da hali ta iya hulda da jama'a sosai, yo wani namiji ne zaice bazai iya auren mace irinta ba? Wann karya, Lefin me tay masa shine asalin amsar datake nema ayanxu.


Rudani da baqin ciki mai tsanani atake suka lullubeta.


Hatta Duniyar daukewa cak tay wa halisa ta tsaya cak akan kafafunta tanata kallon bakin meenal dake fidda mata bayanai mafi muni da saka karsashi, tuni kwakwarlta yadenajin motsin komi harna tsawon mintina goma dan ji take kamar gangan jikinta yana yawo a iska a can sama dan kwata kwata kurwanta baya tare da gangan jikinta a wannn lkcin.


Baqin ciki mai cike da tukiki da karsashi shiyake tsagata tun daga tsakar kanta har ixuwa jijiyar jininta yanamai mata yawo a sassan jiki yana kuma mamayar kowani lungu da saƙo na jikinta da kwakwalta.


Duk sai ta rasa awani duniya take dan jira take ace mata mafarki takeyi


Ahnkli Ta fixge jikin ta ajikin kowa ta tsaya a tsakiyarsu cak kamar an dasata..jiri da duhu take suka rufeta.


Tsabar yadda xuciyarta da kwaakwalta yake  tafasa da baqin ciki bata iya yin komi ba saida ta dau minti goma masu  kyau in shock dan ko motsawa wani sassan jiikinta baya iyayi.


Iyakar Munanan qaddarorin da suka gudana a Rayuwar ta gaba daya sune suka hau mata ziriya acikin kwayar idanunta da kwalrta tana kallonsu daya bayan daya kamar wani film.


Acikin zuciyarta dake bugawa kamar zai fatso waje take cewa "Laifina na ne.. its all my fault..laifi na ne..dan kuwa babu wani abu na farinciki daya ke raɓata saina baqin ciki,i knw that nothing good will ever happen to me in this life amma haka na rufe idona nabiyewa zuciyata na amshi soyayyar zach inata tunanin samun sauki da rayuwata mai dadi awajenshi.


Nabashi dukan yardata da zuciyata..na so shi so na haqiqa wanda babu na biyunshi a duniyar soyayya,dan  tun bayan rasuwar mahaifina da mahaifyata ban karayi wa wani dan adam irin wannan soyayyar ba.


Maybe i am born to suffer and dwell in pain


Maybe ubangijin daya halicceni baya kaunata.


Datatuna irin baqar azabar datasha da rayuwa bayan rasuwar iyayenta atake taji Wani irin gulluton abu mai nauyi ya shaketa a kirjinta tanajin tsitttt tsittt kamar jijiyon zuciyan zasu tsinki haka taji sunata tsananin zafi sun kuma kameta taciki.


Lumshe idanunta tay sosaiiii jin kawayenta na kuka agafenta sosai


Sai kuma tausayinsu ya kamata, gani take kamar yauma itace silar digawa ma zuciyoyinsu baqin ciki da tashin hankli.


A tunaninta duk wanda ya rabeta dolene yay baqin ciki sabida haka Allah ya halicce da munanan qaddarori.


Cike da dauriya Juyowa tay tana kallonsu ganin mamaki dake kwaranya akan fuskansu ganin halisa bata yanki jiki ta fadi kasa ko ta suma musu ba.


Hawayenta masu sanyi suna sauka muryanta a sanyaye sosai ahankli tace  musu"its Okay, ni na dauka wani abune ya sameshi ashe ashe wai

Zach Ya duba ne yagani cewa ban dace dashi ba, ragwabben murmushi ne ya kufce mata bazata, gyada kanta tayi cikin tukikin rudani snn tace..ders no big deal. Lets just...call dis weding off ...kowa yaje gida ya huta.


Kawayen nata Zasuyi magana ta hade ranta cikin dakatar dasu in a subconsious mind wanda kusan kowa awajen yasan bata cikin hayyacinta,hawayen ma duk ta gogeshi a fixge cikin zafin nama tace shema,vicky, hadiza, and meenal, girls... ku make sure kun rabawa kowa souveniers and all the food we got kafin mubar nan wajen. 


A raunane hadiza tace akan me? Halisa why r u doing this to urself,..take a break. ure in pain...


Ranta a bace yasa bata tsaya taji karshen zancen hadizar ba ta juyo tace and so what if am in pain dijaa..am use to it..pain is part of my life now.

Inde har kuna tare da ni dari bisa dari toh kuyi abunda nace muku kawai mubar nan wajen. This respectable pppl waited for hours for my weding to take place bai kamata ace mubarsu su tafi haka empty handed da taqaici ba..


Vicky tace and what about u ?


Tace im fine, zan jiraku anan..i just need my space right now pls u guys shud understand me.


Shiru sukayi sai can snn kowa tahau share hawayenta hadiza tace lets go guys. 


Vicky da shemau sun taso meenal tace ita zata zauna tare da halisa amma haka firr halusa taki ta amince mata hakanan ta hakura ta bisu suka kyaleta ita kadai awajen 


"U think she is going to be okay ayadda muka kyaleta ita dayan nan..?


Hadiza ce tay wann tambayar 


Meenal tace ni nasan halisa..mace ce jaruma mai karfin zuciya da kuma hakuri.


Tunda kikaga ta umarce mu muyi hakan bana tantama she is going to control her emotions.


Gyada kai hadiza tay sai basu kara cewa junansu komi suka wuce direct stalls din souvernier da wajen harhada abincin


Within 30 min shemau da hadiza suka saka aka yi good packaging na kayattaun abincin dale wajen aka zuzzba su a hadadun a take aways.


Meenal da vicky kuwa tuni suka gama da wajen masu sourvenir jakuna da tsarabar biki masu tsada aciki, dake suna da list din iyakar bakin da suka gayyata abun bai wahalar da su koya ci musu lokci ba, sai yan dedeku wanda a radin kansu suka zo wajen duk suma an providing musu nasu tak aways din


Bayan an kammala komi aka baza ma'aikata sula soma rabo mutane nata mamaki ganin cewa ba a daura aure ba amma ana raba musu kayayyakin tsarabar biki.


Ana daf da karewa meenal ta saci jiki batare da sanin kowa ba ta koma domin duba amarya halisa..


Tana ficewa acikin church acikin sauri da sassarafa ta karaso baya inda halisar take..kanta ne ya sara ganinta a yanaynin da bata taaɓa ganinta aciki ba.


Tsantsar Soyayyar datakeyi ma zach a zuciyarta shine yake neman ya zautar mata da kwakwalwa aynzu

Sai huhh huhh take tana furzan iska da karfi sosai alaman iskan ma yamata kadan.


Tun bayan tafiyarsu take ta kakalo tunanin tana lisafin abunda ta masa a rayuwa da zai saka mata da haka bayan soyayya mai tsafta da dadi dake wanzuwa a tsakaninsu.


A ragwabe ta kasance  kafafuwar duk sunyi sanyi sunamasu kasa iya daukarta,zama tay daɓas a kasa ayayin da ta cusa kanta tsakanin cinyoyinta hawayena zubowa daga cikin kwayar idanunta masu tsananin zafi da ciwo marar misaltawa ..


mental depression da anxiety yasaka ta kame jikinta kamar wacce take kkrin zaucewa 


Har meenal ta karaso wajen kallonta kawai takeyi, ahankli ta rusuna daf da ita dan da alaman ma bataji motsin isowarta ba.



Saukr Hannun meenal din kawai taji ta dago kai suka hade ido yanayinta sodai ya razana meenal din muryanta a ragwabe  tace "Halisa..


Tsareta tay  da wani irin raunatattece ragwabben murmushi tare da cewa "har kun gama ne?


Meenal bata iya cewa komi ba ta gyada mata kai..


Hannu ta mika mata alaman ta dagota sama

Babu musu ta aikata hakan suka miƙe tsaye


Jiri sosai ke dawainiya da ita,duhu duhu kawai take gani agabanta amma haka ta daure tace meenal lets go the church.


Meenal tace mezakiyi a church halisa muje gida mana halisa.


Hawayenta  ne

suka sauko tace a'a..

Sanin kanki ne bana tsoron fuskartar wani qalubale ma rayuwata koda kuwa baqin ciki ne ya cikeshi. Sabida ni mutanen nan sukazo dan haka abunda ya dace kawai zan aikata.


Meke nan zaki aikata halisa..did u realise dat akwai yan jarida da bloggers awajen.


Halisa tace and so what meenal..trust me

Am not going to do anything stupid..


Meeenal batace komi ba ta rrikota suka taho ahankli har izuwa cikin church din.


Already lkcin waje ya kaure da cece kuce jamaa ana ta tambaye tambaye ana neman amsa.


Tsayawa halisa tay alan alter tanata kallonsu ayayin da ta hanaa kowa matsowa kusa da ita.


Nan da nan Attention din kowa ya koma kanta ganin yanayinta da ya gaza boye halin tashin hankli da baqin ciki datake cikii


Nannauyar ajiyar zciiya ta sauke,  snn tay murmushi tana kallon dumbin mutanem da suka dominta, da kalaman Godiya masu tausasa zuciya ta soma baza takaitaccen jawabinta.


Daga bisani ta dan babbasu hakurin zaman jira data sakasu sukayi, bayan nan cikin dauriya sosai ta hau sanar dasu in formal and calming manner ba araunace ba, "cewa tayi auren ta bazai yuwa ayau ba batare da ta furta musu dalili ba, ta kare da cewa tanay wa kowa fatar ya koma gidansa lfiya.


Tunda ta kammala furta hakan church din ya guntse da wani irin surutu na fitar haankli kowa na neman amsa 


"why why meya faru whats going on.


Wani irin kallon juna Uncle dinta kawu karami da matarsa mama G sukayi wa junansu dan dama a hatsale suke da dan tsarabar da aka basu bayan sunga manyan mutane an basu mai yawa mai tsoka sukuwa da ba a gayyata ambasu wasu abubuwa na yaku bayi kuma aganinsu sunfi karfin abasu iya wannan.


Kawu karami ne ya soma mikewa tsaye yana zage zage da bakai ba gindi yana wani huci yana cewa aikin banza aikin wofi..duk baqin cikinsa da basu hadu da ango sun aiwatar da cikar burinsu na samun kudi da masauki awajensa ba.


Sanin cewa yan jarida zasu mata cha yasaka meenal da hadiza suka zagayeta suna bata cikakken tsaro ayayinda shemau da vicky suka kirawo attention na security aka soma matching din jama'a izuwa waje.


Kusan acikin rudani kowa ya bar harabar church din, wasu na harsashen matsala aka samu daga ango,wasu tausayin halisan kawai sukeji aransu, wasu kuma takaici ne ya lullubesu na bata lkcin su anan da sukayi.


Bakaramin drama akayi da media ba sede aka kusan watsa musu tear gas snn aka samu kwancyar hnkli ahakan ma sun nanike a gate suna neman amsar tambayonsu abakin halisa.


Within 10 min church ya zama daga su saisu kafin kace wani abu halisa ta ragwabe akasar alter dan ji tay kamar duk wani karfi daya rage mata a gangan jikinta ya gushe, is like yanzu ne ma datay hakan takejin mugun radadin zafin rasa zach da kuma tozarcin daya faru da ita yana me mamayeta sosai.


A hannu a hannu kawayenta suka ririkota domin sukaita mota.


Meenal da vcky ne suka shiga motar tare dabita suna danne mata kirjinta sabida hauhwan da nunfashinta yakeyi ayayin da su hadiza suka hau binsu abaya 


Ana bude musu gate din church din mutane suka bi bayan motocin su yuuuu kallo da kuma maganganu.


Lokcin halisa batasan ina hanklinta yake bama.


Hadadden Gidan hadiza dake kan hanyar Victoria Arobieke street no 305  a anguwar lekki suka wuce da ita direct dan nan yafi tsatsauran security dan ita minister of petroleum resources take aura.


Duk da haka suna isa kofar gate wasu jounalist din har sun iso suna neman tada hayaniya,tun ba abude musu gate ba suka wawuso kansu da tambayoyi kala kala game da rushewar auren halisa,abayan su kawu karami ne da matarsa ta gama zugashi akan sam bai isa suyi biyu babu ba.


Sun kashe kudin motarsu tundaga benue sunzo amma ba aure babu cikar burinsu borance masa tay snn tace masa sede suzo su amshi salalan kudadensu da sukayi asararshi awajen zuwa auren halisa inba haka ba seta kashe shi dan itama bashukan mutane taciyo dan suzo.


Bakaramin Tsoron mamam G kawu karami yakeji ba,tun daga bakin gate din gidan hadizar security sukayi ca akan yan jarida.


anata kkrin bude musu gate su shige ciki kenan saiga kawu karami ya taho da mugum gudu kamar wani mahaukaci haryana tumbul yanata ihu yana cewa wallahi ba'a isa ba. Uba nake awajen halisa ba a isa arainani ba kee Halisa keee halisa.


Da yarensu na idoma ya soma ce mata ta sauka kasa ta same shi suyi magana tun kafun nan ya soma tona mata asiri.


Ya memeta hakan yafi sau biyar kuma da ihu yakeyi yan jarida kuwa sai daukarsa sukeyi


Halisa Tana layi amma ahaka ta tsinkayo mummunan Muryansa ahankli ta mike ajikinsu meenal tana jin jiri jiri muryanta asanyaye tace musu abarsa ya karaso tanason taji meke tafe dashi..


Hakan yasaka duka kawayen sukayi parking motocinsu abakin gate dan su tsaya mata har halisar ta sauko daga cikin motar a hankli


Sakeshi akayi ya taho yana wani huchi yana fiffixgewa.


Cikin rada mata a kunne Meenal tace halisa pls dont speak da karfi kuyi maganan ma kawai ayarenku kinga media suna daukarku.


Gyada mata kai halisa tay ta tsaya kafin nan kawu karamin ya isota cikin bunƙasa yana wani fadi yana hura hanci kamar bijimin kauye.

Atayani sharing izuwa grps please dats all am asking👏🏻


To join my postin grp caht me 08060712446

No comments