Breaking News

Cheaters Club 5

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin Æ™arfe...)_ 



#ROMANCE

#FICTION


#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER


BY

 _SURAYYAHMS_

 _08060712446_



⏯️5️⃣


Jita jita da Hayaniya akan labarin rugujewar auren halisa sai dada sanyi yakeyi a media saboda babu wani sabon abu dazai assashi domin kuwa tsananin tsarone da takunkumi kawayenta suka kakama atakota ina wanda yasaka kusan kowani tantirin blogger Da É—an jarida yake tsoron shigewa trap dinsu.


Bayan kwana biyu kacal da faruwar komi iyakarsu din ne suke mamaye aganganta cikin bata kulawa duk da ma bata farka ba, bayansu sai kuma uztaz dake kwana a asibitin a daf abakin kofar dakin da halisa take kwance yanamai gadinta shima,a tare da security police men guda biyu da aka kawo musu  masu basu tsaro wanda har sun fara sabawa da uztas din sosai.


Baqin ciki da takaicin zach haryau bai kaurace a zuciyan kawayen nan ba,shema'u marafa data dau mugun zafi sai zuga sauran kawayen takeyi akan su daukar wa halisa fansa akan zach koda shima zai dandana yaji abunda halisa taji amma haka meenal taki sam ta dinga kawo musu tauhidi dan kawai bata son garin daukar fansa aje asirinta ya tonu.


Duk sanda suka tada maganar itace zata nuna masu tafi kowacce cikin su damuwa da rayuwar halisa. 


A kalamanta takanyi amfani da rauni wajen cusa musu tunanin cewa halisar yanzu tana bukatar samun sauki da kwanciyar hankli ne ba daukar fansa ba.


Shema'u kuwa gani take kamar insuka bar zach ahakan ai tamkar yaci dasune abanza, snn su kansu basuyi wa halisar halaccci ba, hadiza da vicky suma sun karfafa wann lafuzan abakinsu amma haka fir meenal ta tubure tace musu hakan ba dede bane kawai abarsa da ALLAH a rife maganan sabida lfya da kuma kwanciyar hanklin halisa.


Hakan ya jawo kowa yake dan shan qamshi da ita,tun bayan data kushe lamarin daukar fansa wa halisa sauran kawayen sukayi sanyi suka dena yawan kula hirarta sosai aganinsu sunada kudi me dumbin yawa da kuma ikon da zasu iya yin hakan acikin sauki sann abun kunyane agaresu duka ace basu tsayawa halisa wajen yaqi da zaluncin da zach yay mata ba aduk irin shakuwansun nan. daga haka suka zamto saidai suyi magana daddaya da meenal amma badai su sake mata fuska sosai ba.


A kwana na ukun ake tsammanin halisa zata farka kamar yadda likita yace musu dan haka yaune kowaccensu ta wuce gidanta domin samun karamin hutu da kuma dedetuwar hanklin  fuskartar halisar agobe.


Kusan dolensu ne su zamto masu kara mata karfin gwiwa a shawarce hadiza tace musu karda kowacce acikinsu tazo da baqinciki ko ta nuna rauninta da tausayinta agaban halisa inta farfado inba haka ba bazasu iya fizgeta acikin halin deprssion datake ciki ba.


Sai can Wajajen karfe hudu na yamma snn suka fito izuwa harabar asibitin dayaji wani irin greeny soft landscaping da kuma adon fulawowi yay kyau sosai.


Hanklin mutane atake ya koma kansu babu wani halitta dake harabar da bai juyo ya zuba musu idanu ba.


Gasu da cikakken dirin kuguna ga kuma manyan nonowa wanda sukaji gyara,fatar jikinsu yana sheqi yawani cika fam fam Kana ganinsu dai kaga irin matan nan masu son gyara jikinsu, matane kalar hutu irinsu sai wane da wane masu cin duniyarsu da yar tsinke.


Atare dukkansu suke takowa gwanin ban sha'awa takunsu me cikeda Aji da salona sassnyar kamiya, vicky ta sake albarkatun gashin kanta na asali daya wani zubo mata yabi kan  kafadarta sauran suka kwanta har gadon bayan ta tana tafiya tana dan yarfashi da hannu a fakaice.


Dumbin mutanen dake harabar asibitin sai satar kallonsu suke wasu har na cin karo da juna, atare suka nufi inda tsadaddun motocin su na manyan jeepa jepai sukenan a parke kowacce ta shiga nata personal driverta ya hau tukata izuwa gida.


Adede marabar hanyarsu kowace acikinsu ta doshi anguwar da mansion dinta yake..


Nan hadixa meitama ta wuce hamshakin gidan da mijinta ya gina mata a  no:305 Victoria Arobieke street a anguwr lekki  gidan tamkar aljannar duniya haka yake an narka nera wajen kerashi da kayan kyale kyale saidai cike yake da duhu da baqin ciki da takaici da rauni musammn daya kasance kamar ita daya take rayuwanta acikinshi.


hadiza tana cikin wani irin narkakken daula mai lullube da kewa da tashin hankli na rashin samun gamsuwar zaman aure daga wajen mijinta Alhaj Yusuf Kyari.


mijinta babban ministan man fetur ne na kasa sam baida lkcin kansa ma bare na matarsa arayuwa,dan sai hadiza taci tsawon wata daya ko biyu koma fiye da hakan agidan itakadai, daga ita sai dumbin masu aikinta batare data hade ido da mijinta ba tsabar shige da fice da harkan siyasa daya saka agaba.


At age of 26 already hadiza har ta kamu da cutar hawan jini da ciwon damuwa, musammn da bata samun cikakken kulawar mijinta sosai akanta, shiyasa abu kadan na tashin hankli inyazo mata zakaga ta rude sosai tana kuka fiyeda kowa sabida wann rauni daya cikke fadar zuciyarta, gashi tanada wani irin tsananin kishi, snn a duniya babu abunda hadiza ta mugun tsana kamar kalmar kishiya.



Daga dayan bangaren Vicky ta wuce nata gidan mijin dake cikin anguwar Oba akinjobo Avenue ikeja wato asalin cikin garin lagos. Dake vicky din sananniyar senior lecturer of economics ce a hadadden exclusive private university din nan wato pan Athlantic university dake anguwar lekki tayi karatu sosai shiyasa tafisu duka a shekaru cos she is curently a 33 years old lady .


Ita yar asalin garin edo ce, tana jin yaren yarbanci snn tanajin yarensu na edo state din sosai, Ta auri mijinta dan oyo state, cikakken bayarbe ne dake da alak da historical obaseki kingdom of edo amma mahaifyarsa inyamurace cibiyar Anambra state irin jan inyamurai din nan ne masu kalar fatarsu so fresh and yellowish  a kuma murmure dan haka danta ya fito farisol dashi kyakkwa sosai na fitan hankali. Wanda Tsabar Kyan sa da iya nuna bajintarsa wajen saka sutura da hawa motoci nagani na faÉ—a dayake tukawa agari yasaka akecemai prince of all time.


Cikakken sunanshi shine "femi falana". Amma duniya da masoyansa sunfi cemai "prince femi falana". Tsabar Kyaunsa da ajinsa yasaka yake da ruwan farijinin mutane dan haka yana yawan yin harkansa ne  big and rich international companies da kuma manya manyan kusosin kasa bana wasa ba.


 Irin manya manyan multi million nera contract na alfarma dayake samu a hannun yan siyasan lagos har saiya baka makurar mamaki saika rasa ta ina yake cin karo da irin wann sa'ar arayuwan shi. Ya iya kashe kudi ne kamar baisan zafinsu ba.


shiyasa Daya tashi yin aure yaje ta can edo state inda ake masa ikirarin sunfi kowanne kabila a nigeria mata masu fasalin kyau da albarkattun diri na gani na fada, anan ma saida ya durje sann ya zakwalo matarsa wato victoria williams baltimore Sabida aganinsa itace tay daidai da ta zamo matarsa a duniya sabida ilimi kyau aji da sauran qualities dinta da ya tabbata kowanne É—a namiji zaiso ace ya samu irinsa ajikin macen daya aura.


Liver pool estate apapa anan shema'u marafa take da zama, mahaifinta Alhaj marafa tsohon ministan Aviation ne mahaifyarta kuma hajya hajara retired chief judge ce a adamawa state dan nan ne asalin garinsu dake su fulani ne. Karatu da aure ya kawosu zama a garin lagos, shemau bada wuri tay aure ba saida takai age of 30 sabida ta riga da ta rantse cewa itadai bazata aure talaka ba sai hamshakin me kudi.


Shekara biyu kenan da aurenta, tana auren wani shahararren building contractor irin babban civil engineer din nan ne dayay karatunsa a china ya fito da first class, babu lefi suma sun tara millions of nera snn suna rayuwarsu ne cikin arxiki da wadata sosai duk dama shema'u wani bin takan kalli matsayinsa dana sauran hamshakan mazajen kawayenta duk sai taji aranta ta rainashi musammn inta dubi irin duniyar daular da hadiza take zaune aciki.


Shikuwa mijin nata mai suna alhaj engr mahmud Bello a kullum kkrin sakata a aljannar duniya yakeyi da kulawarsa da soyayyarsa dan bakaramin masifar sonta yakeyi aransa ba.


Iya wann makahuwar soyayyar dayake nuna mata shine yasaka haryau shema'u bata fito fili ta asalin nunamai cewa ta raina arzikinsa ba, dan komin tsadar abu a duniyan nan inta nema awajen sa bata rasashi godewa Allah ne kawai bata iyayi aranta..


 itade arayuwa kullum ciwon zucyarta nagakan rayuwar hadiza ce, gani take kamar rayuwa cikin narkakken daula data gama tsarawa kanta shine ayanxu hadiza ta sameshi a memekonta.



Hakan yasaka shema'u marafa tafi kowa raÉ“uwa da kuma kusantar hadiza  fiye da kowa acikin sauran kawayen,irin shakuwa da Amanar dake tsakaninsu kamr na meenal da halisa ce 

Izuwa ynxu shemau tasan dukkan wani sirri da matsalan aure dake tafe da rayuwar auren Adiza dan sun shaku da juna bana wasa ba.



"A nan Herbert marculay way dake anguwar mainland na lagos state Hadadden Gidan Amina Ali talba wato meenal talba yake.


A first street kyafaffen gidan nata yake, daura da Gidan Wata shahararriyr fashion Celebrity ana ace mata jasmine tacha,ita model ce na kayayyakin sakawa ajiki,both cikin kasa da waje. dan haka ne ma suka san juna da Halisa mansa sosai, dake dacan sana'ar da halisar tafarayi kenan bayan ta kammala karatunta na jamia da zimman saita samu wasu yan kudade snn tafara neman aiki dan tanada gudun kaskanci da walankaci.


Halisa mansa tana fara modeling kuwa Allah ya saka mata albarka aciki, modelling shine silar dayasaka halisa tasamu daukaka da shahara da kuma suna kafin ta fito ta gina kamfanin kanta tana handling busineses dinta batare da kowa ya rainata ba..halisa tayi huzzling da fadi tashi arayuwa sosai,tay aiki kala kala har Allah yazo ya bata arziki mai yawa da temakon saurayin ta zach. 


Seda Halisa tay kudin kanta sann ta siya ma kantan wani white  luxurious mansion a anguwar masu kudin gaske da bakowa yake samun kasancewa ciki ba wato victoria island.

tana rayuwarta ne acikin makeken gidan nata na nan a Akin Adesola street dake anguwar victoria island din tare da uztaz da sauran security men dinta da basu fi su biyu  ba dan bata debe tarukucen mutane  agidan nata ba.




Ata dayan bangaren kuwa Wannan gida na meenal talba ya shahara ne sabida tsantsar kyaunsa da yadda aka kawata gaban sa da shuke shuken fulawowi masu ratsa hasken idanu,sai kuma uban tashen kima da mutunci da mijinta Dr Alhaj khaleel Abubukar yake dashi. He is a 35yr old millonaire and a medical Doctor. Vibrant, Young and handsome gashi sam baison hayaniya arayuwarshi. Shidin cikakken dan garin maiduguri ne yaren kanuri. 



A jikin babban whitish gate din shiga cikin gidan nasu aka manna silver bell plate mai bala'in dauke ido anrubuta 4033 residence.


Yadda tawaje yake a kawace da shuke shuke hakama cikin gidan yake koina an tsarasa ne cikin tsafta da kwarewa dan haka mikakkiyar hanya guda daya ne zai kaika har cikin harabar gidan dake dauke da wata wadatacceyiyar parking space da aka jera kala kalan motoci na zamani.


Asalin main building din yana tsaye cur a tsakiya ne, gidan akwai filli sosai dan zaka iya zagayeshi gabaki daya hartacan bayansa batare da kakai bangon sa ba,sai ya kasance filin daketa bayan gidan yafi na gaban gidan yawa alaman su mutane ne da ke bukatar sirri a personal life dinsu.


Dik wani kele kelen Swimming pools da karamin relaxation outdoor palors da main garage da Duk Wani abu na shakatawarsu Duk anan abaya suka zuba bata gaban gidan ba..


Cikin gidan kuwa bangare hudu kacal yake dashi.


Shashe na farko na dauke da 2 rooms and a big palor masu kyau fadi da kuma yelwa.


anan shashin farko Meenal talba take da zama, Dayan bangaren shima iri dayane da nata Sedei mijinta Dr khaleel ne ke zama aciki kowa dai acikin su na da personal space nasa da room dinsa, dan meenal talba din wata iriyar murdaddiyar mace ce agidanta sam bata taɓa amincewa wai suyi sharing room da mijinta ba.


sai sauran rooms guda biyu din da suka rage ake barsu kamar quest rooms dayan room din anyishi tsarin dakin mai aiki ne amma mjinta yaki sam akawo mata me aikin sabida yasan tana da mummnan zargi aranta sosai. 


Dayan room din kuma anyishi ne a design din dakin bacci da falo mai kyau musammn dan in baqo na jini ne ko na kusa da su sosai yazo.



Main palon su an kerasa ne da set din kujeru uku guda shida bakwai given a total of 18 luxurious chairs, bangare guda na wasu mahaukatan milk colour turkish royal chairs ne masu golden crown,dayan bangaren kuma wasu mahaukatan cozy lush sofas ne wanda aka kera design dinsu da silk nd velvet sai Italian sofas masu kalar brizzle brown throw pillows.


kujerun nasu sunyi matukar kawata gidan sabida da bold colours aka tsarasu, komi na cikin gidan tsaddade ne me daraja,wani irin sanyi mai dadi dake fitowa daga airmores din falon wanda shine ya kame jikin bangon falon ya sakamai yanayi me kwance gajiya sosai ajikin dan adam.


Meenal talɓa ce ta siya gidan gabaki dayansa da kudinta dan gidan da halisa ta siya a victoria island ya mugun tsaya mata arai,.tay hakan ne danta kwaco kanta daga boyayyar kishin kawarta halisa dataji ya kamata na irin daukakar datake cin karo dashi, tunda suka taso aranta sam batay tsammanin har halisa zata miƙe ta zamo cikakkeyr mace me sa'a a duniya ba, Duk dama siyan gidan datayin shiyayi silar da haryau surukunanta suke samun matsala da ita.


Hasalima a dangin mijinta babu wanda yake zuwa gidan ko ya mata magana hatta iyayenshi.


Matsalar ya soma ne ayayin da suke shirye shiryen aurensu da mijinta Dr khaleel, wann shahararren gidan nasu ya zaɓa ne zai siya da kudinshi domin ya sakata aciki, sede girman kai, hassada da son nuna isa yasaka meenal talba taje ta rigashi siyen gidan at a double price domin kawai cikar burinta da kuma son asaka gidan nasu a sunanta bana mijinta ba.


Meenal tana wani irin jiji dakanta tana kuma baza alfahari sosai da dumbin dukiyarta na gado hadi da cewa mahaifiyarta ta tarbiyantar da ita ne awani siga na sakalci da nuna mata ita watace a duniyan nan.


Meenal ta taso ne acikin narkakken daula dan haka tarbiya da iya girmama dan adam yay karanci a kwakwlwarta, arayuwarta ita kanta kawai tasani bata son wani mutum yay wani abu arayuwarsa face saida amincewarta.


She is a very controling lady, And an Emotional blackmailer. Meenal  Kwararriyar Macijiyar sari ka noke ce, Zata iya tsula maka mugunta abayan idonka amma sai tazo gabanka tayi maka kuka ta nuna a duniyar Allah nan tana dare dakai dari bisa dari.


Itade muddin rayuwanka bai tsaya a iya matsayin data ajeka ba toh tabbas sai tasan hanyar da zatayi ta rabaka da Abun da bataso aranta din.


Tanada wani irin boyayyar mugun hali najin cewa duk wanda yake tare da ita dolene yakasance a kasan ta karde a fita da wani abu sann kowama yay rayuwarsa akan bisa tsarinta ba akan nashi ba.


Duk wani abun farinciki ko daukaka idan ya sameka inhar abun bai gamsheta ba toh komin shakuwarrku saitay kkri ta ruguza abun a boye. Snn haryau bbu wanda ya fahimci wann hali nata sabida yadda ta mugun kwarancewa a wajen saka fuska biyu، iyakar mahaifyarta datake dora ta akan komi itake ke lura da wann mugun halin nata.


Gidan da suke ciki da mijinta a yanzu haka nata ne, koda khaleel ya nuna bacin ransa lkcin dataje ta siye gidan sai tanuna mishi tsabar sonshi datakeyine yasa ta siya musu amma bada wani manufa ba, iyayen mijin nata kuwa sun ji baqin cikin hakan da tayi dan mahaifiyarsa ta riga ta fahimce kamr meenal din so take ta zamo itace me controlling din gidan khaleel amma bashi ba.


Anyi tashin hankli sosai kafin aurensu, da chan ma kamar za'a fasa auren amma abune da Allah ya qaddara.


Haka iyayensa sukayi hakuri suka amshe karereyin ta na cewa so ne ya jawo ta siye gidan dansu zauna aciki..


Sedai ba awani jima da yin aurensun ba Doc khaleel ya fahimce komi daga cikin munanan halayyar meenal talba. 

Domin kuwa karamin sabani in ya shiga tsakaninsu haka zata bushe idonta ta soma masa gori tanamai cewa in bazai bi abunda take so ba ya fita mata agida ai bada kudinshi ta siya ba. Tay masa munanan gori irin haka a farkon aurensu yafi sau a kirga.


Intaga yay fushi zai fice sai kuma sauya kalar tausayi harta kame kafafunshi tayi ta kukan fitan rai tana wani irin rikitaccen birgima akasa tanamai bashi hakuri tana cewa sharrin shedan ne.


Haka Doc khaleel  yayita fama da ita musmmn a farko farkon aurensu har abun yazo yabi jikinshi ya soma danne zuciyarsa akanta yana hakuri da ita sosai.


Sosai ya fahimce cewa Baida cikakken iko akan matarsa meenal iyakar abunda tayi niyya shi takeyi agidan bata damu da hakkinshi na aure ko wasu abubuwan da yake so aransa ba.


Iya abunda ke cusa mai tausayi aransa shine sanin cewa meenal tana mutuwar sonshi aranta bana wasa ba, inkomai zai kasance masa karya a duniya amma son da meenal take masa shikansa yasan na gaskiya ne, duk sanda yace su rabu koda a wasu ne to babu shakka abubuwa mumunana ne yake biyowa baya. Sau tarin yawa yaso ya rabu da ita din  tunma kafin aurensu amma meenal intaji hakaan rikicewa takeyi, takaiga hatta poison saida tasha dan ta mutu akansa. Tabbas Zata iyayin komi domin mijinta amma saukar da kai da biyayya ne kawai bazata taÉ“a iya mashi ba.



*********

Tun barinsu asibiti meenal take juya tunani dayawa aranta, 4:30pm dede driver ya iso da ita bakin gate ya danna horn mai gadi ya taho a guje yana kkrin budewa, dagata glass din windon motar ta hango motar mijinta Dr khaleel atake fuskarta ya sauya tahau yamtsusahi acan kasar wuyarta taja wani irin takurarren tsaki.


"Barka da zuwa hajiya

Allah ya temakeki.Allah ya tsareki..."


Mai gadi ne ke miƙo gaisuwa cikin rusunawa da girmamawa amma ko kallo bai isheta bare ta amsashi.


Saida driver yy daf da zai shiga ciki snn tace stop a dakilance cak ya tsaya awajen.


Glass taja ta wurga wa me gadin wani irin kaskantacce kallo baisan lkcin daya sunkuyar da kansa kasa ba.


Dauke kai tay sann tace 

"Kai me gadi..Yaushe Doctor ya dawo gidan nan??


Bakinsa na bari bari ya budi baki yace Allah ya temaki ki hajiya ai Baima fi mintina 20 da shigowarsa ba.


Daga nan batacemai komi ba ta maida glass din motar ta rufe sann ta umarce driver daya juya yakaita office dinta kawai

Dan aranta tasan dolene in tashiga ciki zasu samu matsala dashi aranta tasani sarai dolene mijinta yanemi ya bukaceta duba da kwananta goma sha bakwai kenan tana can gidan halisa suna shirye shiryen biki hade da kwana biyu da sukayi a asibiti..


and if ders one thing she hates very much shi ne sex a aure. A nata ra'ayin 

Gani take kamar yawan bawa namiji sex shiyake kawo raini tsakanin miji da matarsa. Besides tafison ana kwana da itane ayayin da take bukatar hakan bawai idan mijinta yana bukace ba.


Meenal is a chronic feminist at heart dan bata fotowa fili ta fada amma kuma tsarin rayuwartan bisa akan haka yake tafiya ba karya .


Itadin irin matayen nan ne da suke da ra'ayin cewa mace da namiji have equal right, in zatay girki shima dole yayi, in zai gaisheta zata gaishe shi, in zata kwana dashi dolene sai tayi ra'ayi. Awajen ta namiji ba shugabanta bane bare kuma tay jagora da shi, yadda zaiyi yadda yakeso da rayuwarsa haka itama zatayi da nata rayuwar but deep down inside her heart she still expects him shidin ya kasance tamkar wani bawanta, as handsome and rich as he is awajenta babbanabun alfaharine agareta taga tana juyashi sosai, so take ya saukar mata da kai ta mulkeshi while he humble down and worship her needs and desires as his wife a duk lkcin datake son haka...

Atayani sharing izuwa grps grps da kuke ciki please.


08060712446 chat surayyahms direct.

No comments