Breaking News

Cheaters Club 8

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin Æ™arfe...)_ 



#ROMANCE

#FICTION


#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER


BY

 _SURAYYAHMS_

 _08060712446_

*Don't call please*



⏯️8️⃣


Duk da azaban sanyin asubahi dake busawa a farkon safiyar bai hana halisa kunna Acn motar datake tukawar ba,Ahnkli cikin kasala da rashin karfin jiki sosai take murza stiring, kowani dakika sai ta sauke nishi mai karfi da karsashi.


zazzafar numfashin dake kufcewa yana fita daga bakinta har wani turiri yake hade da fatar jikinta daya dau wani irin zafin zazzabi kamar wacce ake gasa matashi acikin wuta.


Ganin babu kowa akan hanyar yasa take tuki da hannu daya kuma a hankli,dayan hannu ta da bata dorashi akan stiring ba ta sakashine akan kyakkawar fuskarta tana tare zafafan hawayenta da suke kin dena zubowa mata akan fuskarta.


Aranta ji take kamar zafin datakeji aranta bazai taɓa karewa ba gashi har tagaji dashi sosai.


Tunda tabar harabar asibitin tadauki hanya tunanin rayuwarta da zach kawai takeyi aranta batama san inta dosa ba,itade kawai tafiya take gaba gadi kwakwalrta kuwa tuni ya shiga gararin neman amsoshn tambyarta akan yuyuwar rugujewar aurenta da zach.


Ji take kamar duk wani lallashin duniya da gata da zata samo awajen kawayenta bazai saka zucyarta yay sanyi har ya kuma gamsu da kalaman da zach ya aiko mata ba har sai in shidin ne ya furta mata dakansa taji.


She desperately needs answers,komin munin shi..tanasonji..kodama zata samu nitsuwa acikin zuciyarta da rayuwarta.


Tasan zach bashine autar maza ba, amma shidin na daban ne a rayuwarta tunda shine É—a namiji tilo data tsaya tayi masa so na tsakani da Allah dan tun bayan rasuwar iyayenta bata taba samun nitsuwar yin soyayya ta gaskiyadda amana ba sai akanshi.


Hanyar anguwarsu ta victoria island ta nufa inda hadadden gidanta yake..


Da kyar ta iya karasawa bakin fankakacecen gate dinta dake nan golden colour snn taja ta tsaya, dake asubahi ne sanda tadoka horn kamar sau uku kafin mai gadinta ya leko da torch dinsa mai haske ta bulin gate din a gurguje yanamai dubawa.


Saukar da glass dinta tay a hankli suna hade ido da mai gadin yabi ya rikice da mamakin ganinta a yanayin datake bakuma tare da ustaz ba..


Aggaggauce yasaka key ya bude mata gate ta shigo cikin makeken harabar gidan tun baima kammala rufe gate din ba ya barshi ya dawo da gudu yataho domin ya bude mata motar danta fito...


Ahankli ta kashe motar snn ta kife kanta akan string tabi ta lumshe idanuwanta hawayenta na tsilala sosai,Tafi minti uku ahaka kanta na kife da stiring tanata sauke ajiyan zuciya, dakyar kafin nan tasaka hannu tahau gogesu sanda ta gogesu tasss kafin ta bude motar ta sauko kasa ahankli.


 Kallonta mai gadin ya dingayi da mamaki musammn ma dayaga kafarta fayau ko talakmi babu akai daga ita sai rigar asibiti ga wani irin jaaa da idanunta yay da saida ya bashi tsoro. 


Kansa yadan sauke kasa kadan kafin nan ya dago ya kara kallonta a sigar tausayawa dan Duk wani labarin abunda ya faru da ita saida sukaji abakin yan gulma sedei zucyrsu sam batayi musu dadi ba,ko shinan dayake gadin gidanta haka kawai inya tunoda irin soyayyar da zach yayita nunawa halisa saiyaji baqinciki da takaici ya kamasa aransa. Duk wanda ya san irin shakuwar da sukayi zai gane cewa zach sam bai kyauta mata ba.


atake yahau kada kansa yana neman tsari wa yayansa da zuriarsa da shiga taskon irin wayann mazajen masu yaudara da sigar soyayyar gaskiya, jikin shi ya dadayin mugun sanyi,.

Muryansa a rarrabe ya taho daf kamar zai rusuna kasa cikin girmamawa Yanamai cewa Allah shi baki lafiya Madam snnu da zuwa,

Barkdai madam ina kwana. ya jikinki madan Allah ya baki lafiya...

Allah ya saka maki, Allah maida miki da mafi alheri. Allah ya baki lfiya me dorewa. ahnkli ta dago ta kalleshi jin kalaman sa dake fitowa can daga cikin zuciyarsa 


kyakkwayan murmushi ta sakar masa hawaye take suka ciko idanunta ganin yadda ma'aitakanta suke damuwa da ita sosai..


To inde har halinta mai kyaune meyasa zach zaice bazai iya auren mace irinta ba snn ya tozarta ta aranar aurenta?


Wann tambayar zuciyarta yake jefa wa kwakwalrta wanda atake Hawaye suka biyo baya tanayi tana kuma murmushi.


mamki ne ya turnekesa ganin halin datake ciki wanda ko makaho ya ganta yasan ba adede take ba, Duk dama danne kukanta takeyi amma bai hanata masa murmushin ba.


Zaiyi magana cikin katse shi Tace "Karka damu malam liman am fine, na kuma gode da kulawa

cikin disashen muryan ta dake fita ahnkli ta fada wanda ba lallai na nesa yaji me takece masaba.


Gyada kansa yay yanami dada mata addua aransa Har bakin kofa ya rakata ganin tana takawar ne ahnkli  jiri jiri na damunta sosai.


She is soo down to earth ita sam bata daukar ma'aikatan ta abun kyama ko kasakantatun duk dama addininsu ba daya ba. Uztaz da malam liman mai gadinta duk suna sallah, security man na gidan ne kawai dan uwanta christian dan garin jos ne ana ce masa  jeff amma asalin sunan shi jerfery ne, shine yake kulawa da ccctv cameras da duk wani motsi dake gudana while uztaz yana makale da ita akowani lkci. Shikuma malam liman shike musu gadin gidan gabaki daya. Iya sudin ne kawai agidan sai ita bata tara tarkacen mutane sosai ba.


Suna kaiwa bakin kofar malam liman yay sauri ya Juyo agaggauce da alaman sauri zai koma dakinsa, yana juyi halisa ta dakatar dashi tanamai cewa ina zakaje aggaguce kuma?


Yace hajiya zanje na dauki wayana ne na kira uztaz ya taho kusa koda kina bukatar wani abu.


Babu yabo ba fallasa 

Tace a'a malam liman kabarshi kawai yagaji yana baccine. nima hutawa kawai zanyi.


Hakan datace yasakashi sake ransa kadan snn yace toh shikenan hajiya inadaga nan idan kina bukatar wani abu zanzo da wuri. Yabi ya karashe da cewa Allah ya baki lfya.


Murmushi kawai ta masa batace mai komi ba snn ta wuce cikin main house dinta dayake nan a kyafe da cozy sleek designs na zamani tamkar da hannu ta zauna ta kerashi izuwa taste dinta tsabar irin narka masa kudade masu yawa datayi wajen kawatashi.. .


Bata wani cikamai tarkacen kele kele ba parlour ne mara tarkace amma yana da azaban kyaun tsari, katoton wallpaper ne baqi mai zanen rose flower fari da jaaa zagaye da bangon daga tsakiya kuma akwai fararen kujera masu L shape da throw pillows dinsu red colour wanda suke manya manya saidan karamin round Table da ke gaban su da Wani sharbeben smart tv screen dayakusa cinye rabin bangon wajen...


Wani kamshi ne mai mugun dadi ke fitowa daga labulayen falon na traditional incense asalin qamshin turaren shuwa arabs na maiduguiri hade da iskan Ac mai dadi da ya kama falon mai sanya wata nitsattsiyar nitsuwa.


Ita kanta halisa data shigo cikin falon jin sanyi mai gauraye da qamshin turare na ratsata saida hakan yasaka taja ajiyan zciya.


Wani bene mai golden rail ta bi snn ta sauka a daidai setin dinning area mai dauke da wani madaidaicin dinning table shima white colour with little touch of gold all over it Wanda Already an kawata kan dinning table din da manyan decoration verses na alfarma wajen ya karayin haske sabida crystal chandelier dake sama ta tsakiyar su yana fidda wani uban haske...


Cak ta tsaya akai tanata kallon dede setin da zach yake zama idan yazo, ragwabbben murmushi ne ke kufcewa akan fuskarta tuna irin yadda yake mutuwar jin dadin girkinta intay musu ,he likes her food he likes almost evrything about her shiyasa gabaki daya ta rasa gane kan komi ayanzu.


Rabuwarta da zach wani lamari aranta mai wuyar dauka, sati biyu daya wuce,ranar ta dafa masa tuwon pounded yam da egushi soup, wanda bayan ya gamaci ne ya bata wasu tsadaddun kayan sawa kyauta snn ya kaita wani waje mai shegen kyau kuma abazata. The place was full of candle lights, rose flowers and melodious guiter sound. Anan ya mata tambayar daya zanca mata rayuwarta gabaki daya. Inda yakai kafarsa can kasa snn  ya durkusa tare da gayamata dalilai masu yawa da yasaka ta dace da zamowa matar aurensa snn ya saka mata zobensa na alkwarin aure..


Ko wani jimawa da yin hakan ba ayi ba kuma aka fara shirin auren cikin nunawa kansu so da shakuwa.


so..what changes?

"Tambaya take makanta "shin Menene ya faru....menene  kuma ya sauyawa zach ra'ayi a kanta a dede wann lkcin bayan adacan yagama bada kyawawan dalilinsa na kasancewarta matar datafi kowa dacewa da zama da shi na har Abada??


Kafin ta kammala wayann tunanin kanta ya gama rikicewa sosai hawaye masu rauni sun wanke mata fuska. 


Juyawa tay ta wuce sama ta bude dakinta ahankli tana daf da zata kife kan gado danta fidda kukan datake dannewa aranta nan da nan taji kafafuwanta sunci karo da wani abu maidan karfi daga karkashin gado.


Tsugunawa tay ahankli dan ta duba menene ya buge mata kafarta. Dake da dan duhu duhu bata kunna hasken dakin ba so bata gani sosai.


Hakan yasaka ta zura hannunta kasar gadon jin ta kamo wani abu mai ƙarfi kamar gurasar da aka gineshi da turbaya.


Kallon abun takeyi dan atake taji Tsikar jikinta ya tashi ayayin data riko abun da hannunta sanin meta riko yasa jikinta gabaki dayansa ya saki ya kuma ragwabewa


Ita kanta bata san ya akayi ta mike tsaye da abun a hannunta ta nufi wajen swtch ta kunna wutar dakin ba dan Babu dandanin karfi ajikinta.


Ta kalle fondant dream castle din da akayishi da white sugar wanda kamar master plan ne da suka gina burrikansu da rayuwarsu aciki da ita da zach.


5 kids,more love..till they reach thier grand ages.


Agefe taga mazaunin kabarrukansu guda biyu sun tsufa har an binnesu right beside each oda, da red roses akan graves dinsun,ga kuma gunkin yayansu dana jikokinsu gewaye dasu suna tsaye.



Sulalewa kasa tay tana murmushi mai wani irin sanyi mai kuma shigewa jijiyoyin kwakwalwa dan ji take kamr soyayyar ta da zach ne yakemai dada dawowa ma zuciyarta sabuwa.


Hannunta dake rawa sosai takai tana tattaba dream castle din, ta wani lumshe idanunwanta hawaynta na zuba akai sosai da sosai. Kkrin mikewa tsaye take sai kuma jiri ya kwasheta batare da shirya ba ji kawai tay rigifffff akasa dream castle din ya subuce ya fado kasa tare da tarwatsewa.


Kararsa dayaya tayau yasata razana taja da baya jin kamar zuciyarta ne ya tarwatse akasa ba castle din ba. Da wani irin uban sauri jikinta na rawa ta sauka akasa da gwiwanta agaban castle din ganin yadda komi ya ruguje kamar bashi ba.


Hawayen da batasan da su ba sune suka tsilalo she knws in her heart the this is a bad luck sign


Rungumar kanta tay Ta lunshe ido sosai sauran pieces din castle din ta rungume akan kirjinfa gam gam tana wani irin gunjin kuka mai tsumayi


Da kyar take iya bada soyayyarta da yardanta ma mutum shiyasa muddin ya shigeta da kyar yake iya ficewa 


Dan itakanta ta rasa yadda akayi haryanzu soyayyar zach yake kkrin dafata ta ciki batare da ta shirya masa ba , all she can feel is love and intense anger, but not hatred. Dan dukkan abunda zach yace  akanta haryanzu bata gama gamsuwa da shi ba.


Jefar da abun tay ta mike tsaye cikin azama da zafin nama jin dolene kawai ya kasance mata da ta fita ta nemo zach suyi magana ido da ido dan ya furta mata komi da bakinsa taji.


A gurguje ta bude scroll hanger dake cikin wardrob dinta batama tsaya dubawa ba iya kayan da hannunta ya sauka akai kawai ta zaro tahau sakawa ajikinta bayan ta cire na asibutun ta jefar musu shi akasa agaggauce.


Rigar polo ce baki da wandon jeans blue colour dayay mata das das ajikinta ta jawo sleepers ta zura akafarta tuna cewa key din motartan ma tabarshine acikin motar awaje yasaka ta fice wajen agaggauce cikin sauri. 


Wajajen karfe biyar da rabi na asubahi lkcin daf malam liman ya fito kenan daga dan karamin ginin masjid din dake kofar gidan.


Motarta ta nufa ta bude da sauri zaata shiga Ta hangosa yana kkron tahowa wajenta da sauri cikin sassarfa.


 Atunaninsa hutuwar datace masa zatayi bacci kawai hala zatayi.


budan baki yay zai mata magana ganin ta dakatar dashi da hannu yasaka yay shiru. Kunna motar tay sann ta dubeshi ta ciki tanamai cewa ka  bude min gate malam liman.


Jikinshi a sanyaye yaje ya bude irin mummunan fixgar motar dayaga tayi saida ya yakoma da baya  a rude yana salati da karfi.. ko mint  biyu bai karayi ba yaga keyanta acan hartakai kan titi tana sharara wani uban gudu akan hanyar.


Da sauri ya koma gidan yana shiga room dinsa ya dau wayarsa ya hau bugawa uztaz kira kusan miscalls tara ya masa bai dauka ba sai ana karshen ya dauka hankli atashe yace salam Alaikum malam liman


Jin muryansa wani iri yasaka malam liman yace wa alaikusalam uztaz lafiya kuwa.


Yace ina kuwa lfya na farka da tashin hankli munata neman madam bamu ganta ba.


Cikin katseshi malam liman yace wata madan din?...uztaz ya ja tsaki a kufule kaji wani shirme dama can wata madam muke dashi banda miss halisa mansa?, Zai magana ya tsaresa a masife kai malam liman in baka da abun fadi ni zan shiga gari ynxu nemanta securityn mu duk sun fita amma bazan iya zaman jiransu ba gaskiya.


Agaggauce ya fada Yana shirin katse wayar cikin sauri Malam liman yace dakata uztaz,yace toh menen kuma fadi da sauri..yace  dama na kira na gaya maka ne cewa madam fa tun karfe hudu na asubahi ta dawo gidan nan tacemin hutawa zatayi, ynzu ma na kiraka ne in gaya maka cewa ta kara ficewa kuma kamar naga bata cikin hayyacinta dan Allah kayi kkri kaje ka nemota kar taje tay hatsari ko wani abu yaje ya sameta.


Bakin Uztaz na rawa sosai yace dagaske kakeyi malam liman???

..tunkan ya amsashi yace tohh to nagode kashe wayar kawai ina zuwa.


Yana katse wayar ya fice acikin asbitin da uban sauri ya fita can waje ya nemo abun hawa ya wuce gidan agaggauce.


Already security sun riga sun bazama hanya ana neman halisa sanin cewa da motarta ta fita..


Ita kuwa ta baya tabi inda babu hanya mai kyau within 40 min max ta fito awani sharbaben anguwan masu kudi anan ta inda kyafaffen gidan hadiza yake wato anguwar lekki.


Wani coner na daban ta dauka nan ma tay tafiya me dan nisa kafin ta iske hadadden mansion din zach..


Nunfashinta dake kkrin daukewa cak ta dedeta snn ta Rage kudin motar gani datay kamar ana kkrin bude gate din.


Ahankli ta soma tahowa tun ma bata iso daf ba taga gate din abude anata kkrin loda wasu heavy luggages abayan booth din wata black range rover.


Kirjinta na bugawa ta rasa menene takeji gabaki daya dan wani irin tsinkewa da faduwar gaba mai tsanani ne suka rufeta a lkci guda sai taji kamr ta rasa nitsuwarta ne ma gabaki daya. Jikinta atake yahau karkarwa shikadansa.


Tanakaiwa daf da gate din tun batagai ga horn ba idanunta yaci karo da  siffar wata budurwa a tsaye farace sollll sosai kamar ba yar kasar nigeria ba daf da motar zach din ana kkrin bude mata domin ta zauna aciki, a daskare halisa ta kuresu da idanu, sai wani rigima take ta sako dark green silky gown iya kan cinyarta, rabin nonowarta na waje tasha uban heels ga wani kwalliyar kece raini da ta zubawa fuskarta.


Hawaye yuuuu suke sauka da ga idanuwan halisa izuwa kasa, ji tay kamar notinan kanta na kwancewa, dan Harga Allah halisa batasan yadda akayi ta iya danne tsananin azaban kishin dataji ya cakke zuciyarta ayanzu ba.


Kkrin saukowa take da sauri jikinta na rawa taga  wai harsun kammala sun fito, gani tayi sun dau kan hanyar dake gabanta dake ita ta baya ta fito da alaman basu ganta ba.



Sauri tay ta isa gaban megida,muryanta na rawa tace hey, ya juyo a tsorace ganin itace jikin shi sai yay sanyi.


Goo...good morning maam..akwaita da iya danne zuciyarta sosai dan haka calmly tace masa morning, da harshen turanci tacemai zach ne awaccn motar?

Bai iya mata karya ba ya gyada kansa  sabbin hawaye yaga yana sauko mata sai yaji ta bashi tausyi sosai..

tace  can you Please tell me where he is heading to..


Yace Airpot maa.

Muryanta na kukan tana kkrin danneshi amma ina kukan yaci karfinta ta ciki, ahankli Tace but I tot he is in london?..


Mai gadi yace eh amma jiya yazo deben kayansa yaune dai zai koma .


Batare da ta kalleshi ba Tace okay thanks. Kafin ya amsata Ta juya da gudu ta koma motar tawani wainashi da mugun gudu ta shiga binsu abaya.


Kukan datake dannewa ta sakeshi a fili tanayi kamar dama jira take a ballo matashi .


Aranta Ta mugun yarda da zach, yaukoma wacece acikin motarsa tare dashi tabbas yau ta dandanwa zuciyarta wutar kishi mai zafi da radaddi.


Dake sun mata nisa yasaka baima lura da cewa tana biyosu ba


Ita kuwa gudun data sharo dashi yasa harta kusa cimmasun dan daga inda take tana iya hango bayan motarsu.



Daga ta bangaren uztaz kuwa yana sauka abakin gate ya gamu da malam liman atsaye,agaggauce yahau tambayarsa shikuwa bai boye masa komi ba ya gaggaya masa abunda ya lura dashi.


Cikin sauri uztaz ya shige cikin gidan ganin falonta is intact yasa ya wuce cikin dakinta direct.


Yana bude kofar idanuwansa suka sauka akan fasasshen castle din nan daya rugaje akasa daganan ya soma fahimtar komi..


Da mugun gudu ya sauko kasa yana salati nan danan ya zari key din wata sport car na kamfanin camaro mai falfala uban gudu ya fice da ita yay hanyar lekki.


Koda ya isa kofar gidan zach da kyar mai gadinsa ya kulashi,..


Jin cewa airpot duka suka nufa yasaka shima yay nan acikin gaggawa.




6:30 am na safiya on the dot yay masu zach a farfajiyan fili safaran jiragen sama na murtala muhammad intnl airpot lagos.


Shi din mai kudin gaske ne dan haka baiya bin kowani irin jirgi saita haya,dan haka sashin su aka wuce dasu kai tsaye

Inda jirginsa zai tashi dashi around 6:45am shikadansa aciki.


Budurwan dayazo da ita tun daga london danta dan ragemai ciwon kewar halisa yasaka aka tsaya domin a sauketa Adaf wajen shiga asalin normal entrance wanda harya saka an kama mata first class flight dazata koma london din dashi around 7 am itama. 


Motarsu na tsayawa awajen cak sai ga na halisa ya karaso.


Daga cikin motar kuwa banda kkrin shawo kan zach da nonowarta babu abunda budurwan nan takeyi, dan kuwa jiya ya bata mamaki bana wasa ba. 


Atunaninta ya daukota ne danya kwana yana sex da ita amma sai taga duk hakan bai faru ba, yaxo gidansa da itane kawai dan baison ya kasance shikadai ne a gidansa dats full of halisa's true love and memories bare haryakaiga ya shiga wani hali na tunanin abunda yay mata a matsayin cin amana ko mugunta.


Suna sauka abakin kofar shiga ya dan jingina da motarsa yanaa mai sanarda ita cewa ya riga ya tura mata kudaden service dinta, wani Rungumar bazata budurwan ta sakar masa tanamai shishege masa

Tanamai ce mishi cikin kunne da sexy voice nata" Are u sure u dont want my company in dat plane?...miskillalan murmushin gamsuwa dakansa yay najin babu wata macen data isa ta rudar dashi. Ya turata ahankli hannunsu sarkafe da juna yace mata "no am fine"..Sosai budurwan taji wani iri, ganin tanata kallonshi yasaka yay murmushi tare da sauke mata karamin kiss agefen kuncinta. Ahankli yace go..i work with time.


Ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi tace okay goodluck to you sir  and thanks for the money 


Baice komi ba harta ja luggage dinta ta bashi baya, yana dago idanuwansa sama karaf sukaci karo da ruwan kwayar idanun halisa dake da cikke da tsananin kishi data zubamai bata ko kiftawa.


Wani irin shocking yaji yabi jikinshi atake ya mamayeshi yanamai masa ziriya tun dagakan tsakar kansa har izuwa kafafunsa da suka tsaya cak agabanta basa iya ko motsawa.


Yanayinta dayagani yasaka jikinsa ya mugun mutuwa yanjin wani yarr ajikinshi na yanyameshi.


wani irin kallon juna sukeyi da tsumayi mai ragbarwar cikin yanayi mai ciwo da zafi marar fasaltuwa, thousands od words going tru deir minds at the same time, 


jikin halisa na rawa sosai ganin yadda zach ya lumshe idanunsa ya kuma budesu, Duk sun juya atake sun dawo ruwan jaaa, ..ahankli ta ke kallonsa da idanuwanta da sukayi jaaaa din itama sosai wanda tsabar kuka har sun dan kumbura sun sauya mata kamanni, jin bazai iya tsayawa kallonta ahaka ba yasaka ya fixge nashi idanun acikin nata da karfi cikin sauke ajiyar zuciya da basarwa ya juya agaggauce ya nufi hanyar private entrance dinsa inda jirginsa ke jiran shi.


Securities dinsa sunkai su biyar take suka wani rufamai baya suna masi biyedashi, sai sauri yake yana tafiya yana duban agogonsa yana kallon time da ya rage masa wanda baifi nan da minti goma jirginsa ya tashi ba.


Da kyar halisa ta fixge kanta acikin ruwan kishi dayagama sasssare mata sassan gabobin jiki.


Binsu tahauyi cikin gaggawa godiyan Allah da babu hayaniyar mutane awajen duba da private area ne .


Sunanshi take kira tana tahowa da sauri sauri jin zuciyarta na bugawa da tsananin karfi kamr zai ballo waje.


Gabaki daya rauni ya gama nakasata, she cant even hold on anymore kuka takeyi ahakli kamar yar karamar yarinyar datake bibiyar mahaifyarta ayayin datake guje mata.


Zach...zach..wait...

Li..sten... Zach pls wait!!


Hakan take maimatawa da disashen muryanta mai tafe da kuka


Yanajinta amma hakan baisaka yaji aransa da ya dakata ba, itama bata fasa ba harta isko su daf securities dinsa ne suka juyo suka rirriketa.


Hakan yay mata ciwo bana wasa ba. Cikin birkicewa da kuka ta fara daka musu tsawa .

"Hey,  What are doing

How dare u touch me, Get off me..dont touch me. Zachhhhhh..pleasse.

Ta karashe cikin kuka sosai.


Zuciyarsa kamar zai tsage haka yakejin ciwon kukan nata aransa, sede wani irin taurin zuciya yake dashi, iya tausayi da rauni halisa tasakamai ayanzu amma kuma...


Har ya kama handle na no go area zai shige ciki sai yaji gabaki daya ya kasa yin hakan.. dan yasan in ya shiga nan ya rabu da halisa kenan na har abada .


Juyowa yay ahankli yaganta acan tanata kuka tana kokowa da  securities dinsa duk ta rikice tanason tanayi magana dashi.


Dawowa yasomayi ahankli batare dayasan yay hakan ba, halisa tana daga kai yay kamar zai koma ta kwala ihun sunansa cikin kuka tace "Zach, zach please dont go.. just listen to me...once .. this once. .

Nayi maka alkwri after this bazaka sake gani na a inda kake ba.. 


Lumshe idanuwansa yay tsam jin hakan daya diro masa abazata yakuma tsaga kahon zuciyarsa kamar wuka.


A tunaninsa halisa is here to beg him to come back to her...which yasan bazai taɓa yin haka ba.


Saide cewa datayi bayan yau bazata kara zuwa inda yake ba yasaka shi jin tsananin ciwo da kuma muguwar zumudin son jin meke tafe da ita..


Dedeta numfashinsa da nitsuwarsa yay snn yay hannu wa securiteis dinsa suka kyaleta.


Tsayuwar cak tay tanata sauke wasu irin tagwayen gajiyayun numfashi masu azaban nauyi.. yana tsammani yaga ta taho da gudu tazo ta zube akan kafarta agabansa dan yaji dadi gaya mata abunda ke ransa amma sai yaganta tana tsaye


Dedeta kanta tay snn ta hau share hawayenta saida ta share fuskarta tasssss ya zamo babu dison hawayen kafin ta sauke ajiyan zuciya cikin wata nitsuwar da bata san dashi ba ta tako ahankli har ta iso gabansa.


Kallon juna suka shigayi kirjinsu duka na bugawa da wani irin karfi.


Ta budi baki kenan zatay masa magana cikin dakatar da ita yace 


...."5 minutes". Say what eva u want say and just leave.


Yanayin daya fadi hakan yay mata ciwo amma ta basar tana duban cikin idanunshi, fuskarta a dore sosai .."tace i have nothing to say to u coward; ure the one who have sumtin to tell me..

zach what is happening i dersve some xplanations.


Shiru yay nadan wasu lkci dan kuwa Zuciya da Karfin gwiwar dayagani a idanuwanta yasashi jin kansa na tafasa ta ciki da rauni da kuma tsoro.


Just 2mint ago she was weak and crying and shaking amma yanzu ynzu harta shanye duka hakan ta dawo masa tamkar wata dutse wanda bbu dandanin abunda yake girgizata.


Wani Tsawa ta dakamai a bazata wanda saida ya dawo dashi cikin hayyacinshi daga duniyar mamakin daya lula ciki


Nace Kafadamin abunda ka gayawa meenal da bakinka..tell me u never loved me..and i am not the woman you ever wnted to marry..kafada min yanzu, agabana, idan ba haka..........


Cikin katseta a karsashe yace Idan ba haka ba meye? What will u do girl? ...tace ohh, nothing! Except that u will never have this chance in ur life again and u will regret it.


Cike da zafin nama yace ya isa haka,..im not scared of anything.


Tace goood..then tell me


Hannunsa ya dungule da karfi snn Ya lumshe idanunsa sosai sai can snnn ya budesu tareda zubasu acikin nata, wani irin tausayinta yaji yafara magana acikin nitsuwa.


Yace Babu wani abu danaso araina dayafi minke halisa..u were perfect. .kuma Nayi tsammanin zan samu rayuwar danake buri atattare dakke,Sede hakan bazaiyu ba..

Rayuwarki na da can danawa ba iri daya bane.

Altho I am not scared to live with ur past..but what about my future???.

What about my familys reputations..my own reputations..


Cikin katseshi Adan daskare takoma baya murynta na rawa Tace ".....my past?..a...a ina kasan past dina...did u knw dat u dont own a right to my past..meya kawoshi cikin wann maganan..which past are you talking about...


Ta karashe maganan acikin rudani mai yawa hakan yay saurin sanar da shi cewa meenal batagaya mata gaskiya ba kenan.


Shikuwa Bai boye mata ba ya soma gaya mata tun daga yadda kawunta yake sakata karuwancin dole dan ta siyar musu da kayan tallarsu, kwana da ita da kawun yayi da cikin datay masa kuma ta zubar, da kazamin rayuwar datayi a lagos wanda tayisu dan ta samu na cin abinci wajen kwana da na biyan kudin makarnta.


"But it seems like shafin kazantar kawai akafi rero masa batare da ansanar dashi dalilanta na shiga  cikin wann irin rayuwar ba..


Bai daukesa wani mintina biyar ba ya gama mata bayani game da abubuwan da meenal talba tafada mishi akanta batare daya ambato sunanta acikn bayanyin ba


A daskare take kallon bakinshi har ya kammala yay shiru jin wani irin girmammen mamaki na rifeta yana kuma tsilleta tsaffffff tun daga kan kafafuwarta, ji tay kamar a mafarkine zach ya  bankado cafta cafta na littafin rayuwanta yana kuma yi yana rufa rufa baya son kama sunan kowa aciki.


Juyin duniyan nan tay dan ya gaya mata inda yaji wann labarin amma ce mata yake babu amfanin fada mata hakan kwata kwta..


Yace mata shi baida lkcin tsayawa yin wata doguwar magana da ita, kawai dai bazai iya auren ta bane ahaka..badon kansa ba saidan yaransa da familynsa da mutuncinsa.


Maganan nasa ya sosa mata ranta tare da mata ciwo bana wasa ba.


rufe idonta tay snn tace Zach saiyau na amince da cewa baka taɓa kaunata ba tunda dai qaddarata da ya wuce ne zai saka ka walakntani snn ka tozartani aranar aurenmu.


Yace halisa karkice min haka..i have my own life too. kuma nine nake da ikon tsara abunda ya dace da rayuwata


Tace kuma bakasan ban dace dakai bako sai aranan aurenmu? Ahankli cikin sauke ajiyar zuciya tace mishi " ..dats not fair..


Wani irin Shiru yay baice mata komi ba sai yanzu yakejin aransa kamar bai kyauta mata ba.


Kanta na kallon can kasa aftr some minute taja numfashi, ahankl ta dago kanta ta kalleshi wani ragwabben murmushi ta sakar masa daya raunata masa zuciya fiye da komi  


Tana murmushin tace 'Okay,..its fine..lets say ur reason is validated. Zach i wish u all the best..ta sake sunkuyar dakanta tanajin zafi sosai, ta kuma dagowa tana murmushi snn tace  in ur life..Good bye zach!!!


Tana fadin hakan ta juya a nitse zata barshi anan atsaye, harta fara tafiya da wani irin shauki mai tattare da rauni taji an fixgota baya.


Zach din ne ya fixgota jikinshi idanuwansa sun dada yin ja kamr zasu fidda wuta..Yace iya abunda zakice min kenan Halisa..all the best in my life?..murmushi tayi mai yawa snn tace what do you xpect? Kasa magana yay yanata kallon cikin kwayar idanunta dan a duk sanda namiji yaso rabuwa da mace yaga bata zautu tanason ta mutu akansa ba toh dolene  wani abu daga ego nashi saiya raunatu.


Normally maza sukanyi tunanin cewa muddin suka samu wata babban gurbi na dasa soyayyarsu a zuciyar mace to koda zasu tozarta ta bazata taɓa iya rayuwa babu su ba.


Zach yasha tsananin mamakin karfin zuciya da irin calmness din dke tattare da halisa awann lkcin.. He tot mental maturity is for men not men. He was wrong!!! And He hate to be wrong!!!


Da karfi yace Halisa tambayar ki nakeyi.


Da karfi ta kwace kanta anashi tace i askd u too dama me kake tsammni


Yace really. Cikin katse shi tana murmushi tace

Tace yeah..kaine kace

Min rayuwarka yana da tsari kuma na fahimceka

Nima Nay maka fatan alheri. So, Now is left for me to go and find sumone who can love me truly including my past .


Ahankli ya wani irin lumshe idanuwansa jikinshi a mugun sanyaye sede kafin nan ya bude idon halisa hartayi nisa.


Yafi minti goma atsaye awajen kamar andasahi yanamai hangen bayanta da idonshi da sai aynzu suka soma zubar da ruwan hawaye sosai.


Ji yake kamar ya fice aguje yaje ya tarota amma ina bazai taba iya aikata hakan ba..

 Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauÆ™e snn ya zaro glass dake aljihunsa gaban rigansa ya saka akan idanuwansa ya juya aggauace ya shiga jirgi.


Yana zama captain din ya fara shirin lula su sama saidai har iyanzu zach hawayen ciwon rabuwa da halisa yake saukewa sam sam kwakwalsa bai dawo masa daidai ba.



Halisa na ficewa a airpot din tun kan takaiga motar ta taji jikinta ya mata nauyi atake atake zazzabi mai zafi ya kuma rufeta.


Ta dora hannu akan murfin motan kenan taji jiri mai karfi ya kwasheta zatayi baya ta fadi kasa saiga uztaz ya karaso a gurguje yazo ya tareta..


He was right der yana hangen lokcin da halisa take tattaunawa da zach din sede shi baije kusa dasu ba ya jiratane ata waje 


Tana sume suka iso asibitin aka kara bata gado, allura doc ahmed ya mata snn aka dan jona mata engine taya numfashi kwata kwata batafi mintina goma sha biyar ba ta farka tare da bude idanuwanta.


Lokacin ana neman karfe tara da rabi na safiya.


Banda Muryoyoyin kawayenta abakin kofa babu abunda takeji.


Ruwan Masifa kawai suka rufe security da uztaz dashi akan labarin da sukaji na cewa halisa ta fice a asibitin tun 4am batare da sanninsu ba


Ta inda suke shiga bata nan suke ficewa ba, nan din ma daga shemau ne sai vicky sai hadiza meenal talba bata samu karasowa ba tukuna...

Atayani Sharing please

SURAYYAHMS IS EVERYWHERE ON WATTPAD,IG, FACEBOOK AND AREWA BOOKS U CAN SEARCH AND FOLLOW THANKS!!!!

No comments