Breaking News

Cheaters Club 9

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_ 



#ROMANCE

#FICTION

#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER



BY

 _SURAYYAHMS_

 _08060712446_

*Don't call please*




⏯️9️⃣


sassafe meenal din ta fito daga wanka kirjinta daure da dan karamin towel ɗaya na hannunta tana daddanawa ajikinta tana shasshare fuskarta dashi, tana kammala hakan ta cilla towel din yy gefe tayi zamanta agaban dressing mirror Tana ta kallon kanta tana zuba wasu irin kayatattun mayun murmushi,da alaman wani irin ji da kanta yau takeyi wani sabon salon rigima takeyi ita kadanta tana yaba kyaun da Allah ya bata wanda aganinta duk wanda ya sameta a Duniyarsa ya gama kure sa'ar samun hadaddiyar mata..


Hade da murnan cewa yau halisa zata farka su cigaba da rayuwarsu.


koyaya ne ma she needs halisa's presence in her life dan aranta tasan da cewa babu wata ƙawar amana mai kaunarta da gaskiya a duniya sama da ita dan Halisa ta riga ta dauke ta ne kamar yar uwan jini.



Very soft hands dinta ta sakala ta bude dan karamin drawar gaban mirrorn wanda ta rikeshi da fingers dinta sama sama kamar wacce take kyamar handle din,yana buduwa ta hau fiddo wasu mahaukatan kayan gyaran fata dana kwalliya gasunan dai birjik kala kala iri iri daga exclusive har zuwa yan daidai kai da alaman yau kwalliyar kawai take ji dashi just based on yadda ta matsu dataga tayi kyau ta haska ace tafi uban kowa acikin kawayen nasu.


Kusan minti ashirin ta dauka a wajen shafa mai kawai,saboda tsilla tsilla take bin jikinta starting frm body moisturizers, face toners,face hand and feet cream,oil and face enhancers.


Tayi kyau kuwa babu laifi,after like 30 min ta mike ta bude wadrob ta dau kayanta data shirya already cewa shi zata saka,brown lace an mata bubu gown mai kwalliya da bakin lace din dan kadan ata gaba.

 

Favourite turarenta na shafawa jiki ta jawo ta duba, tsaki ta saki ganin yadda ya rage dan kadan Aciki kuma duk cikin collections dinta tafi kaunarsa sosai,ajiyar zuciya mai qarfi tasauke tana jujjuya kwalban turaren a hannunta.

Tay rau rau da idanunta Thinking of yadda zata soma tunkarar mijinta khaleel da batun kaita shoping duba da irin  walakancin datamai jiya da daddare.


Murmushi tay aranta dasanin cewa dolenshi ne ma ya yafe mata inta buga emotinal game dinta agabansa. Khaleel yana da imani da kuma tausayi on and on tasha masa laifuka masu yawa da girma wanda yaci ace da yanxu ya saketa amma daga ya huce sai dai yay mata nasiha a wuce wajen.


Murmushi ta dingayi tana tuna kyawawan halayyar sa, shi namiji mai kulawa dan Duk yawan kudin tan nan nashi kudinne tafijin dadin kashewa sabida dukkan abunda ta nema awajensa yakan bata batare da gunaguni ba.


Dan kadan ta shafa turaren a gefen wuya da armpit tana kafa kafa dashi dan karya kare mata..,tana kammala shafawa ta maida shi inda ta ciro takalminta na gucci dats sooo high tahau kai ta zare wani katoton mayafi sannan tayi waje batare da ta neme inda mijintan yake ba.


Acikin wata black colour Mercedex benz ake janta saida ta somaa biyawa offishinta kafin nan ta fito ranta a mugun bace jin cewa wai yau fadila bata fito aiki ba snn layinta a akashe.


Da kyar hajya zainab magajiya ta dauka sabida biyan bashin bacci datakeyi.


Meenal ta tambayeta ina fadilar take ko haryanzu tana wajenta ne?


 Acikin gigin bacci tace mata ai fadila kam tun safe ta sallameta harda cewa hala ta biya wajen saurayinta ne shiyasa ta kashe musu waya.


Da tsaki mai kauri meenal ta kashe wayar ranta a mugun bace da fadila tana Allah Allah ta dawo ta mata walakncin da ba a taɓa mata irinshi ba.


Daga bangaren fadilar kuwa tunda tabar hotel din wani asibiti ta wuce aka bata gado anakan dubata.. 


Banda hawaye babu abunda takeyi dan Aranta Bakaramin lissafin matakin da zata dauka akan rayuwarta takeyi ba.



Likita ya riga yagaya mata cewa tana cikin risk din kamuwa da cutuka masu haɗari ga rayuwarta sosai sakamakon duk masu kwana da ita ba amfani sukeyi da kororon rubber ba.


Yace mata zata iya kamuwa da sexual transmited diseases ko infections kama daga kan su gonorrhea,genital wart da herpes, har izuwakan babban su wato HIV da sauransu.


Sosai fadila ta tsorata da jin hakan bana wasa ba.


Likita yace hanya mafi sauki da zata kamu da cuttuka iri iri shine ta hanyar luwadi da madigo

Wann cusa yatsar hannu da shan gaban juna ayayin da sukeyi da amfani da namiji ta tsuliyar kashi bakaramin kashe garkuwan jiki yakeyi ba.


Hakan yana nufin zaka kasance soo open to any kind of disease and infection..ko malaria ko typhoid  kai ko tari ne in zaiyi ma wani illa toh da dan sauki, sai kaga kaida kakeyn harkan su luwadi da lesbianism karamin cuta sai ya jijjigaki sosai sabida garkuwan jikinki sam babu karfi.




Daga dayan bangaren kuwa Tun Ahanya akan hanyar zuwa asibiti aka kira meenal aka gaya mata halin da ake ciki da halisa..


Kirjinta na tsananta bugu da tunanin inda halisar ta nufa dan haryau tanata fargaban karda halisa ta kira zach suyi magana asirinta yaje ya tonu.


Tsoro da kuma tsananin fargaban karda asirinta ya tonu ya hanata shigowa asibiti cikin sauran kawayensun,So she went direct to the state commisoners office dan tayi bambami da fafa ta nuna nuna masa isarta yakuma san cewa bada wasa suke son ayi musu aikin gadin halisa ba.


Tafi awa guda a office din commisioner tana hakimce akan kujera daga ta sakashi ya kira wann sai akira wancan,

Hanklin commisoner bai kwanta ba saida uztaz ya kira securities din nan ya sanar dasu cewa yasameta duk dama sunsha masifa da query awajen ogansu.


Tanajin cewa an same halisa nan da nan tay marmaza ta dauki jakarta ta fito daga wajen commisoner daya rakota har gaban motarta, bayan sun tattauna kadan ya koma ciki ita kuma driverta ya bude mata gidan baya ta zauna tayi shiru.


Driver na saka key ta dakamai tsawa tanamai wurgo masa wasu kyamataccun kallo.


"Are u stupid...Did i ask u  to drive? Da wani irin sauri ya kashe engine din motar yanamai cewa am sorry ma..nan tabishi da wani irin kakkauraran tsaki tanacewa sorry for yourself idiot. Sann ta dauke kanta tanamai sauke ajiyan zuciya jin drivern har ya kunna mata Ac kamar yasan abunda take bukata kenan.


She is soo high on anxiety sabida batasan me zataje ta tarar awajen halisa ba, ko ina halisar taje oho, itade tasan koma ina taje dazun bazai wuce yana da kyakkwan alaƙa da lamarinta da zach ba..sede hnklinta yana dan kwanciya idan ta tuna cewa zach is not even in dis country..


Haka ta dinga juya tunani kala kala aranta, can ta fara scrolling kan lambarsa da zimman kiransa ta tambayesa ko halisa tazo amma tsoro da fargaba duk yabi ya cikata. Ganin duk wann bazai ficceta ba yasaka ta kyabe bakinta tare da dage kafadunta sama alaman to meyene ma in halisar taji iyakaci ne kawai ta bata hakuri.


Da wann tunanin tadan bawa kanta kwarin gwiwar isa asibiti within 10 minuts suka isa.


Tunda ta sauka acikin motar ta dauko wata sharbabeiyar dark eye spectacles ta dorashi akan kyakkwan fuskarta, 


Ahankli cikin tattali take takowa bata kallon ko ina sai gabanta as usual driventa na binta da wayarta da jakarta abaya.


Tana shigowa ciki gabanta na faduwa amma haka ta basar ta sako fuska kamar wanda batajin komi aranta sai tausayin kawarta halisa.


Tana daf da isowa kofar indasuka saba zama ta soma jiyo surutunsu shema'u dan ita tafi kowa zaƙewa da masifa tanata tuhumar uztaz akan ficewar da halisa tayi. Hadiza kuwa tunda tay masa sau daya bata kara magana awajen ba tayi shuru sabida yau din ta tashi amma gabaki daya jikinta baya mata dadi. Vicky ne ke taya shema'u cikin masa fada kamr wani karamin yaro.


Shide shiru yay musu bece musu komi ba kuma bai gaya musu inda halisa taje ko da waye ta hadu ba.


Suna tsaka da masifeshi saiga nan halisar ta sauko daga kan gadonta ta fito waje, da sauri suka barshi suka nufi wajenta suna masu jera mata sannu cikin yanayin tausayawa hadiza na kkrin riketa tay mata murmushi tare da ce mata its okay am fine dije. 


Sai tambayoyi shema'u da vicky suke harbo mata


Halisa why will u get up Karde surutun mu ne ya taso ki.


Shemau tace Halsy ko kina bukatar wani abu ne


Vicky ta kuma cewa

Ko na kira maki doctor Ahmed?


Batace dasu uffan ba Agefen uztaz din tazo ta zauna ganin yadda ta sunkuyar dakanshi yana dan satar duban yanayin ta duk yabi ya damu sosai, ajiyar zucya ta sauke kawayen dukansu suka zuba mata ido muryanta adan dishe dan ba ama jin ta sosai, cikin sanyin jiki tace musu surutun me kukeyi ne hakan waya tabo ku?...


Hadiza tace dole ne muyi surutu cemana akayi fa waikin bace agadon asibiti While these lazy and useless securities are busy sleeping like he goats.


bude baki tayi ayanayin nemansu da magana wanda yasaka suka dan sake ransu kadan..Tace  jibeku ba fa "To sai inkama in ɓata akan gadon asibiti sai kace wata karamar yarinya? Kumadai kunsan inna fice anan to dalilin dolene yasakani ficewa


Dede nan meenal ta taho setin kofar shiga wajen saidai bata karaso ciki ba ta laɓe abakin kofar tanajin zancensu.


Da kyar Halisan take magana sabida bata jin karfi ajikinta sosai tace pls karku blaming uztaz its All my faults.


Shema'u taja tsaki  mai kauri dan ita akwaita da iyajin tsanan talaka aranta,tabi halisan da harara aikam kullum dai haka kike kareshi shide awajenki baya laifi...


Vicky tace is true bai dace ace sun barki kin fice awann yanayin ba bafa halisa..


Hadiza ce ta katsesu ta hanyar dafa kafadun halisar datayi ahankli..


Muryanta a sanyaye sigar lallami Tace babe where did u go to? I knw u did dis on purpose.

..whats soo important da baki daukeshi wannn din (ta nuna uztaz da yar yatsa) kunje dashi ba.


Ajiyar zuciya halisa ta sauke jin yadda hadiza tamata tambayar calmly ,zata budi baki kenan shemau ta harare uztaz tanamai dakamai tsawa"...kai kazami,wiill u get out frm this place kazo wani kasa kunne kanajinmu munafuki wawa kawai jibeshi.


Uztaz na mikewa Halisa ta riko hannunshi tace shemau please calm down mana..nace miki bbu hannunsa acikin wann abun...badon shiba da halama bazaku taɓa sanin halin da zan kasance aciki ba.


Fadin hakan datayi yasaka jikinsu yay sanyi sai shemaun ta kyaleshi.


Gefe yaje ya tsaya abayn halisar ayayinda ta soma basu labarin haduwarta da zach...


Kirjin meenal dake raƙube da bangon wajen kamr zai ballo ya fito waje driverta kuwa sai kallon ikon Allah kawai yake, dan mannuwa sosai da bango tayi snn ta kasa kunnunwanta tanajiyo bayanan halisan sosai.


Wani kuuui kakejin cikinta na tsurewa musammn yadda taji shemau ta soma daukar zancen da wuta wuta meenal kam Kamar zata saki fitsari a wandonta haka ta dingaji daga waje .sai daga can karshen labarin ta fahimci cewa ashe zach bai ambace sunanta ba

Hasalima ayanzu haka halisa babu wanda take zargi kamar matar kawunta wato mama g dan tasanta da mugun kwadayin abun duniya


Aganinta itace kawai tayi mata tsanar da har zata ita juye sirrikanta ma zach tunda tagane cewa har sunsan me kudi zata aura kuma sunyi tattaki tun daga benue sunzo lagos halattar bikinne sabida abasu kudi.



Wani irin Dafe kirji meenal tay tabi ta jingina bayanta da bango tanamai sauke ajiyan zuciyar samun sauƙi.


Tuni jikinta ya soma rawa taji atake tanason ta shigo cikinsu akada gurmin da ita.


Jakarta da wyarta ta karbe ta kore driver waje, saida ta dau mintinta tana Kimtsa kanta tare da dedeta nitsuwarta snn kai tsaye suka ganta ta faso cikinsu kamar anjefota daga waje


Tana shigowa ta jefar da jakarta akasa rigijif jikinta har na wani irin shaking, take take ta sako da wasu zafafan mahaukatan hawaye acikin yanayin tsorata taje ta wani sakar ma halisan runguma mai tattare da tsumayin soyayya irin na yan uwan jini..


 Rungumar junansu sukayi sosai tanamai lallashin halisa cikin ce mata ta tsorata sosai dataji cewa ance tabar gadon asibiti shiyasa ma ta wuce wajen commisioner danta dagamai hankli.


Duk sauran kawayen sai da suka jinjina ma raunataccen yanayin meenal ganin irin soyayya mai tattare da amana da shakuwa datake nunawa halisa agabansu..


Ahankli halisa ta kwace kanta ajikinta tanamai ce mata she is fine babu Abunda ya sameta..


Kafin suce wani abu meenal ta fixge kanta daga jikin halisa cike da huci tayo kan uztaz 

Rai amugun bace, a zafafe tace mishi 'U bastard..ina kaje da zaka barta harta fita batare da saninka ba.


Hannu ta daga sama zata sharara masa mari akan fuskarsa halisa tay saurin shigewa tsakiyarsu sai tayau marin ya sauka akan fuskarta.


A mugun fusace meenal take duban uztaz wanda already duk ya rikice ganin halisa Ta amsar masa mari agaban sauran kawayenta.


Ranta a mugun hautsine cikin masifa tace and What is wrong with u halisa????


Sauran kawayen take suka tattaso zasuyi magana halisar ta daure fuskanta sosai tace "Enough...ta juyo ta kalle uztaz dake bari abayanta  fuskanta a dore ta masa nuni da hanya akan ya fice yadan basu waje .


Da sauri ya fice wasu suka bishi da kallo wasu da kakkauran tsaki sam zuciyarsa batayi masa dadi ba.


Budan baki meenal tay a hatsale zata tuhumeta akan marin data tare masa...cikin katseta halisa tace "ya isa haka meenal..nasan ranku ya bacine sabida kun damu da lafiyata da rayuwata amma nasha gaya muku bazan bari kuna cin mutuncin mutane agaba na ba. For god sake he is not a child.


Meenal tay rolling idanunta a kyamace tace but He is nothing but a mere worker meyasa bazaiyi aikinsa da kyau ba 


Halisa tace And so what meenal?wayace miki baya aikinsa, Shi Wooker ba mutum bane..i was once a worker, a club striper. Me rawa tsiraraa agaban dumbin mutane a clube dan na biyawa kaina kudin makaranta shin Akwai kaskantaccen aikin dayafi hakane?


So why zaku saka shi agaba kamar karamin yaro kuna zaginsa akan laifin da bai aikata ba...he was more than worried about me. If not bcos he followd me and save my life wayasan a halinda nake ciki yanxu karku manta fa dukanku da kuke daga jijiyar wuyan nan lkcin dana fice din kuna gidajen mazajenku ne shidinne akaina babu dare ba rana.


Tanakaiwa nan wani raunataccen Kuka ta fashe musu da shi tana mai cewa Dan Allah acireshi acikin wann maganan. I have alot of problems now..and i tot u girls will help me calm down ..


Tun kan ta karasa hadiza ta karaso ta rungumeta  tanata rarrashinta kafin nan vicky ta taho sunata bata baki.


Nan Shemau ta dube meenal tace to ai gashinan kin sakata kuka ke wai uwar zuciya da Allah can matsa, meenal ta murguda mata baki batace komi ba.


Bayan komi ya lafa kadan meenal saida ta saka halisa ta kara bata labarin haduwarta da zach haka kowa ya shiga jinjinawa sai meenal din kuma ta ɓata shiruuuuuu acikinsu zuciyarta yahau gararin tunanin yadda zatayi ta binne wann maganan na har abada musammn dataga kamar kawayen tan basu taɓa iya yafewa duk wanda yakai gulman nan wa zach ba.


Wann karon Hadizza ce ma dakanta take kawo shawarar cewa lallai zatay amfani da ikonta wajen datse babban contract din da zach zai samo a london dan ta kuntatamaai kamar yadda ya kuntata ma halisa,shemau da vicky duk suka hau goya mata baya..alkcin duk ji suke sun tsane zach jin cewa wai akan past din halisa yay mata wann abun


Halisa kuwa shakkunta nagakan matar kawunta ne bata damu da wani daukar fansa ba. Dan tasan cewa Allah yana tare da ita sosai shine zai sakamata.


Shirun da meenal tay yaso ya sako musu shakku aransu shemau ce ta datse mata tunani da cewa ke meenal yaya ne kam baki ce komi ba are u in or out?????


Absent mindedly ta dago kai tace me kuka cewa wai?


Vicky tabita da kallon mamaki snn tace munata magana akan zach kinyi shiri bakice komi ba .


Wani nannauyar ajiyan zuciya tayi snn ta mike tsaye cikin jeka ka dawo irin ta gwada musu cewa she is still in  shock na jin wayannn abubuwan da halisa ta furta musu.


Sai Cahn ta tsaya tana wani irin huci kamar wata kububuwa..ciki bacin rai da rantsewa da Allahn da ya halicceta tace in dai ita yar halak ce toh taci alwashin tona asirin duk wani dan iskan dayakai gulman halisa wajen zach kuma ko dama ace kawuntan ne dakansa to tay alkwari saita dandana masa azaba tin a duniya dan duk wanda ya taɓa halisa kamar ita ya taba dan haka bazata masa da sauki ba.


Duk kawayen sunata bata baki ganin yadda ta zafafa abun ta kuma rantse agabansu ta ci mummunan alwashin daukar fansa.


Daganan hira kadan sukayi daya danganci Lamarin, halisa tace musu kawai sucewa likita a sallameta batajin zata iya zama a asibitin nan gidanta take son komawa.


Basu ki mata ba sabida sosai tattaunawa da su akan lamarin da yadda suke nuna cewa suna tare da ita sosai yasaka ta sake jikinta sosai.


 At around 11 am na safiya suka dunguma suka rakota har gidanta dake victoria island.


Haka suka sha hira suna janta cikin tadi, vicky tay musu girki ita da hadiza dan dama sune kadai sukadan iya girki idan akacire halisar datay tasowar wahalar rayuwa.


Bayan yan wasu lokuta bayan sun tursasa halisa taci abincin kadan nan tay wanka ta dan samu bacci wajajen hudu na yamma kowacce acikin kawayen ta wuce harkan dake gabanta hankli kwance da sanin cewa halisa is getting better now.


Office Meenal ta wuce da zimman dubawa ko fadila ta dawo mata da files dinta data tafi dasu gidan hajiya.


Daga fannin hadiza kuwa asibiti direct ta wuce domin ta samu tattaunawa da therapist dinta jin kamar ciwon hawan jininta ne yake kkrin tashi. Shema'u kuma ta wuce gidanta agaggauce jincewa surkuwanta zatazo daga kaduna kuma ayaudin zata koma a late nite fligh kusan dolenta ne ta kasance tana gidan dan bakaramin yar bariki bace surkuwan nata.



Sabida traffic yasaka sai Wajajen karfe shida saura vicky ta isa gidanta dake ikeja.


Agajiye ta turo kofar tanamai kwalawa mijinta kira tun daga nan honey i am home..baby where are you?


Shiru taji wanda yasata bankado kofar ayayin da taji kirif mutum ya fadi akasa timmmmm..


Ihun mace taji arazane ta shigo ciki da sauri ganin uwar mijinta ta ture akasa batare da sanninta ba ga kuma akwatunanta an fito mata dasu anjerasu abakin kofa sai taji ta kuma rudewa.


Da sauri tayo kan matar tana kkrin dagata amma sai ja da baya take kamar taga mayyya

Aka bar victoria da cewa

"Mama am sooo sorry

Bansan kina bakin kofa ba ..kkrin dagota akasar take kanyi cike da tausayawa tana mai cewa sorry maaa am so sorry i hope ure not hurt???tana miko hannunta ta Wani irin Bangaje hannun da karfi tanata nishi nishi tabi ta biyota da harara mai zafi


tsaye victoria tay tana kallon ikon Allah.


Can sai ga wata yar budurwa da bazata wuce shekaru sha tara ba ta fito da half gowb ajikinta wanda kallo daya ya isheka kasan cewa daga kauyen futuk ta fito kan nan duk aciicinye.


 A ladabce yarinyar kuwa ta gaishe da vicky ta amsa ta bayabo ba fallasa tanabinta da kallo


Tsohuwar na daga kasa tace Sophieeee dont touch dat witch, come here .. come and and caryy me and then go back upstairs and tell my son that his wicked barren wife has pushd me to the ground oooo


Yarinyar tana dagota ta haura sama da mugun gudu zatakai aikan da aka gayamata wajen mijin vicky da tun zuwansu yaki ma ya kulasu bare ya sauko


Vicky duk ta rude ta rasa nayi dan bata fahince komi ba tukuna, itama a gaggauce ta juya zata haura saman jin ance mijinta naciki..


Tana daga kafafunta taji wani wufff tsohuwa ta mata damkar yan dambe


Jawota waje tayi da bala'in karfi ta watsata akasa..tana cewa enough is enough yau na kawo ma yarona mace mai haihuwa ,3yrs witout a child..shame on victoria or what eva ur name is...see u must leave my son's house today today..


Daga can sama prince falana yake kallonsu wani shuumin smirks ne ya kufce masa akan fuskarsa snn ya maida hanklinsa kan chatting din dayakeyi.


A wani lambar dayay saving da "Boss"

Ya rubuta "Hurry am waiting for ur replies please.


Yanakan jira saiga yar kauyen nan tazo bada sako baima saurareta ba ya hantareta ta sauko kasa a tsorace.


Ringing wayarsa ya dauka ganin video call ne yasaka yay murmushi yahau gaggayara kwanciyar gemunsa da zaman rigarsa daya dan matseshi yanamai bayyana siffar faffadar kirjinshi, yadan kikkimtsa dai.


Saida ya tabbata yay kyau snn ya amsa video call din,. Wani kyakkwan mutumi ne fari soll dashi wanda bazai wuce shekaru 58 ba ya bayyana yana wani irin murmushi ganin irin rangwadin da prince falana yake aiko masa mai cike da maɗe irin na masoya..


My baby my baby so What is wrong my baby


Take Prince ya kwabe fuska kamar macce cikin sautin shagwaba yanayi yana rangwadi yace 

My love na riga na gaya maka cewa ina shirin zuwa normal wajen  haduwarmu  kawai saiga mama na ta faso da wata yarinya daga kauye

Waita kawomin mata mai haihuwa ko ce mata akayi nawa matar bata haihuwane oho.


Mutumin yace toh ya ake cikine nifa ina matukar bukatar ganinka babyna..kasan jiya na dawo daga europe akwai stress na tafiya yakamata kazo mudan shana yau koya?


Cikeda rau rau da ido Prince yace okay toh what shud i do..? Inna ce zan fita mama na bazata kyaleni ba...


Mutumin yace just give her money and send her away, bazataji haushinka ba zatace matarka ce take zugaka ..besides in kazomin yauma zan baka wata sabuwar kall din contract akwai kudi sosai akai. Kawai kayi bla bla ka fito karabu dasu aisu mata ne basuda damuwar data wucce abasu kudi


Murmushi prince ya somayi snn yace okay i will do as u say..but inaga sai gobe da safe zan korata ta tafi gida ynzu dare yay.


Daga haka suka katse wayar, ya jefa wayar a aljihu yana sauka kasa yaje ya samesu sunata drama saiya hade ransa yayy pretending cewa ana nemansa a office dinsa urgently koma miyene su bari inya dawo zai sauraresu.


Ahaka nan ya tafi ya barsu inbanda ruwan gorin haihuwa da bakaken zagi babu abunda vicky ta wuni sha awajen surkuwanta.

Mutane dayawa suna son adinga yin typing akai kai amma kuma basa sharhi taya kenan zansa kunajin dadin labarin bare na ji zimman yinshi sau biyi arana? Inkuna son cangin yanayin post to ku daure dai kuyi yi sharhi iya sharhi😁😁

Ayi sharing please.



Surayyahms 08060712446 chats only

No comments