Breaking News

Rainon Soja 33-34


33~34
_________________________

Close rabi’s chapter let’s continue to chapter 33 ???????.
Chapter for #Ma’eesha#Doctor Bulama#Ali haidar#nurse Narret#Hajiya Hajara#bushira#General sale yelwa house#mami#jidder#close with chapter 33~34 can’t wait for the chapter 35????????.

A matu?ar gigice ya tashi daga Zaunen da yake , gani tayi ya juya da Sauri yana barin Office ?in nata inda take masa bayani ita da Doctor Bulama akan matsalar ciwon Ma’eesha . Hada Ido suka yi da Doctor Bulama inda cikin Sauri ya furta “ mu bi bayan sa , ki yi ?o?arin…..Kai Doctor don Allah bakai ne zaka fa?a mun Aiki na ba , ai nasan aiki na Yalla?ai , ta furta tana Ficewa daga Office ?in cike da tsayayya irin na likita da nurse . Fuuuuu da sauri ta biyo bayan Aliyu haidar inda tuni ya isa Special room ?in da aka ?wantar da Ma’eesha . A hankali yake tunano da Al’amura masu yawo a memory ?in shi ”. Wayyo Uncle mutuwa xanyi . Huhhhhhwwww Saurin matsawa yayi inda yake jin sambatun ta , alamu barci take yi a wannan lokacin amma babu abin da take yi face mafarkin gata yana bata horon zama Soja . Tsugunawa yayi yana rage Tsawon sa gaban Gadon da take kwance dai dai wannan sa’ilin Nurse narret da Doctor Bulama na shigowa . Hannun sa yasa yana shafa Gyefen Saman Goshin ta kana rintse idanun sa . A hankali ya furta “ Na sauya komai , a yanzu ba zan takura Miki sai kinyi soja ba, Zan saka ki zama cikakkiyar mace Wanda ko wani ?a namiji zai Alfahari dake Ma’eesha . You’re always my champ. My whole world Ni ka?ai ne nasan hakan , Ya furta yana dafe ?arayi guda na ?irjin sa dake buga masa dai dai .

Kallon Doctor Bulama Nurse narret tayi kana ta harare sa sai kuma ta taka a hankali tana isa inda Aliyu yake kamin tace “ Ka kwantar da hankalin ka Sir , a yanzu magunguna za’a ?aurata akai , Sannan komai zai dai dai ta inshallah . Ai ba wani babban matsala bane . Da’alama na lura kana son wannan ?anwar taka sosai .

Wani irin kallo Aliyu yayi mata da idanun sa suka ka?a suka yi Jah , Cike da dakakkiyar Muryar sa na babu wasa ya furta “ Har mutuwa zan iya yi akanta , ki tabbatar kin bani maganin da Ma’eesha na zata dawo yanda take , sannan kuyi bayanin komai da komai naku zan saka a tura maku ”. Okay sir . Ta furta tana dan rage Tsawon ta na girmamawa . Don zafin kan sa ya burgeta ya kuma kara mata jin ?aunar sa a zuciya ”. tabbas namiji ne! Ta furta tana wani taunar ?asan la??anta .

Muryar Doctor Bulama ne ya katse ta yana dawo da ita daga Hayyacin ta don tuni ta fara lulawa duniyar rayuwar ta gata ga Sojan nata Wato Haidar . Sir! Don Allah ka sauke ta ta warware kana sai ko zuwa gobe ne a sallameta. No I want always to be with my baby . Ali ya furta yana ?aukar ta cak tare da kokarin barin room ?in . No sir ni da kaina zan kula da ita … Nurse Narret ta furta tana kokarin kai hannu tare da Amsan ma’eesha wacce ya ?auketa tamkar wata ?aramar yarinya small baby.

Cike da jin kan nan nasa ya Girgiza kai cikin mulki irin na ?a namiji bare kuma shi dama ga gadara da izza ta SOJA, wuce su yayi yana fara nufar Farfajiyar Asibitin inda moton sa take fake . back seat ya bu?e yana ?wantar da ita , kana ya rufe yana dawowa mazaunin sa duka suna biye dashi , har ya shige moton kana suyi sallama a ta?aice .

Bayan ficewar sa ne daga Asibitin nan take ya fara tunanin barin garin Kaduna zuwa Lagos. Sauke numfashi yayi haka kurum yake jin tsanan garin a Zuciyar sa wanda bai san dalilin hakan ba . Hannun sa ya kai yana gyara mirror dake Hasko masa fuskar Ma’eesha wacce har a lokacin barci take yi. Murmushi naga ya saki yana furta “ Tana girma muni take yi ma , Amma a yarintar ta cutie ce ?? but now ita ganin kanta take yi wata mai ?yau can can saboda yanda ake kambamata Bama kaman Daddy da yake kiranta da Queen of beauty ?? murmushi yayi yana ?an ?auke kallon sa daga gareta tare da kallon bakin hanya da yanda masu Ababen hawa ke wucewa .

Gidan sa na nan Kaduna ya nufa don bai son zaman barikin ma a yanzu kwata² . Wannan yasa shi nufar gidan nasa da ita kai tsaye ”.
**
Wata irin kya?y?yawar mace ce yar dattijiwa wacce a shakaru ba zata Haura 42 ba a duniya ta fara shigowa cikin farfajiyar gidan General Saleh Yelwa . Motoci ne ke bin ta alamun masu mata rakiya ne . Kai da ganin irin wannan motoci kasan matar dake cikin wannan moto ba ?aramar mace Bace , haka zalika sune ake kira da Duniya ta yarda dasu .

Sai da motocin suka gama tsayuwa ne a layin su ,kana Wata Hajiya ta fito tana takowa tare da bu?e Murfin moton na biyu , inda Ni a kallon farko na ?auka itace ma aka yi ma rakiyar zuwa gidan General Saleh yelwa . Cike da mulki ta sako ?afarta ?aya inda naga Wasu irin awarwaro da rings na gold suna walwali tare da kare hasken ranan wurin . ?afar nan nata fari tarrrrr gashi lu?wi dashi wannan zai shaida maka mai ?afar macece babba kuma mai jikin mata wato mai ?iba . Jakarta Ta mi?o kana ta fito gaba ?ayan ta . Ohhhh mashaallh shine Abin da na iya furtawa . Yar gayu gayu gayu ce ta ?arshe . Fuskar nan nata yasha make Up na zamani wanda a shekarun ta baka ce zata yi shi ba . Ta ?ayatu kuma sannan ta ha?u Ainun ma?ura . Sanye take cikin wata jallabiya ta mata wanda tsadarta ta haura 100k maroon Color . Doguwar mace ce mai jiki ga tsaho sai ta dirkake tayi dai dai . ?an motsa la??anta tayi wanda yake she?i kana ta furta “ Bushira ri?a mun Wannan jakar , ta ?are maganan tare da ?an datsar la??anta na ?asa Wanda yayi sanadin motsawar 2 dimples ?in ta yana lo?awa na gyefe da Gyefen fuska . Tom Ranki ya da?e Hajajju , Bushira ta furta tana Amsan jakar da tsadarta ya haura 150k ha?e da takalmin ta mai ?an tudu daga ?asa . Hannun tasa tana gyara Hular jallabiyar tare da gyara zubuwar gashin kan ta , wanda da fari na ?auka Attachment ne , sai daga bisani na fahimta gashin ta ne yasha wannan ?an bara’uban gyaran har gadon baya . Ko mayafi babu gandasdas ta fara takawa tana shiga ixuwa cikin gidan Saleh Yelwa, tana bin ko ina da kallo . Yayin da Bushira ke take mata baya , sauran makarkaban nata suna tsayawa daga Waje . Gilashin idanun ta shi kan shi tsadar shi irin wanda ake yi da ruwan gold ne wanda a ku?in mu ta Nigeria zai kai 800k . mai haske ne , amma anyi shi da fa?i wanda ya tsaya ya kara mata kyau da cikar hajittaka ta manya .

Bushira zan iya bin stairs kuwa ? Babu lifta ne a gidan ? . Muryar ta mai kama da na shuwa ya katse Ni . afuwan Hajiya a?wai tuba nake ko zamu bi tacan .

No..
No! Na ?an mi?a ?afa ai . Ta furta tana ?are shigewa tare da hayewa matattakalan .

Mami!! Mami come out and see something surprise ???????? “ Jidder ta furta da gudun ta tana saukowa daga stairs ?in falon tana takowa inda Hajiya Hajara ke washe mata baki tana furta “ Come on my baby , give a warm hug ?? ”. Da gudu Jidder ta fa?a jikin ta tare da cewa “ I’m happy to see you mom , I’m so much happy ma’am . Murmushi Hajiya Hajara tayi tana Rungume Jidder kana tace “ Yeah my babe happy to see too . Kin ganki yanda kika ?ara ?yau ? .

Murmushi Jidder tayi tana gya?a kai tare da cewa “ Yessss Mom I’m always prettie , Sannan Mami kinyi kyau sosai Kema , duka ?akin Hajiya Kaka babu mai ?yaunki me yasa? Ko Alhaji tsoho kika biyo sune yar larabawan mali ……. Murmushi Hajiya Hajara tayi tana bu?e baki zata yi Magana kenan idanun ta suka sauka akan babban hoton family na dake ma?ale a bangon falon…dukan su cikin Farin ciki suke a wannan sa’ilin sai dai nata Farin cikin da harkar yafi na kowa . That’s how she is ….Which girl is that? Wacece wannan na ganta a family photo naku ? Mamin ta ?ara haihuwa ne ban sani ba…………………?

 

Don girman Allah kar ki karanta indai baki biyani ba , haka kuma kema kar ki fitar mun da Littaffi????ga masu bu?atar payment regular group ?500 Vip group ?1000 SPC payment ?1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 only WhatsApp . Idan kuma Vtu transfer ne send it via 090614666409 only call thanks love ???? .

Next chapter 35 is on the way??????? .#mrs usm…#Antymmnteddy.
[1/21, 2:57 PM] Real~Mamanteddy: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written….??? Aysha Mamanteddy Mrs Usm*

 

_________________________

*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*

 

*Littafin na ku?i ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ?500… Vip group ?1000… SPC payment ?1500 via 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#?????? .*

 

No comments