Breaking News

Rainon Soja 68-69

68-69
*Littafin na ku?i ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment?500 Vip payment?1000 SPC payment?1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409….?????#Mamanteddy#mrsusm.*



Book 3
“……Meye na rufe ?ofa da key…?
Ammmm motsa baki yayi zai mata magana Daddy da ya Khalil suka shigo Bedroom din Wannan yasa shi yin shiru , duka nufar gadon da Ma’eesha take suka yi ba tare da sun bi ta kan Aliyu ba . Wanda da ganin Khalil ya Gimtse fuska yana aikin cika ma?oshi . My Queen ya jikin naki,Ashe baki ji da?i ba jiya …..? Daddy ya furta yana shafa kan ma’eesha cike da kulawa. Gya?a masa kai tayi tana cewa “ Daddy Ina ?wana! Ya Khalil an tashi lafiya?” . Lpyl alhmdlh Khalil ya amsa kana yace “ Ya jikin baki? Ina ne ke yi Miki ciwo ?….kai da ba likita ba meye amfani sanin inda yake mata ciwo zai maka…” Muryar Aliyu ya katse su , inda cikin Sauri Daddy ya furta “ Ai Doctor Isma’il yana hanya yanzu zai taho sai ya duba ta ”. ?an lumshe ido mami tayi tana Girgiza kai a zuciyar ta tana mamakin kishi irin na Aliyu da masifa babu ha?uri ?wata-?wata ”.

**
Gidan Alhaji Adamu ( Yes da No)?? .
A yanzu ne ake yin ta , duka matan nasa sun banzama wurin bokaye kowa burin ta ta zama ta gaban gaba a cikin wannan gida. Inda Hajiya Falmata ta lashi takobin duk wanda ya nemi shan gaban ta , to sai ta aika shi lahira kamar yanda ta aika Rabi . A yanzu Halin da ake ciki Hajiya Atika da kan ta ta fara Yabaawa aya za?i , don kullum a ciwo take , ta kaima ko wajen falo bata iya fitowa sai dai kullum a wuri ?aya a tattare kaman tsumma. Wanda wannan ba Aikin kowa bane face Na Hajiya Falmata da ta saka a sakar mata da ciwo wanda zai ta cinta har Ajali. Hasbunallahu wani’imal wakeel…?? .

Alhaji Adamu ne ya kalli Aminin nasa Malam barau wanda yake cigaba da cewa “ Gaskiya Alhaji lamarin rayuwar ka da iyalinka babu gaskiya a cikin ta. Wannan wani irin mata ne Allah ya baka , tabbas rashin Ahali ba dadi , Gashi duk cikar su babu wacce ta ta?a ko ?atan wata ….sai dai kowa fa da rashin halinta. Girgiza kai Alhaji Adamu yayi yana furta “ Allah kenan! Shike juya ma ko wani bawa Al’amarin sa . Kowa da kallon nasa ?addarar a rayuwa , Ni kuma wannan shine ?addara ta. Yanzu ba abun da na kama na samu sau?i da matan nan da ya wuce karatun Alkur’ani. Wallahi ?ur’ani kariya ce babba barau, A da baya kai ka isa ka fa?a mun Aibun mata na musamman ka ha?a da Hajiya Falmata , don ji nake gaba ?aya ?wa?walwata tamkar ba nawa ba. Amma a yanzu Alhamdulillah wallahi Ni ban ?i duka na rabu dasu ba na zauna Ni ka?ai har mutuwa don na cire ma raina ganin wani daga cikin a halina ”….. subhanallah! Kayya Alhaji….Don Allah ka bar wannan maganan , Addu’ar mu ba zata ta?a fa?i ?asa banza ba.

Shiru Alhaji Adamu yayi yana ?an tunani kana yace “ Wallahi ji nake kamar na ta?a rayuwa da Iyali na , Tom idan haka ne a yanzu ko suna Wani hali? Shin ina da Yara ko kuwa ma babu su , kamar yanda nake a yanzu? . Cike da ?wantar masa da hankali Malam barau ya furta “ Kayi ha?uri Alhaji komai bai gagari Allah ba , mu cigaba da fauwala masa al’amaran mu ”.

Saurin kallon malam barau Alhaji Adamu yayi sakamakon jin hayaniyar da ya kara?e farfajiyar gidan .

Subhanallah meke faruwa kuma ? Allah dai yasa lafiya! Mu fita daga Waje….Alhaji Adamu ya furta yana ?o?arin mi?ewa daga ?ayataccen kujeran da yake zaune . A’a Alhaji ka zauna ,kai da kake fama da jiki ,Bara Ni na le?a na gani . Barau ya katse shi yana mi?ewa. Girgiza kai Alhaji Adamu yayi yana cewa “ A’a ko ?aya mu tafi dai tare zai fi ” .

A farfajiyar gidan Alhaji Adamu kuwa yan aikin gidan ne cike da su Hajiya Falmata da Turai matar Alhaji Adamu ta uku . Kowa na sallami tare da fa?in Albarkacin bakin sa bisa ga Ganin Basiru da suka yi ya zauna a ?asa yana zunduma ihu tare da tsine ma Rabi , yana tona ashirin duk abun da suke yi , Tare da fashewa da kuka yana cewa “ Ashe tana da cutar karya garkuwar jiki HIV . Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un……Kalmar da kake ji mata nayi kenan suna tafe hannu . Ihu yake yana karawa yana me yasa Rabi zaki mun haka ? Rabi kin cuce Ni.

Ran Malam barau ne ya ?aci da tun da suka iso wurin basu yi magana ba suna sauraren duk abun da ke faruwa. Muryar Hajiya Falmata ce ya katse su tana cewa “ To ai sai a kira Uwar ?akin ta Atika , tazo taji Ashe ?ar ?akin nata Cutar ?anjamau take dashi. Tafe hannu Bibbiyu Turai tayi tana cewa “ To ko dai itama ?anjamau ?in ne da ita , Wannan jinya ta fara yawa……Ahirr! Ya ishe Ni haka!! Muryar Alhaji Adamu ya katse su cikin fushi da tsaye . Wannan wani irin shashanci ne kuke yi haka . Kowa ta wuce ta bani wuri. Nan take kowa ta juya , da makar?abanta . Shi kam Barau cike da fushi ya fa?a Basiru da fa?a da zagin ?wal kana yace “ Idan ba kai cikakken Mara kunya ba , ku gama lalata kazo kana fa?a mana anan uban me zamuyi maka. Wallahi duk ranan da ka sake dawowa cikin gidan nan sai na Saka An yi maka raga raga dukan da tun da uwarka ta kawo duniya babu wani mahalu?i da ya ta?a yi maka tashi ka fice mawa mutane tantirin banza.

**
11:am (Lagos)
Jirgin su ya sauka .
Don dama da Wuri yake son su isa. Bin airport ?in take da kallo . Kana ta kalli Aliyu dake sauka stairs ?in idanun sa cikin ba?ar gilashin nan nasa na Rashin kirki . Murmushi yayi mata yana kai hannun sa tare da ri?o nata, a hankali ya ?an rage Tsawon sa zuwa saitin kunnen ta yana furta “ Ina sonki Ma’eesha….Allah ya taimaka mami ta Bani ke da ?yaaar…” Huwwwmmm Numfashi ta sauke ba tare da tace masa komai ba , don a yanzu duk wannan surutun nata ta ne meshi ta rasa. Ko me yasa??? .

Wani irin kallo tayi masa cikin sauri tana bin Motocin da ta gani na sojoji da kallo , kaman Wani Shugaban ?asa. Motoci ne kusan 12 , guda 7 duka sojoji ne a ciki ….Wayyo Uncle mu gudu sojojin nan fa basu da imani baka fuskokin su ba? . Ta furta maganan ita sam ta manta Uncle ?in nata fa Soja ne babba. Don a gida take ganin sa bata san shi ba a waje. Hannu tasa tana shigewa jikin sa tare da ?an?ane shi tana furta “ Uncle tsoro nake ji bindigogi ne fa a hannun su”. Murmushi yayi yana yin ?asa da Muryar sa kana yace “ Babu abun da zasu yi Miki kin manta Uncle Aliyu shima soja ne ? Mu tafi kinji ki saki jiki. Cike da Yarinta ta sakin masa murmushi don ita sam ta manta ta burkice gaba ?aya . Oho yanzu na tuna, to mu tafi. Ta furta tana kokarin sauya hanya ba inda Sojojin suke jiran su ba …..Hannun sa yasa yana ri?ota tare da nufar motocin nasu, Ma’eesha kuwa duk……………!
[1/28, 5:24 AM] Real~Mamanteddy: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

No comments