Breaking News

Wata karuwa 3


Tafi takeyi batare da tasan inda ta dosa ba idanunta da ƙafafunta sunyi mata nauyi daƙyar suke ɗaukar ta jiri na ɗaukar ta tana neman faɗuwa a dole ta nemi guri ta zauna rungume da bahon Shinkafarta tanata shassheƙar kuka me dukan zuciya jin ruwan ya fara dawowa ne yasata dafa ƙasa ta miƙe daƙyar taci gaba da tafiya jiri na ɗibanta ga ruwan saman sai ƙara ƙarfi yakeyi tunanin tare ɗan sahu ma ya kasa zuwar mata.
Tayi tafiya me tsayi cikin gushewar hayyaci da Æ™unar zucci taji anayi mata horn bata juya ba taci gaba da tafiyarta ta kumajin anyi mata horn ganin batada niyyar tsayawa yasashi fitowa a motar ya nufeta da sauri yasha gabanta yace “Am bakiji Ba Hanisa meye yasa kikayi dare haka har Æ´ar’uwarki ta koma gda”
Kawar da kanta tayi ta sake É—aukar hanya tana shirin barin gurin ya riÆ™o hijjab É—inta yace “dare yayi Hanisa kizo na kaiki gda kinga hadarin nan Æ™ara haÉ—owa yakeyi fah” sabon hawaye ne ya wanke mata fuska tace “Na gode Abdul-Ahad kaje kayi harka gabanka” juyawa tayi ta tafi yabi tafiyarta da kallo faÉ—uwar gaba ta dirar masa yace “Innanillahi wa Innah Ilaihirraji’un Hanisa meye ya faru dake haka?” DurÆ™ushewa tayi a gurin ta rushe da kuka tana girgiza masa kai.

 

Matsowa yayi gabanta yace “Tashi muje akwai matsala fah Anisa alamu sun nuna yau kin shiga sabon yanayi don Allah ya akayi haka ta faru dake garin yaya Anisa?” Kukanta ta Æ™arawa Æ™arfi tace “Na rantse da Allah bantaÉ“a jin a raina zan sarayar da budurcina don neman duniya ba tsoron faÉ—an Mama ne yasani zama har hadarin nan ya riskeni ashe cikinsa littafin Æ™addarata zai fara buÉ—ewa Abdul-Ahad na rasa budurcin dana daÉ—e ina tanadi domin mijina na rasa Æ™imar da take kankarowa duk wata mace Æ™ima sanadin tallah Na yarda da Lawwali yau ga ranar da yardar tayimin yayi reaping É—ina yayimin fyaÉ—e kuma banida ikon neman haƙƙina kawai don na kasance mara galihu wayyoh Allah wayyoh Babana Allah dama mota ce ta takeni na mutu nasan nayi shahada”
Wani mugun matsanancin tausayin yarinyar ya ɗarsu a ransa yinin yau sur da ita ya yini a ransa duk da ya ɗauki yar uwarta Hasina sun fita shan minti ya kasa hassala mata komai lissafinsa ya goce daga lkcn da idanunsa ya sauka akan Anisa ashe ita tananan wata mummunar ƙaddarar na shirin faɗa mata.

 

Wani tuÆ™uÆ™in baÆ™in ciki da baisan daga inda ya taso ba ya cika masa zuciya ya miÆ™e yace “Ok tashi akwai wani asibiti anan baya muje su baki magani sai na kaiki gda yau yaron nan bazai kwana a É—akinsa ba wlh sai nasa an É—auke……. Saurin rufe masa baki tayi da hannunta daketa rawa tace “Aa Abdu idan ka taÉ“ashi asirina zai tonu don Allah ka barshi wannan ba komai bane Æ™addararmu ce Æ´an talla ba shine da laifi ba Mama itace me laifi tunda itace ta É—ora min tallan da bata É—oramin ba aida hakan bata faru dani ba”
Bawai don ya bari ba yace mata ok muje a dubaki dare na ƙara yi shiga motar tayi yaja suka nufi wata hanya ya shiga cikin wani asibiti yayi parking suka fita yanata kallonta kyakkyawar yarinya itama rayuwarta ta gurɓata.
Office na likitan suka shiga yayi musu bayanin komai dake asibitin kuÉ—ine nandanan suka dubata suka bata magunguna yayi musu gdy suka fito suka nufi unguwarsu ya sauketa tare da bata kuÉ—i masu kauri yace “Gobe zanje Lagos ki kula da kanki ki kuma kula da shan magani zaki samu Æ™arfi kada kije tallannan gobe don Allah kinji”

 

ÆŠaga masa kai tayi ta buÉ—e bakinta cikin sanyinta na halitta tace “na gde” gdan ta shige babu kowa a tsakar gdan saboda ruwan da akayi ta ajiye kwanukan ta nufi É—akinsu ta kwanta saman tabarmasu ita kaÉ—ai tasan azabar da takeji a Æ™asanta wani tunani ne ya faÉ—o mata na ta tashi taje Madafi ta haÉ—a wuta ta samu ruwan É—umi ta gasa Æ™asanta ko ta samu sassauci.
MiÆ™ewa tayi daidai lkcn da Mama ta bankaÉ—o labulen tayi saurin komawa ta zauna harara Mama ta zabga mata tace “Duk uwar daÉ—ewar nan da kikayi don lalacewa baki iya siyar da abincin nan ba kekam na rasa baÆ™in jininki a rayuwa talla ma idan kika É—auka kwantai kikeyi” sosai kalaman Mama suna dukan zuciyarta saidai bata iya mayar mata kamar yanda Yaya Hasina take mayar mata saidai tayi kukanta ta cinye a ranta, jakarta ta duba ta zaro dubu huÉ—u ta miÆ™a mata tayi saurin karba ta Æ™irga nandanan ta saki ranta ta fara rawa tana juyi tana cewa “Masha Allah masha Allah itama ta dau hannu Hanisatu wannan kyalla kyallan kuÉ—aÉ—en hala juye akayi miki?” Kawar da kanta tayi wasu hawaye masu É—umi suka zubo mata, nan Mama ta kira Hasina ta fara raba musu cefanen gobe Hanisa cikin kuka tace “Wayyoh Allah Mama wlh bazan iya tashi ba marata ciwo takeyi Æ™afafuna zasu karye”

 

No comments