Breaking News

Wata karuwa 4


Tuni firgici ya shiga Mama ta matso da sauri tace “Ya Hayyu meye ko al’ada zakiyi” hannunta takai jikinta taji jikin zafi zau tace “Na shiga uku Ni Indo Hanisa ruwan nan kika bari ya dakeki wannan muguwar cutar taki me cin kuÉ—i take neman tashi ko?” Fita Hasina tayi da sauri tace “Ai dama da naga hadarin saida nace ta taho mu tafi taÆ™i yanzu ai ga irinta nan bari na juye miki ruwan can da na É—ora zanyi wanka saiki watsa zakiji daÉ—in jikin”
Ficewa Mama tayi hakan ya bata damar miƙewa daƙyar ta nufi bayin tana dafa bango ta shiga ta watsa ruwan ta zauna cikin bahon tana yarfa hannu saboda azabar da takeji hawayenta naci gaba da tsiyaya ta mike ta daura zaninta ta koma ɗaki daƙyar tayi sallar Isha tasha maganinta ta kwanta har zuwa lkcn shassheƙar kuka takeyi me taɓa zuciya.
Daidai lkcn Hasina ta shigo gabanta ya faÉ—i jin shassheÆ™ar kukan Æ´ar’uwar tata, da sauri ta kunna fitilar su ta É—akin ta Æ™arasa inda Hanisa ke kwance tanata rawar sanyi tace “Wai jikin ne har yanzu Hanisa meye ne yake damunki haka?” Sake gyara kwanciyarta tayi taci gaba da kukanta batare data iya bata amsa ba. Ganin tayi shiru yasa Hasina zama a kusa da ita tace “Duk da munsha bambam ta wajen É—abi’a da halayya Hanisa karki manta munyi alÆ™awarin duk rintsi duk wuya bazamu É“oyewa juna damuwarmu ba zamu faÉ—awa juna matsalarmu mu samawa kanmu mafita, shin meye yasa kikeson karya alÆ™awarin nan Ƙanwata?”

 

ÆŠora kanta tayi saman cinyar Hasina ta sake rushewa da kuka Hasina ta kwanto jikinta yanda takejin kukan Æ´ar uwar tata tasan daga zuciya yake fita itama kukan ta saki tace “Don Allah ki cireni daga tashin hankali Hanisa ki faÉ—amin matsalarmu”
Tashi tayi zaune ta buÉ—e idanunta da suka kaÉ—a sukayi jawur tace “Kiyimin alÆ™awarin zaki rufamin asiri Yaya Hasina banason wannan mgnr ta fasu don Allah” riÆ™e hannunta Hasina tayi tace “Wlh ko kisa kikayi zan rufa miki asiri Æ™anwata bare ma nasan bazai taÉ“a zama hakan ba” rungume kanta tayi cikin cinyoyinta ta sake rushewa da kuka tace “FyaÉ—e akayimin Yaya Hasin…..” “Me?” Hasina ta faÉ—a da Æ™araji sai kuma tayi saurin rufe bakinta da hannunta tare da komawa inda ta tashi da sauri jikinta na É“ari tace “Garin yaya Hanisa waye yayi miki wannan aika²r?”
Cikin kuka ta zayyane mata komai Hasina ta miÆ™e tana zagaya É—akin kanta da zuciyarta na bugawa da Æ™arfi wasu hawaye masu É—umi suka rinÆ™a sintiri a fuskarta jikinta na rawa daidai lkcn da wayarta tayi ring takai hannu ta É—auka ganin sunan Abdul yasata É—agawa muryarta na rawa tace “Abdu….” Katseta yayi da cewa “Ina Anisah?” Ajiyar zuciya tayi tace gatanan a zaune” shima zuciyar ya ajiye yace “Ina fatan tana cikin aminci?” Dake Hanisa ta sanar da ita shine ya taimaketa ya kawota gda batayi mamaki ba tace “Eh sama² dai Abdu tabbas yau tafimin kowacce rana muni cikin rayuwata wlh bantaÉ“a jin ciwon rasa budurcina ba domin Ni ganin dama nayi na bayar dashi Abdu zuciyata zafi takeyi saboda abinda ya samu Æ´ar uwata meye yasa Hanisa rayuwarta take a hargitse ne duk abinda take gudu yafi samunta?”

 

Sauke wani Gwauron numfashi yayi yace “Bani ita inason magana da ita” miÆ™a mata wayar tayi ta karÉ“a jikinta na rawa tace “Abdul-Ahad” cikin sanyin murya da kasala yace “Na’am Anisah ya jikinki?” Da shassheÆ™a tace masa naji Æ™arfin jikina da nayi amfani da ruwan zafi kamar yanda kace sannu fah na gde ubangiji yabar zumunci”
Shiru yayi zuciyarsa ta lula masa duniyar tunani saida ta kuma cewa “Abdul-Ahad ka Taimakeni ka rufemin sirrina wlh muddin sirrin nan ya fasu bazan iya zama tare da Baba ba na gwammace na shiga duniya saboda kullum Baba roÆ™ona yakeyi na kiyaye kaina na riÆ™e darajata yana yawan faÉ—amin ba talla ne matsala ba masu tallan ne da masu siyan matsalar nikam zanji kunyar ranar da asirina zai tonu baba yasan nima na rasa Æ™imata”
Murmushi yayi me ciwo yace “kina nufin abar Lawwali yaci bulus gobe ma ya samu damar aikatawa wata irin abinda ya aikata miki?” Shiru tayi a ranta tana jinjina Æ™arfin halin mutumin yace “Anisa tun ganina dake na farko zuciyata ta É—arsu da tausayinki inaji a raina idan Æ™anwata Maryam hakan ta faru da ita zan iya bari kuwa, Anisa bazan bari ba saboda haka kema bazan iya bari ba kedai kawai kija bakinki kiyi shiru”

 

*OUM HAIRAN*
[12/16, 2:33 PM] Oum Hairan&Affan: *WATA KARUWA*

 

*OUM HAIRAN*

No comments