Breaking News

Wata karuwa 7


*WARNING❌*
_Only matured ahead idan kika zageni ban yafe ba domin banyi littafina don Æ´ammata ba idan kinga zaki iya go ahead._

 

Buɗe ƙofar gdan nasu tayi ta tsaya jikin ƙofar tana nazarin gurin iyakar hangenta wata mota ce kawai a gurin ƙirar Benz baƙa sai sheƙi takeyi, zuba idanunta tayi akan motar tanason ganin abinda ke ciki tunaninta na bata to waye baƙon Yaya Hasinan da bataganshi ba?
Juyawa tayi zata koma Cikin gidan taji ance ““Am babe bakiji ba” tsayawa tayi tare da juyowa ta zubawa me mgnr ido a ranta tace “Itakam Yaya da kwashe² take wannan kuma ina ta É—eboshi? A zahiri kuma saita rusuna tace “Sannu ina yini? Murmushi matashin Saurayin Wankan tarwaÉ—a me Æ™irar Æ™arfi yayi daya fito da kyawawan haÆ™oransa masu É—auke da siririyar wushirya yace “MiÆ™e mana Ƴammata ai bakya tsugunna ba” miÆ™ewa tayi ya jingina jikin motarsa yace “Dama ba kece Hasina ba?” KaÉ—a kai tayi tace “Eh sunana Hanisa” lumshe lumsassun idanunsa yayi yace “da kyau Aneey Ni inama tunanin kece Hasina dake sunan yayi tambari so duba da yanayinki sai nace duk yanda akayi kece am karna cikaki da zance nidai sunana Ibrahim ana kirana da Mu’azzam na jima ina huccewa ina ganinki inajin wani yanayi game dake saidai ina fargabar yi miki mgn sai yau dai na daure na tunkareki ina fatan bazaki Æ™i amsa tayina ba?”

 

Kanta tayi Æ™asa dashi gabanta na faÉ—uwa tace “buÆ™ata kuma? Wacce irin buÆ™ata?” Murmushi yayi ya matsota sosai har suna jin numfashin juna yakai hannu zai kamo hannunta ta janye yace “Kinga Aneey ki saki jikinki ni nan da kike ganina idan inason mace babu abinda banayi mata nidai burina ki bani damar nuna miki Æ™auna zakiji daÉ—ina kinsan kamar yanda mace me wushirya take da ruwa da garÉ—i wajen rayuwa haka namiji ma me wushirya yake da É—anÉ—anon gamsarwa”
Wani baÆ™in ciki ne ya tokare mata maÆ™oshi ta dubeshi hawaye ya zubo mata me haÉ—e da murmushin ciwo tace “Wai meye yasa fuskarmu take bada damar kowanne shirme azo mana dashi ne Mu’azzam kake ko wa? To kamar yanda kake tunani ba haka nake ba banjin zaka samubiyan buÆ™atarka Indai irin wannan buÆ™atar ne…..” Juyawa tayi ta shige gda tabarshi tsaye shanye da baki cike da mugun mamaki yace “kayy dama akwai irin waÉ—annan yaran Æ´ar talla ce fah kayy aa saidai ko idan nine banyi mata ba amma bari na gwada wata dabara” yaro ya kira yace ya shiga gdan yace da Mama za’a shigo a gaisheta” yaron ya shiga ya isar da saÆ™on nandanan Mama da Ramma suka hau tsumar gyara shimfiÉ—a aikace da yaron yaje yace ya shigo.

 

Shigowa yayi ya zauna a tsakar gdan suka gaisa da Mama ya gabatar da kansa ya zaro kuÉ—i masu yawa ya aje mata ya miÆ™e zai tafi tanata kwarara masa gdy Hanisa na jinsu tana daga É—aki tayi Æ™wafa taci gaba da ninkin kayansu tana jerawa a jakarsu bayan ta gama ta shafa mai ta zura kayanta tana kiciniyar zuge zip Hasina ta shigo ta Æ™arasa ta zuge mata tana cewa “Meyesa bakida sabo da sakin jikine Hanisa mutumin da zai cutar dakai ai daga yanayi zakaga alama yanzun ke zuciyarki ta karÉ“i abinda kikayima Abdu mutumin da yaketa É“arnatar da Dukiyarsa da Lkcnsa duk saboda ke idan Abdu yanada nufin cutarwa gareki da bai taimakeki ba haba don Allah Hanisa meyesa kike haka daraja ta rinÆ™a cin arziÆ™in daraja mana yanzu saiki tashi muje yana Æ™ofar gda”
Gabanta ne ya faÉ—i ta dubi Hasina da sauri tace “biyoki yayi?” Murmushi tayi tace “Eh cewa yayi sai yazo ya baki hÆ™r” girgiza kai tayi tace “bawan Allah Ni baimin komai ba kawai dai naji tsoro ne” murmushi tayi tace “shima tsoron da yaga kinji ne yasa yakeson ya baki hÆ™r”

 

Sunkuyar dakai tayi kamar me nazarin wani abu Hasina ta taÉ“a ta tace “kije kinsan maza basu fiye son jira ba” tama manta da yana jiranta badon Hasina tayi mgn ba ta É—auki mayafinta ta yafa tayi kyau sosai cikin gown É—in ta shadda ruwan toka abinka da Chocolate saita haskata sosai gashin gaban goshinta ya kwanto har kusan girarta sajen nan kamar na maza da suke gyarawa ya kwanta luf me laushe fuskarta kullum cikin murmushi koda yanzu ma da take cikin damuwa smaling face nata bai canza ba.
Tsayawa tayi a kusa dashi ta dubeshi tayi murmushi tace “Yanzun Abdul-Ahad saboda Ni ka sake fitowa” É—ago idanunsa yayi da suka kaÉ—a sukayi jawur ya É—an taune lips É—insa yaja numfashi ya sauke yace “Abin da tausayi da gigita zuciya lamarin yakan faÉ—armin da gaba yana sani cikin zullumi da firgici shin ya al’amarin zai kasance idan har abinda yake faruwa ya tabbata gaske wanne kallo duniya zatayiwa abin?” Da rashin fahimta ta dubesa tace “Me kenan?” Murmushin takaici yayi yace “Manta kawai Aneey amma don Allah kiyimin Alfarma É—aya” jingina tayi da motarsa tace “wacce irin alfarma Abdu?” Ƙasa yayi da gwiwarsa yace “ki daina guduna don Allah wlh bazan cutar dake ba Al’ada ce kowa da irin tasa Aneey addini ne É—aya Ni banga kuskure cikin abinda nakeyi miki ba tunda har yanzu ban nemi wani abu saÉ“anin Shari’a a gurinki ba” dariya kalmarsa ta bata ta durÆ™usa ta riÆ™e tausasan hannayensa zuciyarsu ta buga da Æ™arfi tace “bayan wannan saime?” Murmushi yayi ya É—agota suka miÆ™e yace “ki mayar dani kamar Hasina kada ki rinÆ™a É“oyemin komanki farin cikinki damuwarki dariyarki kukanki nima zanyi miki haka”

 

No comments