Breaking News

Ameenatou 12

 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#Arewabooks@Mamuhgee

#ZafafaBiyar





12

A bangaren su Alh Lameenu abubuwan sun jagule musu gabaki Daya sbd wankin hula na Neman kaisu dare,Daren ma mara kyau sbd rayuwar Omar jeden Daya rak tana Neman gagararsu dauka bayan tsare tsaren da suka ringa yi ana kaiwa rayuwar hari,


Kan Mam ya dauki zafi matiqar gaske Dan gaba Daya kaman anyi masa asiri Jin yakeyi idan ba cike burinsu sukai ba kwata kwata bazasu taba samun Kwanciyar hankali da nutsuwa ba musamman yanzu da kullum Omar seelah ne yanzu a jaridu da labarai,


Shi Lameenu matar Omar ce ta tsaya masa a Rai da maqoshi Dan kuwa jikinsa na Basu zata iya Bata musu aiki kwata kwata daga ranar data samu ciki ko makamancin Hakan Dan haka shi idanuwansa akanta suke tafara barin duniyar gaba Daya yakeso kafin su sake dawowa kan Omar din Dan haka Kai tsaye ya Yanke shawarar ayi me yiyuwa a huta kafin su zauce akan dukiyar da bata shigo hannunsu ba har yanzu kaman abin Baki sai wahala sukeyi shekaru da ciwon Rai da baqin cikin da kullum zuciyoyinsu ba lafiya.


Shi Mam ba iya matar Omar yakeson a gama Dan matsalarta yanzu ba harta Omar din Dan ya gaji da ganinsa a gabansa Kuma samansu,

Ya gaji da Jin sunan Omar jeden na shiga kunnuwansa,

Ya gaji da Jin sunan Omar jeden a kafofin yada labarai,

Shi kansa Omar jeden seelah din ya gaji da ganinsa Yana yawo Yana numfashi Yana samun mutuntawa da respect da cika idanuwan mutane,

Ya gaji da duk wani abu Daya shafi Omar ga uwa Uba 'dansa dayake tsananin son ya kasance a karkashinsa Yana tareda Omar din Yana sonsa kusan fiyeda yanda yake sonsa shida yake ubansa Daya haifesa Dan haka ya gaji a rufe chapter din Omar din kawai a huta.


Wani numfashin Jin nauyin zuciyarsa na rayuwa Lameenu ya sake Jin abubuwan da Mam din ya fada Dan Shima Kam yakai maqura,

Wani mugun nauyi ne danne da zuciyarsu duk tsawon shekarun Nan tin daga ranar da arzikinsu kasim ya bayyana a ashalawa. 



*******

Koda cikin Amina ya shiga wata Tara ya Isa haihuwa har lokacin Babu Wanda yasan dashi bayan uban cikin da Aminansa Ahmed da Aron sai su Babbah,

Duk huldarta da muamalarta dasu mum Atey Basu taba lura da ciki a jikinta ba sbd boyewa takeyi cikin hijab hakama ko gidan lameenu Basu San da cikinba sbd Aminar nada zurfin ciki sosai hakama faruwar tashi tashen hankalin Daya ringa samun mijinta ya sanar da ita kada kowa yasan da cikin shiyasa ta sake Adana kanta ma da cikin ya tsufa kwata kwata ta Dena fita koina ko gurin mum Atey din ta Dena zuwa kwata kwata sedai Haroon ne ke shigowa sosai Kuma Shima Bata taba barin yaga cikin ba.


Shirye shiryen fita da ita ta haihu a Poland Omar keyi hakama su Babbah sunacan sunata zumudi da Shirin haihuwarta Dan sunso abarta ta dawo haihuwa Amma Sam Omar yaqi yarda da Hakan dole suka hakura suka bar zancen Amma dai zasu taho idan ta haihu.


Dayake tamkar yar cikinta dadah Kejin Amina tini ta hada mata kayan fitar zaqin haihuwa da wasu maganin gargajiyar da zai Sakata samun saukin nakuda babba zai kawo mata ya dawo kafin ta haihu su taho tare.


Shi kansa babban cikin zumudin zuwan yake Dan duk yaga Omar wata sabuwar jakar arziki yake samu daga garesa Dan haka Baya ganin wahalar Nisan tafiyar kudin yake kalla da Kuma Amina dazai Gano.


Ranar asabar da asuba Babba yabar gombe yahau motar Lagos zuciyarsa cikesa zumudin haduwa da 'yar uwarsa wadda hakanan yake Jin sabuwar soyayyarsu ta jini tana qaruwa a ransa har kirjinsa na nauyi

 fatansa dai ya Isa lafiya.



Acan Lagos kuwa tin safe da Amina ta tashi takejin yanayinta Babu dadi kwata kwata,ciwon mara da nauyin marar takeji sosai gashi Omar Yana gida kwata kwata ya Dena fita a kwanakin sbd hatsarin da rayuwarsa take ciki yayi yawa Dan haka aka dakatar dashi daga fita sai an gama bincike.


Rashin fitarsa ya Saka masu jiran fitowan tasa basuda zabin Daya wuce kawo aikinsu har cikin gidansa sbd tarkonda aka hada masa a waje Yana jiransa bazai taba tsallakesaba Daya fita da tabbas sai yabar duniya a ranar Daya fitan shiyasa ma daga Aron har Ahmed sun Kai matiqar wuyan lameenu da mam sbd sun zama kamar wasu makaman kariya ga Omar din.


Batareda ta nuna halinda take ciki ba sbd kada ta damar da Omar din Amina ta ringa kulawa dashi sbd Shima Yana fama da ciwon Kai gashi masu debe masa kewa da firarrakinsu idan har suna gida to suna babban garden na Bayan gidajensu dashine ya hade gidajen nasu uku ta kofofin Baya acan suke zama suna hutawa tareda wayoyinsu hatta abincin Daren yawanci acan sukeci tare wani lokacin gaba dayansu harda iyalinsu tare suke ci cikin kulawa da shakuwa.


Mam Baya kasar Yana Poland yaje dubo Jamaal haka kawai,

Lameenu ma a ranar yayi tafiya da safe zuwa Abuja wani meeting.


A jikin mijinta ta kwanta bayan dataji karfin jikinta duk Yana Neman karewa Amma har lokacin Bata nuna masa abinda yake damunta ba.


Kwanciyarta a jikinsa ya sakashi Jin wani irin sanyi da kaunarta data cikin dayake jikinta na sake dabaibayesa musamman yanzu da kowanne lokaci zata iya haihuwa shiyasa ma ya matsu suyi tafiyar.


Qamshin jikinsa ta shaqa ahankali tana Dan rufe idanuwanta suka Danyi laushi sbd rashin kuzari.


Shi kuwa yanda take sauke numfashi ahankali cikin jikinsa tana sake narkewa ya sakashi Jin Sonta na hanasa riqe kansa Dan haka ahankali ya fara shinshinarta Yana shaqar nata qamshin Yana Jin dadin dumin jikinta a fatarsa.


Tanajin Hakan ta lumshe idanuwanta ahankali tana lafewa Dan tasan me Hakan zai haifar.

Rungumeta yayi dakyau Yana hade fuskansu guri Daya yayi kissing hancinta ahankali kafin ya hade bakinsu Yana lumshe nasa fararen idanuwan masu kyau Yana zare doguwar rigar Dake jikinta a natse.


Cikin sanyi da nutsuwa ya tafiyar da ita har sukai wata nutsatsiyar making love daga Nan bacci ya daukesa me nauyin gaske bayan yayi wanka.


Itama lallabawa tayi mararta na sake kullewa taje bedroom dinta tayi wankan tsarki ta sake wani wankan ta fito tayi sallan laasar itama ta shige daki tanason Jin ko zata iya baccin Amma Sam baccin yaqi zuwa.


Safiyya ta kira Mai aikinta datake kulawa da kusan komai na gidan tace ta kawo mata ruwan Tasha Amma Mai zafi bamai sanyi ba.


Koda Fatima ta kawo mata ruwan Taga yanayinta cikin kulawa ta tambayeta ko a kira doctor ko Akira mum Atey.


Girgiza mata Kai tayi tana sake danne abinda takeji Amma Sam Baya dannuwa Amma dai duk da haka Bude Baki tayi cikin sanyi tace


"Karki sanar da kowa zuwa anjima idan jikin baiyi sauki ba zan sanar da Daddy"


Numfashi Mai sanyi safiyya ta sauke ahankali cikin tausayin Aminar idan nakuda ce tace


"Toh shikenan Allah ya Baki lafiya yakuma saukar Dake lafiya"


"Amin" Aminar ta amsa daqyar tana Dan daurewa bayan ta amsa ruwan a dogon glass cup Tasha kadan ta ajiye.


Bayan fitar safiyya sosai tafara Jin yanayin na karuwa har Akai magrib ta tashi daga Palo Takoma bedroom tayi alwala tayi sallah,

Tana idarwa ta fito taje bedroom din Omar bayanan ya fita sallah.


Koda ya dawo a tare suka zauna palonsa sukaci abinci Wanda kadan ya Bata a baki tace ta koshi ta tattara kayan da kanta ta fita dasu.


Daga can Bata dawowa dakinta a ta shige tayi sallar ishai tayi Shirin bacci ta kwanta a dakinta sbd batason zuwa dakinsa ya gane halinda take ciki.


Yana masallaci sallan ishai Babba ya iso ba qaramin mamakin ganinsa yayi ba sbd Babu Wanda yasan yana tafe har aminan Bata saniba.


Cikin kulawa da farin ciki sosai ya tarbesa suka shigo Kai tsaye masaukinsa suka nufa sbd Amina tariga tayi bacci dukansu sun sani Dan haka babban yace abari da safe kawai tagansa har murna saitafi ma.


Ba musu Omar yayi Naam Dan Hakan Dan haka take aka kawo masa abinci kala kala aka sake gyare masa boys quarter din aka kawo cartons na ruwa da drinks aka Saka a fridge sukai Saida safe ya fice yabarsa akan Saida safen.


Har bedroom dinta yace yaga bacci ya dauketa me sanyi da nutsuwa Dan haka Bai tayarda ita ba ya kyaleta ya wuce bedroom dinsa kawai sbd yasan tana buqatan hutawa sosai Akai Akai sbd cikin jikinta.

#MAMUH#

#MAM#LAM#OMAR#SEELAHS

#JAMAAL JEEY SEELAH

#DEEP

#HAROON SEELAH

#LOVE

#CRAZINESS

#ZAFIN KAI

#AMEENATOU SEELAH


ASHNA BEAUTY SKINCARE 

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku


*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments