Breaking News

Ameenatou 25


 *_Arewabooks@Mamuhgee_*

25

Dad na ganin Hakan yayi saurin kallan Abdul Yana cewa Maza a fiddo mota a biyo bayansu da ita sbd yasan koma ya cewa Jamaal yayi zamansa ba zaman zeyiba Dan haka ya koma ciki Ya Sako jallabiya doguwa fara kal ya fito.


Koda ya fito tini Jamaal yabar gidan Dan haka Kai tsaye shi da mum da securities suka mara masa Baya zuciyarsa na nauyi da fatan kada komai ya samu 'yayansa a cikin wannan sililin Daren ace sun fita Babu Wanda yake tareda jamian tsaron lafiyarsa a cikinsu har gwara Haroon ance security Daya ya bisa

To Jamaal fa¿.


Mum kuwa duk a tsorace take ma kwata kwata sbd tsoron idan ba wani abin ne ya faru ba me girma ko zai faru,

Koma dai Menene itadai fatanta Allah ya tsare mata 'yayanta ya Basu kariya da kaucewa musiba da masifa kowace iri.


Dad daya kasa tantancewa ko canko Menene yake faruwa shiru yayi Yana fatan Isa ga yayansa cikin gaggawa kafin kome zai farun ya faru tukuna...


Bayan motar Jamaal suke hangowa Yana gudu sosai Wanda ya Saka jinin Dad fara Hawa Yana Jin zuciyarsa na wani irin tsalle da rawar tashin hankali Dan kuwa Jin yayi kaman zuciyarsa ne a cikin motar Jamaal din ana wannan gudun da ita.


Mum kuwa idanuwanta a rufe ma suke tana Jin alamun itama BP dinta ya haye sama a take.


Hanyar gidansu fadila da suka nufa ya Saka Dad Jin wani irin Abu me nauyi Yana saukowa daga maqoshinsa zuwa kirjinsa sbd ya tabbatarda idan ba ciwonta yayi ajalinta ba to tabbas lameenu ya aika su BB rufe aikin kwata kwata kafin asanar da Jamaal sakamakon Wanda Shima akwai tanadin da yayiwa Hakan Amma a cikin sanyi da cike aiki take batareda barin kowace alama ba.


Tin daga nesa wutar Dake cin gidan sosai suke ganinta

Take jikin mum ya dauki rawa hawayen tashin hankali na ciko idanuwanta sbd Jamaal kada yace zai shiga gidan.


Dad da Shima dukkanin jikinsa ke cirewa sbd wannan tsoron tini yace ayi parking cikin daga murya.


Ko gama parking baayiba Dad ya Bude motan ya fito yayi gurin Jamaal da sauri Yana Kiran sunansa hankalinsa tashe sedai Jamaal din Baya jin komai fadila kawai dayake buqatan Gani a hannuwansa.


Haroon da siddeeq ne suka hango zuwansa da gudu Haroon yayo gurinsa ya tareda tareda rungumesa sosai daidai isowan Dad idanuwansa kaman zasu fado sbd tashin hankali da sauri ya rungume Jamaal din ta Baya Shima Yana Jin zufa na tsinko masa.


Jamaal zare jikinsa yakeson yi Amma sun masa wata irin kyakkyawar runguma Haroon na cewa


"Fadila is safe siddeeq ya fito da ita"


Wannan kalaman ne suka Saka Jamaal din jikinsa ya saki tsawon minti Daya kafin ya dago idanuwansa jajir Yana buqatan ganin fadilan.


Ambulance ta asibitinsu ce ta iso cikin gaggawa aka dauki Fadila wadda batasan Ina kanta yake ba tareda umma wadda itama take a sume sbd hayaqin Daya bugeta.


Motan kashe gobara ce itama ta iso daidai lokacin sukuma suka bar gurin zuwa asibiti cikin gaggawa.


Siddeeq barinsa Akai tareda mutane da masu kashe gobara harma da Police da suka iso gurin cikin tashin hankali sbd baba Dake cikin gidan baa fiddosa ba,


Mum asibiti suka marawa su Jamaal Baya itada da Dad Wanda yakejin Yana dawowa hayyacinsa daidai sbd barin yayansa gurin Dan motan Haroon ne bayan ambulance din sukuma suna bin tasa motar.


Ana Isa asibiti cikin gaggawa likitoci suka amshi fadila da umma aka shige emergency dasu 

Haroon kuwa da Dad Jamaal din suka zauna tareda dashi Dan basa karfin gwiwa.


Mum da ita aka shiga emergency din Dan taimakon gaggawa fadilan take buqata sbd Bata tareda oxygen nata tini ya fizge yana can.


Zaman jiran tsammani me azabar gaske sukeyi dukkaninsu tin daga Jamaal din har Dad da Haroon,


Haroon sai Kai da kawo yakeyi Yana Jin kaman ya yayewa Dan uwansa abinda yake ji.


Sai asuba likitocin suka samu shawo kan fizgo numfashin fadila aka Saka mata wani oxygen din bayan mum ta tantancesa.


Umma kuwa Daman tini ta farfado Dan Daman hayaqi ne ya sumar da ita Amma dayake mijinta da yarta ne a ranta tini ta farko cikin sanyin jiki da fargaban baba da akace Yana can tareda siddeeq ita Kuma fadila tana asibitin tareda ita.


Dad da mum ne suka koma gida bayan sallan asuba suka bar Haroon tareda Dan uwansa.


Suma bayan sallan asuba dubo fadilan yai suka dawo office dinsa anan yayi shiru Yana tinanin yanda zasuyi su sanar da umma gawar baba na asibitin.


Siddeeq ya kalla cikeda kulawa da tausayawa Dan Shima maraya ne gaba da Baya su baba dinne gatansa danginsa yanzu baba ya rasu.


Har karfe tara na safe suna asibitin Kuma Basu sanar da umma komai ba sai guraren goma suka taho dakin datake Jamaal ne Kai tsaye ya sanar da ita rasuwan baban cikin dacin zuciya da tausayi me tsanani.


Numfashi ta sauke ahankali me zafin gaske batareda ta motsa ba sbd jikinta ya Bata Hakan Kuma zuciyarta tini ta amsa Hakan ta karbi jarumta.


Dago jajayen idanuwanta dasukai jajir tayi ta Kalli siddeeq Dake Hawaye sosai zuciyarsa na tarwatsewa.


Cikin karfin hali ta Bude Baki ahankali tace


"Haka Allah ya kaddaro Kuma na amsa wannan hukuncin na ubangiji,Allah yaji qansa yayi masa Rahama ya bamu danganar rashinsa."


"Amin" dukkaninsu suka furta cikin damuwa da sanyin jiki.


Karfe goma da Rabi Akai janazah dinsa aka rufesa suka dawo.


Kaman yanda yake ayau din zaa daura aurensa da fadila baa daga ba Dan haka bayan karfe biyu na Rana aka halarci masallacin da zaa daura musu aure.


Cikin fararen kayanda suka bayyanarda kamanninsu sosai shida Haroon suka fito tareda mahaifinsu Wanda Shima fararen kayan ne a jikinsa irin na 'yayansa Wanda aka zuba kudi kaman baa San darajansu ba aka Siya kayan aka Dinka.


Qamshinsa daban yake Dana kowa Dan haka take qamshinsa ya doke nasu nasa kadai ake ji Kuma a Hakan cikin Baya tattareda walwala ko Daya sbd halinda matarsa take ciki duk da haka kawai saukin da Basu tsammata ba yazo mata da safen duk da batada karfi ko kadan har lokacin Amma ta Bude idanuwanta sosai tayi magana dashi tareda nuna masa ta samu karfinda inshallah zata iya adon aurensu da zaayi a yau din.


Karfe biyu daidai Aka daura masa aure da Fadila kaman yanda yake buri da fata ta tabbata cikakkiyar hankalinsa,matar Dr Jamaal Mamman seelah.


Bayan daurin auren Yan jarida da media da ba'ama San ya Akai suka sani ba suka karaso gurin sedai kafin su samu Daman daukan hotinansa yabar gurin batareda ya tsaya komaiba sedai Haroon ne ya tsaya a amatsayin Jamaal din yana miqa godiyarsa ga wainda suka halarta Yana amsa adduoinsu batareda ansan bashi a gurin ba Dan hatta su Dad din Basu dauka Haroon bane Jamaal ya tafi.


Siddeeq ne yake Jan motar Jamaal din har suka Isa asibiti zuciyarsa wani fayau yake jinta jikinsa na sanyi kalau batareda yasan wane irin yanayi ne yakeji a jikinsa ba.


Suna Isa asibitin kusan dukkanin wani likitan Dake asibitin Yana dakin fadila cikin tashin hankali da gaggawan cetan ranta kowa na nuna kwarewansa Dan sanin mahimmancinta Mai tsananin girma ga Dr Jamaal din.


Hatta mum dinsa tana dakin cikin nuna kwarewanta da son cetan ran sirikitarta wadda rashinta zai taba rayuwar danta fiyeda yanda suke tinani.


Ganin umma zaune bakin dakin idanuwanta jajir dukkanin jikinta a Sanyaye zuciyarta tayi wani irin nauyi da kirjinta ke Neman kasa dauka.


Dakatawa yayi cak bakin Kofar dakin ganin yanda nurses ke fitowa da gudu suna komawa cikin bawa abinda sukeyi mahimmanci me girma.


Siddeeq ma kasa motsawa yayi daga inda yake tsaye zuciyarsa na bugawa da karfi ya juya Ina Dr Jamaal din yake ya kallesa da jajayen idanuwansa Dake sauyawa da fargaban abinda suka tarar.



Kasa motsawa Dr Jamaal din yayi tsawon mintina biyu Yana Jin dukkanin wani sanyi na gauraye gangar jikinsa kafin ya daga kafafunsa ahankali ya Isa kofar dakin ya Bude ya shiga daidai kunnuwansa na dauko sautin maganar Dr zayyan.


"Time of Dead 3:06"


Innalillahi wainna ilaihirrajiun" shine abinda mum ta fada jikinta a matiqar Sanyaye zuciyarta na shiga wani irin sanyi da mutuwar jiki me tsananin gaske.


Sauran likitocin ma gaba Daya jikinsu sanyi yayi musulman ciki suna ambatar 


"innalillahi wainna ilaihirrajiun da allahu Akbar"


Kafiran ciki kuwa tausayinta Dana Dr Jamaal ne yake rufesu sbd tasha wuya sosai itama a iyama lokacinda ta fara zuwa asibitin kadai bare rayuwarta ta Baya.


Ficewa likitocin suka fara ganin Dr Jamaal din a tsaye bayan sun rufeta har fuska sun gama rubuta komai a file dinta anyi signing anrufe an ajiye a gefe shikenan ita ta huta da gwagwarmayar duniya.


Mum dinsa ce kadai ta rage ta tako ahankali batareda ta iya cewa komaiba sai hawayen Daya ciko idanuwanta Yana gangarowa ta rungumesa ahankali cikin mutuwar jiki tana basa hakuri hawayenta na Kara gudu.


Fashewan kukan umma me sautin daya sake karya zuciyar kowa ne ya sauka cikin kunnuwansa take ya rintse idanuwansa dasukai wani mummunan ja yanajin dukkanin zuciyarsa na kakkaryewa tana watsewa.


Siddeeq ne ya rungume umma Yana tarota jikinsa sbd kukan datakeyi hadda na mijinta data rasa a ranar kukan Bai fitoba sai yanzu data rasa yarta taji abinda ya dunkule a zuciyarta ya fashe mata.


Wani irin kuka me cin Rai da qunci me tsanani takeyi sautinsa na karya dukkanin zuciyoyin sauran likitoci da Jamaar Dake gurin Amma Babu me iya cewa komai sbd tana buqatan yin kukan.


A ciki ma mum ce keyiwa Jamaal din kukan dashi zuciyarsa Bazata iyaba sbd Jin ma yakeyi baida sauran emotions kwata kwata bayajin komai face dutse a zuciyarsa.


Labarin na Isa gurinsu Dad da Haroon gabaki dayansu asibitin suka dungumo cikin tashin hankali musamman Haroon Dan kuwa JAMAAL ne a ransa,

Jin yakeyi rasuwar fadilan Shima tana gigita kansa da nutsuwansa dan haka a rikice ko Gani sosai bayayi suka iso asibitin.

##MAMUH



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

 _Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments