Breaking News

Tsutsar nama 40

*_Typing📲_*










   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚_


_____________


_ADVERT👇👇_


MKBEES PERFUMERY 

_(GIDAN KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_



_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, 

_KAI DAKA FESA KAJI DADI NAKUSA DA KAIMA YAJI DADI.TOH KU MAR-MATSO KUSA_


_MUN KUMA ZUWA DA  KAYAYYAKIN_KAMSHI MASU SANYA NUTSUWA DA KWANCIYAR HANKALI


_*KU GARZAYO MKBEES PERFUMERY 

_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN  CHADI DA SUDAN  AKWAI OIL PERFUMES,AIR FRESHNER, CARPET SPRAY DA TURARUKAN MOPPING DANA WANKA DANA  GADO,LABULE DA KUJERU , BANDAKI DA DRAWER .


_AKWAI TURAREN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DAHANA TSAMIN GASHI DA KUMA LAUSHI. AKWAI HODAR HAMMATA ME TAIMAKAWA WAJEN HANA WARI DA TSAMI ACIKIN LOKACIN ZAFIN NAN,AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYEN DAYA DAYA. •_


_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._


_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN MKBEES PERFUMERY. 

KO BAKU SIYA KAYA BA KUYI SAVING NUMBER DINTA KUFADA MATA TAYI SAVING NAKU DOMIN KOYON DUBARUN KASUWANCI KYAUTA A STATUS DINTA.


_NAMBAR WAYAR SU: 07011113951,07032456061.

INSTAGRAM :Mkbees_perfumery. 

_YOUR NUMBER ONE PLUG FOR KOMAI KAMSHI A TRIAL WILL CONVINCE YOU.


_______________



.......A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?. Aikin naku ya wuce kisan kai da kidnapping harda sharri kuma. Lallai tatsuniyar gizo da ƙoƙi kenan young man, kasan kuwa gaibu ce dan hikimace kawai irin ta masu iya zance da rubuta hikayoyi. Idan har ka yarda ba'a mutuwa a dawo, to ka ɗauka abinda duk yake a hannun Samraah Gwarzo mallakinta ne ita kaɗai, ko a mafarki bazan taɓa cinikayyarsa da wani ba. An gaya maka nima faƙiriyace bana neman na kaina ne da zan zauna neman a bani fansar kuɗin jinin mutane akan video?. ALLAH ya sawwaƙe, Banyi lalacewar baƙar tasa ba ai, banga kuma wata dukiya da wani zai tara taja hankalina ba dan nima dai kasuwancin nan inayinsa. Ɗan jarin nan na dubu ashirin da ake rainawa na tara wataran sune zasu koma miliyan dubu ashirin ɗin. Dan haka kuma nema wanda ya amsa kuɗinku tun wuri amma ba ɗiyar Abdul-wahab ba. Idan kuma kaine ke yawo da hankalinsa ka faɗa masa gaskiya inma dan kaga baya jin Hausa ne, oho can dai muku matsalarku ce ma wannan dai. Dannni idan har Yaya Musaddiq da Mansoor na numfashi a duniya na maka alwashin nan da kwana takwas iyanzu ina can a tsakkiyar dangina suna shagalin taron bikin aurena tare da ni, yayinda ku kuma zaku kasance a police station kuna amsa tambayoyi”.

       “Yaro bai san wuta ba sai ga taka”. Yaron nasa ya faɗa 

   “Babba bai san yaro ba sai ya latsa”.

Na bashi amsa nima a kausashe ina sake balla masa harara kamar manyan idanuna da ke nuna yanayin bana jin daɗi zasu zubo ƙasa. Juyawa nai shima ogan nasa zan hararesa sai naga ya zuba min ido kamar wanda yay zurfi a tunani. Ban fasa hararar tasa ba, dan haka na maka masa kawai na ɗauke kai ina ƙunƙuni ƙasa-ƙasa (Garama ku sakan tunkan kuja a saka sunanku cikin jerin manyan ƴan ta'addan duniya dan wlhy tona muku asiri zanyi ni babu ruwana). 

      Tsawa yaron nasa ya daka min alamar ya jini, duk da na tsorata amma mai kicin-kicin da fuska naƙi nunawa. Kuma bakina bai bar motsin ƙunƙuni ba. Wani shegen murmushi ogan nasa da tun maganar farko da yayi bai sake nuna yama san da zaman mu a falon ba ya saki. Tare da lumshe idanunsa cike da salo luuuu ya kuma buɗesu a slowly warrr. Batare da ya sake furta komai ba ya miƙe abinsa ya nufi wata hanyar gilashi data mamaye kusan bango guda na falon har kana iya hango ƙyawawan korayen ciyayin dake ta waje da ga nan, fita yay abinsa cikin wani irin takun mazantaka da nuna ƙarfin iko.....

        Wata ƴar siririyar dariyar da yaronsa ya saki ta sakani kallonsa. Ya rumtse hannunsa tare da nuna babban yatsar hannunsa kasa👎 yana wani ɗaure fuska ya furta, “Lallai na tayaki jaje ƴammata. Dan kin taro babban match da baki da defenders balle ƴan kallo. Tunda har kika bari boss ɗina ya taya wannan wasan sai kinyi dana sanin da sai tafi biliyan a cikin koguna biliyoyi. Dan shi giwa ne baya WAIWAYE. Sannan zaki ne ba'a gaba da gaba da shi. Ki jira TAKUN FARKO na wasan kawai, tun anan zaki raina kanki.”

       Baki na laɓe nima, tare da watsa masa harara. Cike da tsiwar ƙarfin hali na ce, “Shi kaɗai ka sani da dukkan salonsa. Abinda kuma ni zan iya sirrina ne, kaga kenan tsakanin ni da shi ba'asan maci tuwo ba sai miya ta ƙare a wasan. Dan haka ina baka shawara tunda kaine abokin sharrin nasa. Ka gaya masa da gaggawa ya maidani inda kuka saka aka ɗakkoni, idan ba haka ba, wlhy sai kunyi dana sanin shiga sabgata. Dan zan ajiye muku tarihin da bazaku sake gwada cutar da wani ba bayan ni. Koda kuwa kasheni kukayi fatalwata bazata barku ku zauna lafiya ba. Dan nasan abinda kuka iya kenan kashe mutane kuyi tsafi da jininsu ko”.

        Dariyar kularwa ya saki da faɗin, “Irinku dama boss yafi buƙata a wasa. Kema shaida ce tunda a gabanki ga faɗa da bakinsa. Tunda kin shirya game ɗin ga fili ga mai doki, ni dama nawa shawara ce. Kuzo ku maidata inda kuka ɗakkota”. Ya ƙare maganar ƙarshe cikin ɗaga murya. Baima gama rufe baki ba sai ga garadan ɗazun sun shigo kuwa..

     (Tofa, Samraah miya faru kuma bayan hakan?).

  Humm Bily komai ma ya faru, dan zan iya ce miki a wannan gaɓar ma ne labarin ya ɗauki dai-dai saitin inda kowa ya kamata ya fahimci raunin daya taɓani da kuma nasarorin dana samu. Dan komai da kika ji a baya dai-dai yake da sharar fage. Konace shimfiɗar labarin. Amma kundinsa wannan gaɓar itace SHAFIN FARKO. An maidani ɗakin da aka fiddoni kamar yanda yaronsa ya bada umarni. Da ga haka ban sake ganin kowannensu ba. Sai dai ana kawo min abinci sau uku a kowanne rana. Kamar yanda na kasance a kulle a wancan gidan nan ɗin ma hakanne. Sai dai akwai masu tsarona anan, kuma na nan sun ma fi nacan firgitarwa. A ƙuntace nake matuƙar ƙunci, ga ciwon jiki dana zuciya. Ga kewar ahalina data masoyi. A kowane cikar minti ɗaya na agogo sai na lissafa sauran daƙiƙun da suka rage na cikar ranar aurena. Hakan yasa a duk sanda tunani ya nema fasan zuciya zaki sameni ina karatun Alkur'ani ne. Ina jin sauƙi sosai a raina, bayan na koma yin salla ma Alhamdullah na sake rungumar ibada ta. Dan akoda yaushe cikin kaima UBANGIJINA kukana nake. Ina kuma jin yaƙinin zai karɓa min.. Zakisha mamaki idan nace dake maganar da yaronsa yay na cewar na buƙaci su bani 500m kuma sun bada 250 a cewarsu ban wani sakata a raina ba. Danni a nawa wautar kawai sun faɗane bisa raɗin kansu da son min barazana ne dan na basu abinda suke son, dan haka na cigaba da harkar gabana kawai na manta da duk wani gargaɗinsu balle zuciyata ta fara min wani hasashe mai muhimmanci daya kamata ace nayi, ban san rashin yin shine zai zame min babban kuskure ba kuwa. Dan da'ace nayin maybe da abubuwa basu kasance a wani matsayi daban taɓa tsarama kaina ba bisa ƙaddarar rayuwa. Karna cikaki da zance muje zuwa dai.....


       💞☞💞☞💞☞💞


  

      “Ranka ya daɗe zan faɗi gaskiyar abinda ma sani. Sai dai yanda ka fahimci al'amarin sam ba haka yake ba. Wlhy wlhy duk abinda zan faɗa maka shine gaskiyar abinda ya faru. Tsoro ya hanani faɗar gaskiya tun ma a farkon fara case ɗin. Amma na gwada yin hakan tun sanda naji zancen ɓatar Sam-G da kuma kama Salis da akai. Ni bani na saceta ba, hasalima ban san ita za'a ɗauka ba. Wanda kuma ya ɗauketan wlhy ban san kidnapping ɗinta zaiyi ba. Kamar yanda na sanar ma abokina Isa da gaske na amashi mashin ɗin Salis ne a hannunsa domin zanje amsar sako tasha da aka turoma Mamana daga Maiduguri, da kuma tayoyi da za'a sakamin a nawa daya samu matsala. Na fito titin anguwarmu kaɗan wani bawan ALLAH ya tsaidani, banyi niyyar tsayawarba, saboda ina da uziri, ban fitoba kuma domin yin aiki ba. Gashi kuma safiya ce sosai dan ko haske gari bai gama yi ba. Sai dai ganin dattijo ne mutumin yasa naji tausayinsa. Dan harma na gotashi na dai dawo, tambayarsa nai inda zaije, dan naji ko yayi dai-dai da inda na nufa. Amma sai da ya shigo ya zauna yake gaya min. Ga abinda yace min da yasa na ɗaukesa tilas badan naso ba. (Yaro dan ALLAH ka taimaka min, Yakasai zanje, yarinyatace take da lalurar aljanu, jiya da dare muka nemeta muka rasa, sai ɗazun nan da asuba ƙanina yay kirana tana gidansa ta kwana acan Yakasai ɗin. To munsan zata iya barin nan ɗin akoda yaushe, kuma idan suka kaɗata bamu san ina zataje ba. Yanzu ma ko gidan bazamu ƙarasa ba zamu ɗan tsaya ne a kan layi data fito mu mata wayo, zan kira ɗan uwanta da zarar mun ɗauketa sai yazo ya ɗaukemu dan in kai tsaye ne bazata yarda ta shiga motarsa ba, amma idan na shaƙa mata maganinta zamu samu nasarar yin hakan). Yanda dattijon ke magana yasa na amince da shi, dan sam baiyi kama da wanda zai yi ƙarya ba, gashi kuma a cikin kamala. Lalura kawai daya kira yasa nai tunanin taimaka masa, dan nima ƙanwata nada irin makamancin lalurar, na kuma san irin tashin hankalin da muke shiga. Cikin nuna damuwa nai mata addu'ar samun lafiya, sannan na sanar masa gaskiyar ba aiki na fito ba, amma idan bazamu jimaba zan taimakesa, sai dai idan ta jima bata fito ba zan sakashi a wata napep ɗin ni na tafi uzirina dan abokina na jiran napep ɗin sa. Babu musu ya yarda da hakan har yana jeramin addu'oi ga hawaye yana faman yi. Ni dai na bashi haƙuri muka ɗauki hanya. Mun isa Yakasai, shine kuma ya nuna min inda zan tsaya, shi kuma ya fita ya maƙale a ɗan nesa dani. Nayi zaman kusan mintuna ashirin duk naji na ƙosa dan babu abinda nake sai faman tsaki, ina ma niyyar barin wajen ne sai gashi da saurinsa yake sanar min gatanan zuwa, dan ALLAH na taimaka kada na bari ta shiga ko wane mashin sai nawa. Yanda naga yana rawar jiki ga hawaye yana sharewa da gefen rigarsa yasa naji tausayinsa, duk kuma yanda ya tsara haka nayi. Mun fito a wajen mai saida lemo da aka tsinta wayarta daka faɗa yace na tsaya ga ƴaƴanta a mota.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments