Breaking News

Diddigar Kaya 10


 DIDDIGAR ƘAYA 

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


                      *Shafi Na Goma*


*PAID BOOK*


*LAST FREE PAGES*


Babu yadda wannan malami da ya shiga tasku ya iya haka ya rubuta don tabbas ya san ƙaramin aikinta ne playing wannan audio wa school authorities daga nan kuma ya san aikinshi gabaɗaya ya rasa, time da ta bashi na cika ta zo ta karɓa tana yi mishi murmushin wulakanci irin nata.


Aiko tana isa gida Momma ta kaiwa don ta san daga momma ta amince to Baba Prof ma ya amince ta ci sa'a kuwa babu wadda ya hanata tafiyan suka shirya suka wuce akan ma Gombe ne bayan flight aka biya musu zuwa Abuja.


Karfe biyar na yamma suka sauka a birnin tarayya Abuja Motoci har biyu suka zo É—aukar su Dukda duka duka su ukun ne kuma mota É—aya suka shiga É—aya na take musu baya, babban masaukin baÆ™in da har gomnoni da kusoshin gomnati ke sauÆ™a matukin motar tasu ya taka birki, masaukin baÆ™in ba baÆ™on su  bane hakan yasa suka fito kowacce janye da karamar akwati mai taya suka yi ciki.


A reception suka haÉ—e da samarin sakina da rahama suka tarbe su har zuwa masaukin su me É—auke da parlor da kuma É—aki daga gani ka san na manya ne, a kujera ta yada zango tana bin su sakina dake lafe jikin samarin su da sunan oyoyo da idanu kan ta taÉ“e  baki ta maida kanta ga wayanta tana cigaba da dannawa.


"Ƙawarmu kiyi ordering duk abunda kike so za'a kawo bari mu je mu zo"


Najeeb yaron É—an majalisar tarayya kuma consultant saurayin sakina ya faÉ—a, kai kawai ta É—aga musu su sakina suna daga mata hannu kan suka fice.


"Wallahi rahama kawarkun nan ta cika ji da kai kamar Æ´ar sarki"


Sakina ta taÉ“e baki tace 

"kuma ba Æ´ar kowa ba ba"


Saurayin ta suhail wadda É—a ne ga ministan lantarki kuma engineer yace

"ya zaki ce ba Æ´ar kowa ba ina gidan Prof kaka ne gidansu? Waye be san su ba a Nijeriya?"


Rahama tace 

"sani daban wayewa daban, gidan kaman rijiya haka yake don ta samu mun fito da ita shine fa ta fimu feleke, ka ga kuwa manyan guys da take Juyawa? Iskancinta na da girma wallahi"


Anan suka bar maganan suka cigaba da harkokinsu na baÉ—ala tsantsan rashin ilimin addini da rashin tarbiya suke nunawa a Filin Allah, ba kuma su damu da su su huÉ—u ne É—akin ba.


Basu dawo masaukin su ba se dare lokacin fita partyn, sun sameta kwance ɗaure da towel tana bacci, tashin ta suka yi kan suka fara shiri suna hiran irin ɗauke hankali da suke son yi barin ma suhail da yace Zubair din jiji da kanshi na dayawa kuma en matan da zasu je wurin are high class hakan yasa suka ƙara zakewa kowacce ta fita fesss kaman ka sure ka gudu.


Wani arnen material lace aka yi mata fitted gown dashi wadda ya fitar da duk wani surarta yadda ya kamata ko numfashi me kyau bata yi amma dayake har ya fara bin jiki bata damu ba, kanta ko É—an kwali babu se wani gyara da ta mishi jelar na reto a bayanta wani high hill shoe da inches É—inshi ya kusa huÉ—u ta saka ta rike wayanta suka fito jewelrys É—inta se dauke idanu suke.


A cikin hotel É—in ne za'a yi sede ta chan baya, ba su isa wurin ba saida aka fara da É—an jimawa.


Kwas Kwas Kwas haka karan takalmansu ya karaɗe ilahirin wurin wadda hakan ya saka celebrant ɗin da ya fara bayani cikin ƙasaita da ji da kai dakatawa.


Chak ya tsayar da fitilun ganinsa bisa kanta, Grey eyes ɗinta da ya ji liner se ɗauke hankali yake, Zubair be taɓa ganin halittar da ya tafi dashi a kallo ɗaya ba sai Akan wannan, don kasa cigaba da bayanin godiyan yayi Dukda su Fauxa har sun sama wa kansu mazauni, class ɗin yarinyar ya burgeshi kwarai don har ta zauna kaman bata san ta fisgi hankalin mutane dayawa daga wurin ba.


Taɓa shi da suhail yayi ya saka shi farga da ya ɓace a duniyar fauxa Dukda ko sanin ta be yi ba, bayanin ya karasa aka mishi tafi.


Yana ba da mic ya koma ya zauna mazaunin shi yana kallon suhail yace 

"wacece wanchan? Na ganta da buduruwarka"


Suhail yace 

"Zubair in zaka É—auke kwalamarka kan wannan ka É—auke sbd ta fi karfin duk yadda kake tunani"


Wani banzan kallo Zubair ya yiwa suhail ze yi magana Najeeb yace 

"kaman yadda suhail ya faÉ—a nima shawaran da zan baka kenan..."


A fusace yace

"saboda ita ɗin ƴar waye kenan? Ta kaini? Ni da na Haɗa sarauta da mulki? Karka manta duk wata kwangila Indai daga fadar shugabar kasa ze fita hannuna yake zuwa, ina juya dala da euro so babu wannan magana, ko ka manta ni ɗin Burin kowacce macece da ta san rayuwa da abunda ya kunsa? Kalli ku ga duka en matan da suka taru anan sun yi ado da kwalliya ne sbd su burgeni har su sace zuciyata kuma kun san babu wacce babanta yake ƙaramin mutum me kuke min tsoro? har ta isa ta yarfa ni?"


Suhail ya ce

"ita ba ƴar kowa ba amma fa uncle ɗinta babu wadda be yi mishi tayin matsayi ba daga mulkin har sarauta ya ƙi, in kana jin Prof kaka to ƴar gidan ce, yarinya ce amma tana da kwarjinin manya daga jininsu ne"


Shiru ya É—an yi, kan ya ce

"ni kuma zan baku mamaki akan yarinyar nan Dukda aurenta nake son yi amma na muku alkawari kan ta bar Abuja se na saye zuciyarta da gwagwalan laffuza da salo na"


Ihu suka mai, suka yi dariya a tare yana kara cin alwashi akan Fauxa É—in.


Kowa kan shi yake serving sede Fauza bata motsa ba bare ta tashi ta É—iba, kanta na kan waya tana kallon wani necklace da yayi mugun tafiya da ita..


"Wow wannan tayi! gashi kuwa ba ƙaramin haskata za kiyi ba da zaran ta hau wuyan ki"


ÆŠagowa tayi ta kalleshi ba laifi kyakyawa ne ajin karshe, magananshi kuma ya É—an bata dariya Tace cikin basarwa 


"sai kuma ya kasance bana neman tayin zaɓin kowa kan abunda na san ze yi min kyau ko akasin hakan"


Yayi murmushi ya ce 

"in kin min izini zan iya zama?"


Tace 

"Allah sarki ai bani da hurumi da kujerun nan É—in don nima a gayyar soÉ—i na zo"


Yayi murmushi me kyau yace

"Ai zuwanki ya fi min zuwan shugaban ƙasar Ingila don ni kaɗai na san irin farin cikin da na shiga da ganinki"


Ta É—an É“ata fuska tace 

"farin ciki??"


Yace 

"yeah, farin cikin na samu matar aure"


Kanta ta mayar kan wayanta kaman ba ita ce tayi tambayar ba, kaman ma bata ji amsar da ya bayar É—in ba, shima shiru yayi yana jan class É—inshi.


Sun shafe mintuna kusan talatin kan yace 

"Wow! Zaki yi kyau da sarauta"


Idanu ta É—ago ta watsa mai kan ta É—aga tana kallon mutanen wurin da aka fara watsewa ana komawa cikin hadaddiyar club na hotel É—in inda anan ne asalin chasun, nan an rage lokaci ne da É—an abinci da snacks. Ba tare da ta ce mishi komai ba ta sake maidawa kan wayanta.


"Princess let's go in its time for the real fun"


Mikewa kawai tayi suka jera, yace 

"sunana Zubair turaki am the celebrant, dukda baki tambaya ba"


Se sannan tace 

"oh happy birthday"


Yace

"thank you! Where's my gift?"


Dan murmushi tayi kawai daidai lokacin suka shiga cikin club É—in da mata suke ta rawan sanda kida na tashi sai de ba sauti sossai.


"What do you want as the gift?"

Tayi mishi tambayar.


"Just ur heart, kina ban zuciyarki kin yi kyautar da ba zan taɓa manta ta ba"


Dariya tayi gayen nan na da aiki, basu sake magana ba saboda kiÉ—ar da aka sauya sauti har wani baya jin maganan wani ana ta rawa color bulb na Juyawa daga blue zuwa yellow zuwa red.


Cikin ihu yace 

"Do you mind a drink??"


Itama da karfi kaman yadda yayi tace 

"Non-alcoholic"


Kallon mamaki ya mata, kan ya juya hanyar toilet da ya hango suhail yayi yace

"bata shan komai?"


Kai suhail da yake ba a hayyacinshi ba ya gyaÉ—a mai, murmushi yayi kawai ya juya ya tafi gaban bar, inda ya sa aka yi mishi mixing kalar fine wines da yake sha, ita kuma yace coke, ana tsiyaya rabi ya sa aka sa mata whiskey marar taste yadda ba zata ji ba, ya riÆ™o ya kawo mata tace 

"thanks!"


Shan Nashi ya fara yana ganin yadda take rike da nata tana rausayawa a hankali, bakinta na bin waƙar dake tashin.


Suuu ta tafi zata zube a sadda ta gama shan drinks É—in yayi hanzarin sa hannunshi ya rungumo kwankwasonta cup É—in hannunta ya faÉ—i ya fashe, murmushi yayi yana shafa fuskanta da ÆŠayan hannun nashi yana Juyawa da ita.


"Ashe jininki bashi da ƙarfi" ya faɗa a kunnenta in a whisper.

Sossai ta bugu tun tana luuu luuu har ta fara ihu da ƙarfi kaman wacce ke jin daaɗin club ɗin ta fara rawa sossai yana rike da ita yana ƙare mata kallo cikin murmushi, be taɓa Tunanin birthday ɗin shin nan ze zama fun haka ba se yanzu.


Sun yi rawa har sun gaji en mata dayawa sun kwashi takaicin ganin shi da ita, ita kam gabaÉ—aya ta rasa hankalinta.


Da sauri sakina ta riÆ™o hannunta tana Kallonshi tace 

"Zubair kayan maye ka sa mata?"


Sakina tace 

"mun shiga uku! Haba Zubair ka kuwa san me ka aikata?"


Yana smirking yace 

"normal ne fa, am very sure zata ji daaÉ—in hakan idan ta dawo hayyacinta"


"me nufin ka?"

Suhail ya jefa mishi maganan, basu kula da surutan ba..


"Guys calm down ba fa abunda nake nufi, kuma babu abunda zan mata..! A hankali time É—in da kuke yiwa tsoro ze zo, am very sure nan kusa da kanta zata neme ni da soyayyar abunda kuke yiwa tsoro it's just a matter of time"


Ya karashe yana dariya sossai, ajiyar zuciya suka sauke sakina tace 

"ka bi a hankali wallahi baka san kalar haukan Fauxa bane"


Riko ta yayi yana cewa

"kuyi abunda ke gaban ku"

Yana kai nan ya janye ta suka fice.


Da sassarfa yake sauƙowa daga matakalar jirgin idanunshi kan tsadaddiyar agogon dake ɗaure a farar fatanshi, sanye yake da baƙin wando da kuma farin shirt wadda kallo daya zaka mishi ka san pilot ne, baƙin necktie ɗaure a wuyan shi, jacket da karamin brief case a hannun hagunshi.


Sauƙar su kenan daga Adis Ababa, da sauri aka buɗe mai gaban wata Prado dake Parke don shi ya shige, drivern dake sanye da kaya me tambarin jirgin da ya tuƙon ya ja suka fice da gudu daga airport ɗin.


"Sir ina muka nufa?"


ÆŠan kallon hanya yayi kan yace 

"transcope hotel"


Saita hanya yayi saboda shirun da garin ya É—auka yayi ta tsuga gudu bai tsaya ko ina ba se harabar na transcope, sauÆ™a yayi yana furta 

"thanks" 


Ciki ya nufa ba tare da ya jira amsar drivern ba, daga yadda yake tafiya zaka san wannan É—in zakin namiji ne, fuskanshi a kame sai de be hana kyaunshi bayyana ba.


Reception ya dakata ya biya room VVIP, ya karbi key ya nufi elevetor daidai lokacin su kuma sun bi ta bayanshi sun shiga, yana shirin rufuwa yayi saurin saka hannu tare da sanya kai ciki...


**Tou Readers anan na kawo karshen free pages ɗin Diddigar ƙaya da Naira ɗari uku kachal zaki mallaki sauran ki sha karatu cikin kwanciyar hankali**


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments