Breaking News

Diddigar Kaya 11


 DƘ


11


Sau ɗaya ya sauke ganinshi kan su ya ɗauke kai yana jan tsiririn tsaki, yana rasa me matasa suka ɗauki baɗala suka ɗaurawa kan su a yanzu, in har kana da kuɗin kama suit a hotel ɗin nan kayi sharholiya why not ka ajiye ka fara shirin aure ko mata nawa ne? Duk takaicin shiga cikin elevator ɗin ya cika shi, a hawa na sha ɗaya elevetorn ya tsaya tare da buɗewa.


"Babe mu je ko?"

Zubair ya faɗa yana ɗago Fauxa da gabaɗaya jikinta ke sake, ture shi tayi ya sake saurin tarota ganin tana shirin faɗuwa garin haka ne gashinta ya sunce ya rufe mata fuska daidai lokacin da Faizan ya sake waiwayowa ganin suna ɓata mai lokaci.


A hannunta dake cikin na Zubair ya fara sauke idanu kan ya kai jikinta zuwa fuskar ta da gashi ya rufe kana ganinta ka san ba karamin buguwa tayi ba, Jan ta Zubair yayi ganin elevatorn na shirin rufuwa, da wani irin disgusting look yake bin su har suka fita, ita da fuskanta ke facing elvetor ɗin ta sa hannu ta gyara gashin nata daidai lokacin da elevatorn ya gama rufuwa.


Gabanshi ne ya faɗi, ko tantama babu wannan fuskan ɗan gidansu ne Dukda kai tsaye baze ce wacece ba amma tabbas wannan yarinyar tana da alaka da gidansu, floor na 13 elevatorn ya kaishi haka ya fasa sauka ya sake danna na sha ɗaya, da sauri ya fito daga elevatorn yana dube dube, sai de babu su ba alamar su, ya jima tsaye yana tunani a wurin kan ya koma ɗakin da ya kama, zuciyarshi na faɗa mishi Fauziyya ce sai de taya zata bar gida ta zo har Abuja babu wadda yayi noticing kuma ta sha kayan maye? With this her young age? Kai be amince da abinda zuciyarshi ke faɗa mai ba.


Bai gansu ba amma ya sha alwashin sakawa floor ɗin idanu sossai ko ze sake ganinta.


Ɗaki ya koma ya watsa ruwa yayi sallar isha da shafa'i da wutiri, haka ya kwanta da tunane-tunane a ranshi sbd idan har tabbas yarinyar chan ne lallai ta tabbata annoba kuma se inda karfinshi ya kare wurin ganin an hukunta ta daidai da abunda tayi a cikin zuri'ar su.


Da sassafe ya danna kiran Mammi, gama azkar ɗinta kenan tana shirin shiga kitchen sama ma mai gidanta abincin safe ta ga call nashi, ta ɗan yi mamaki kam kan ta ɗaga 

"Assalamu Alaikum warahmatullah mammi barka da safiya"


Ta amsa tana zama bakin gado

"Wa'alaikumussalam warahmatullah barka ka dae babana, ka sauƙa lafiya?"


"Alhamdulillah mammi, ya ciwon kafafunki hope da sauƙi?"


Ta amsa da 

"Alhamdulillah"


Ɗan shiru yayi kan yace 

"mammi ni kam yarinyar nan tayi tafiya ne?"


Shiru mammi tayi cikin tunani kan tace 

"wace yarinyar kuma?"


Yace 

"wannan na gidan baba Alhj, marar jin."


Girgiza kai mammi tayi kan tace 

"Fauziyyar ce baza'a ka iya faɗa ba sai ka yi ta juye juye? Eh sun tafi excursion Gombe daga makaranta"


Da sauri ya miƙe tsaye kenan ba gizau idanunshi ke yi ba ita ɗin ce, yace 

"mammi yarinyar nan ba Gombe ta tafi ba, jiya na ganta da wani a halin maye da shigar banza!"


"Faizan!"

Mammi ta kirashi daga jin muryarta ya san ranta ne ya soma ɓaci.


"Faizan don baka son yarinyar nan shine zaka ɗauko hanyar yi mata sharri? Buguwa fa ka ce? Sannan da namiji a hotel?"


Yace 

"kin san ban taɓa miki ƙarya ba, kuma a kan wannan annobar ba zan fara ba. Ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba, zan kira Farhan ya je min makarantar ya bincika don bazamu lamunta ta ɓata mana sunan gida ba, Never!"


Mammi tace 

"sunanta Fauziyya, kada ka sake ce mata annoba, sannan takarda da tambarin makaranta da kuma stamp da sa hannu ta kawo ni ta fara kawowa kuma tafiyar ba ita kaɗai ba ce, kar in sake jin irin wannan zance daga bakinka, karka manta ƙanwarka ce kuma karka manta tarbiyar gidan da ka fito"


Tana kai nan ta kashe wayan, hannunta har rawa yake, ta san Faizan be taɓa yi mata karya ba, idan ba akwai abunda ya tsana karya ne, sai dae bazata taɓa yardar wa zuciyarta Fauza ya gani a hotel a Abuja ba, kila kama ce kawai.


Har ta gama girki tana nazari, Farhan na shigowa gaisheta bayan sun gaisa tace 

"Farhan ina so ka je min makarantar yaran nan ka samu vice wadda ya sanya hannu a tafiyar su Fauza ya sake tabbatar maka da tafiyar, sannan ya kira wani a Haɗa ku kaji lafiyarta"


Farhan yace 

"mammi wani abun kuma ya faru ne? Na san Fauza sarai yadda kike maganan nan kuma kaman kina ɓoye damuwa ne a ƙasan ranki"


Tace

"Babu komai Farhan, ka tabbatar kayi duk abunda nace maka"


A ladabce yace 

"To mammi"


Mikewa yayi ya fice.


***


Yana sauke wayan daga kunnenshi yayi shrugging kafadanshi, a ranshi yana furta 

'ina ma ruwana'


Ya gyara kwanciyar shi ya fara bacci gajiya tuni ya mance ma da wata Fauza.


Ita kuwa a ɓangarenta bacci take yi kaman gawa, ko Asuba bata iya ta tashi tayi ba, karfe takwas na safe wani irin amai ya tashe ta, da gudu ta nemi bayi ta fara kwararawa cikinta na Juyawa, saida ta gama tsab tana dafe da kanta dake sarawa kaman zae rabe gida biyu, a hankali ta wanke bakinta kan ta mike tsaye tana kallon bayin da take ɗin.


A hankali Tunanin abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo mata.


Wani irin tashin hankali ne ya bijiro mata, jarabar masifarta ta sa har bata gani da kyau, bata san sadda ta lalubo Kalmar "innalillahi wainna ilahi rajiun" ta fara ambata ba.


"He drugged me!" Da sauri ta kai idanunta jikinta, tana taɓawa hankalinta in yayi dubu ya tashi.


Da sauri ta fito daidai lokacin shima yake shigowa, kanta yayi yana furta

"Babe kin tash...."


Zazzafar Marin da ta sauke mishi hagu da dama ne ya saka magananshi ɗaukewa. Cikin ihu da masifa tace

"Zubair or what so ever, who the hell did you think you are da zaka yi drugging ɗina? U even had the audacity na bani kayan maye?"


Yace 

"am sorry babe! Am so sorry don't be mad I knew I messed up, but listen...."


"Ba zan yi listening ɗin ba, get the he'll out of my way!"


Ta faɗa da karfi tana nufan waje, hannunta ya riƙo ta juya ta mishi wani wawan tura da saida ya faɗi kan kujerar ɗakin, da sauri ta fice tana danne hawayenta..


Tana fita ta nufi room da aka fara kama musu, abun takaici Bacci ta samu suke yi, toilet ta faɗa ta sakarwa kanta shower kan ta fashe da kuka, abu guda ya saura mata a hanyar da ta ɗauko shima yana zuwa, tunda har ta iya ɗanɗana kalar buguwa watarana zata faɗa zina.


Ta fi mintuna talatin kan ta fito, ta samu Sakina na waya, gata nan sir.


"Yayanki Farhan ne yaje office na vice wai yana son Magana dake"


Abun Dukda ya mata banbarakwai kuma gabanta ya faɗi haka ta sa hannu ta karbi wayan ba tare da tace komai ba.


"Ina kwana ya Farhan!"


Yace 

"kina lafiya?"


Ta amsa da.

"Eh"


Ba wani magana suka saba ba, don haka yace 

"mammi ne ta matsa a zo a ji lafiyarki"


Tace 

"Allah sarki! Ina lafiya gobe ma zamu dawo, an fasa sati Ɗayan"


Duk kallonta suke, har ta kashe wayan.


Se a sannan ta fitar da ɓacin ranta

"am so so disappointed in u sakina nd rahama, kun san bana shan giya don Zubair ya bani na bugu na san ba laifin ku bane amma taya Zaku fara barin shi ya tafi dani na kwana gado ɗaya dashi? Me kuke tunani?"


Rahama tace

"kiyi hakuri muma duk sadda ya tafin daken ba a hayyacinmu muke ba bare mu hana shi tafiya dake"


Sakina tace

"to menene ma don ya tafi dake ɗin, ai tunda kika zabi wannan hanyar dolen dole watarana kin sha kayan maye, ita ma abunda kike yiwa gudan dole ne ya sameki so just chill ki sake jiki, ki waye pls"


"tir da wayewar zina da shaye shaye, kun kuwa san azaba da fitinar dake cikin waennan abubuwa?"


Kallon juna sakina da rahama suka yi kan suka washe da dariya, sakina tace 

"lallai ashe ƴar gidan malamai ce"


Tafiya tayi gaban kayan ta ta fara Haɗawa ba tare da tace komai ba.


"Haɗa kayan me kike? Cewar rahama 


"gidanmu zan koma."


"Amma ai sati guda muka ce zamu yi"


"ba zan yin ba".


Tunda ta fara basu amsa a haka sun san in suka cigaba be gameta ba su samu gagarumin matsala se suka kyale ta.


Knocking aka yi, Raham taje ta buɗe, samarin guda uku ne, duk suka janye en matansu suka bar ta ita da Zubair a ɗakin.


Gabanta yaje ya durkusa bisa gwiwowinshi, cikin lalama yace 

"am very sorry! Na san ban kyauta miki ba amma wallahi ba da wani mugun nufi na baki ba, na zata kina sha a lokacin ne kawai ba kiyi niyyar sha ba shiyasa na baki don na tsokane ki, zuciyata zafi take min ina ganinki cikin wannan yanayi Fauxa, na tuba please"


"leave me alone zubair"

Ta faɗa calmly Dukda fuskanta a mugun haɗe yake.


Kanshi ya duƙar daidai kafafunta sai digar ruwa taji.


Da sauri ta ɗago, a take yayi deceiving ɗinta da crocodile tear ɗinshi yace 

"am sorry please Fauza"


Tace 

"Abunda ya faru ya riga ya faru"


"Kin yafe min?"


Ya tambaya cikin murmushi da yayi mata kyau, kanta kawai ta mayar kan wayanta, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani box me kyau daga idanu zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba yace 

"accept this as my apologies dear"


Ɗagowa ta sake yi ta kare mishi kallo, ba laifi Zubair kyakyawa ne, sai de kallo ɗaya zaka mishi ka san crook ne, ga kuɗi ga iskanci.


Hannu ta sa ta karɓa ta buɗe, kasa ɓoye excitment ɗinta tayi tace 

"isn't it that necklace..?"


Wadda take kallo jiya har yake cewa ze mata kyau.


Murmushi ya saki ganin ta saki ranta, ta mishi godiya.


Zama yayi a gefenta suna hira jefi jefi, duk yadda suka so su hanata tafiya a washegarin tace ita sam gida zata koma.


Duk abunda take chan Kasar zuciyarta bakin ciki ne fal na kayan maye da ta sha, ga sallar asuba gari ya gama wayewa, se istigrafi take yi haka dae Zubair yayi ta lallaɓata yana yaudararta bata yi wani fushi mai nisa da shi ba..


Washegari da safe da kanshi ya kaisu har Airport ya mata sayayya mai yawa ya hada da kuɗi, duk da ya burgeta, sai de fa bata nuna ba.


Sauri sauri ya shigo Airport ɗin don shi ze tuƙa Max Air ɗin zuwa birnin Yola daga Abuja, gashi ya so yayi letti, a cikin jirgin ya haɗu da sauran crew ɗin da kuma wadda ze taimaka mishi suka gaisa, he supposed to be a mazauninshi tunda har an soma shiga amma se ya tsaya daga bakin kofan, waya yake amsawa lokaci lokaci ya kan ɗaga idanunshin nan ya kalli masu shigowa ɗaya bayan ɗaya.


Gudu gudu suka karaso don ana final announcement ne, Sakina ce a gaba sai Rahama kan ita, loggage ɗinsu bai da nauyi so kowacce na riƙe da nata ne a hannu, Sakina ce ta fara wucewa ta mika ticket ɗinta, aka bata na seat number ɗinta ta shige, rahama ma ta shigo tayi hakan sai Fauza ta sanyo kafafunta cikin jirgin....


*Toh Alhamdulillah! Free pages sun kare saura ni daku da kuka biya paid, na san kaunar da kuke yiwa labarin ne ya saka ku nuna wannan soyayya sai dai har yanzu ina kara jaddadawa ba zan san kuna kaunar littafin ba idan har baku comment, ni karan kaina ba zan ji kwarin gwiwar yi muku typing ɗin ba due to squeezing time kawai nake nake yi don ina aiki, bani da enough time na kaina, sannan typing in kun ga kun samu da rana to shikenan amma ka'ida sai dare in shaa Allah zan din ga yi don nafi samun time between magrib, isha.   Looking forward for ur comments and love🥰🙏




DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. 

Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               🖤Gureenjoh🖤

No comments