Breaking News

Diddigar Kaya 7


 DIDDIGAR ƘAYA 

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


                 *Shafi Na Bakwa*


*PAID BOOK*


ÆŠANÆŠANO


**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️**


"Aunty wallahi son shi ze kasheni! Kin Reneni ne da soyayyar shi hakan ya bani karfin gwiwar kwallafa rai a kan samunshi sede gashi har yanzu shi bana gabanshi, yanzu har fa su fa'iza sun san nice me cusa kai a gareshi shi ba ta ni yake ba! Aunty kinga wulakancin da ya min a gaban su Fa'iza da kannenshi maza?"

Ta karasa tana me kara rushewa da kuka.


Aunty tayi saurin sa mata hannu a baki tace 

"Haba Fatima! Me yasa ke kam kullum rashin haƙurinki kara gaba yake? Na faɗa miki na kara jadadda miki idan har Faizan be aureki ba to wallahi ba ze auri wata ba, wannan alqawarin da na daukar wa kaina ne tun kan in shigo gidan nan, tufka nake ana warwarewa amma ba matsala ki kwantar da hankali na miki alqawari Faizan ba ze bar garin nan ba tare da an tsayar da magana tsakanin ku ba!"


Wani wawan tsaki Fauxa ta ja kan ta juya ta fice daga gidan gabaÉ—aya, a chan gefe da sashensu inda aka yi wasu kujeru haka masu kyau na tayoyi ta zauna, tana me kallon qonannan hannunta, murmushi ta saki na jin daaÉ—in ba ita ba aikin gida har se ta warke, makaranta ma in ta je ba rubutu ai kuwa za'a sha neman tsokana.


Bata san iya adadin lokutan da ta É—auka a wurin ba, chan ta hangosa yana tahowa cikin tafiyar nan tasa me cike da natsuwa kaman saraki, sanye da wasu kananun kayan still farin Jean da navy blue shirt a ko yaushe Adonshi da shigar shi masu kyau ne da salo irin na burgewa.


Maganan Fatima ne ya faÉ—o mata bata san sadda ta kwashe da wani irin dariya ba har da hawaye, wai amma Fatima tayi asara ta taÉ“e duniya da lahira fisabilillahi ta rasa abun so se wannan? Dariya take tayi tana sakewa wai fa har da kuka Fatima ke yi sbd shi? Ta kara kwashewa da dariya tace 

"Taabbb Allah ka rabani da aikin wahala"


Har ya wuce tana babbaka dariyar ta kaman sabon kamu inda Allah ya taimake ta ba Kallonshi take ba don ta san in har ya san dashi take yadda ba kowan nan se na lahira ya fi ta jin daaÉ—i, ji fa yadda yake tafiya, ita wallahi tafiyar da yake yi ko ita mace bazata yi irin shi ba, dariyarta tasha daidai sashensu na samari ta ga ya É—an tsaya ya waigo, daidai itama ta É—ago ta kalle shi se suka HaÉ—a idanu, kallon kanki ya taÉ“u ya watsa mata. 


Ko seconds biyu be yi ba ya juya ya karasa shigewa sashen, mikewa tayi tana share hawayen dariyarta kaman wacce duniya ta yiwa daaÉ—i ta wuce sashen Jaddah, tana shiga ta narke tana tafiya kaman marar lafiya.


Jaddah tace 

"zo ki karbi tsarabar ki na wurin Faizan"


HaÉ—e rai tayi, Fa'iza tace 

"ke kinga rikicin da aka kwasa da ya Faizan kan Jaddah ta kwasar miki chocolates É—in nan karfi da yaji? wlh ki gode mata ta san yadda kike son chocolates shiyasa, ga su da daaÉ—i kaman zasu tsige kunne"


Kallon chocolates É—in tayi masu tsada ne sossai, daga gani ma maybe ba a nan Nijeria ya sayo su ba sede tunda daga hannunshi ya fito basu ba ta sha'awa ba, kau da kai tayi tace 

"Jaddah da baki wahalar da kanki ba don ni kam ba sha zan yi ba"


Jaddah ta saki baki zata yi magana kenan Fauxa ta fara kukan hannunta na zugi, da sauri Jaddah ta karÉ“e hannun tana salati tace 

"Faozia garin yaya? Me ya sameki haka?"


Ai jin tambayan Jaddah yasa ta kara narkewa tana fashewa da kuka, she's so fragile in tana abu kaman little baby, Fai'za tace cikin damuwa.

"Jaddah ita da ya Faizan ne"


Nan ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, Jaddah tayi ta masifa ta kuwa ci alwashin se ta saɓa mishi wani irin mugunta da bakin hali ne wannan?


A kan cinyar Jaddah ta kwanta tana jin daaÉ—in yadda Jaddah ke ta zuba mitan abunda ya farun, ta kara da 

"mutum ne se baƙin miskilanci yanzun nan yasa yarinyar da yake ikirarin buduruwarshi ce kuka amma ko a kwalan riganshi"


Kau da maganan Fauxa tayi don be shafe ta ba, anan ta kwana ma yau..


Washegari Monday ko aiki É—aya bata yi ba da taje school ma babu abunda ta rubuta se surutu da neman magana, a ranar Ammi ta dawo itama Seda tayi faÉ—an hannun nata sede baba Alhj be ce komai ba.


Bayan 2days ta É—an samu sauki ta cigaba da aikinta, zuciyarta kuwa na kiyasta mata yadda zata rama abunda ya mata sbd ta sha wahalan qunan sossai.


Yau tana kwance bisa kujerar Jaddah tana danna Æ´ar karamar wayar jaddahn sbd ita ba kaunar kallon tashoshin wa'azuzzuka da shi kaÉ—ai suke dashi gabaÉ—aya gidan take ba, jaddah ta fito rike da tray tana kallonta tace

"Fauziyya don Allah miƙawa Faizan abincin nan kinga yaran duka suna wurin Ibrahim(baba prof)"


HaÉ—e rai tayi tace 

"Jaddah eyyah ki jira su in sun dawo su kai mishi"


Jaddah ma rai ta É“ata tace 

"zan saɓa miki wlh Fauziyya, ki wuce ki tashi ki kai in dodonki ne se ya cinye ki, in kuma baza ki je bane ki gayamin"


Hawaye ne ya cika idanunta, ita ba mikewa take son yi ba don ko da yaran suka je wurin baba prof da be ganta ba seda ya aiko fakiha tace mata tace tayi bacci idan kuwa bata ce haka ba se ta kirɓa ta in aka dawo sake kiranta, gashi yanzu Jaddah zata saka ta kaiwa wannan azzalumin abinci.


Mikewa tayi ta ɗauki tray ɗin da Jaddahn ta dangwalar ta fito, shiru tayi tana tunani, in ta taɓa ji da kyau Jaddah ta taɓa maganan rashin son yajinshi sbd muguwar ulcer ɗinshi ko yaya ya ci yaji se ya kwanta, murmushi ta saki taje kan kujerun tayunsu ta ajiye tray ɗin da gudu ta koma gidansu taje ta fara binciken drawer ɗinta akwai wani yaji me zafi da ta daka ranar girkin Amminta sbd an yi mata dole daka yajin shinkafa da waken, kowa da wahala yaci yajin sauran ne ta kulle ta boye a sif ɗinta.


Da gudu ta dawo ta buɗe miyan kubewa danyen ta juye duka, cokalin da ta biya ta ɗauko a kitchen ta saka ta juya kan ta ajiye shi a wurin, ta dauki abincin ta nufi sashensu, a gaban site ɗin ta kalli Haɗaddiyar beymach ɗinshi baƙi siɗik se ɗaukar ido yake da yayi parking a wurin, baki ta taɓe ta isa kan motar da sbd yanayin kyaunta mutum kan iya finshi tsawo ta ɗaura a kai ta juya tayi tafiyar ta.


Tana nan kwance a parlorn na Jaddah har wuraren karfe tara da rabi, wayan Jaddah ne ya fara ringing ta ɗauko ganin Faizan ta taɓe baki ta mayar ta ajiye tare da lumshe idanu kaman tayi bacci, Seda ya kira sau biyu a na ukun ne Jaddah ta fito tana tambayar Fauziyya kam bacci tayi ne ana ta kira bata ji.


Ganin baccin take yasa ta É—auki wayan tare da amsawa ta kara a kunne, cikin kamillalliyar Muryarsa da se ka saurara zaka ji sbd rashin son hayaniyarsa yace 

"Jaddah abincin fa? I've been waiting."


Jaddah ta kalli Fauza tace 

"ba'a kawo bane? Tun fa É—azu na bayar a kai maka, ikon Allah.."


Yace 

"wa kika bai wa?"


Ta  fara jijjiga Fauziyya sbd nauyin baccin da ta riga ta sani tace 

"Fauziyya! Ina abincin da na baki ki kaiwa yayanku ne?"


Juya keya tayi kan tace 

"yana kan motanshi mana"


Ba tare da yace komai ba sbd yana jin duk abunda suke yi ya katse wayan, Jaddah na ta mamakin ikon Allah akan Fauxa se kawai sallamanshi taji, juyowa tayi zata yi magana taga ya nufo su hannunshi riƙe da ruwa me sanyi wadda ya fara kankanra na kamfanin Faro babba yana tafiya ne cikin ƙasaitarshi yana me buɗe murfin.


Kan Jaddah ta ankara ya fara tuttulawa fauxiyyan ruwan sanyin, a firgice ta mike zaune tana jan numfashi sbd sanyin ruwan gashi a duniya ta tsani ruwa ya taÉ“a ta yanzu se tayi mura gashi ya zuba sossai a kanta da fuskanta, hawaye ta fara don sossai ta firgita sanyin ruwan kuma ya ratsa ta, ko a jikinshi cikin muryarshi me taushi yace 


"wuce ki É—auko!"


Mikewa tayi tana share hawayenta ta fito, ko da ta É—auko abincin don tuna muguntan da ta mishi a ciki bata san sadda murmushi ya subuce mata ba, a gabanshi ta dire ta juya ta fice ya ja tsaki kan ya buÉ—e ya zuba kaÉ—an.


Spoon ya É—auka sbd shi fa irin mutanen nan ne da ko tuwo zasu ci seda spoon, da bismillah ya kai loman abincin bakinshi Sam be kula da bala'in dake ciki ba seda ya haÉ—iye ya É—aura na biyu a bakinshi.


A firgice ya dawo da abincin yana sakin tari kaman ze shiɗe, da sauri Jaddah ta dauki ruwa ta mika mishi ya amsa ya sha sede ba sassauci, tari yake kaman ze mutu gabaɗaya ya Haɗa zufa, idanunshi sun rine sun zama jajazir, da kyar ya samu tarin ya lafa se kuma gefen cikinshi ya riƙe.


Salati Jaddah take tayi tace 

"na shiga uku! Yaji ne a abincin ko me?"


"Zaliha! Zaliha!!"


Zaliha ta fito da gudu ta zube a Æ™asa Jaddah tace 

"ke Zaliha kin saka attarugu a markaden kayan miyan nan ne?"


Girgiza kai tayi tace 

"ban saka ba Jaddah ai kin ce yallaɓai Faizan baya so, wlh ko kaɗan ban saka ba"


Fauxa dake daga window tana ta dariyar cin nasara, kwanciya yayi a kan kujeran duk dauriyarshi ulcer na azabtar dashi shiyasa yake mugun kiyayewa.


Kaman wasa Seda Faizan yayi ciwo sossai kan ya samu sauƙi, kaman yadda itama saida tayi mura da zazzaɓi, kowa kuma Seda yayiwa Zaliha faɗan saka attarugu a abincinshi baiwar Allah gata da gaskiya sede babu yadda ta iya haka take shiru take bada hakuri.


Zaune yake gaban baba prof kanshi a ƙasa, baban ya tambayeshi jiki, cikin girmamawa ya amsa da da sauki Alhamdulillah, bayan shirun seconds kan yace.

"In Allah ya kaimu Laraba zan koma Abuja sbd akwai tafiyar da zamu yi da shugaban ƙasa"


Murmushi baba ya saki, a ko menene ya kan yi alfahari da wannan yaron nashi, Faizan ba irin normal pilots bane, yana daga cikin manyan pilots da idan ba da su ba shugaban kasa baya tafiya ko ina, bayan nan yana da hannayen jari da kampanunnuka ba daya ba ba biyu ba, Sam be dogara da aiki É—aya ba, yaro ne shi me tsantsan biyayya ga iyayenshi, babban É—abi'ar shi kuma kunya yanzu ya san akwai abunda yake son faÉ—a mishi ne sede yana jin nauyin maganan shine yake ta kwana kwana.


Baba yace 

"masha Allah, Toh Allah ya kaimu ya nuna mana"


Yace 

"Ameen baba!"


Baba ya kalleshi yace 

"akwai wani abu ne kuma? Naga kaman kana son yin magana"


Kanshi ya dukar yana shafa kwantaccen Suman keyanshi yace 

"dama akan maganan Fatima ne"


Murmushi baba ya fadada yace 

"masha Allah, ka shirya auren kenan.. Toh tunda har ka furta wani satin in shaa Allah zamu je wurin mahaifinta mu tambayar maka ita, ai Fatima yarinyar kirki ce ta samu tarbiya me kyau daga Mahaifiyarta Allah ya tabbatar mana da alkhairi" 


Da Ameen Faizan ya amsa, dukda maganan magana ne da ya kamata yayi farin ciki sede ko kaɗan be wani ji daaɗin hakan har chan ba, hira suka taɓa kadan da baban har baba Alhj ya shigo suka kara tattaunawa kan ya musu sallama ya fice.


Bayan ya koma aiki da kwanaki biyar aka tambayar mishi Fatima kuma an bashi sede an ja auren se ta gama secondary school in ya so se ta fara jami'a a gidanshi.


****


Kwance take kan gadonta jikinta yayi tsami da bugun da ya Farhan ya mata da magrib ɗin saboda bin wata ƙawarta da tayi gida bata dawo ba se da ana kiran sallahn magrib tun karfe 1:30, da farko basu so dukanta ba sede Sam ta ƙi faɗan inda taje hakan yasa ya Farhan da Ya Faraj suka zane ta har Seda Baba prof da za shi masallaci ya karɓe ta, Allah ya isa take ta ja tana cin alwashi kala kala a kansu, fa'iza dake ɗakin tun da suka dawo daga sallar isha'in bata ce mata komai ba...


Suna daga É—akin Fatima ta shigo a wurin Aunty Amarya da Ammi dake bisa taburma a tsakar gidan suna cin Tuwon dare ta zauna, tace 

"waii wallahi Aunty mammi na jin jiki, ciwon kafan nan baya mata ta daaÉ—i É—an zaman da na yi na awanni a wurintan nan baki ga ba, komai se an yi mata"


Ammi tace

"Allah sarki, Allah dae ya bata lafiya ai kafa shine komai a jikin mutum, Allah dae ya sa kaffara ne"


Aunty Amarya tace 

"Ameen Ammi, Fatima se ki dinga zuwa kina taya Asiya (É—iyar Yayar mammi É—in) kula da ita"


Fatima tace 

"In shaa Allahu Aunty ai Mammi kaman uwa take a wurina, bari na shiga na dubo su Fa'iza mu ci abinci"


Mikewa tayi ta nufo É—akin nasu, tana shiga suka HaÉ—a idanu da Faozia dake kallon kofan, É—auke kai Fatima tayi yayinda Faozia tayi tsaki me karfi tace 

"Fa'iza kin san Allah ko?"


Fa'iza tace 

"me aka yi kike tambayana na san shi mana"


Faozia tace 

"DaaÉ—ina dake baki iya cin riban zance ba, ko da shike manta ma... Dama Tambayarki zan yi da munafukin É“oye da na bayyane don Allah wanne ya fi?"


Fa'iza da bata fahimci zancen ta ba tace 

"ai munafunci ko ya yake sunan shi munafunci kawai dae gwara wadda ze nuna maka a bayyane ka san dashi da wadda ze nuna maka Musa a fuska fir'auna a zuciya"


"sannan in zaka yi abu kayi don Allah da nufi É—aya ni fa shiyasa bana son hulda da duk munafuki a duniya.." Fauza ta karasa


Fatima da ta tsaya kikam tana Kallonsu se hawaye ya fara kwaranya a fuskanta, Aunty ce ta fara shigowa ta buge Bakin Fa'iza tana cewa 

"yanzu Æ´ar uwarki zaki HaÉ—a kai ana cusguna mata a gidan nan Fa'iza? Tana gayamin ina karyatata ashe da gaske ne? Fa'iza..!"


Ammi da ita ma ta shigo tayi kan Fauxa zata make tana cewa 

"Ai ba ita zaki daka ba Auntynsu ita uwar iyayin nan zaki mara har se taga wuta.."


Dira Faozia tayi ta Ɗayan gefen kan Ammi ta zagayo ta fice da gudu harda bangaje Aunty goshinta ya ƙume da kofa salati duk suka saki ita kam ko waiwaye babu tayi sashen Mammi da gudu.


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 

09039206763 

Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments