Breaking News

Diddigar Kaya 8




 DIDDIGAR ƘAYA 

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


               *Shafi Na Takwas*


*PAID BOOK*


ÆŠANÆŠANO


**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️**


Karshe dae Aunty bata iya bacci ba seda Baba Alhj ya danne mata goshin aka shafa man zafi, takaici ya hana shi cewa komai, ya aika a kira mishi Faozia É—in aka tarar bata nan sede Jaddah bata ce bata nan ba kawai cewa tayi a ce tayi bacci Dukda bata san wani laifin ta sake aikatawa ba.


Ita kuwa Faozia tana zuwa wurin Mammi ta shagwaÉ“e tana faÉ—amata abunda ya faru, Mammi tace 

"Gaskiya Farhan da Faraj basu kyauta ba ai da lafiyata ƙalau babu wadda zan bari ya taɓa ki su da suke gantalinsu akwai wadda ya hana su ne?"


Cikin jin daaÉ—in goyon bayan da aka bata tace 

"ai shine"

Mammi tace 

"Faozia am ki rage nemarwa kanki magana kin ji? Bana son yadda kowa ya buÉ—e baki yace Faozia, Faozia É—in nan wallahi har raina bana jin daaÉ—i"


Fauziyya tace 

"In shaa Allahu Mammi bazan sake ba"

Mammi tayi murmushi Dukda ta san labarin kanzon kurege ne kullum haka take cewa baze hana gobe tana fita ta jajiɓo wani tashin hankalin ba.


Ƙin zuwa wurin jadda tayi wai tana fushi a lokacin da su Farhan ke bugunta jadda bata zo ta karɓeta ba kuma ta tabbatar sarai tana ji.


Asiya mammi ta kira akan ta zo ta dubo wa Fauzan abunda zata ci.

Faozia tayi Charab tace 

"Mammi bari na shiga kitchen É—in da kaina"


Har ta fita ta dawo tace 

"ke fa Mammi kin ci abinci?"


Tace 

"Ina ga Tea zan sha Faozia kubewa suka girka a gidan ni kuma ba so nake ba, je kiyi abunda zaki yi ke kam"


Kitchen ta wuce, Asiya dake zaune a parlorn ta bita da harara ko Kulata Faozia bata yi ba don ta jima da sanin Asiya irin mutanen nan ne da suke bari hassadar wani ya gurɓata musu rayuwa, ba tun yau ba ta fahimci Asiya bata ƙaunar ta shiyasa itama bata shiga harkarta.


Hijab É—inta ta ajiye ta fara dube dube a kitchen É—in Seda ta fidda duk abunda zata bukata na aikin da take son yi kan ta fara aikin, Yawan bin kawaye da take har ana dukanta duk akan girki ne tana matukar kaunar girki babu abunda yake bata nishaÉ—i a rayuwa irin ta ganta a katon kitchen tana girke girke, idan kaga Faozia a school ta natsu to kallon recipes take a wayan kawaye don gidansu kam ba'a abubuwan zamanin nan.


Shawarma da suka yi É—azu har sanadiyar shi aka Chasa ta tayi guda biyu na beef, banda kamshi babu abunda ke tashi a kitchen É—in tana yin Shawarmanta kuwa tana biski ba me yawa tayi ba É—an kaÉ—an ne sosai da kidney sauce, fancy plate ta É—auka ta zuba biskin daga gefe in a stylish way kan ta zuba kidney sauce É—in shima a gefe ta watsa parsley a kai kaÉ—an yadda ya bada wani garnish na burgewa.


Shawarmanta guda biyu ta É—auko suma ta saka su a plate ta É—aura Duka a tray ta É—auko ruwa masu rangwamen sanyi tare da daukawa kanta wani mango drinks ta nufi É—akin Mammi, tana zuwa ta ajiye tray É—in tace 


"Mammi guess what I made?"


Mammi tana murmushi tace 

"Ina zan sani ina zaune a nan na dae ji kamshi na tashi kuma duk hasashe na na rasa gane menene.."


BuÉ—e plate É—in biski da kidney sauce tayi tana dariya cike da jin daaÉ—i tace 

"Tadaaa..!"

Tana dariya sossai wadda ya saka Mammi murmushi tace 

"Masha Allah, Kice daughter na na shirin zama Chef eyee a ina kika koyi irin wannan delicious É—in?"


ShagwaÉ“e fuska tayi tace 

"ba irin su bane na bi Zee koyo a gidansu kuma da nisa shine ban dawo da wuri ba su ya Farhan suka bugeni ba..!"


Mammi tace 

"masha Allah, am impressed gaskiya karki damu in shaa Allah na miki Alkawari da kaina zan saka ki a catering school Æ´ata ta zama Chef Faoza.."


Murna Faozia ta fara harda tsalle, Mammi na ta dariya Faozia is such a wonderful child da zama da ita kaÉ—ai ka iya saka ka farin ciki she's so lively in har ka san yadda zaka tafi da ita, Mammi ta matsarwa plate É—in tace 

"bismillah Mammi"


"thank you bitty" 

Spoon ta sa ta fara ci tana yabon hannun na Fauza a girki, itama Shawarmanta taci tas ta cinye ta sha mango juice É—in kan ta tattare wurin ta fitar, da taimakonta Mammi taje toilet tayi duk wani abunda zata yi ta dawo da alwala, ita ta taimaka mata har ta kwanta...


Tana shirin shiga wanka se taji sallaman Baba Prof hijab ta saka, Seda ya shigo ta gaishe shi ya amsa da kulawa kan ta fice ta bar su da Mammi, ɗakin yaya farida da babu abunda Mammi ta taɓa ciki ta shiga, akan gyara akai akai hakan yasa ta nufi toilet ɗinta tayi wanka, bayan ta fito ta duba wardrobe ɗinta ta kuwa samu kayan bacci sabo dal a Leda Dukda ya ɗan yi mata yawa haka ta saka.


Seda ta É“ata lokaci mai yawa kan ta fito ta koma É—akin Mammi ta samu Baba prof ya tafi, Har zata juya Mammi tace 

"Fauza"


Dawowa tayi tana cewa

"Na'am Mammi ko kina bukatar wani abu ne?"


Mammi tace 

"A'a ki hau gado ki kwanta, kiyi Adu'a kin ji?"


Kai ta gyaÉ—a tare da rage musu hasken É—akin ta hau gadon na Mammi ta kwanta tare da jan bargo.


Chan cikin dare Fauza ta tashi saboda fitsarin da ya matse ta se ta hangi Mammi zaune dafe da kai, da sauri ta mike tace 

"Mammi!"


Mammi bata É—ago ba, sauÆ™a tayi ta nufe ta ta duÆ™a a gabanta tace 

"Mammi lafiya? Baki jin daaÉ—i ne?"

Tayi maganan hawaye na cika mata idanu Mammi ta É—ago idanunta duk sun sauya tace 


"Na kasa bacci Fauxa kafana se harbawa yake"


Hawaye ne ya zubowa Fauxa cikin tausayin Mammi, zama tayi gaban kafan tace 

"bari na miki Adu'a Mammi"


Bismillah tayi sau Uku kan ta É—aura da 

بِسْÙ…ِ الله! بسم لله!! بسم الله!!!

"Ø£َعُوذُ بِااللهِ ÙˆَÙ‚ُدْرَتِÙ‡ِ Ù…ِÙ†ْ Ø´ِّرِ Ù…َا Ø£َجِدُ ÙˆَØ£ُهـَٰØ°ِر"


"Bismillah! Bismillah!! Bismillah!!!

Auzibillahi bi qudratihi min sharri ma ajidu wa uhadhir".

Kafa bakwai ta shafa mata a kafan ta kara da qulhuwa uku, falaki uku, da nasi uku. 

Manzon Allah yace babu wani ciwon dake damunka da zaka dafa wurin ka karanta wannan Adu'a ba tare da Allah ya yaye maka ba, walau ciwon ciki, ciwon kai, ciwon kunne ko ma wani irin ciwo ne.


Cikin ikon Allah bayan ta gama yi mata ta ci gaba da massaging kafan har Mammi ta Samu bacci ya É—auke ta, wani irin ciwon kafa ne wannan Fauxa tayi maganan a zuciyarta tana kallon tarin magungunan na Mammi, daga na Asibiti har na gargajiya zuwa na musulunci, komawa gadon da Fauxa bata yi ba kenan a nan kasa ta kwana se da Asuba taji Mammi na tashinta.


Mikewa zaune tayi tace 

"Mammi ya kafan?"


Mammi tayi murmushi tace

"sannu Fauziyya! Sossai na ji daaÉ—in Adu'ar da kika min kwanana hudu rabona da baccin dare se gashi yau nayi harda mafarki"


Murmushi Fauxa tayi tace 

"to bari na sake miki"


Adu'ar ta fara mata yayinda ma ta zuba mata idanu tana kallo, ta rasa me take hangowa a rayuwar Fauxa wadda kowa baya hanga kowa kawai ya tashi Fauxa bata ji, Fauxa kaza Fauza kaza ita Sam banda haske babu abunda take gani a rayuwarta, yarinya ce me tarin É“oyayyen baiwa amma influence na mutanen dake zagaye da ita ya hana shi bayyana. 


Jin za'a shiga sallah yasa tace 

"Fauza tashi je kiyi alwala ki tafi masallaci bari nima na miƙe"


Da taimakon Allah ta kai kanta bayi tayo alwala yayinda tuni Fauxa ta fice masallaci, anan tayi sallah ta sake kishingiɗa tana me sake samun wani baccin saboda sauƙin kafan.


Fauxa ko É—ar bata ji ba ta wuce sashensu abunta, yau itace da wanke wanke da kuma gyaran É—akin su, Seda ta fara shara da gyara É—akin tana cewa 

"Wallahi in an ga dama a wargaza kan a tafi ba ruwan Fauxa"


Falaq tace 

"amma kin san dole a shirin su Fakiha su wargaza É—akin nan kam ko?"


Cikin kunkuni tace 

"suna da hannu ai, se su gyara! Ni de na san nayi"


Tana kai nan ta hau sharewa ta fitar da Sharan a memakon ta kwashe se ta watsa tsakar gida alhali Fatima ta riga ta wuce nan a shararta na tsakar gida, tana watsawa ta bi ta kan tsintsiyar Fatima da ta sake baki tana kallonta tayi wurin wanke wanke ta fara yi, dama kowa ya san wanke wankenta kwanuka kam se sun bugu iya buguwa in akwai na fashewa kuwa to se ya fashe.


Ammi da suke aikin kari da Fa'iza bata ce mata komai ba, don in tace zata yi magana kuka ze iya fin karfinta Fauziyya ta riga ta fi karfin duka yanzu kuma se Adu'a.


Da yamma bayan sun dawo makaranta Fatima na wankin uniform na su Fakiha yayinda fa'iza ke wanke wanke, ita kuwa uwar gayyar kitchen take tana taya Aunty Amarya sa magana tunda ba aikin take ba duk abunda Aunty Amarya ta saka ta se tayi mata shirme da gangan.


"Ni sumayya! Yanzu Fauziyya daka attarugu ma se kin zuzzubar a ƙasa haka? Ai ko Faazila dake karama a gidan nan karankap zata daka min kayan miya in kwashe lafiya lau ke kam babu abunda kika iya goɗe goɗe dake se sa mutane magana? Wani irin jaraba ne wannan?khaih Allah ya shirya mana in na shiryuwa ne"


Kunkuni wadda Aunty Amarya bata ji ta hau yi. "Yen yen yen yen... Se ki zo ki shirya ai tunda charbi nake ko jigida" kawai se Aunty Amarya ta saki kuka. Baba Alhj da shigowar shi gidan kenan ya tarar da faÉ—an da Aunty Amarya ke yi kuma yana kallon lokacin da take gungunin sede gudun kar ya ce ze buge ta yanzu ya karya ta yasa ya shige parlornshi kawai.


Aunty Amarya tace 

"tashi ki tafi bana son aikin, in har aikin da zaki sani magana ne, nayi maganan kuma ki zage ni don baki dauke ni da daraja ba tunda ba ni na haife ki ba jeki karki sake sakamin hannu a aiki"


Mikewa kuwa tayi ta fito ko a jikinta, ta zo wucewa ta gaban Fatima suka HaÉ—a ido a saman labbanta tace "munafuka" tana ball da bucket É—in wankin har ruwan ya kwararare.


"Fauziyya!"

 Baba Alhj ya kirata cikin wani irin kaushin murya.


Se Fatima ta fara kuka mikewa tayi ta wuce ta gaban Fauziyya ta duƙa a gaban Baba Alhj tace cikin sanyin murya

"Baba Don Allah ina so kayi min izini ina so in koma wurin mahaifina haka..."


Cikin tausayinta yace 

"Babu inda zaki koma Fatima, nima mahaifinki ne in akwai wacce tafi cancanta da ta bar min gida Fauziyya ce!"


A razane Fauziyya ta É—ago ta kalleshi, Ammi ma da ta fito se idanu ta zuba mishi yana kallon Fauziyya yace 


"Eh kin ji abunda na faÉ—a! Na gaji bazaki kasheni tun kwana na be kare ba, ke kaÉ—ai ranki guda kin zama sheÉ—aniy...."


"A'uzubillahi Sule!"


Jadda da ta shigo bikon ƴar gidanta sbd ta ƙi shiga wurinta tun jiyan nan ta faɗa tana karasowa ta kama Fauxiya da ta zama speechless tana kallon mahaifinta.


"Ƴarka na cikin ka kake kira sheɗaniya Sule? Wani irin baki ne wannan? Me tayi maka da zafi haka?"


Kanshi a Æ™asa yace 

"Mama na gaji da halayyar Fauziyya, dubi goshin uwarta Sumayya yadda tayi mata jiya, babu wadda ze faɗa magana Fauziyya bata bashi amsa ba, ta sakawa yarinyar nan karan zuƙa tana mata gadara da gidan uba! Ita ɗin ai ba daga Bishiya ta faɗo ba, gwara Fatima sau dubu don bata sa uban ta da uwarta zub da hawaye ba... Wallahi wallahi Mama Fauziyya ta gama sane min cikin yarana har raina na gaji da komai nata"


Ammi kuka ta fashe dashi tace 

"ba kinji ba Fauziyya? Wallahi ki guji duniya, uban da ya haife ki ma yace ya gaji dake to wa ze iya zama dake? Da wannan halayyar naki Fauziyya gwara ki sa wuƙa ki mana yankan rago mu huta da zafin zuciya kullum a kanki"


"Ruqayya! Sulaiman!! Ya isheni haka, tunda mutuncina da ganin idanuna be sa kun kasa amayo da kalaman bakinku ba, ni kuwa ba zan tsaya in cigaba da saurara ba, karku manta yaranmu kaman kiwo suke a garemu Allah ya kan jarabceka ta hanyoyi daban daban maybe ita ɗin itace jarabawar taku, idan kuka yi hakuri a matsayinku na iyaye kuka kai zuciyarku nesa kuka cigaba da mata adu'a har zuwa sadda Zaku Rabu lafiya kila ku samu rabauta ta sanadiyar ta, yanzu da duk kuke aika mata da kalamai marasa daaɗi ta karasa lalacewa kuma haka Zaku ɓata lahirarku saboda se Allah ya tambayeku, abunda ya saura ku ce shine kawai ta fita ta bar muku gida tunda har ka fara attempting to zan tafi da ita sashena ku zuba ruwa a ƙasa ku sha"


Tana kai nan ta janyo hannun Fauza da take tsaye kaman icce suka fice.


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 

09039206763 

Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments