Breaking News

Rainon Soja 76-77

76-77
*Littafin na ku?i ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment?500 Vip payment?1000 SPC payment?1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409….?????#Mamanteddy#mrsusm.*







Book 3
?ago da Idanun ta tayi tana gya?a masa kai Alamar eh kamin ta sakar masa murmushin nan nata tare da bin sa da wani irin kallo wanda ita kan ta bata san yaushe ta fara yi masa irin sa ba , Kallo mai cike da tausayin juna da kuma soyayya. Ina sonka Uncle Haidar…ta furta tana kallon Manyansu idanun sa. Wani irin nauyi yaji Zuciyar sa yayi , farin ciki da jin da?i na rufe Zuciyar sa. ?an murmushi yayi wanda sai da Hushiryar sa suka bayyana kana ya ce “ Mu shiga daga ciki , ki kimtsa sai muci Abinci ko ?……”
**
Waye wani Alhaji Adamu Billionier? Kamata yayi ko waye shi ka saka a kama mun…….Hajara! Muryar General Saleh ya katse Mom Hajara dake surfa masifa , Yanayin Muryar sa ya sauya . Hajara Wai yaushe zaki daina Wannan Masifar taki ne ? Ki dakata mu bi komai ……A’a janar na fahimce ka , kamar cin mutuncin da wannan yarinya tayi bai dameka ba . To Ni zan saka ayi da ?arfin iko na! Hajara! Ya kuma kiran sunan ta yana katse ta daga magana da take. Mami ne dake gyefe ta fahimci yanayin sauyi daga janar wannan yasa ta amshe wayan tana karawa a kunnen ta tare da cewa “ Janar ko ma mene ke faruwa ina son sani yanzu , Wacece yarinyar? . Huwmmm Wani irin gwauron Numfashi ya sauke kana yace “ zan taho gida yanzu , ku shirya cikin shirin ku zamu tafi tare daku ne duka ”.

?asa mami tayi da Wayar tana kallon Mom Hajara wacce itama ita take kallo.

Na ji kamar bashi bane , duka ya sauya har a Muryar sa …meke faruwa ne? Mami ta furta tana kallon Hajiya Hajara. Koma meye ai dai yace yana zuwa yanzu ko? To mu jira isowan sa . Ta furta tana ja baya tare da zama a kujeran falon tana karka?a ?afa .

A can ?angaren General Saleh Yelwa kuwa , Abubuwan ne suka faru tamkar a mafarki tabbas wannan shine ake kira da ikon Allah . Don shi mutum ne mai dattako da girma. Wannan yasa shi ko da yaji labarin Mahaifin Nasreen sai yayi tattaki da kansa ya nufi Gidan Alhaji Adamu. Anan ne abu ya dawo tamkar a yanzu aka yi . Daddy ya kwashi mamaki ya kuma ga ikon Allah . Wanda ba su zata ba a rayuwa ko a mafarki wai yayi Arziki shine Allah ya azurta da ?azamin ?u?i wanda bai san ?arshen su ba . Wato Alhaji Adamu Yes da No ??. Gaba ?aya a halin gidan an ru?e don A sa’ilin Daddy yana ganin sa cike da rawar baki da murya ya kira sunan sa………SALIHU!

Tsayawa Alhaji Adamu yayi yana jin kan sa na juya masa sunan sa kawai da General Saleh ya kira da Salihu. Tun daga nan bai ?ara sanin halin da yake ciki ba , har yanzu da Daddy suka gama magana da Su mami ….
Don Alhaji Adamu yana Asibiti a na basa taimakon gaggawa .

**
Wannan wani irin masifa ne Nasreen kika janyo mana muna zaune lafiya ? Shikenan Yanzu duka zamu tashi a banza a wofi . Don kuwa Alhaji Adamu yana da wowa cikin hayyacin sa yan uwansa ?ila ma har da iyali kin ga mu mun tashi a banza a wofi kenan ……Hajiya falmata ke maganan tana kaiwa da komowa a tsakiyar falon Hankali a tashe……!
[1/31, 4:34 AM] Real~Mamanteddy: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

No comments