Breaking News

Tsutsar Nama 12




 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒍𝒗𝒆_




.......(Kutumelacy). Na faɗa a zuciya lokacin da yay sallama da wata jarumar muryarsa cikin yanayin mazantaka da nuna kamewa tamkar wanda akama dole, dan hatta lips ɗin ma da ƙyar yake motsasu. Bayan an amsa ya cigaba da miƙa saƙon gaisuwa da sannu da zuwa nan ɗin ma dai a fiffisge alamar maganar ta zame masa dolene ko kuma gayune ko kuwa girman kai irin na masu hannu da maiƙon kaza oho masa. Ga wata hausarsa da ta gama gurɓacewa da harshen ƴan kudanci ko nace harsuna da yawa dan tamkar ba cikakken bahaushen da akace an haifa a gari irin Kano ba. A wata gaɓar ma hausar ƙwace masa take sai dai ya kwakuso turanci ko faransanci ya maka a wajen ya kuma fuske ya cigaba da jawabinsa. Kuga wani ɗigimi, da dai a turancin ya tsaya da yafi, to waye ya wani iya faransanci anan?. Koda yake ban sani ba tunda naga taron duk nasu ne na masu jiki duk chocolates. Haka dai ya haɗa jawabin mintuna uku da ƙyar yana faman mana haɗin gambizar yaruka uku a lokaci guda da kai hannu saman kai ya murza tabbacin dai maganar ta dole ce a garesa. Hummm duniya makaranta, yo ALLAH na tuba su mu kuma indai zance ne ai ko akkun farkon ƙarni ta sama mana lafiya, duk da dai nima sai naso nake nawa surutun. Amma dai na ƙara ilimi, tunda naga yayin ƴar jan ajin nan ake da fidda zance ɗaɗɗaya billa sake kame kaina zan dingayi tunda ban sani ba ko nan gaba nima na kuɗance. Yo Bily abin ai na ALLAH ne, bafa zaune nake kurum ba daga aikin jarida sai na gida. Ina ƴar sana'ar sai da hijjabai da takalma duk da jarin bai wuci na dubu ashirin ba. To nadai fi su o'e ai masu cika gida da munsharin barci ko.

       Duk da fa jawabansa sun ƙayatar sun kuma tsaru tamkar daga takarda yake karantowa ni ƴar iyar taku sai da na taɓe baki. Yayinda wajen ya ɗauki tafi gaba ɗaya, a cikin ƴan jaridar mu harda masu yin fito. Hakama wasu gungun samari ƙyawawan da kallo ɗaya zaka musu kasan akwai ƴan canji dan kamar sun zaɓo kansu ne dan ƙyau da gayu, bana kuma raba ɗaya biyu abokansa ne sai salute nashi suke suma dai cike da isa da ƙasaitar. A haka taro ya cigaba da tafiya cikin nutsuwa, mudai ƴan jarida munata ɗaukar rahotanni babu mai damar cewa komai a yanzu sai nan gaba. Dan ya bada damar a masa tambayoyi a karo na biyu da zai fito, amma akan abinda ya shafi Companyn kawai. Nikam na taɓe baki, dan na shiryo nawa questions ɗinne akan komai kuma in sha ALLAHU sai na masa su duka, dan zan fara da manya-manyan cikine da dole sai ya magantu koda baya son hakan.

        Ana tsaka da sauraren jawaban sauran manyan mutanen wajen fitsari yay mugun matsata. Sosai hankalina ya tashi, na shiga dana sanin shan shayin da nayi kafin na fito. Tun ina daurewa har dai na shiga mutsu-mutsun da Khulsoom ta lura dani.

     “Samraah lafiya kuwa?”.

Ta faɗa tana tsareni da idanu. Fuskata dake cikin facemask a marairaice na ce, “Ina fa lafiya Khulsoom. Wlhy wani mugun fitsarine ya matseni kamar zai zubo. Dan ALLAH ki tashi ki rakani kada ayi abin kunya a bainar nasi. Maimakon mai buɗe Company ya zama topic of the day ni na zama.” dariya ta nema saki, amma ganin yanda na ɗaure fuska ya sata daurewa ta ƙunshe abarta. Cikin raɗa ta ce, “Kima Mansoor magana ya raka ki, dan wlhy tsoron waɗan nan jami'an tsaron da aka baza nake yi”.

     Wata hararar na sake watsa mata a karo na biyu, batare dana tanka mata ba na miƙe dan gab fitsarin yake da zubowa. Kasancewar wajen tsitt yake babu wani hayaniya kuma kowa a zaune yake a nutsensa sai tashina ya jawo hankalin mutane da yawa gareni. ALLAH ya soni komai nawa a rufe yake, idan ka cire tafukan hannuna da yatsunsu suka ƙawatu da jan lallale, na tabbata yau da ace ba hijjab na saka ba wannan idanun na jama'a sai ya sakani sakin fitsarin a wajen. Gudun karna taka doka ko yin abinda zai jawo min kunyata kai tsaye na nufi security dake kusa damu sosai. Gaishesa nayi cikin girmamawa bayan na sauke mask ɗina dan karma ya fassarani da abinda bashi nake nufi ba sannan nai masa bayani. Hakan da nai kuwa ya sakashi jin daɗi, dan har I'd card ɗina saida na nuna masa tunma kan ya buƙata. Wata mace a cikin jami'ansu ya yafito da hannu, ta iso wajen tana mai ƙamewa da salute nashi. Nuna mata ni yay yace ta rakani restroom. Da girmamawa ta amsa masa nan ma. Sannan muka wuce ta can bayan Companyn. Na zata anan bayin yake, amma sai naga ta shiga dani ta wata ƙofa alamar cikin dai Companyn zamu shiga amma ta baya. Dan ta gaba an gama zagayesa da zaren nan mai ribbon kuma ba'a kai ga yankawa ba. Lallai dukiya tayi aiki a wannan waje, duk da fa inda muka shiga bawani ciki-ciki bane ba. Amma tsayawa kwatanta miki Bily walla ɓata lokaci zamuyi. Har ciki muka shiga tare da ita, ta nunamin bayin farko, godiya nai mata munama juna murmushi. Ina shiga wayarta ta fara ƙara alamar shigowar kira, dole ta fita a wajen domin amsawa. Har kuma na gama abinda nake na fito babu ita. Mamaki ya kamani na shiga waige-waige. Ganin dai da gaske bata a wajen na nufi neman hanyar da muka shigo. Sai dai kuma na rikice dan hanyoyin da yawa ne ashe duk iri ɗaya. Canki in canka na shigayi a tsakani, ganin dai ba ganewar zanyi ba na shiga binsu ɗai-ɗai ina taɓawa. Sai dai me kowacce na taɓa sai na jita gam a kulle. Tun ina ɗaukar al'amarin wasa har hankalina ya fara tashi amma dai na dake ina ƙarama kaina ƙwarin gwiwa. Hope ɗina na gab da barina gaba ɗaya wata a cikin ƙofifin ta buɗe. Ji nai kamar na saki ihu dan daɗi, sai dai banyi hakan ba na saki ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna da buɗewa, cike da zumuɗi na sake kama handle ɗin ƙofar na murɗa, ina ƙoƙarin danna kai ciki naja wani wawan birki sakamakon abinda naci karo da shi mai ɗimauta zuciya da tunani.

       Sosai jikina ke rawa idanuna a matuƙar ware kansu. Ganin hankalinsu bai kawo kaina ba na sake jawo ƙofar sosai ta yanda bazasu iya ganina ba. Video recording na latso a wayata na fara ɗaukarsu. A dai-dai lokacin ya zare wuƙar da ga jikin mutumin, wani irin gurnanin ƙarasa fitar rai yayi ya ida zamewa da ga jikin bangon da yake yay ƙasa. Mutumin daya buɗe masa mota ɗazun ne a gefensa, gaban mutumin da suka kashe ɗin  ya kai duƙe yana mai saka yatsunsa biyu a saitin hancinsa, a wani irin yanayi ya furta, “Ya mutu Sir”.

      Kansa ya ɗauke tamkar baiji miya faɗa ba. Hakan yasa wancan ɗin miƙewa batare daya sake cewa komai ba shima ya buɗe wani farin ƙyalle. Wuƙar ya saka masa a ciki tare da handkerchief ɗin daya riƙeta, sannan ya bar wajen cike da takun isa, bathroom dake cikin ɗakin ya nufa. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai gashi ya fito yana goge hannu da ƙaramin farin towel alamun wankewa yayi. Sai da ya gama goge hannun yana ƙoƙarin ajiye towel ɗin yake faɗin, “Lukman ya shigo da kayan can, ya fita da gawan zuwa can anguwan”.

     Kai yaron nasa ya jinjina masa cike da girmamawa. Ƙofa ya nufo, dan haka nai saurin tsayar da video ɗin na koma wani ɗan lungu na lafe. Wajen sauri face mask ɗina dake a hannuna ya faɗi ƙasa. Cikin takunsa da baya fidda sauti ya fito, cak ya tsaya tamkar wanda ake controlling da remote yana kallo mask ɗina dake yashe a ƙasa. Sosai na waro idanuna waje ƙirjina na wani irin mahaukacin bugawa da sauri-sauri. Lokacin da yake ranƙwafawa yana ƙoƙarin kai pen ɗinsa mai masifar ƙyau ya ɗauka facee mask ɗin dashi jinai kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Sake lafewa nai sosai tamkar ina shirin keta bangon na shige ciki. Yayi kusan sakan ashirin yana kallon mask ɗin, sai kuma ya zaro wani ƙyaƙyƙyawan handkerchief a aljihunsa ya warwaresa ciki ya saka. Da baya-baya ya koma yana ɗan waige-waige, ƙofar ɗakin daya fito ya ɗan buɗe kaɗan, sai kuma ya maida ya rufe ya sake juyowa. Kusan taku goma ya sake tsayawa cak. Da sauri na kai hannuna kan bakina na rufe kamar zan saki kuka dan tashin hankali. A hankali ya juyo da alama dai yana ji a jikinsa akwai mutum a wajen. Bakina na sake dumtsewa tare da hanci ina mai runtse idanuna da ƙarfin masifa. Nafi mintuna biyu a haka kafin na buɗe a hankali, wayam na gani alamar ya fice. Cikin sauri na zame nai ƙasa ina mai janye hannuna da sakin numfashi mai ƙarfin gaske. Inaga tunda nasan kaina nai hankali ban taɓa cin karo da matsanancin tashin hankali irin na yau ba. Kisan kai fa, na mutum ba wani ƙwaro ko dabba ba. Lallai mutum abin tsoro ne, taya zakai tunanin wannan mutumin zai iya aikata wannan ta'asar, jibesa kamar wani mutumin kirki. Koda yake wanda ke iya zana tattoo a jikinsa ga ɗan kunne ya kuma ɗaure gashi a kai kamar wani mace ko yay kitso komai ma ai zai iya aikatawa. Aiko bazan taɓa yin shiru ba, dolene nai gaggawar nunama duniya wanene shi, yanzu kuma ya kamata a cikin taron nan ba sai anjima ba. Zaram na miƙe kuwa ina tattaro wayata dake yashe a ƙasa da sauri........✍️




        _“🤯🤯Na rasa abin faɗa Samraah.  Yaya kin tona asirin nasa kenan?”._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments