Breaking News

Tsutsar Nama 13


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒉𝒊𝒓𝒕𝒆𝒆𝒏_



......Humm Bily nayi yunƙurin hakan kamar yadda na faɗa miki. Sai dai ina miƙewa aka buɗe wata ƙofa da sai yanzu hankalina ya kai na fahimci a itane muka shigo tare da jami'ar nan ɗazun. Wani ne ya shigo da kaya a hannu, da alama Lukman ɗin daya faɗa ne. Jikin bangon na koma na sake lafewa, har sai da ya shige. Maimakon na sake yunƙurin fita sai zuciyata ke bani shawarar tsayawa naga yanda zasu fita da gawar. Ga kiran Mansoor sai shigomin ya ke da alama jirana suke. Sauƙina ma wayar a silent take. A plane mood na sakata, na sake shiga video recording. Ko sakan goma ba'ai ba sai gasu sun fito da gawar kuwa, duk da an naɗeta cikin wani abu jini duk ya ɓata mayafin. Da ƙyar na iya tsaida karkarwar da jikina ke min. Suna ficewa nai saurin fitowa da hanzari nabi bayansu nima. Inayi ina waige-waige. Maƙalewa nai ta jikin ƙofa ina cigaba da ɗauka har suka sakata a cikin motar. Ina ganin sun kammala Lukman ɗin ya shiga motar ɗayan na shirin juyowa ciki na sake komawa wani lungun da gudu. Dan kar yaji sautin hakkina hijjab ɗina na kama na cusa a bakina har sai da ya koma ɗakin, babu jimawa sai gashi ya fito da mopper yana goge duk inda jinin ya ɓata. Ganin ya sake komawa ɗakin na fito da sanɗa, ta hanyar da muka shigo nabi na fita. Inda wani zai ƙuramin ido tuni zai gane a gigice nake, gashi babu mask ɗin a fuskata yanzun. Dawowata wajen taron dai-dai ana mimmiƙewa zuwa inda ribbon ɗin nan yake. Hakan ta bani damar isa inda su Khulsoom suke. Bag ɗina kawai na amsa a hannunta na jefa wayata na ciro wani face mask ɗin na shiga sawa. Ganin yanda suka tsareni da ido ya sakani ɗaga musu hannu cikin dakewa na ce, “Kuyi haƙuri ina a inda bai kamata na ɗaga waya bane ba. Badai har yay jawabi na biyun ba ne ko?”.

        Khulsoom ce ta amsa min da “A'a bai yiba sai an gama yanka abin can.” kai na jinjina mata alamar fahimta. Yayinda nake ɗan satar kallon Mansoor ta gefen ido, dan shi baice dani komai ba face zubamin idanu da yay kawai. Da alama bai gamsu da amsar dana bada ba. Dama nasan in kowa bai fahimci halin da nake a ciki ba shi sai ya fahimta. Dan akwai shaƙuwa ta musamman tsakanina da shi ta yanda ko motsi ɗaya daga cikinmu yayi sai ɗan uwansa ya fahimci mi yake nufi. Ban sake yarda na kalla inda yake ba muka nufi inda za'a yanka ribbon ɗin. Duk yanda naso kame kaina daga kallon mutumin nan na gagara haka. Mamaki abinda ya faru a cikin ƴan mintunan da basu wuce talatin ba kawai nake. Ban fahimci na tafi tunani mai zurfin da har bana fahimtar mi ake a gurin ba sai da Khulsoom ta zungureni. Numfashi mai nauyi na kawo tare da yin firgigit na ce mata, “Na'am mi kike ce?”.

       Da mamaki ta ce, “mike damunki ne wai haka Samraah. Duk kinyi wani iri kamar wadda ke a rikice. Kalla yanda kike zufa ga hankalinki sam baya kan abinda ma akeyi”. 

    Cikin son basar da ita na ce, “Cikina ne ke ɗan juyamin. Inaga awaran da naci ne da kabeji ɗazun da safe.”

         “Ayya sannu, amma tunda kin san yana baki matsala haka ai da baki ci ba, ke da zaki shigo cikin taro babu daɗi kaita zaryar toilet ai”.

      “Haka ne, nima na shafa'a ne kawai. Amma in sha ALLAHU ina fatan ma bazan sake zuwa toilet ɗin ba. Akwai maganin da nake sha a bag ɗina bari na sha shi”.

    Kanta ta jinjina min tana sake min sannu. Inda muke zaune na koma na zauna dan hakan sai yafi min sauƙi. A dai-dai nan aka saki tafi alamar har an yanka. Na sake tafiya a tunani naji saukar muryar Mansoor a kaina. Firgigit na dawo hayyacina ina kallonsa. Sai kuma nai saurin ɗauke idanun a kansa ina ƙoƙarin dai-daita nutsuwata.

       “Samraah mike damunki?”.

   In har kaji sunana kai tsaye a bakin Mansoor babu wasa sam a ciki. Saurin girgiza masa kai nayi da faɗin, “Babu komai fa. Na dawo nan nasha magani ne kawai”.

     “Ƙarya kike”.

  Ya faɗa kansa tsaye kawai. Nasan za'ayi hakan. Dan Mansoor ya gama sanina matuƙa kasancewarsa mutum mafi shaƙuwa a rayuwata bayan ƴan gidanmu. Shekara biyar ai ba wasa ba. Ƙasa nai da kaina kawai ina wasa da yatsun hannuna. Sai kuma na ɗauki wayata nai rubutu na tura masa. Ganin yanda ya cigaba da tsaiwa yana kallona ya sani ɗagowa ina masa nuni daya duba wayarsa. Baiyi musu ba ya zarota ya duba. Da sauri ya ɗago yana kallona. Sai kuma babu shiri shima ya kai zaune a kujerar kusa da ni. Sai da ya wawwaiga gefe da gefenmu sannan ƙasa-ƙasa ya ce, “Da gaske Baby”.

       Kaina na jinjina masa kawai ina ƙoƙarin riƙe hawayen da suka ciko min ido. Sai kuma na kallesa na ce, “Ina son nabar wajen nan yanzu. Dan na yarda face mask ɗina a ciki ya ɗauka. Na tabbatar zuciyarsu dole tana musu wasi-wasi akan dole wani ya shiga wajen. Dan na fahimci hankalin yaron nasa kamar tun ɗazun ma ya rabu biyu akan mutane.”

          “Ba tafiya bace mafita Samraah. Ki ƙara daurewa a kammala komai kawai. Sannan ki dawo da hankalinki jikinki, dan fitarki yanzu a wajen nan bazata zama mai sauƙi ba, sannan zasu ma iya ganewa ta hakan tunda baki da wani dalilin fita na zahiri. Kinga ma tashi mu shiga ciki kinga mutane sun kusa gama shiga za'a zagaya cikin companyn ne”.

      Badan naso ba dole na miƙe. A zuciyata kam sai addu'oi nakeyi. Kar kiga fa kamar na cika tsoro. Wlhy babu abinda ke tada min hankali sai ganin gawar mutum cikin jini. Dan abune da bai taɓa faruwa da ni ba. Kinga ko sanda Babanmu ya rasu banda wani cikakken hankalin daya kamata irin hakan yaban tsoro. Tunda shima har aka binne gawarsa yana a yanayin zubar jini saboda accident. Mamanmu kuma bamma san rasuwarta ba sam, tunda ban wuci 3years ba kwata-kwata. Haka dai da ƙyar na cigaba da riƙe kaina mukabi ayarin ƴan ganin cikin companyn. Ya haɗu matuƙa gaya. Ga wasu manyan machines a wani ƙaton hall da baida iyaka. Da alama daga nan za'a dinga ƙera motocin ko haɗa su ne ma oho musu. Bayan nan akwai wajaje daban-daban masu ɗauke da abubuwa kala-kala da bamusan na miye ba, duk da wani bature a cikin abokan nasa sunata ƙoƙarin yin bayani, ni dai ba wani fahimtarsu nake ba sam. Dan duk yanda wajen ya kai ga haɗuwa a yanzu ni sam baya birgeni. Sai ma ganinsa nake baƙiƙƙirin da duhu. An ɗauki kusan mintuna talatin a ciki kafin a fito. Ɗayan sashen da ya kasance shine ake fara gani daga titi, wanda an yisane da zallar gilashi aka sake nufa. Anan ne offices ɗin ma'aikatan yake ashe. Tun daga hawan farko har zuwa na biyar sai da muka shishshiga da taimakon lift... Duka offices ɗin sun haɗu, hatta na ƙananun ma'aikata dake a hawan farko ma duk da na haɗaka ne komai tsaf. Amma nasa na matsayin oga kwata-kwata yafi kowanne tsaruwa, dan tamkar ba'a Nigeria kake ba. Daga office ɗin kuma akan iya ganin cikin ƙwaryar Kano da ƙyau ta kowanne ɓangare. Sosai abin akwai ƙayatarwa. Sai dai ni bai ƙayatar dani ba. Dan yanzu baƙiƙƙirin ma nake kallon mai Companyn kamar baƙin maciji. Nan ma an kwashi wasu mintuna kafin a fito. ALLAH ALLAH nake kawai yayi jawabin ƙarshen nan na masa tambayar da zan masa na bar wajen. Amma sai akace abinci za'aci a yanzun, sannan aje salla a dawo a ƙarasa. Kamar zan fasa ihu haka naji, sai dai yaya zanyi. Dole yanda suka tsara haka kowa zai bi. An fara gabatar da abincin a nutse, za kuma azo har inda kake a baka zaɓin abinda kake son ci sannan aje a kawo maka. Koda aka yambayen nikam nace a'a. Dan na ɗau alwashin bazanci kuɗin jinin mutane ba. Wama ya sani ko tsafi yake yi ne. Ai dama al'amarin dukiyar tasa da mamaki, shiyyasama mutane suketa wasi-wasi a kansa. Haba mutumin nan ai yayi ƙarami da tara irin wannan dukiyar haka. Kwata-kwata fa bazai wuce talatin ba. Inma zai haura hakan kaɗanne kuwa. Yo ko iya wannan companyn akace ya mallaka a shekarun nan nasa ai abin ayi wasi-wasi ne balle kuma ace yana da ninkin baninkin hakan har dasu jirage. Jirgi ake magana fa dake tashi sama da ɗaruruwan mutane bawai kwale-kwale na katako da ake tsallaka ruwan ɓagwai ba. Sannan bama ɗaya ba, ba biyu ba fa....

         “Baby!!”.

    Mansoor ya sake katse min tunani, dan yanzu a gefena yake. Firgigit na dawo hankalina. “please be smart mana. Ko so kike abokan tafiyarmu su fahimci wani abu ne?.”

     Kaina na girgiza masa. Cikin dauriya na kalla abincin da ya saka a kawo min. Maimakon naji sha'awar cinsa kodan ƙyawun da yay a cikin ido ga kaza har rabi a ciki sai naji sam baya wani birgeni. A hankali na sauke a jiyar zuciya da ce masa, “Na ƙoshi da abincin nan wlhy. Kayi haƙuri dan ALLAH.”

       Kallona kawai ya tsaya yi, ni kuma na ɗauke idanuna daga sashensa gaba ɗaya. Da ga ƙarshe ma na ɗauka wayata na shiga buga game wai duk dan dai na dawo da hankalina jikina. Sai dai tuni na kasa cigaba da buga game ɗin, na koma kallon mutane a ƙasan ido musamman ma yaronsa da duk wani motsin sa......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments