Breaking News

Tsutsar Nama 18

 *_Typing📲_*










   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏_



.......Gyaran murya ya ɗan yi idonsa akan Tijjani. Cikin sauri Tijjani da idonsa ke akan tv ya maido hankalinsa garesa. Kafin ma yace wani abu cikin muryar nan tashi kamar ta rowa ya taresa da faɗin, “Ina za'a samu abinci mai tsafta?”.

       Cikin girmamawa Tijjani ya ce, “Ranka ya daɗe akwai gidajen abinci masu inganci dake tsaftace abincinsu sosai a garin Kano. Harma da masuyi a cikin gidaje sai dai kawai ai order suna da masu delivery da zasu iya kawo maka har inda kake, ko aje a amso”.

       “Good. Sai ka samo duka gidan. Ka tambayi kowa abinda yake buƙata”

     “In sha ALLAHU yanzu kuwa ranka ya daɗe”.

   Bai sake cewa komai ba ya maida idonsa a television dan an fara gabatar da program ɗin da yay zaman kalla. Hayatu ne ya miƙawa TJ kuɗi masu yawa. Ƙasa-ƙasa ya ce, “Nidai jallop rice da ƙirjin kaza nake so.” 

      Dariya TJ yayi ƙasa-ƙasa yana ƙumshe baki dan karta fito. Sai kuma yayma Hayatu nuni da ogan nasu da ido. Kai Hayatu ya jinjina masa yana sake gyara nutsuwarsa da maida hankalisa garesa ya ce, “Sir za'a karɓo maka kaima ko?”. Shiru kamar bazai tanka ba, dan yamayi biris tamkar baiji ba. Sai kuma batare da ya kallesu ba ya ɗan kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai shegen ƙyau. Ya ɗan yamutsa fuska da jan siririn tsaki. “In dai bazai jima ba a samo min tuwon semo.. miyan kuka”. A tare suka amsa da girmamawa. TJ ya fita da hanzarinsa dan sun san baya cin abincin dare late, wani lokacin ma bai fiya ci ba. Yau ma suna ƙyautata zaton dan baici komai bane tun black tea ɗin safe. Haka yake abinci bai damesa ba, shiyyasa ga shi nan ko kaɗan baida wani tunbi, jikin ma badan yana haye-hayen waɗan nan tarkacen machines ɗin na motsa jikin zamani ba da zai kasance ne falen-felan.

       TJ na ficewa Hayatu ya katse tunaninsa tare da matsowa inda yake. Da ga tsayen da yake kamar soja ya ɗan rissina yana fito da flash da ga aljihunsa da faɗin, “Sir ga cctv footage ɗin an samo”. Juyowa yay ya ɗan kalli Hayatu ɗin a yanayin jin daɗin hakan. Sai dai kuma ko kaɗan fuskarsa bata nuna komai ba tana nan a ɗaurenta tamau. Kujera ya nunama Hayatu. Zama yay yana ɗaukar laptop dake a Centre table ajiye ya saka flash ɗin jiki. Kafin ya miƙe yaje har gabansa batare da yayi playing video ɗin ba. Ajiye masa yay a stool ɗin daya jawo a hankali gabansa sosai. Sannan ya zauna a saman carpet kusa da ƙafafunsa yana shiga inda folders ɗin videon suke. Duk zubama screen ɗin laptop ɗin ido sukai. Cikin ƙwarewar aiki Hayatu ya zaluƙo video ɗin sashen da abin ya faru, tare da dai-daita lokacin da komai ya faru sai dai baiyi playing ba ya ɗan ɗago ya kallesa.

         A hankali ya furta, “Kunna”.

    Kunnawar yayi. Ko'ina ya fara nuna shiru babu kowa babu motsin komai. Kusan minti ɗaya da wasu sakanni sai ga Samraah na bubbuɗe ƙofifi bayan ta fito da ga wani lungu da suka san restrooms na ma'aikatane a wajen. Yanda take taɓa ƙofofin tana ɓata fuska kamar zatai kuka zai baka tabbacin ta ɓata ne. Can cikin takaici ta fincike face mask ɗin fuskarta. Ƙyaƙyƙyawar fuskarta da babu zanen komai na kwalliya ta bayyana. Hayatu dai ya gagara haƙuri sai da ya furta “Masha ALLAH” a hankali. Dan ko makaho ya laluba fuskar Samraah yasan yarinyar ƙyaƙyƙyawa ce, duk dama eyeglasses ɗinta har lokacin yana a idanunta shi bata cire ba. Isowarta ƙofar da suke ciki ya sanya Hayatu waro idanu sosai, sai dai bai iya cewa komai ba. Ta buɗe ta ɗan leƙa. Sai kuma tai baya a rikice alamar akwai abinda ta gani. Wayarta data zaro tai danne-danne ta kanga tabbacin video take musu yasa Hayatu kasa haƙuri ya furta, “What! Sir itace kenan?”.

       Bai samu amsa ba, dan ogan nasa ko motsi baiyi ba har sai da ya kai ƙarshe. Fitowarsa, tsintar nurse mask. Har cigaba da video da Samraah tayi sanda suke fita da gawar mutumin. Cikin ƙanƙanin lokaci Hayatu ya gama haɗa uban gumi kamar wanda ke a filin kokawa. Shi kam duk da a birkice take video ɗin yaga matuƙar ƙarfin halin yarinyar nan. Motsin da ogansa yayi yasa hankalinsa dawowa jikinsa. Ya ɗan ɗago ya kallesa. Sai da gabansa ya faɗi ganin yanda cat eyes ɗinsa suka canja launi. Dan gaba ɗaya gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama ƴar siririya exactly yanda na mage suke komawa idan suna a cikin haske. Batare da ko kallon Umar ɗin ya sake yi ba ya miƙe ya fara tafiya. Sai da yaje gab da ƙofar bedroom ɗinsa sannan cikin dakiyar muryar dake tabbatar da ransa a ɓace yake ya furta, “A nemota duk inda take. A cigaba da bin duk wani motsinta daga nan zuwa sati biyu”.

        “An gama Sir. Amma in baka manta ba ka bata damar yin hira da kai ma”. Hayatu ya faɗa cikin tsumar jiki. Cak ya tsaya daga ƙoƙarin shigewa da yake yi kamar mai nazari, sai kuma batare da ya juyo ba ya furta “Zanyi tunani akan hakan”. 

     Buɗe baki Hayatu yay zai sake magana cikin nuna gamsuwa, sai dai harma ya riga yay shigewarsa shi. Hayatu ya rabga tagumi tare da faɗin, “Tab ƙyaƙyƙyawa kin shiga uku wlhy, bama ke ba duk zuri'arki kin sakasu a masifa. Ke miya kaiki shiga gonar da bataki ba. Aikata wannan aikin da ba'a sakaki ba, karanbaninki ya ɗebeki shiga fadar sarkin aljanu. Dan oga ALJANI ne irin ifiritan nan.” yana cikin wannan sambatun nasa TJ ya shigo da ledoji masu ƙyau an musu tambarin gidan abinci. Firgigit Hayatu ya dawo hayyacinsa tare da gyara yanayinsa. TJ da ma bai wani lura da halin da yake a ciki ba ya ajiye masa tasa ledar sannan ya ajiye wata a Centre table yana faɗin, “Wannan tuwon oga ne. Shi na tsaya ma sai da akayisa yanzu-yanzu gashi nan da zafinsa yanda zai masa daɗin ci.”

        “Ai wannan tuwon mawuyacine ya samu shiga kuma yanzu”.

    Idanu TJ ya waro a rikice ya furta, “Na shigangaɗi Hayatu badai na makara ba? Wlhy babu tuwonne amma matar tace zatayi da sauri tana da miya. Ni kuma naga tunda yace yana buƙatarsa yana so ne shiyyasa nace tayi da sauri...”

      “Kai ka kwantar da hankalinka badan ka daɗe bane ba kawai dai wani abunne daban ya ɓata masa rai. Amma bari na gwada faɗa masa ka dawo mugani”.

     Ajiyar zuciya TJ ya saki, duk da kuwa yanayinsa bai warware ba. Dan in har ogan nasu na cikin ɓacin rai ko damuwa suma sukan shiga matuka saboda yanda suka ɗauki al'amarinsa da matuƙar muhimmanci a rayuwarsu. Tashi Hayatu yay ya nufi hanyar bedroom ɗin nasa, sai da yay jimm a tsaye bakin ƙofar kafin yay knocking a ɗarare. Ko motsi ba'aiba, bai gajiyaba ya sake yi tare da sallama. Nan ma anja kusan minti ɗaya kafin ya amsa masa a daƙile. Sake nutsuwa Hayatu yay kafin cikin dauriya ya ce, “Kayi haƙuri Sir, dama TJ ne ya dawo, a kawo maka abincin nan ne”.

        “No! I'm okay”. 

    Shiru Hayatu yay cikin nuna damuwa ƙarara a fuskarsa. Sai kuma ya sake raunana murya ya ce, “Please Sir, duk yau fa bakaci komai ba. Ko nace ma rabonka da abinci tun shekaran jiya a Lagos. Abu mafi saka Ummie damuwa a rayuwa shine ka kwana da yunwa. Dan ALLAH ko kaɗanne ka daure kaci, saboda nasan duk da bata tare damu zata ji a jikinta kamar yanda ta saba”.

      Wani irin cizar lips yay da ga zaunen da yake a bakin gadon hannunsa dafe da kansa. Hayatu ya matuƙar sanin lagonsa a rayuwa. Dan shine kaɗai yake iya bi da shi fiye da kowa bayan mahaifiyarsa. Hakan kuma nada alaƙa da sanin da yay masa tun ƙuruciya. Duk da dai shi ya girmi Hayatun da kusan shekara biyar ma, amma kasancewar sun tashi ne shi da iyayensa a cikin gidan kakansa da ya haifi Ummien sa yasa yay masa farin sani na gaske. Ya jima a gurin kamar bazai motsa ba sai kuma a daƙile ya furta, “Kawo nan”. Cikin sauri Hayatu yabar jikin ƙofar cike da farin ciki bawan ALLAHn kamar cikinsa zai kai. Babu jimawa kuwa sai gashi da tuwon. A can ya shirya masa shi saman table ɗin gaban sofa dake bedroom ɗin, har lokacin kuma yana a zaune bakin gadonsa hannunsa dafe da kansa. Yanayi ne dake nuna yana cikin zafin rai, dan Hayatu ya sanshi a rayuwa fiye da tunanin mai tunani. Ganin Hayatu ɗin baida niyyar fita yaja siririn tsaki yana ɗagowa, harararsa yayi da faɗin, “Ka tsaya gadi na ne sai naci ka gani?”.

         Ƙasa Umar yayi da kai yana ɗan murmushi. Sai kuma ya rissina tare da faɗin, “Ayi haƙuri Sir”. Daga haka ya fice a ɗakin. Wani tsakin ya sake ja sannan ya miƙe zuwa gaban sofa ɗin ya zauna. Hatta ruwan wanke hannu Hayatu ya tanadar masa. A nutsensa cikin yanayinsa na rashin gaggawa akan komai ya fara cin tuwon dan yana son tuwo sosai saboda fevorite food ɗin Ummien sa ne, ada sanda yana yaro idan tayi tace sai yaci yakan zauna yayta kuka shi bazaici miyan daddawa mai wari ba. Amma bayan wani lokaci da rayuwa ta canja kanta zuwa abinda bai taɓa mafarkin riska ba a cikinta sai ya maida tuwon fovorite nashi shima. Yaci kusan rabin malmala ɗaya ya ajiye duk da kuwa tuwon ya masa matuƙar daɗi,  sai dai bai cika son cin abinci late haka ba. Shiru ya ɗan yi zaune a wajen kafin ya tashi zuwa toilet. Brush yayi da sake gyara jikinsa ya fito. Ya samu Hayatu har ya shigo ya tattare komai harda sakama ɗakin freshener ya ƙara dai-daita masa ac. Komai baice ba ya rage kayansa zuwa na barci, sai dai maimakon kwanciyar zama ya sake yi a sofar yana ƙoƙarin kunna laptop ɗinsa, dan yana son ƙarasa harƙallar wani business ɗinsa kafin ya kwanta. Dai dai kuma mi hakan kamar neman gagararsa yake. Dan tunda ya kunna ya gagara danna ko keyboard ɗaya tunaninsa ma neman tafiya yake wani sashe daban. Da ga ƙarshe dai ya ture laptop ɗin gefe ya ɗauki wayarsa. Wata number da aka saka Dude ya nemo tare da danna  kira.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


No comments