Breaking News

Tsutsar Nama 19


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆𝒕𝒆𝒆𝒏_



......Kusan lokaci ɗaya muka iso garejin da Mansoor. Dan haka babu ɓata lokaci muka nufi cikin motarsa, dan nan ɗin zaifi mana zama sirri fiye da ko'ina saboda abinda zamu tattauna ɗin. Gaba Yaya Musaddiq ya shiga ni kuma baya. Sun gaisa da Mansoor cikin mutunta juna kamar yanda suka saba nima na gaishesa. Amsawa yay idanunsa a kaina ta cikin mirror. 

       “Ya kamata ki huta da kukan nan Samraah. Sai kace kece kika aikata laifin nan. Kinga kuwa yanda idanunki suka koɗe”. Mansoor ne yay maganar cikin nuna damuwa matuƙa. Yaya Musaddiq dake saurarensa ya ce, “Ai ita haka take bata bin al'amarin rayuwa a hankali ka ganta nan. So take sai ta jama kanta wani ciwon muma ta sake sakamu a wata damuwar sannan”.

     Idanuna na cikowa da hawaye na ce, “Kuyi haƙuri Yaya ba haka bane. Wlhy na kasa mantawane da ganin gawar kawai. Amma in sha ALLAHU bazan ƙara ba”.

    “ALLAH yasa hakan” Yaya Musaddiq ya faɗa. Yayinda Mansoor yaja numfashi ya fesar tare da amsawa da Amin. Idanuna na share tare da ƙoƙarin yin magana wayar Mansoor ta shiga ruri. Tamkar an saita sai tawama ta fara. Kusan a lokaci ɗaya duk muka kai hannu domin ɗauka. Sai kuma muka kalli juna tare da sake ɗagowa duk muka kalli Yaya dake tambayar mu “Lafiya kuwa?”.

        “Daga office ne”. Mansoor ya bashi amsa yana ƙoƙarin kai wayar kunnesa. Nima dai tuni nakai tawa tare da yin sallama. MD ne ya amsa daga can, batare daya bi takan gaisuwata ba ya ce, “I'am Sorry Samraah muna son ganinki a office yanzu Please”.

      “Yallaɓai lafiya kuwa?”. Na faɗa da sauri hankali a ɗan tashe.

     Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, “Kinga kwantar da hankalinki ba wata damuwa bace. Mun samu baƙuncin babban baƙone mai matuƙar muhimmanci da muka daɗe muna fata. Ya kuma ce da ke kaɗai yake son ayi hira da shi”.

         “Ni kuma oga? Duk mutanen dake a gidan sai yace sai ni. Wanene haka da ƙarfin halin nan? Sai kace wani abin cin rabo. Ya kamata Ku faɗa masa ba sashin da nake aiki ba kenan”.

      “Humm Samraah Please mana. Dan ALLAH ki shirya kawai ga driver na nan ma na aiko gidanku ya ɗaukeki a motata”.

    Sake tashi hankalina yayi, sai dai kafin nayi magana oga ya yanke kiran. Sagale nai kawai ina kallon wayar kamar wata gunki. Wane irin baƙone da zai tada hankalin oga har haka. Sannan kuma ma yace ni yake so nai hira da shi. “Kodai mutumin nan ne?”. Na faɗa a zahiri batare da nasan maganar ta suɓuce min ba. Atare Yaya Musaddiq da Mansoor da shima yay zororo alamar kiran da akai masa nada nasaba da nawan suka juyo suna kallona. 

     Yaya Musaddiq ne yay ƙarfin halin cewa “Wane mutumi?”. Firgigit na dawo hayyacina. Dan na fahimci zancen zucini ne ya fito fili. Idanuna ne suka cicciko da ƙwalla. Cikin rawar murya na zayyane musu komai da MD yace min. Mansoor ne yay saurin faɗin “Tabbas akwai alamar tambaya. Dan nima akan abinda suka kirani kenan. Amma ina ganin ki kwantar da hankalinki bari muƙarasa office ɗin domin ganin wanene ɗin ko kuwa Yaya Musaddiq?”.

         “Tabbas shawararka yayi Mansoor. Tunda akan aikine bai kamata ayi sakaciba kam. Kuje idan kun dawo ma ƙarasa maganar in sha ALLAH. Nima zuwa lokacin na ɗan ƙara yin nazari.”

    Mansoor ne kawai ya iya amsa masa. Nikam sai binsu da kallo kawai nakeyi. Yaya Musaddiq ya fita yana buɗe baya yace na fito na dawo gaban. Ganin banda niyyar hakan ya buɗe ya kamo hannuna ya fiddoni ya maida gaban. Key kawai Mansoor yayma motar ya haura kan titi. Babu wanda ya iya sake yin magana a cikinmu. Kafin mu isa office ɗin kuma sai danno mana kira MD yake yana kuma sakawa amana. Da wasu kalar shegun zuƙa-zuƙan motoci na alfarma muka fara cin karo a harabar gidan. Sai mutane cikin baƙaƙen kaya tsatstsaye ƙiƙam kamar masu tsaron ƴan fashi. Mudai wucesu mukai muka shiga abinmu. Duk da lahadine mun samu ma'aikatanmu dake duty a wannan ranar dukansu. Harma da wadanda aka kira irinmu da ranar suna hutu suma kamar mu ɗin dai. Office ɗin MD muka wuce kamar yanda aka sanar damu yace muyi. Anan ɗin ma mun tadda mutane biyu irin waɗanda ke a haraba su biyu a jikin ƙofar. Matsa mana sukai muka shiga bayan Mansoor yayi knocking an bamu izinin shiga. Mun fara cin karo da ƙamshin turare mai armashi sosai. Sai sanyin ac a office ɗin kamar ba safiya ba. Wannan kuma ba halin MD bane zama cikin ac da ƙarfi haka. 

        Akan MD idanunmu suka fara sauka. Kafin dattijon dake zaune a kujerar kusa da shi cikin shigar ɗanyar shadda mai tsananin ƙyau da ɗaukar hankali sai maiƙo take da walwali. Ƙyaƙyƙyawane sosai baƙi ga dogon hanci da shiryayyen farin gashinsa daya ƙawata taswurar fuskar tasa. Gaishesa muka farayi kawunanmu a ƙasa. Dan tun shigowarmu ya zuba mana idanunsa manya farare yana murmushin bajinta. Yanzun ma da fara'ar ya amsa mana. Sai kuma ya kalla MD ɗin yana faɗin, “Inaga idan kun shirya mu fara abinda ya kawomu kawai. Dan na faɗa maka zanbi jirgin ƙarfe biyu ne domin komawa Lagos, ina kuma da wasu uzirin bayan wannan. Gashi yanzu 10:30.”

       “Hakane ranka ya daɗe” MD ya faɗa cike da tsantsar girmamawa ga dattijon. A karo na farko muka kalla juna ni da Mansoor. Sai kuma muka maida kan MD da yay kiran sunanmu a tare. Idonsa akan Mansoor ya ce, “Mansoor ka duba tare da tabbatar komai yayi dai-dai a can ɗin. Muma gamu nan fitowa.”

       Amsa masa Mansoor yay cikin nuna ƙaulani, sai dai baice komai ba ya juya ya fita. MD ya maido da idanunsa kaina yana miƙamin takardun hannunsa. “Ke kuma Samraah ga wannan. Sune tambayoyin da zakiyi, ki ɗan dubasu ko. Sai kuma ya kamata kije ki gyara makeup naki kema gamu nan fitowa.”

        Ɗan jimm nayi kamar bazan amshi takardar ba, MD ya wani marairaice fuska tamkar zai fasa ihu cikin nuna alamar roƙona da idanu. Jinai kamar na balla masa harara. Amma dai na daure na amsa takardun kawai ina faɗin, “Okay Sir” a hankali. Ina daga tsayen na dudduba komai, batare da nace komai ba na ajiye masa a saman tebir ɗin. Sannan na juya na fita. Da ga shi har baƙon nasa ina jin idanunsu a kaina. Da ƙyar na iya ficewa zuciyata na ƙara nauyi ga mamaki da cushewar kai na rashin iya gane komai a wannan al'amari. Dan magana ta gaskiya duka tambayoyin da MD yace sune zan masam sun matuƙar bani mamaki. Na kuma sake tabbatar da lallai akwai wata a ƙasa. Watan da shi kansa MD idan yay wasa sai ya zurma ciki ƙwarai da gaske....


       “Tofa, mi kuke tunani masu karatu🤥? Nima fa kamar na shiga ƙaulanin ne🤔”.


     


✨・o・✨・o・✨・o・✨


           Sosai yasha barci mai lafiya a safiyar ta yau kasancewar a daren jiya ya jima bai kwanta ba. Dan tunda ya dawo massalaci sallar asuba da Ummiensa kawai yayi waya ya sake komawa ya kwanta. Bai tashi ba sai yanzu babu jimawa. Wanka kawai yayi tare da gyara jikinsa cikin wando 3quater mai laushi kalar baƙi da rigarsa fara da adon baƙi kaɗan itama mai laushi. Dogon hannune da ita tare da hula. Sai dai ya saki hular a bayansa, sannan bai saka zip ɗin rigar ba. Hakan ya bama farar singlate ɗinsa damar fitowa sosai tare da ɗamammen cikinsa da har kana iya ganin kwanciyar gurayen kansa dake nuna shi matsayin mutum mai tsananin motsa jiki. Yau dai bai ɗaure gashin ba, sai dai yasha gyara sosai dan daga shi har siririn kwantaccen sagensa sai uban ƙyalli da ƙamshi sukeyi. Ga gashin ya ɗan sakko masa har kafaɗa kaɗan. Magana ta gaskiya babu wanda zai kalla bawan ALLAHn nan ya yarda wai ya haɗa jini da baƙaƙen fata. Dan sam baya kammani da su sai dai fatarsa da tai ɗan diff ba kamar na fararen dake kasancewa jazur ko fari fat ba. Amma shi yanayin da fatar tasa take ma sai ya ƙara masa wani ƙyawu na musamman. Kai tsaye ga coffee machine ɗin sa da ke a falon ya nufa. Cikin mintina kaɗan ya haɗa coffee. Ƙyaƙyƙyawan mug ɗinsa na zallar farin glass ya ɗauka ya tsiyaya fin rabi a ciki. Sannan ya tako a hankali yana kaiwa bakinsa zuwa cikin falon sosai. Furucin daya fito daga cikin television dake aiki a falon ya sashi karkata hankalinsa ga tvn. Dai-dai nan Hayatu ya shigo kamar wanda aka koro. Kaɗan ya juyo ya kallesa cikin yanayin nan nasa na rashin sakewa, sai kuma ya sake maida kansa ga tvn yana sake kai mug ɗin kan ɗan ƙaramin bakinsa ya zuƙi coffee ɗin duk da zafin da yake da shi.

        Hayatu da gaba ɗaya hankalinsa ke a tashe ya ce, “Sir kaga abinda ke faruwa kuw......” sauran maganar ta maƙale sakamakon saukar idonsa akan tvn shima. Da sauri ya ɗan yi baya kamar wanda ke shirin faɗuwa. Ya dai samu nasarar dafe hannun kujerar dake kusa da shi yana bin ogan nasa da ya ƙarasa ya zauna cikin kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya da kallo. Yasan halinsa sarai akan dakiyar masifa dayin biris da abu kamar bai damar ba. Amma magana ta gaskiya wannan bai kamata ai biris ba. Zama yay ya samarwa kansa nutsuwa. Kafin ya furta, “Amma Sir mizai sa Baba prof.. zuwa Kano a yau har yayi hira da yarinyar nan ne? Kodai ya amince da batun buɗe companyn yanzu? Wlhy ni du kaina ya kulle ma”.........✍️



      _Ni ma dai mai ɗaukar rahoton neman ruɗar fani ɗin kuke Hayatu PA.🤥🤔_

    



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments