Breaking News

Tsutsar Nama 21


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚-𝑶𝒏𝒆_



.......Humm Bily a zahirance banda wani dalilin yin hakan kamar yanda kowa zai iya gani ko fahimta. Sai dai ni a ƙasan zuciyata ina jin dole-dolene bai kamata na amsa koma miye ɗin ba. Dan babu dalilin hakan bisa hujjoji da dama. Amma ban sani ba ko kema zaki iya fahimtar hujjar tawa a yanzu. Ko kuma sai anan gaba cikin abinda zai zo a labarin nan nawa. Dan a yanzu kam tabbas babu wani dalilin da nima zan tilasta miki gamsuwa dani. Amma dai muje zuwa ofishin MD dake kirana. 

     (Babu musu na jinjina mata kai, amma magana ta gaskiya al'amarin wannan Sam-G ɗin taku yana ɗan rikitani. A ido zaka iya mata kallon like innocent people. Sai dai a ɗan zaman da nai da ita na fahimci taƙadarar kanta ce. Sannan akwai taurin kai yana jinjirin jaki. Kar dai na cikaku da zance ku muje zuwa dan jin yaya ta kaya a offishin MD)


       Tsaye na samesa yana faman kai kawo a tsakkiyar office ɗin nashi. Sai faman furzar da huci yake kamar wani bajimin rago. Ko ɗar banji ba a raina na rafka sallamata. Juyowa yay yana kallona da idanunsa da suka kaɗa sosai. Kamar wanda ke shirin dukana ya wani zaburo kaina har sai da na ɗan ja da baya ina waro manyan idanuna waje. 

       “Samraah kin san mi kikayi kuwa? Kin san wanene wannan mutumin kuwa? Kin san ƙyautar mi ya baki kuwa? Amma kika watsa masa ƙasa a ido ta hanyar maida masa bayan ya fifitaki sama da kowa. Kuɗi duk ya bama sauran 50-50k, amma ke makullin mota ya baki batare da ko dubawa kinyi ba kika ɗauka kika maida masa...”

        “Mata fa dai?”.

    Na tambaya da iya gaskiya ta. Shima cike da ƙwarin gwiwa ya amsa min da “Yes Mota Samraah. Shiyyasa a kullum nake faɗa miki ke ɗin mai sa'a ce dear”.

      Kaina na ɗan girgiza da murmushin basarwa, na ce, “Humm to amma Sir mi zanyi da shi idan na riƙe? Sannan wace amsa zan bama iyayena idan sun tambayen a ina na samu mota? A shi karan kansa mi ma zaisa ya mana irin wannan ƙyautar haka dan kawai munyi hira da shi?”.

      “Tab ɗin, wlhy yarinyar nan baki da hankali...” ya faɗa cikin ƙunar rai, a take na sake tamke fuskata dan kalmar tasa ta mun matuƙar zafi a zuciya. Duk yanda naso na shanye na gagara hakan, kai tsaye nace masa, “Sir minene abin rashin hankali anan? Bayan kuma na faɗa maka hujjata. Wannan fa rayuwata ce”

         Wani irin tsayawa yay duka hannayensa riƙe da ƙugunsa kawai yana kallona tamkar ya samu television. Ni kam na sake fuskewa kamar ban san yanayi ba. Na fahimci takaicina ne ya maƙureshi ya hana shi cigaba da magana. Dan a fusace ya sa ƙafa ya tunkuɓar da flower base ɗin da akai ado da ita a office ɗin, sannan ya ce, “Samraah out. Get out of my office now..”

      Ko kallonsa banyi ba na juya nai ficewata. In ma ca yay na bar Company ɗin gaba ɗaya daga yau banda matsala da hakan. Ko takan Mansoor banbi ba nai ficewata gaba ɗaya daga gidan. Napep na tare zuwa garejin su Yaya Musaddiq. Na samu suna shirin shiga sallar azhar, sai dai shi Yaya bai kai ga tafiya ba yana ƙoƙarin ɗaura alwala ne. Tun kafin na ƙarasa inda yake na fahimci ya zuba min ido. 

       “Lafiya kike?”.

   Ya faɗa dai-dai ina isowa gabansa shi kuma yana wanke ƙafarsa. Mai makon amsa sai na tura masa baki. Kansa ya girgiza kawai yana sake faɗin, “Je can ki zauna muyi salla to, idan na dawo sai kiyi taɓarar”. Daga haka ya wuce ya barni a wajen dan ya kammala alwalar...



  💫´⊙ω⊙💫⊙ω⊙💫⊙ω⊙`💫


             

        Zaune yake a falo tare da Hayatu da Juliet, tab.. ce a hannunsa, ƙafafunsa miƙe saman Centre table da aka turo gabansa sosai. Hankalinsa gaba ɗaya nakan screen ɗin tab ɗin, hannunsa ɗaya rike da haɗaɗɗiyar chocolate yana ci a hankali tamkar baya so. Yayinda Juliet ke bayani akan abinda ya zaunar da su ɗin, dan itama dai laptop ce a hannunta, sai Hayatu dake riƙe da takardu ta gefenta. Abinda juliet ɗin ta faɗa na ƙarshe ne ya sakashi ɗagowa cikin rashin sakewar nan tasa ya zuba mata ido. Da sauri ta risinar da nata dan Maash nada wani kwarjini dakan hana mai kallonsa iya masa kallon ido cikin ido na tsawon lokaci, koda kayi jarumtar yin hakan da zaran shi ya zuba nasa cikin naka zaka ji ka takura. A ɗan daƙile ya ce, “Ina son magana da Mustapha. Sannan ai cancel ɗin Thailand a cikin schedule namu a maida Finland”.

       Atare su duka biyun suka amsa masa dan zancensa ya shafi kowannensu. Babu ɓata lokaci kowanne ya shiga yin abinda aka saka shi. Juliet ce ta fara ɗagowa cikin harshen turanci tana tambayarsa, “Sir  komai zai zama ne de same date?”.

            Kamar baima jita ba aikinsa yake, sai da ya mula dan kansa sannan ya bata amsa da “Uhm”. Cikin girmamawa ta jinjina kanta da amsa masa ta cigaba da aikinta. Dai-dai nan shima Hayatu ya taso daga inda yake da waya a hannunsa. Ta gefensa ya ɗan tsaya cikin risinawa ya miƙa masa. Batare daya ɗago ba a hankali ya furta, “Sa a hans free”. Da sauri Hayatu ya maidata hans free, sai ga muryar wancan da ya kira da Mustapha rangaɗam. Duk da a cikin waya yake cikin girmamawa ya gaishesa, zaka tabbatar da hakanne ta yanda yake magana cikin ƙanƙan da kai. Shikam kamar yanda ya saba ya amsa a taƙaice. Sannan suka tsunduma maganarsu, duk dai akan harkar business ne, mafi yawan maganar kuma Mustaphan keyinta.. ba wata doguwar magana sukai ba ya barsa suka cigaba da magana da Hayatu. Dai-dai Hayatun na ajiye wayar shima alamar sunyi sallama ɗaya daga cikin securitys ɗin gate yay sallama tare da yin knocking. Hayatu ne yaje garesa yana amsa masa sallamar. Jin abinda security ɗin yace ya sashi ɗan wara ido waje. Sai kuma ya juya cikin falon da sauri. Cikin ɗan yanayin rawar harshen wanda ya shiga ruɗani ya ce, “Sir Baba prof.. ne a gate”.

      Cak Maash ya dakata da abinda yake, sai kuma ya lumshe idanunsa tare da buɗesu luuu gaba ɗaya akan Hayatun. Bashi da alamar cewa wani abu, Hayatu kam duk ya ƙagu yace ɗin. Idanun nasa ya maida ga tab ɗin abinsa batare da yace komai ba. Sake birkicewa Hayatu yayi, sai dai baida tacewa. 

        “A buɗe masa”. 

     Zabura Hayatu yay yana sauke nannauyar ajiyar zuciyar da sai da ta saka Juliet danne dariya. Dan haka ya harareta ya nufi hanyar fita da sauri. Shiko Maash aikin gabansa ya cigaba dayi hankali kwance. Mintina huɗu ba'a cikaba sai gasu kuwa. Baba prof.. ne a gaba. Tun a taku biyu ya tsaya yana bin falon da kallo, kafin ya sauke ƙyawawan idanunsa na tsufa akan santalelen jikan nashi mai ji da lokacisa. Murmushi ya saki a hankali, sai kuma ya cigaba da shigowa cikin falon guards ɗinsa guda biyu biye da shi. Sai Hayatu a gefe. Juliet ma tuni ta miƙe tsaye. Cikin girmamawa ta shiga gaishesa, ya amsa mata da kulawa, har lokacin kuma Maash bai motsa ba balle ya kalla kakan nasa. Hayatu ne yayma guards ɗin Baba prof... da Juliet magana dan haka suka fice suka barsu su biyu.

         A karo na babu adadi Baba prof.. ya sake sakin murmushi. Idanunsa akan Maash ya ce, “Fushinne har yanzu? Common sweetheart ya kamata ka huce mana. Kaifa yanzu babban mutum ne ba little Awwab ɗin nan ba mai hawa saman wuyan grandpa ɗinsa yay doki saboda fitinarsa. Be a man mana my baby boy”.

      Fuska Maash ya sake tsukewa. Batare da yayi magana ba ya dangwarar da tab.. ɗin hannunsa yana miƙewa kamar a fusace zai wuce. Caraf Baba prof.. ya damƙo hannunsa, jawosa yay kawai ya faɗa jikinsa ya rungumesa tsam-tsam yana dariya. Sun jima a haka Maash nata faman sauke ajiyar zuciya, yayinda Baba prof.. keta murmushinsa shi dai. Sai da ya tabbatar ya gama haɗiyar zuciyar kafin ya ɗagosa. Hannu yasa saman kansa ya birkita gyararriyar sumarsa da yau bai ɗaure ba. Babu shiri Maash ya saki murmushi daya sake ƙawata ƙyawunsa. Baba prof.. kuma ya ƙyalƙyale da dariya tare da jamasa dogon hancinsa sannan ya sake maida hannunsa kan sumar tasa ya shiga kwantar da ita yanda take.

       “Dibeka so cute idan kana murmushi. Amma ka dinga ɗaurema mutane fuska har ni ɗin ma Kakanka ban tsira ba. Kai nidai naga takaina da kai balaraben Nigeria”.

      Murmushin Maash ya sake yi, batare da yace komai ba ya girgiza kansa kawai yana nufar kujera ya zauna kamar yanda Baba prof.. yayi. Cikin girmamawa ya gaida kakan nasa, shiko ya amsa masa cike da kulawa, sai kuma yabi falon da kallo yana cigaba da faɗin, “Mutumina alƙawarin ALLAH dai ya cika ka dawo mafari. Hakan nada ƙyau kuma naji daɗi kwarai da gaske. Ina fata kuma za'amin afuwa da rashin cika alkawarin dawowa da nai jiya. Gangar jikin nawane kawai acan, amma zuciyar na nan. Shiyyasa ma ina sauka a Lagos ko gida banje ba na sake biyo jirgi zuwa nan ɗin.”

         “Ba komai ya wuce ai, ina fatan ka dawo cikin ƙoshin lafiya”. Maash ya faɗa cikin tausasa harshe duk da dai maganar da ƙyar take fita. Baba prof.. bai damu ba, dan yafi kowa sanin wanene jikan nasa. Wannan yanayin nashi kuwa halittarsa ce, tun yana ƙaraminsa baida sakewa da mutane. Sannan haka yake dai babu yawan magana. Wasu abubuwa da suka faffaru kuma suka sake maidashi dunɗun dukum ya zama miskilin gasken gaske. Gashi nan dai babu yabo babu fallasa a ɓangaren kirki. Dan babu wanda ke ɗaga masa yatsa bai karya ba. Ya iya rikici da rigima ƴar gaske. Dan tabbas Maash akwai rikici, tsagerane na bugawa a jarida, sai dai yanayinsa na shiru-shiru yasa sai ya zuba maka tsiya yay kamar bashine yayi ba, in kuma za'a tambayi mutum dubu su shedesa suma akan bashi ɗin ne yay ba. Sai dai su da sukai masa sanin ciki da bai na rayuwa, musamman ma shi kakansa da mahaifinsa da mahaifiyarsa sun san shine ya yin......✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments