Breaking News

Tsutsar Nama 20


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_



.......Kamar yanda Hayatu yasan bazaice komai ba baice ɗin ba kuwa. Sai ma aikin shan coffee ɗinsa da yake hankali kwance idanun nasa dai a tvn dan har an fara program ɗin. Gaba ɗaya hirar anyita ne akan abinda ya shafi harkar ilimi a Nigeria. Da rawar da su malamai ɗin suke takawa domin ganin matarbar ilimin ta dawo hayyacinta da ga mutuwar tsayen da tayi musamman daya kasance tun daga tushene. Dan yanzu secondary schools tafi kowace gaɓa lalacewa a harkar karatu, in ba makarantar kuɗi zaka kai yaranka ba sai a hankali. Gashi kuma Sakandire ɗin nan ne ake ganin tamkar mahaɗar dake riƙe da kowanne reshen ilimin dan anan ne ake karatu tuƙuru cikin halin ƙuruciya da babu wasu damuwoyin fara fuskantar ƙalubalen rayuwa irin na girma. Wannan hira ta matuƙar ɗaukar hankalin mutane, inda ta haifar da cecekuce sosai tare da yaba ma prof... ɗin. Dan tun kafin a kammalata saƙwanni sun cika kowane dandalin sada zumunta na wannan gidan tv da rediyo. Yayinda wasu ke tattaunawa a dandilansu na sada zumunta. A cikin awa ɗaya da akai da Prof.. K/Mashi an amsa harda wayoyin mutane, ya kuma bada cikakkun amsoshi masu jan hankali da suka sake birge mutane da ganin kimarsa da girmansa. Duk da a baya ana zaginsa akan yanda yake aiki tuƙuru ma kudancin Najeriya ɗin kasancewarsa mazaunin can shi da gaba ɗaya zuri'arsa. Dan wasu na ganin a komai nasa bama ya alaƙanta kansa da arewa sam, tamkar ma baida wani alaƙar dasu, musamman idan yana sukar ƴan siyasar arewan da ƙalubalantar shuwagabannin yankin.

         Koda aka kammala ma babu alamar Maash zaice wani abu. Zuwa yanzu dai kansa na jingine da kujerar idanunsa a lumshe. Ta ƙasan ido Hayatu ke kallonsa da nazartarsa. Sai kuma a hankali ya furta, “Sir miza'a kawo maka breakfast?”.

      Shiru babu alamar zaima motsa balle ya tanka masa. Sai kuma dai cikin motsa lips da ƙyar ya furta, “Waka ɗora akan aikin bincike akan yarinyar nan?”.

           Ƙasa Hayatu yay da kansa, cikin girmamawa sosai ya amsa da, “Da kaina nayi Sir. Dama abinda nazo kawo maka kenan. Sai kuma wanda zai ringa bibiyar tata ne kuma ina kan nazari. In sha ALLAHU daga nan zuwa yamma zan kawoshi shima.”

    Yana daga kwancen ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonsa. Hayatu ya ƙara rissinar da kansa yana ɗan murmushi, dan yasan abinda yay ɗin ya faranta ran ogan nasa koda bai fito ta faɗa ba. Ci gaba yay da faɗin, “Sunanta Samraah Abdul-wahab Gwarzo. Wasu kan kirata Sam-G. Tana da yaya Musaddiq da ƙani Hafizzullah. Musaddiq ɗin makanike ne, shike riƙe da rayuwarsu, ƙanin nata kuma na jami'ar Umaru Musa Yar'adua dake Katsina yana karatu. Iyayensu sun jima da rasuwa, a hannun Uncle ɗinsu suke tun suna ƙanana. Akwai wani yaro Mansoor da ko yaushe suna tare shine zata aura dan har maganar iyaye ta shiga. A zahiri Samraah bata da hayaniya ba kuma sabgar kowa take shigaba sai in itace taso hakan. Sai dai kuma tana da tsiwa a wasu lokutan musamman ga wanda ya shigar mata hanci. A shekarun baya kaɗan ta fara rubuce-rubuce kan abubuwa masu muhimmanci musamman da suka shafi ƙananun yara mata dake tallace-tallace a tituna. Sai dai tunda ta fara wannan aikin ta ɗan rage hakan. Bincikena kuma ya tabbatar min tanada fans sosai, dan a duka shafukanta akwai fallowers dake fallowing ɗinta sosai. Na tabbatar da yanda suke jin daɗin karatun rubuce-rubucen nata ne ta hanyar comments da suke mata. A office kuwa tana fannin ƙananun ma'aikata ne. A ɓangaren rediyo ta fara aiki kuma. Sai dai ƙwazonta da yanda program ɗin data bada shawarar samarwa akan matasa ya amsu, ya saka suka maidata itace mai gabatar da program ɗin. Da kuma a iya rediyo kawai akeyinsa, amma yanayin karɓuwarsa yasa suka koma gabatar da shi har da television, sannan shi MD ɗin su ne ya bata power sosai a al'amarin. Shiyyasa ma ake zargin yana sonta ne duk da yasan akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninta da shi wancan yaron Mansoor, amma har yanzu bai san iyayensa sunje gidansu ba ma har anyi maganar aure.” ɗan matsawa yay gabansa yana yunƙurin ajiye tab.. ɗin dake a hannunsa yana cigaba da faɗin, “Nayi fallowing duka shafukanta, gashi ko zaka duba”.

        Hayatun ya ɗan kalla sai kuma ya ɗauke idanun nasa. A daƙile ya ce, “Ba buƙata. Ka kammala komai dan zuwa jibi maybe zamu wuce. Ka tura ma MD nasu takardar amsa gayyatar da tai min, sai dai kar ya wuce gobe” daga haka ya miƙe. Har ya shige bedroom ɗin sa Hayatu da kansa ke ƙasa na binsa da kallo. Sai kuma yaja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi yana kaiwa zaune cikin lallausar kujerar dake a falon. Tagumi ya zuba da hannaye biyu, gefe ɗaya mamakin komai yake yi, wani gefe kuma na ayyana masa akwai abinda ogan nasa ke shiryawa. Kuma tabbas da wahala ace zai kasance mai daɗi, yana tausayin yarinyar nan, dan ta taroma kanta match. Bashi da zaɓin daya wuce cika umarni, dan haka ya ɗauka tab.. ɗinsa. A take yay kiran wani tare da buƙatar number ɗin MD na gidan tvn na AlHERI. Ko mintuna biyar ba'a cikaba kuwa sai ga saƙon Number ɗin ya shigo masa. A take ta shirya text message ya tura musu kamar yanda Maash ya umarcesan.....


    Yayanmu nima fa ka fara ban olo gaskiya😌🥺🥺.


      🌟(☉。☉)!(☉。☉)!(☉。☉)🌟


          

          Sam nutsuwa bata ɗan dawo jikina ba sai da aka kammala duka program ɗin. Bayan an ɗauke camara daga kanmu na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi ina mai lumshe ido. Ɗan kallona prof.. yay a kaikaice sai kuma yay ɗan murmushin manya yana miƙewa. Yana fita a ɗakin shi da MD sauran ƴan uwana ma'aikata sukayo kaina. Ruwa aka fara bani nasha, na sake samun nutsuwa sannan nima na miƙe. Muna daga harabar gidan ni da Mansoor dake lallaɓani muje muci abinci aka aiko kiranmu. Dole cikin muka koma. Inda muka samu dukkan ma'aikatan da suka bada gudunmawa a program ɗin har ƴan bayan fage a office ɗin MD. Zama mukayi kamar kowa muma. Daga haka Prof.. ya fara mana bayanin godiya, tare da sanar mana dalilinsa na gabatar da wannan program ɗin cikin gaggawa haka. Sosai muka nuna gamsuwarmu. Musamman ma ni da kaina duk ke a ɗaure da farko. Ƙyauta dukanmu ya danƙa ma kowa a envelope ɗinsa. Daga haka yay mana godiya muma muna masa. Sai dai me ni sam hankalina ya gagara tsayawa waje guda akan hakan. Kallo na fara bin sauran ƴan uwana da shi, kafin na miƙe zaram kamar wadda akaima allura nabi bayansa da sauri. Mansoor na ƙoƙarin tsaidani da son jin ina zanje bamma sauraresa ba na fice da sassarfa. Isowata yayi dai-dai da buɗema prof.. mota zai shiga. Ga mutanensa zagaye da shi kamar zasu iya hana mutuwa ɗaukarsa. Amma ko'a jikina nai sallama kaina tsaye. Su duka juyowa sukai suna kallonna musamman MD da yay rakkiya tare da Prof.... 

        Fuska ɗauke da murmushi Prof.. ya ce, “A'a ɗiyata ko kinyi mantuwa ne?”.

    Ƙasa nai da kaina ina ɗan murmushin ƙarfin hali. Kafin cikin ladabi da dakiyata na ce, “A'a ranka ya daɗe. Dama uhm....” sai kuma nai shiru na kasa cigaba da faɗa ganin yanda suka tsatstsareni da idanu su duka. Murmushi mai sauti Prof... yayi yana sakin murfin motar ya juyi gareni da ƙyau. “Daughter yi maganarki ƙofa a buɗe take ai. Ko mu koma gefe ne?”.

     Da sauri na ce, “A'a Sir ba sai munje ko'ina ba. Mun gode sosai da karamcinka garemu, amma dan ALLAH kayi haƙuri zan dawo da wannan dan ana biyana albashi akan aikina, kuma yana wadatar dani”.

      Bashi ba hatta MD ina ganin yanda yay wani irin sororo yana kallona. Ni dai na ɗauke kaina ina miƙama yaronsa daya raba mana envelope ɗin. Ganin ya tsaya yana kallona bashi da niyyar amsa na ɗaura masa kan kayan hannunsa na juya a nutse na bar wajen. Ina jin yanda idanunsu sukai min riiiii aka. Amma ban waiwayo ba. Cin karo muka kusan yi da Mansoor da alamu suka nuna biyoni yayi. Na ɗan ja da baya ina faɗin, “Ya salam I'm sorry ban san ka taho bane”.

        “Babu damuwa” ya faɗa yana kallon hannuna. Fahimtar hakan yasa kai tsaye nace masa “Na mayar musu ne?”.

     “Mi ɗin?”.

   Ya faɗa cikin waro idanunsa sosai waje. Bakina da ke cikin face mask na tura gaba da faɗin, “Yo abinda suka bamu. Ni gaskiya bana ra'ayi dan zuciyata sam bata ma kwanta waje ɗaya ba. Ta yaya mutum zai taso rana tsaka ya ce muyi hira da shi babu wani goron gayyata babu notes sannan ya kuma kawo wani abu ya bamu wai matsayin ƙyauta. Dan ALLAH kai baka ji abin banbarakwai ba? Shine fa wanda kwanaki akaita kace-nace ɗin nan akansa game da abinda ya faɗa akan shugabannin arewa. Gashi kuma da bakinsa ya faɗa shi haifaffen jihar Kano ne. Amma bai ragi balle ragowa wajen sukar mana mutane kamar wani maƙiyinmu”.

       Idanu kawai Mansoor ya zuba min kamar mai nazari. Ya buɗe baki zaiyi magana sai ga MD ya iso kamar a fusace. Dan cikin yanayi kamar faɗa-faɗa ya ce, “Samraah sameni a office”.

        Sai da na taɓe bakina dake a cikin face mask sannan na amsa masa da to ciki-ciki. Yana juya baya kuma na bisa da harara. Ƙin tafiya nai har sai da Mansoor ya mun magana. Batare da shima na tanka masa ba na wuce fuu nabi bayansa........✍️



     *_“Amma Samraah miyyasa kika ƙi amsa bayan kuma kema kin gamsu da bayanin da yay muku na dalilin hirar? Sannan kin siffantashi da mutane kirki a halittar jiki da yanayinsa, kuma bayanansa sunja hankalin mutane da yawa a yau ɗin har hakan ya sake ɗaga darajar gidan tvn ku?”._*



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments