Breaking News

Tsutsar Nama 25


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒊𝒗𝒆_



.......A karon farko na sauke ajiyar zuciya. Sai kuma a hankali na ce, “Kayi haƙuri Sir an samu kuskuren fahimta ne kawai saboda ni bakamin bayanin komai ba. Kuma nima banƙi amsar ƙyautar tasa da wata manufa bane, kawai dai albashin da ake bani ya wadatar dani”.

       “Humm kuma gashi ya dawo min da abinda ya bakin akan lallai na maida miki. Na kuma baki haƙuri tare da roƙonki kan ki amsa dan ALLAH.”

    “Gaskiya bazan amsa ba Sir kuyi hakuri. Dan Yayana zai ɓata min rai matuƙa. Nima kuma a karan kaina ma nayima kaina alƙawari a gafarce ni”.

       Shiru kawai yay yana kallona. Nasan mamakin taurin kaina yake yi. Dan har fuskarsa ta fara nuna jin haushi. Sai dai bai sake cewa komai ba akan batun face, “Okay ba damuwa. Sai batun mutuminki, a jiya PA ɗinsa ya turo mana takardar amsar gayyatar da kikai masa. Tare da bamu zaɓin lokaci amma kada mu wuce yau. Adai taƙaice yanzu haka ya tabbatar mana zai shigo kafin 11am, amma awa ɗaya kacal zai yi da mu. Dan haka yanzu zaki je ki kasance cikin shiri, nama su Tsanyawa magana akan su shirya kayan aiki da zauren da zaman zai kasance. A yanzu haka kuma sun fara in sha ALLAH”.

          Har cikin raina sai da naji zantukansa na dukana. Amma sai na dake na amsa masa da to kawai. Shima bai sake cewa komai ba ya miƙamin takardar gabansa. “Ki nazarci wannan, idan kina da wata idea sai ki ƙara, nan da awa ɗaya ki kawo min na gani. Zaki iya tafiya”.

       Zaram na miƙe kuwa na fice abina ko waiwayensa banyi ba. Zuciyata kuwa sai wani irin kai-kawo take. Ina fita kuma na dallama office ɗin harara. Ɗagowar da zanyi muka haɗa ido da Bashira, ashe tana tsaye a wajen bata tafi ba. Ko takanta banbi ba dan ba'itace a gabana ba nai wucewata a raina ina faɗin (Ballagaza kazar sakarai). Koda na koma office duk yanda naso samun damar tunani hakan bai yiwu ba. Dan su Ruƙayya tuni sun baibayeni da surutu akan ɗan ta'addan mutumin can mai kisan kai dako sunansa ban riƙe ba. Bana kuma fata ko ra'ayin riƙewar ma. Dan haka nafi maida hankali akan aikin gabana fiye da hirar tasu dan dama ba tofawa nake ba. A haka har lokacin da MD ya ban ya cika. Miƙewa nai na fita maida masa file ɗin. Yanda naga yana faman washe baki na tabbatar da abinda nai ɗin ya masa. Dan a take ya ɗaga waya yay kiran sauran wanda zamuyi aikin tare. Bayani ya sake mana ta yanda zamuyi komai ya ƙayatar ya kuma sake ɗaga kimar gidan namu. Ni sai ma naji kamar na makesa. Dan na fara saka MD a cikin jerin sunayen mutane mayun kuɗi. Jiba yanda yake rawar ƙafa tamkar zai ci da ka. Yana sallamar mu muka fice zuwa inda aka gyara domin gabatar da shirin. Makeup ɗin da akace na ɗanyi ƙi nai, sai ma shashsha musu ƙamshi nake famar yi. Sai da MD ya dinga lallashina sannan na ɗan sake saka fauda da ɗan lips gloss, daga haka ban sake bi takan komai ba na nema waje na zauna.


       10:42am dai-dai aka sanar da isowar sa. Gaba ɗaya wanda ke a ɗakin MD yace mu fita a tarosa. Ko motsi banyi ba. Bamma da alamar hakan. Ganin MD na ƙoƙarin maido hankalinsa kaina nai saurin miƙewa nace zanyi fitsari. Babu yanda suka iya dani dole suka barni na fita zuwa bayi, su kuma suka fita tarbosa. Sai da na kwashe mintuna biyar da nake jin tabbacin duk ƙasaitarsa ya riga ya shigo sannan na koma. Har yanzu face mask ɗina na a fuskata dan haka baka isa gane yanayina ba. Tun kafin na ƙaraso na fara cin karo da gardawansa. Kallo ɗaya na musu na ɗauke kaina, dan ganinsu ma takaici yake sani. Yo banda rashin tawakkali miye na ajiyesu shi ba jami'in tsaro ba, shiba jinin sarauta ba, kawai dai giyar kuɗi da iyayi. Koda yake maybe al'adarsu ce hakan, tunda naga shima kakansa da nashi shekaran jiya. Baki na laɓe dai na ƙarasa shiga cikin takuna na nutsuwa da kowa kema kallon na yanga. Kaina tsaye na koma ɗakin da za'a gabatar da shirin, iya ma'aikatan mu kawai na samu a ciki suna ƙara gyagygyarawa. Ciki-ciki na sauke ajiyar zuciya ina mai ƙarasawa ciki. Ban tambayi kowa ya iso ko bai iso ɗin ba. Sai Usman ne yay tsulum yana faɗin, “Sam-G ki kasance cikin shiri baƙonmu na office ɗin MD yanzu haka. Nan da ƴan mintuna zasu shigo nan”.

       Cikin taɓe baki na ce, “In dai ba mala'ikan mutuwa ne zai zo ba kuma dai Usman ai shirina yayi”.

     Dariya ya sanya ƙasa-ƙasa. Ni kuma na cigaba da duba takardar hannuna. Goma da mintuna hamsin da biyar dai-dai Tsanyawa ya shigo yana sanar mana gasu nan tafe shi da MD. Sake kimtsawa kowa ya shigayi, banda ni kam, dan ko motsi banba daga yanda nake zaune balle na cire idanuna daga takardar dake a hannuna. Duk da face mask dana saka bai hana turarensa dukan hancina ba. Wannan dai fitina da yawa take, nikam bana rabe muku ɗayan biyu shima turaren na jinin tsafi ne shiyyasa yake danne ƙarfin duk wani turare idan mai shi yana waje. To nidai gaskiya ba yafewa zan ba, dan nawa kamfanin turaren suna iya nasu ƙoƙari suma. Jin yanda ɗakin yay tsitt kamar babu mutane yasa takaici sake kume ni. Chewing gum PA ɗin nan nasa ne ya fara shigowa, dole ne a kirasa chewing gum saboda koda yaushe dai yana manne da shi. Kusan a tare suka shigo da MD, sai wani rawar jiki yake da ƙanƙan da kai abin takaici. Duk wanda ke a zaune miƙewa sukayi, banda ni da takaicin MD ya sani ɗauke idona da nake musu kallon ƙasa-ƙasa da ban san mike faruwa ba. Ashe su Usman da ke zaune a inda nake duk sun tashi wai domin girmamawa.

         “Samraah!”.

    MD ya kirani ƙasa-ƙasa, banji ba dan haka Usman dake tsaye ta gefena ya ɗan bubbuga kujerar. Da farko sharesa nayi, dan nazata surutunsa ne ya tashi, ganin ya cigaba na ɗago ina harararsa. Idanunsa ya ɗan rumtse cikin yanayin matse fuska tare da mun nuni da MD ƙasa-ƙasa. Sai lokacin na lura da kallon da MD ɗin ke mun. Kowa na ɗakin nabi da kallo, ganinsu duk a tsaye shi kaɗaine zaune a inda za'a gudanar da program ɗin PA ɗinsa tsaye a kusa da shi ya ɗan ranƙwafa yana nuna masa abinda ke cikin tab ɗin hannunsa ya sani miƙewa batare dana sake kallon MD ba na ce, “Sorry Sir”. 

     Kansa kawai ya ɗan girgiza da mun nuni da can ɗin. Komai ban sake cewa ba na wuce inda zai kasance nawa mazaunin. Kujeru ne guda biyu kacal suna ɗan facing juna kaɗan, sai table a gabansu an ɗaura glass cup guda biyu masu ɗauke da ruwa, sai dai an rufe su da ɗan ƙananun fai-fai. Ta ƙasan ido na ɗan kallesu dan koda na zauna ban tanka musu ba ban kuma cire face mask ɗin fuska na ba. Yau ma dai suit ɗinne jikinsa milk colour, rigar ciki, belt da takalmansa ne kawai suka kasance coffee. Sai wani almurin agogo dake hannunsa da duk da ban san kuɗin agogo ba a kallo guda zaka san ba'a sayesa da kuɗi kaɗan ba. Dan coffee fatarsa ma kawai ka kalla kasan ba'a magana. Yau ma babu kitso bai kuma ɗaure gashin ba. Ya sakesa ne kawai baya ya sakko masa har akan kafaɗa kaɗan, akwai kuma coffee ɗan kunne ɗaya a kunnensa na dama yau ma ya manna. Sannan babu neck tie, maɓallan ma rigar cikin ta sama a buɗe suke.... Umarnin cire face mask ɗin fuskata da aka bani ya maidoni hayyacina. Cikin taɓe baki na janye idanuna dake cikin eyeglasses daga kansa ina yin abinda akace ɗin, dan lokacin fara gabatar da shirin yayi. Shima PA ɗin nasa wajen ya bari, yayinda ɗaya daga cikin abokan aikina ya ƙaraso gabansa, cike da ladabi ya maƙala masa abin magana a jikin jacket suit ɗinsa. Nima miƙomin yay na maƙala a jikin hijjab ɗina. Sai da aka tabbatar mun gama kimtsawa sannan aka ɗora camara a kanmu. MD ne cikin yanayin marairaicewa yay mun alamar na ɗan saki fusakata, jinai kamar na hararesa, amma na dake kawai cikin basarwa. Kamar bani ba, tuni yanayina ya koma zuwa sauƙaƙa fuska, sai da na kalla camara naima masu kallo sallama tare da gaisuwar barka da wannan lokaci da musu albishirin shiryawa tsaf domin ganin babban kamun da wannan shiri yayo musu yau a bazata sannan na juya garesa a yanayin jan class ɗina na ce, “Assalamu alaikum ranka ya daɗe”.

       A hankali ya motsa lips ɗinsa ya amsa min da “Wa'alaikissalam” cikin muryar nan tasa a daƙile. Bazaka taɓa fahimtar kallona yake ko ba hakaba, saboda akwai eyeglasses mai duhu a idonsa. Yinai kamar ban damu da abinda yay ɗin ba nima, na cigaba da faɗin, “Wannan shiri na maka barka da zuwa, tare da nuna farin ciki matuƙa na cika alkawarin amsa gayyata a cikinsa a lokacin da kowa baiyi zato ba. Na tabbata hatta masu kallo ma zasu kasance cikin farin ciki maybe ma harda mamaki. Amma dai barkan ka da zuwa”.

       Nan ma a takaice ya furta, “Barka. Tare da fatan alkairi ma kowa”.

    (Ɗan rainin hankali) na faɗa a zuciyata. A zahiri kam na ce, “Masha ALLAH. To masu kallo, zan iya cewa duk sai ku sake matsowa gaban akwatinan talabijin naku, masu rediyo su ƙara sauti domin ji daga bakin babban baƙon namu.” Sake juyowa nai garesa ina faɗin, “Ko zamu iya sanin cikakken sunanka ranka ya daɗe?”.

      Cike da wani salo da sake harɗe ƙafafunsa da yay crossing cikin motsa lips ɗinsa kaɗan ya ce, “Awwab El-Mu'azz K/Mashi. Sai dai Maash akafi sani”.

    “Aiko nasan masu kallo zasu so sanin minene ma'anar Maash ɗin nan ranka ya daɗe?”.

       Sai da ya bushi iska na wasu sakanni sannan yay wani ɗan murmushin gefen baki, a taƙaice ya ce, “Kwanar Mashi ne ainahin sunan tushena kenan, abokai suka maida shi Maash tun ina secondary school, daga nan kawai ya zama ana kirana da shi”.

     “Uhhm Masha ALLAH. To ko zamu iya sanin wanene Maash a takaice. Dan wannan amsa ce da mutane suka jima suna son ji daga bakin ka amma basu samu damar hakan ba?”........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments