Breaking News

Tsutsar Nama 24


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_



......Sallamar Yaya Musaddiq da naji a falo bayan sallar isha'i ta sani miƙewa daga kwancen da nake zazzaɓi ya rufe ni. Nasan kuma ba komai ya jamin hakan ba sai caskalen da mukayi dan da gaske naci duka a wajensu. Daga inda nake na zubama Yaya Musaddiq daya dire baƙar leda a gaban Abba idanu na dake cika da ƙwalla. Yayinda kunnena ke sauraren abinda yake faɗa.

       “Abba ga kuɗin sarƙar nan a bata. Naira dubu ɗari huɗu ne kamar yanda ta faɗa”. Daga haka ya miƙe ya nufi hanyar fita. Cikin sauri na take masa baya batare da nabi takan shewar da Mom keyi ba kuɗin daya ajiye ɗin a hannunta dan bata bar Abba ko taɓawa yayi ba. “Yaya!”. Na kirasa da sauri ganin bai san ina bin bayansa ba. Tsayawa yay tare da juyowa yana kallona. Ina isa garesa na kamo hannunsa na wani ƙankame ina mai fashewa da kuka mai ƙarfi. Shiru kawai yay yana kallona. Tsahon minti ɗaya batare daya ce komai ba ya kama hannuna kawai muka nufi ɗakinsa. A bakin tabarmarsa ya zaunar dani, sai kuma ya sake fita batare da yace dani komai ba nan ma. Tun ina kuka daga zaune har na zame na kwanta Yaya bai dawo ba. Sai da ya ci kusan mintuna goma sha biyar sai gashi da ledar magani da dafaffiyar indomie. Zuwa sannan nabar kukan sai jan ajiyar zuciya nake kawai.

     Abincin ya tasani gaba mukaci tare cikin lallashi, ya kuma bani magungunan nasha suma da ƙyar dan bana son magani, allura kam tsoron da nake mata ai ba'a magana. Ganin baida niyyar cemin komai har sannan akan kuɗin daya basun muryata na rawa nace, “Yaya ina ka samu kuɗi ka basu bayan kasan kuma ban aikata ba. sharrinsu ne kawai ya tashi ko kuma makircin Mom dan ta samu kuɗin dama”. 

     Ɗan murmushi ya saki tare da ɗora hannunsa a kaina. “Ki kwantar da hankalinki kada kuma ki damu da abinda sukayin, tunda ALLAH yasan bake kika ɗaukar musu kaya ba ya rage nasu. Bana son naga kina wannan kukan sam. Kuɗi kuma wanda nake asusune dama akan hidimar aurenki tuni, ALLAH zai kawo mana mafita kafin lokacin dan shi mai rahama ne mai jin ƙai, dan ko a yanzu da suka amshi wannan nasan bazamu kunyata ba daga abinda ta rage mana. Kar kuma ki saka abinda sukayi ɗin a cikin ranki ko kice sai kin rama dan na sanki kuma bajin magana kike ba, ki bari UBANGIJI da kansa ne zai rama miki wannan faɗan, dan bazan gushe ba ina mai kai masa ƙarar su garesa, kasancewar sa Sarkin daya haramta zalunci a karan kansa balle ga bayinsa nasan bazai barsu ba Samraah. Ki cigaba da haƙuri kinji, watarana sai labari, komai zai shuɗe tamkar ba'a taɓayi ba. Kwana nawa ma ya rage miki a cikin gidan, ƙarƙari ki ƙara wata biyu fa, dan ko yau mun sake magana da Mansoor a weekend ɗin nan iyayensa zasu sake dawowa a tsaida rana, dan su sun ma so ayi komai a randa sukazo Abba ne bai basu haɗin kai ba. Ke dai kawai ki cigaba da haƙuri, dama in aski yazo gaban goshi yafi zafi”.

       Wasu hawayen ne masu zafi suka sake ɓalle min, Yaya Musaddiq yasa hannu yana sharemun da murmushinsa. Wanda ni nasan yana yinsa ne kawai amma shima ransa a ɓace yake matuƙa. Dan idanunsa jazur suke sosai.....


    

💦💦💦💦💦💦

   

     Da ƙyar Sani ya iya nutsuwa Hayatu ya masa bayani dan shigar 500k ɗin nan a account ɗinsa ta rikitashi matuƙa, daɗin daɗawa kuma Hayatu ya ƙara masa da 100k ƙyauta injisa kash a hannu. Ga kuma key ɗin mota da zai yi aikin da ita. Sai kawai Sani ya fashe da kuka. Dan abunne yazo masa ɓakatatan babu zato. Harga ALLAH zai iya rantsuwa bai taɓa ganin dubu ɗari biyar a dunƙule ba. Dan su talakawane sosai, ko karatun nan yayisane da ƙyar cikin buga-buga saboda yana matuƙar son yin karatu a rayuwarsa. A hakanma da ƙyar aka kammala, dan dai ALLAH ya bashi ilimine ma dan yanada basira sosai.. Kasancewar Hayatu har gida yaje yayma babansa bayani akan ogansa ya ɗauki Sanin aikin tuƙi koda yaje gida da mota babu wanda ya tambayesa, sai ma murna da suka taya shi. Kuɗi kuwa ko na wajen hayatu ma bank ya wuce aka saka masa su. Da dubu ashirin kawai ya shiga gidansu kamar yanda Hayatu ya bashi shawara, gaba ɗaya a yinin wannan ranar bakinsa yaƙi rufuwa. Motar ya kai aka duba kamar yanda Hayatu ya umarcesa, bayan an tabbatar komai zam ya koma da ita gida...


        

🌟💞🌟💞 🌟💞 🌟


      A ɓangaren su Hayatu da ogansu Maash kuwa babu wanda ya sake saka shi a ido sai da la'asar, dan shi baya sakaci da ibadarsa, duk wanda ya san Maash ya sanshi akan hakan. Mutum ne mai matuƙar riƙo da ibada, ko'a tsakkiyar taron turawa yake, komai muhimmancin kasuwancin da yake in har lokacin salla yayi sai yay excusing kansa ya fita yayita, koda kuwa zai iya rasa wannan kasuwancin ne hakan bai damesa ba. Koda ya dawo sallar ma ciki ya koma abinsa. Sai bayan sun dawo sallar isha'i ne Hayatu ke sanar masa saƙon da gidan tv'n ALHERI suka turo game da amsa gayyatarsu da yayi. Sun buƙaci ya bada lokacin da duk yake so daga takwas na safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu har zuwa tara na dare. 

      Sai da yay ɗan jimma kamar bazai tanka ba kafin ya kalla agogonsa. Da wani salon lumshe idanu dai-dai yana ɗagowa ya furta, “Ƙarfe nawa Abubakar zai zo?”.

     “Eh Sir kamar yace zuwa four na pm ne. Dan zai baro Abuja kamar Three”.

    “Kafin lokacin akwai wani abu ne?”.

     “A'a gaskiya. Dama dai ganawa da Senetor Kibiya ne, kuma kace Juliet tai magana da shi.”

           “Okay ka sa musu ten to eleven kawai. Dan awa ɗaya zan iya basu”.

     “Ai hakama sun gode Sir”.

   Hayatu ya faɗa yana danne mamakinsa. Da ga haka Maash bai sake tankawa ba. Dan haka Hayatu ya fice ya barsa dan ya huta.....



(◕‿◕)➜(。◕‿◕。)➜(◕‿◕)


         Washe gari Monday da ƙyar na iya danne zuciyata nai aikin gidan kafin nai shirin fita. Nayi aikinne kawai dan nasihar Yaya Musaddiq. Ina kammalawa kuma ko karyawa ban ba nai ficewata. Na samu shima Yaya Musaddiq ya shirya, dama yace min yanada uziri akwai aikin wani mutumi da zai ƙarasa saboda yau da safe zai zo ya amsa motarsa. Tunda muka fara tafiya babu wanda ya tankama ɗan uwansa tun bayan gaishesa da nayi, a haka har muka iso. Yana ajiyeni ya bani 1500. Godiya na masa na shige shi kuma ya wuce.


        Sani da tun fitowarsu gida yake biye da su daga can nesa da wajen ya samu waje yay parking. Kujerar motar ya kwantar abinsa yay kwanciyarsa ya buɗe data da sabuwar wayarsa daya siya jiya. Tunda yanzu babu aikin wahala ai kuma abinyi ya samu kenan. (🤣)


      Ina shiga office ɗinmu na samu kira office ɗin MD. Takaici kamar nace bazanje ba amma dai na miƙe dan nasan hakan bai dace ba. Kamar yanda na saba sai da nai sallama ya bani izinin shiga sannan na shiga. A ciki na samu wata ma'aikaciyarmu mai suna Bashira, tunda na fara aiki a  gidan nan nake ji ana faɗin son MD take kamar ta mutu. Amma shi yaƙi bata haɗin kai. Ina shiga da harararta na fara cin karo, ni saima taban dariya, amma dai banyi ba na ɗauke kaina kawai dan ba itace a gabana ba. Batare dana sauke face mask ɗin fuskana ba na ce, “Good morning Sir?”.

        A sake ya amsa min da “How are you?”. Kamar bashi ne jiya ya gama tijareni harda korana a office ɗinsa ba. A taƙaice na ce, “Alhamdullah Sir ance kana kirana”.

       “Eh zauna”.

    Ban musaba na zauna saboda ganin cika da batsewar da Badhira keyi. Sai da na zauna a daƙile nace mata, “Morning”. Duk da tana sama dani. Aiko harzuƙa naga ta sake yi. Sai dai kafin tace wani abu MD ya tari numfashinta da faɗin, “Uhhm inaga na gama da ke ko Bashira, zaki iya tafiya zuwa anjima zan shigo department ɗin naku dan ina son ganin yanda zakuyi aikin”.

       Kamar bazata muƙe ba sai kuma dai ta tashi a fusace tana cewa, “Okay”. Fuuu ta fita a office ɗin harda bugo ƙofa ji kake jifff. Daga ni har shi ƙofar muka kalla, ya girgiza kansa ni kuma na taɓe baki. Sai kuma ya kallan yana yin ƙaramar ƙwafa. “Sam bata da wayo. Ban cika son mace shasha mara aji irin haka ba”.

    Ban tanka masa ba ni dai, dan babu abinda ya shallan sunfi kusa. Nima ban wuce ya zagan da abinda yafi haka ba tunda dai namiji yake. Ganin ban tanka ba shima sai ya saki batunta ya kama wani. Cikin lallashi ya ce, “Samraah sam banji daɗin abinda kikayi jiya ba ga babban mutum irin professor K/Mashi ba. Mutum ne mai mutunci da dattako. Yanda kike zatonsa sam ba haka yake ba. Kuma bada wata manufa ya mana wannan ƙyautar ba face dalilin abinda kikayi a wajen taron jikansa. Yaji daɗin yanda kika sakashi ya maganantu har ya amsa zaiyi hira da wannan gidan tvn namu. Maganar yin tasa hirar kuma bawai a jiya ne aka shiryata ba. Dama mun jima da tura masa goron gayyatarmu har a karo uku tun sanda akai wannan dogon yajin aikin na wata biyu daya shuɗe har yaya wata magana akan gwamnonin arewa datai matuƙar tada hazo amma yana bamu haƙuri saboda baya ƙasar, yana india ganin likita ne. Yanzu haka a jiyan kuma daga can nan ya sauka saboda taya jikansa murnar buɗe company da kuma amsa gayyatarmu. Kuskuren da aka samu dai shine da yace ba zaiyi hira da kowa ba sai ke saboda abinda kika yi a jiyan ya matuƙar ƙayatar da shi”.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments