Breaking News

Tsutsar Nama 29

 *_Typing📲_*
















   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆  𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_



........Washe gari kamar yanda Mansoor ya faɗa muna a hanyar dawowa gida ya turamin saƙo na jerarrun kalaman godiya ga ALLAH. Tare da sanar min an tsaida wata ɗaya kacal, nanda kwana talatin in sha ALLAHU na zama mallakinsa. A gidansa zanyi azumin watan Ramadan. Duk da naji farin ciki ban maida masa reply ba, dan ina cikin mood mara daɗi na rabuwa da Hafizzullah. Shima mun barosa harda hawayensa. Munko samu gida cike da kayan sweet, biscuits da drinks a falo. Harda su goro sai akwatina guda biyu. Yanda babu wanda yay min magana akan kayan nima banma kowa ba. Sai auta ne ke faɗamin Uncle Mansoor ya gaya masa kayana ne. Sai kuma habaicin da Baby keta saki ranta a ɓace. A kallo ɗaya da nai mata kuma na fahimci tasha kuka. Ban kulata ba dan ba itace a gabana ba. Washe gari Monday na wuce aiki da wuri. Bayan mun dawo na tarar da Gwaggo Gudidi tazo daga Dawanau. Kakace a wajenmu, dan ƙanwar kakarmu ce, mahaifiyar su Abba da mamanmu kenan. Ba sosai take zuwa gidan ba saboda wulaƙancin da Mom ke musu. Mu kuma Abba baya barinmu zuwa wajenta, garama Yaya yanzu daya mallaki hankalin kansa yana zuwa abinsa. Yanzun ma shine ya kirata ya gaya mata komai ganin Abba baida niyyar saka danginsa ko ɗaya a batun auren nawa. Ƴan Gwarzo kuwa sun kwashi nasu kason kayan da za'a rabama mutane sun wuce dasu tun jiyan, dan bamu samesu ma a gidan ba. Nayi murna ƙwarai da ganin Gwaggo Gudidi. A take na shiga hidima da ita dan naga babu alamar ko abincin kirki ma an bata. Duk da hararar da Mom ke mun banbi takanta ba na shiga hidima da kakarmu. Bayan sallar isha'i kuma Yaya ya sayo mata kayan ƙwaɗayi yazo ga zauna muka sha hira. Dan dole Abba ma yazo ya zauna akayi da shi shima. Mom da ƴaƴanta kuwa kowa yay shigewarsa ɗaki sai Auta da uwar gulma Bibaa kawai a wajen. Bamu tashi a falon ba sai sha biyu. Abba ko tun sha ɗaya matarsa tazo ta tasashi suka shige ko kunyar Gwaggo Gudidi bata ji ba balle mu ƴaƴa. Shimfiɗata na barma Gwaggo, dan Yaya Musaddiq ya kawo mata babban bargonsa. Zan kwanta a ƙasa tace na hawo kan bargon. Badan naso hakan ba na hau dole. Sabuwar hira muka buɗe da ita har sai ɗaya sannan barci ya kwasheta. Niko alwala na tashi nayi nai nafilfilina kamar yanda na saba sannan na kwanta. Hakan kuma bai hanani tashi uku da rabi ba na shiga ayyukana. Kafin kace mi na kammala, dan har abinci naima Gwaggo na saka mata a kula nakai ɗaki dan nasan ba lallai da rana a bata na kirki ba. Gashi ban dawoba lokacin. Kalacin ma isashe na ɗiba mata. Itako tanata mitar yanda nake wannan uban aiki ga fitar safe kuma. Ni dai bance komai ba face murmushi kawai. Yau kam Yaya Musaddiq ya shigo gidan domin gaisheta. Ya ajiye mata kayan shayi da ƙaton bread ɗin ta harda soyayyan ƙwai. Albarka ta dinga saka mana sannan mukai mata sallama muka wuce dan kar mu makara.

       Gwaggo Gudidi itace ta raba komai na kayan sa ranar nan. Har maƙwafta sai da tasa Auta ya kai ma kowa gida-gida. Sannan dangin su ta ƙulla na kowa daki-daki. Wanda ke anan cikin Kano ta saka Yaya Musaddiq ya kaita ta kai ma kowa. Na Gwarzo ma tare sukaje takai duk na ɓangaren danginsu dai. Yaya Musaddiq ma da Hafizzullah ta ɗiba musu. Nima komai sai da ta ɗiba min. Hakama jama'ar gidan kowa da nashi. Kuma kowa zai iya rabama abokan arziƙinsa idan yaso. Amma sai Mom tai biris da nata anan falo har Gwaggo ta wuce bata ɗauke ba daga ita har ƴaƴanta. Abba dai ganin Gwaggon yasa shi zama ya ƙuƙƙula ya fita dasu wai zai rabama abokansa da ƴan wajen aikinsu. Ya raba ko bai raba ba oho masa.

       A ranar da nakai ma ƴan office ɗinmu kowa ya sake sanin alaƙata da Mansoor, dan wasu basu ɗauka gaske soyayya muke ba saboda yanda muke komai cikin taku. MD kuwa ai kamar zai mutu. Dan masifa yayta zubama kowa a wannan yinin babu gaira babu sabar. Har dai ƴan uwana ma'aikata suka fahimci kishi yake yi. Ni dariyama ya bani wlhy. Mansoor kam yaji daɗin abinda nayi, dan bai ɓoye ba sai da ya sanar min. Murmushi kawai na masa nidai. Bayan an tashi aiki ya buƙaci kaini naga aikin gida da ake ƙarasawa. Amma sai nace masa ba yau ba ya bari weekend zai fi. Shima ya yarda da shawarar tawa. Dan haka ya maidani gida. A ranar ne kuma na fahimci wata farar mota na binmu a baya. Duk da naji tsoro sai banyi magana ba, nace bari dai na tabbatar. Ganin munzo titin shiga layinmu motar ta wuce yasa na sauke ajiyar zuciya har Mansoor na kallona. 

     “Lafiya irin wannan ajiyar zuciya haka kamar wadda nai shirin sacewa. Ko tsoro kike kada na wuce dake ne?”.

        “Ai kaima bazaka fara hakan ba sai an baka”. Na faɗa cikin kauda kai ina murmushi. Shima ƙaramar dariya yay da sake faɗin, “Hakane. Amma da zama a taimaka a banin yau zanfi kowa farin ciki. Maybe ma na ƙara samun ƙarfin aikin yanda ya kamata”.

      “Humm” kawai nace na buɗe motar na fice ina murmushi. Godiya na masa kamar kullum. Yanata son mu haɗa ido amma naƙi yarda da hakan. Sai ma na wuce da sauri na shige gida abina. Amma na maƙale jikin gate ina leƙansa. Yaja kusan minti ɗaya idonsa a gate ɗin fuskarsa da murmushi kafin ya tada motar ya wuce...


      ★★★


   Abubuwa kullum ƙara tsamari suke a gidanmu. Dan kullum al'amarin Mom da yaranta gaba yake yi. Ina sake samun tsangwama da hantara fiye da baya a yanzu sakamakon wannan batun auren. Yayinda Baby ta fito da maitarta akan Mansoor yanzu. Shi kansa ya fara nuna min tana matsa masa. Ashe tun da can ma da bata fiddo abubuwanta fili game da shi akwai abinda take shakka daga garesa, na kuma fahimci wani babban sirrinta ne ya sani duk da yaƙi fitowa fili ya faɗa min.

        Sam ba'a wani shiri irin na aurar da ƴa a gidan, musamman ma mace da bikinta ke da yawan hidima. Ko kaɗan hakan baya damuna. Dan nasan Yaya Musaddiq tsaye yake akan al'amurina ta bayan fage. Dan yanzu kusan duk sati zakiga Gwaggo Gudidi tazo mana. Da alama akwai abinda sukeyi ita da Yayan. Duk da madai ashe shi Mansoor ya samu Yaya akan shi baya buƙatar komai na gida duk zai zuba. Ni shaidace akan abinda ya faɗa ɗin domin ya kaini naga gida. A randa mukaje ɗin kuma na sake kama motar nan na binmu. Hankalina ya tashi fiye da ranar, amma nai jarumtar dannewa saboda kada na tada hankalin kowa. Nayi kuma alƙawarin saka ido sosai dan na tabbatar shin da gasken binmu ake kokuwa zargina ne kawai. Tun daga wannan lokacin na saka ido fiye da koda yaushe. Babbar magana kenan wai ɗan sanda yaga gawar soja, nako tabbatar bibiyata akeyi ɗin. Dan harna haddace Number motar duk da dai mai ita kan canja ne kusan da kala uku, sannan ita kanta motar wani lokacin bada ita ake bina ba da napep ne. Al'amarin ƙuruciya irin nawa da wauta, maimakon na sanarma ko Yaya ne sai nai tunanin kada na tada masa da hankali, gara na fara sanin wanda ke bibiyar tawa dai. Wannan ɗammara dana ɗauka tasa na fara ƙin daina bin yaya na koma shiga napep. Hakama Mansoor wataran sai na ƙi biyosa, ina amfani da yanayin da yake ciki na busy yanzu akan shirin biki. A ranar farko dana fara yin ƙundun balar tarar motar nan sai aka gudu. Karo na biyu ma haka. Ganin haka na sake himma dan a ganina tsorona ake ji. A karo na uku na haɗa kai da ƴan ƙato da goran anguwarmu a ɓoye akan idan ma fita su bini a baya. Na basu numbers na motar da ake amfani da su har kala uku. Abin zai baku mamaki, dan kamar mai motar nan ya fahimci abinda nake ƙullawa ranar sai bai bini ba. Tsahon kwana uku haka na ƙara yarda yaji tsorone na sallami ƴan ƙato da goran. Sai me a randa na sallamesu a ranar na cigaba da ganin motar kuma. Raina yakai ƙololuwar ɓaci. Na fara zargin MD ne kemin hakan ko kuma Abba ko Mom ko Baby. Kai har Mansoor sai da na zarga, to sai dai kuma shi danmi zai sa a bibiyan bayan kullum muna tare. (Bincike) zuciyata ta ayyana min. Ban gamsuba, dan in bincikene ai iyayensa ne zasusa ai musu. Sannan bata wannan hanyar ba, anguwarmu zasu je. Amma duk da haka sai nace bari na gwada kowannensu. 

      Da Baby da Mom na fara. Sai banga wata alamar hakan ba daga garesu. Shima Abba haka. Sai kawai na koma kan Mansoor. A randa na taresa da zancen ina magana cikin tsiwa kan basai fa yasa ana bibiyata ba zai san halina. Idan bincike yake son yi a kaina yazo ga ƴan anguwar dana tashi cikinsu tun ƙuruciya har girma mana. Amma sakawa ana bibiyata kamar son firgitar da ni ne. Tare da nuna rashin aminci a tsakanina da shi. Sagale yay yana kallona da mamaki, sai dai bai iya cewa komai ba harna fita a fusace. To ashe daga nan bai zame ko ina ba sai wajen Yaya Musaddiq suka tattauna akan hakan. Lokacin da Yaya Musaddiq ya dawo aiki yay kirana ɗakinsa.......✍️





_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments