Breaking News

Tsutsar Nama 28

 *_Typing📲_*










   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑻𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_



.......Kamar ko yaushe yau ma Mansoor ne ya maida ni gida, koda na shiga na samu gidan tsitt. Banbi takan kowaba na shige ɗaki, auta na samu yana barci, ga books ɗinsa a gefensa barbaje alamar homework yake barcin ya kwashesa. Ɗagashi nai na maida kan katifa. Sannan na tattare books ɗin na ajiye masa gefe bayan na duba abinda yake. Yaron akwai brain, inba ni ba babu mai zama damuwar koya masa homework, sai idan Abba. Wani lokacin ma sai kika yayi da kansa kafin ma na dawo, sai dai na ɗan masa gyararraki kawai. Wanka nai ƙoƙarin shiga, sai dai bayin duk an ɓata shi, nasan Bibaa ce zatai wannan aikin ba wani ba. Na rasa mike damun kan yarinyar nan, amma zan koya mata hankali. Tanada ɗakinta ita kaɗai amma tsabar shaiɗanci tace tsoro take ji a can, shine Abba yace ta dawo nan mu zauna wai sai ta ƙara girma. Da farko na ɗauka haka ɗinne, sai daga baya na fahimci Mom ce ta sakata yin hakan dan ta dinga ɗaukar rahoton duk motsina tana kai musu. Tun wani lokaci da naji tana faɗama Mom wayar da mukai da Mansoor nagane hakan. Bayin na sake gyarawa sannan nai wankan. Harna fito na gyara jikina banji motsin kowa ba. Ba'a wani ɓata falonba yau sosai, dan haka na wuce kitchen. Shi kam yana nan jibge da kayan wanke-wanke tun daga kofunan kalacin safe har na rana da sukaci. Kaina na girgiza ina mai jin tausayin Bibaa da Baby a rayuwa. Dan ita Mom gani take gata take musu bata san kashe musu rayuwar take ba, haka kullum da rayuwar take a gidan, idan nai aikin safe na fita babu abinda suke kaudawa har sai na dawo na sake yi, badan nima na zama jan wuya ba abincin rana ma sai na musu na saka a kula. Sai da na nuna musu nima tsagerar kaina ce sannan, shiyyasa kullum basu da abincin rana a gidan sai taliya ko cus-cus ko macaroni, indomie. Sai idan akwai stew ne zakiga sun dafa farar shinkafa. Stew ɗin kuma zakiga dole nice zanyita, Mom taƙi yarda a ajiye mai aiki wai ita kishi, randa nayi aure to naga ubanda zai zo ya musu. Kwanikan na fara tattarewa na wanke, ƙafafuna duk sunyi tsami saboda tsaiwa. Haka dai na daure na kammala na maida komai muhalinsa sannan shima kitchen ɗin na shiga gyaransa. Ƙaramar indomie na dafa guda biyu, na raba biyu naci tawa anan na juyema auta tasa a plate. Har lokacin babu wanda ya dawo, mamaki ya sake kamani da tunanin ina sukaje haka ne?.

      Har akai sallar magrib sai mu kaɗai a gidan. Sai bayan an idar Abba ya shigo. Fita mukai ni da auta daya tashi muka gaishesa. Na wuce na kawo masa ruwa na koma ɗaki abina na barsu anan falo. Sun fita sallar isha'i nima zan kabbara tawa naji hayaniyar shigowar su Mom. Banbi takansu ba na tada sallata. Sai da nai har shafa'i da wutiri sannan na fito musu sannu da dawowa. Kaya na tarar barbaje a falon kashi-kashi. Na sakawa dana kwalliya harda na ciye-ciye alamar dai daga kasuwa suke. Ganin hankalinsu baya kaina dan ko gaisuwar ma da kai Mom ta amsa min na juya na koma abina ina mamaki, dan tabbas da kuɗin Yaya na jiya akai wannan sayayyar kenan. Jinai raina ya ɓaci matuƙa, dan haka na fito na wucesu. Yanzun ma hankalinsu babu alamar yana kaina. Ta ihun murnar kayansu suke kawai. Ɗakin Yaya Musaddiq na nufa, yana tsaye da alama yanzu ne yake dawowa massalaci. Ganina rai ɓace ya sashi faɗin, “Jikin ne?”. Kaina na girgiza masa ina kaiwa zaune. Cikin zafin rai na ce, “Wlhy Yaya zancen kuɗin sarƙar nan shirine kawai. Ko kasan matar can yau kasuwa suka shiga ita da ƴaƴan nata gasu can sun baje kaya a falo kamar za'a buɗe kanti. Kasan kuma babu yanda za'ai hakan ta faru Mom ta iya kashe kuɗin sarƙar nan a banza haka da gaskiya ne”.

       Murmushi mai sanyi Yaya Musaddiq yay hana kaiwa zaune kusa dani. Cikin sauƙaƙa murya tare da riƙo hannuna cikin nashi ya furta, “Cool down sweetheart. Sune a ƙasa ai. Bakiji shata na faɗin ku gargaɗi mai gina ramin mugunta ba. Ni nasan dama koda an ɗauki sarƙar ma bata kai ta kuɗin data faɗa ɗin ba. Amma ba komai ALLAH zai bamu wasu. Yanzu ma Abba ya bar ɗakin nan”.

       “Miya faru ya shigo?”.

Na faɗa cikin mamaki tunda nasan dole akwai dalili. Hannuna ya saki yana miƙewa da ɗan taɓe bakinsa. Ya zare jallabiyarsa ya ajiye sannan ya koma ya zauna dan jikinsa akwai dogon wando da t-shirt fara. “Yazo ya sameni akan wai tunda yaga inada kuɗi ni ne ya kamata na miki komai na aure. Dan shi gaskiya yana a cikin damuwar rashin kuɗi. Saboda hakane ma yaƙi yarda su tsaida rana a randa iyayen Mansoor suka zo. Amma da yasan har inada wannan kuɗin haka aida an kammala komai. Dan haka zai kirasu suzo weekend ɗin nan a tsaida ɗin. Na kuma bashi aron 200k zuwa ɗan wani lokaci zai bani..”

       “Kuttt! Amma mutumin nan ko! Wai mike damun Abban nan ne?. Dama ko bai faɗaba waye ke jiran wani abu da ga garesa mtsowww aikin banza. Sannan kuma bashin ka amsa zaka bashi Yaya?”.

    Murmushi Yaya Musaddiq ya saki mai haɗe da dariya, sai kuma ya girgiza kansa. “Kai wannan yarinya masifaffiya ce ke wlhy, wanda basu sanki bane kawai suke miki kallon mai haƙuri. Ni ALLAH har ma na fara tausayin Mansoor bawan ALLAH shi gashi da sauƙin halin tsiya”.

    Baki na tura ina faɗin, “Kai Yaya nice masifaffiyar?”.

      “Ta bugawa ma kuwa a jarida kandala. Wani lokacin da idan kina abu sai naga kamar ma kece Yayar tawa. Shiyyasa Hafizzullah ke cewa da kece Mamanmu da mun shiga uku”.

      Dariya na ƙyalƙyale da shi. Na ce, “Masherancine yaron nan ai. Dan ALLAH Yaya weekend ɗin nan muje mu gansa tunda wancan ya shuɗe. ALLAH ina kewarsa”.

        “Karki damu zamuje in sha ALLAHU. Dan na kammala masa ma siyayyarsa.”

     Cike da farin ciki nace “Yauwa Yayanmu, kuma Babanmu. Yanzu dai yaya mi kacema Abban?”.

       Sai da yay murmushi ya ce, “Mizan ce masa kuwa Samraah. Na gaya masa kuɗin dana bama Mom ɗin jiya ne kaɗai dama a wajena, sai abinda ya rage baifi saura dubu arba'in ba nama cire wani abu a ciki na haɗama Hafizzullah provision. Dama na tara wancan kuɗinne dan na basa shi da Mom ɗin su rage hidimar biki. Ga kuma abinda ya faru yanzu. Ina gaya miki sai kawai ya hauni da faɗa. Wai to wlhy sai nasan inda zan nemo wasu kuwa. Dan shi dai baida wani kuɗin yin hidimar nan bai kuma da hanyar samunsu. Inba hakaba kuwa sai dai a kaiki gidan mijin a haka.. inada yake shiga dai bata nan yake fita ba.”

       Wata shegiyar dariya na bushe da ita harda kwanciya ina hawaye. Yaya Musaddiq kuwa yay sagale yana kallona. Sai da yaga dariyar tawa ta tasamma ta hauka sannan ya ce, “Samraah kin samu motsuwar kai ne?”.

      “Babu wani motsuwar kai wlhy Yaya. Show ɗin ne yay matuƙar burgeni. Su Abba an lallaɓo aci banza. Banza bata samu ba, shine ya ƙare da borin kunya. To waye ya faɗa masa na damu a kaini da kayan ɗaki? Ko cokali ma kada su saya waye zaiji kunya”.

        “Shirme maganinka ALLAH kenan”. Yaya Musaddiq ya faɗa yana girgiza kansa. Da sauri na ce, “Yaya gaskiya fa na faɗa. Ni wlhy ban damu ba amin kayan ɗaki ko a kar ayin. Badai muna son junanmu ni da Mansoor ɗina ba”.

     “Baki da kunya, a gabana kike cewa kuna son juna”.

    Hannu nasa na rufe fuskata ina dariya. Shima sai ya shiga tayani...


        Washe gari koda na kammala aikina na shirya na fito na samu Abba a falo na gaishesa bai amsa min ba. Ko'a kwalar rigata nai ficewata. Yaya ga ɗaukan muka wuce ina bashi labari ina dariya. Shi kam murmushi kawai yayi yace “ALLAH ya ƙyauta”. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya gidan Abba babu daɗi sai haƙurin UBANGIJI kawai. Yayinda a waje aiki ke caja kai kuma. Kamar yanda mukai shiri ranar asabar muka tafi Katsina ganin Hafizzullah. Ƙiri-ƙiri Mom ta nuna baƙin cikinta akan hakan. Ta shiga zuga Abba wai ya hanamu zuwa. Sai dai Yaya ya nuna musu babu abinda zai sakamu fasawar. Haka dai muka tafi Mom na banbaminta na rashin gaskiya. Hafizzullah yayi matuƙar farin ciki da ganinmu. Dan harda kukansa na murna. Ya rame saboda karatu, naita tsokanarsa nikuwa muna faɗanmu da muka saba. Tare da shi muka yini. Da zamu wuce masauki kuma ya bimu akan shi tare damu zai kwana. Nan ma raba dare mukai muna hira kafin su koma ɗakin Yaya Musaddiq su kwanta ni kuma nai kwanciyata ni kaɗai muka sha waya da Mansoor dake bani labarin an shirya komai tsaf gobe in sha ALLAHU za'a tsaida date. Jinai duk wani iri, amma a ƙasan raina ina farin ciki da hakan. Koba komai ai zan samu ƴancin kaina. Na kuma samawa ƴan uwana. Dan insha ALLAHU Hafizzullah gidana zai koma, Yaya kuwa zan cigaba da dagewa akan yay aure..........✍️

          


_Kandala ta malam Mansoor 😘_




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments