Breaking News

Tsutsar nama 34


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_



........“Oh oh wannan irin dogon zance haka Baba, bakinka ko gajiya bayayi. Kayi haƙuri ina jin girman tsufarka a cikin raina duk da ba ganinka nake ba. Sai dai ga saƙo zan baka. Ka faɗama shi wanda ta aikokan shin tsoron Samraah Abdul-wahab Gwarzo yake ne? Ko kuwa shi bai cika namiji bane daya laɓe a bayan tsufarka a yimin barazana? To idan yana kusa da kai ya buɗe kunnuwansa da ƙyau ya saurareni, idan kuma baya kusa ka masa recording. Ni Samraah Abdul-wahab Gwarzo ban yi video ɗin dan aimun barazana na bada ba. Idan buƙatarsa yake mu haɗu gaban hukuma. Idan kuma yana da ƙarfi yazo muyi gaba-da-gabq kwanta. Sai dai ya sani ko dungurin wani da ga cikin ahalina yayi bazai sauke hannunsa ba video ɗin zai baza duniya. Dan haka zaɓi ya rage nashi, ku farka daga wannan nannauyan barcin na barku lafiya”. Da ga haka na yanke wayar tun kafin shi ya yanke. A fusace wanda ya kawo min wayar yake hararata. Amma nai biris da shi na ɗauke kaina. Kiran wayar aka sake yi, da sauri ya ɗauka ya kai kunne. Ban san mi aka faɗa masa ba na ga dai ya sake hararata ya juya ya fita. Nima da harar na raka nasa bayan ina taɓe baki. Da ga haka na zame na kwanta zuciyata na wata irin tafasa. Sai dai a wani gefen ina jin daɗi dan koba komai na samu bakin zaren wanda yasa aka kawoni nan. Zargin mutane da yawa ya fitamun a dai zuwa yanzun, musamman ma jama'ar gidanmu.

        Barcina na sha yau da rana sosai, dan yanzu bani da wani aiki sai inci in kwanta ɗin, sai idan naji na gaji ne da zaman waje ɗayan sosai nakan ta zagaye ɗakin wani lokacin ma na ɗan motsa jikina dai, saboda na fahimci na fara ƴar ƙiba ba kamar sanda aka kawoni da bana cin abinci ba sai yawan kuka. Ganin zan halaka kaina a banza nama masoyana asara yasa na fara cin abincin tunda nasan ban isa canja abinda yazo a littafin ƘADDARA ba ai. A yanayin ɗan ƙarfin jiki dana tashi da shi ya sani jin zan iya tunkaresa koda zai ƙarar da numfashi na, sai dai zan fara da wannan mai kawo min abincin a yau ɗin nan. Amma sai zuciyata ke gargaɗina da hakan kai tsaye, dan haka na shiryama raina wata sabuwar dabara ina kuma addu'ar cin nasarar hakan amma sai na gwada plan ɗin farko baiyi ba tukunna dai.

     Kamar ko yaushe cikin ƙarfin hali na tashi nai wanka da ruwan ɗumi. Kaya na saka na sake dawowa na kwanta a katifar dan jiri nake ji na neman ɗibata. Ina nan kwance tamkar mai barci naji ana ƙoƙarin buɗe ƙofar. Luff na sake kwantawa har aka shigo aka sake maida ƙofar aka kulle. Sai da ya shigo tsakkiyar ɗakin sannan ya tsaya cak. Idanu na ɗan ƙara buɗewa ta can ƙasa yanda zan gansa da ƙyau. Ƙofar bayi yake kallo, nasan kuma dalilin yin hakan, dan kan shower ɗin na ɓalle nabar ruwa nata zuba. Ka ɗan naga ya duƙa yana kai yatsansa biyu ƙasa ya dangwala, sai kuma naga yay saurin ajiye ledar abincin hannunsa ya nufi toilet ɗin da alama ruwan ne ya fara fitowa.

       “Lafiya miya faru?”.

  Na faɗa a hankali. Bai tanka min ba, bai kuma tsaya ba. Na saki murmushi ina tashi zaune. Bayansa na bi. Duƙe na samesa yana ƙoƙarin buɗe hanyar da ruwa ke fita gaba ɗaya da ɗayan hannunsa. Ɗayan kuma ya danne pipe ɗin shower ɗin ya cusa babban yatsarsa a ciki ya tsayar da ruwan. Sai dai duk da haka yana ɗan fita sii. Da wannan damar nai amfani nima na shigo ina faɗin, “Tun ɗazu nake kiranka dan ka duba amma baka amsamin ba.”

     Kaɗan ya juyo ya kalleni sai kuma ya sake maida kansa ga abinda yake yi. Ni ko na duƙa kamar zan janye masa boket dana jiƙa kaya ciki na samu nasarar zare wayarsa. Da sauri na tusata cikin rigata. Na janye bokatin na fita abina. Sake komawa nai cikin katifar nai kwanciyata. Sai dai zuciyata sai faman gudu take a ƙirjina. ALLAH ALLAH nake ya zo ya fita kafin ya farga babu wayar tasa. Amma bai fiton ba sai kusan bayan minti goma. Batare daya kallan ba ya nufi hanyar fita. Cikin rawar jiki ina jin ya kulleni ta baya alamar ya tafi kenan. Na ciro wayar. Naji daɗin ganin babu password jiki, cikin rawar jiki data hannau na saka number Yaya Musaddiq na danna masa kira. Harta katse bai ɗauka ba. Hankalina ya sake tashi jikina har kakkarwa yake. Sake ƙoƙarin kira nake ina kallon ƙofar. Nan ma ta shiga amma har tana neman yankewa babu alamar za'a ɗauka. Nama gama sadaƙarwa dan idanuna har sun cika da hawaye sai ya ɗaga. A yanda yay sallama cikin wani yanayi na mutum mai damuwa yasa idanuna sun ciko da ƙwalla. Cikin rawar muryar alamar son sakin kuka na ce, “Yaya Musaddiq nice. Nice kandalarka. Dan ALLAH kuzo ku fiddani anan karna mutu. Yaya banda lafiya ciwo zai kasheni. Sun kawoni nan sun ɓoye kullum sai dai suyita bani abinci kawa.....”

    Fittt naji an ƙwace wayar daga hannuna. Hannu ya ɗaga zai ɗauke fuskata da mari sai kuma miya tuna oho masa ya tsaya cak. Niko tsoron da naji na kar ya kai ƙaton hannunsa kaina ya sani dunƙilewa waje ɗaya na rumtse ido. Jin shiru banji saukar marin ba na buɗe idona. Dai-dai nan yake ƙoƙarin fita a ɗakin. Na taso kuwa da uban gudu na nufi ƙofar nima, ina gab da ƙarasawa ya datse da sauri. Zubewa nai a wajen na saki wani kalar kuka mai ban tausayi da cin zuciyar mai sauraro.. Ina a wajen ko cikakken minti biyu baiyi da fita ba sai gashi ya dawo cikin sassarfa. Jin saukar handkerchief kawai nai a saman face ɗina. Kamar waccan ranar nayi niyyar yunƙurin tashi amma abinda suka shaƙa min yaci ƙarfina. Kamar ƙyaftawar ido na sulale ƙasa, daga haka ban sake sanin abinda ke faruwa ba kuma..



       ✨●●)(●●)(●●)(●●✨

    


   Gaba ɗaya yanda Yaya Musaddiq da Mansoor suka rikice bama su fahimci wayar ya yanke ba. Dan suna tare ne a mota sanda Samraah ta kira wayar. Da farko hankalin Mansoor ba'a kan Musaddiq yake ba. Sai da yaga yayi wata shegiyar zabura yana ƙwala kiran sunan Samraah jikinsa har wani gab-gab yake na rawa sannan. Wayar shima ya fisga jikinsa na rawa yake faman kiran ta. Sake ƙarɓewa shima Yaya Musaddiq ɗin yayi. Duk sun rikice sun ruɗe, jin dai ɗif ɗin yayi yawa suka ɗan fara dawowa hankalinsu. Sai sannan suka fahimci wayarma ta yanke. Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga rige-rigen sakkoma Yaya Musaddiq. Dan harga ALLAH yana matuƙar ƙaunar ƙanwarsa. Mansoor ma dai idonsa cike yake da ƙwalla, cikin ƙarfin hali ya buɗe motar ya fita. A ɗan zabure Musaddiq ya figi wayarsa dai-dai sanda Mansoor ke fita a motar, dan tunawa da ya dace ma su kira d.c.o fa. Kiran nasa kuwa yayi, sai dai ba'a ɗagaba. Cikin tashi hankali ya cigaba da kira. Har 3 miscall, fita yay da sauri a mota. A jikin motar ya samu Mansoor jingine idonsa a lumshe. Cikin sauri-sauri yake faɗin, “Na kira d.c.o amma bai ɗagaba. Inaga ya kamata mu ƙarasa police station ɗin mu sanar masa”. Shima ɗan zaburar Mansoor yay, cikin alamar gamsuwa da zaburowa ya nufi motar yana faɗin, “Hakane yaya, wlhy ni kaina ma ya tushe na rasa mizan yi, amma bara na kira Yaya Attahir ya nemesa tunda abokinsa ne”.

     Musaddiq ya gamsu da hakan, cikin ƙanƙanin lokaci Mansoor ya sanarma yayansa halin da ake ciki, kafin suma su ɗauki hanyar zuwa police station ɗin. Sosai Mansoor ke gudu, hakan yasa cikin ƙanƙanin lokaci suka iso station ɗin. Sun samu d.c.o baya nan ya fita sai dai Yaya Attahir ya kira Mansoor ya sanar masa yay magana da d.c.o ɗin ta waya, gashi nan zuwa ma su jirashi. Dole sukai zaman jiran dawowarsa duk a ƙage. Sai bayan kusan mintina sha biyar kuwa sai gashi ya dawo. Ganin yanda suke hankali a tashe ya buƙaci fara ganinsu. Suna gaya masa kamar yanda Attahir ya sanar masa tun a waya, shiyyasa ma ya katse abinda yake acan ya taho, ya amshi wayar Musaddiq tare da kiran yaronsa yace ya kwashe number ɗin yanzun nan ai masa tracing. Amsa yaron nasa yay ya kwashe number ɗin ya fita da hanzarinsa.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments