Breaking News

Tsutsar nama 33


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_




......D.c.o ya tura yaransa neman abokin mai napep, sai dai an samu wai baya nan yayi tafiya. Wannan dalilin yasa sukace zasu cigaba da riƙesa har sai an kamo abokin nasa. Hankalin ƴan uwansa ya tashi kamar yanda shima nashi ke a tashe. Amma dai d.c.o yaƙi saurarensu. Dan ya tabbatar musu da yana akan aikinsa ne. Babu yanda zasuyi dole suka haƙura suka tafi. A ɓangaren ƴan media suna nan suna cigaba da tattauna batun ɓatan Samraah. Yayinda hotunanta ke yawo lungu da saƙo kowa na faɗin abinda fahimtarsa ta bashi. Dan wasu har suna danganta komai da cewar ita ta jama kanta. Dama taya zata taɓa irinsu Maash tace zata zauna lafiya. Ai gashi nan ya mata lunbu-lunbu da ga ƙarshe ya ruftata dan mawuyacine ace bashine ya saka aka kwamusheta ba. Musamman in akai dubi da yanda ta samu damar tattaunawa da shi ta yanda manyan ƴan jarida suka daɗe suna fatan haka amma basu samu ba. Wasu ko na ganin wani ne ya saceta dan kawai a ƙullama Maash sharri. Wasu na ganin ko dai MD ɗin nasu ne musamman yanda zancen son da yake mata ya karaɗe ko'ina, ga shi kuma an saka mata ranar aure da ya rage saura sati uku kacal. Wasu dai kuma zarginsu na akan Maash ɗinne dai da tunanin son da yake mata ne ya sashi aikata hakan ganin an saka mata ranar aure da waninsa. Hakama wasu zarginsu bai bar kan Baby ba itama jin TAKUN SAƘAR dake tsakaninta da Samraah ɗin akan Mansoor ba, hakama mahaifiyarta da tun fil azal ba son su Samraah ɗin take ba. Ga kuma abinda tayi a randa aka kai lefe. Kai hatta da abokan huɗɗar Mansoor ɗin wasu a ciki sun shigo zargin jama'a. Tawani fannin kuma akance maƙiyane kawai ko kidnappers ne kawai saboda yanda sunan Samraah ɗin ya samu ɗaukaka cikin ƙanƙanin lokaci game da shirin da take akan matasa da yanda take nuna illar lalacewar matasa a cikin al'umma. Kaso marasa ƙarfi kuwa na ganin adai bunciki sauran samarin Samraah suma dan zasu iya aikata komai ganin Mansoor na shirin wuff da ita, ko kuma shi ƴammatan Mansoor ɗin. Kai zance ne dai gashi nan kala da iri harda wanda ma bashi da ma'ana. Kamar wasa a haka sati ɗaya ta shuɗe ana fakon abokin mai napep. Ba'a samu damar damƙosa ba kuwa sai a randa take cika kwanaki tara ciff.


    ★ “Kidnapping kuma? Ni wlhy yallaɓai bani bane. Mizai sa nai kidnapping mutum? Idan na ɗauketa ma ina zan kaita?”.

     Cikin tsawa yaron d.c.o dake tuhumar tasa ya ce, “Kai karka raina mana hankali. In ba kai bane ba to waye bayan abokinka ya tabbatar da kai ya bama key ɗin napep ɗin tasa? Kuma da ita aka ɗauketa daga nan ba'a sake jin labarinta ba har yanzu”.

     “Tabbas ni ya bamawa yallaɓai. Kuma ba ranar muka fara yin haka da shi ba. Saboda nima lokacin da nake da napep ɗin nakan bashi. Hasalima nine na koya masa tuƙinta, da taimakona kuma aka bashi napep ɗin ma a office ɗin mu. Amma wlhy ni banyi kidnapping kowa ba”.

     “Ƙarya kake yi kai ne. Tunda har ka iya barin gari sai yau kake dawowa a tunaninka komai ya lafa ko”.

   “Ranka ya daɗe ni ban bar gari dan komai ba wlhy. Ƙauyenmu naje da yake ina noma duk shekara. Shine na je nakai taki gonata. Can ɗin babu network shiyyasa wlhy bamma san mike faruwa ba. Sai yanzu da nake ji ma a bakinka. Amma na tuna wani abu, idan ban manta ba da safe abokinmu da shima mukanyi irin haka da shi yazo yace na ara masa key ɗin keken Salisu zai amso saƙo a tasha, tasa na gareji sai azhar zai amso.”

     Da sauri ɗan sandan ya ce, “Ka tabbata?”.

       “Tabbas anyi haka ranka ya daɗe. Dan ƙanina ma na ɗakin a gabansa akai komai. Yaje kusan awa biyu sai gashi ya dawo ya kawomin yay godiya. Har ma naji haushi saboda ya saɓa lokacin daya dace ace na maidawa Salisu kasancewar yana fitar sassafe shi”.

      “Yanzu ina zamu samesa?”.

  “Anguwarmu ɗaya da shi, sai dai ta bayan layinmu gidansu yake. Shima kuma yana harkar adaidaitan, nasan yanzu baza'a iya samunsa a gida ba sai irin takwas haka ko bayan magriba gaskiya”.

            “Karka damu zamu samoshi”. 

     Ɗan sandan ya faɗa yana miƙewa. Kai tsaye office ɗin d.c.o ya nufa. Bayanin da yaron ya masa duk ya maimaita masa. Goyon baya d.c.o ya bashi akan su tabbatar sun samo wancan yaron kafin zuwa safiya. Ya tabbatar masa da in sha ALLAHU za'ai hakan kafin ya bashi damar fita. Cikin girmamawa yay salute ɗinsa sannan ya fice. Shiru kawai d.c.o yay yana mamakin wannan irin juya-juya. Dan case ɗin gaba ɗaya ya ɗauki zafi saboda yanda mutane keta ka-ce-na-ce akan batun yarinyar, shi kansa yanda yaga an ɗauki al'amarin nata da muhimmanci ya sashi bibiyar shirye-shiryenta na baya a daren jiya, tare da shafukanta na sada zumunta dake ɗauke da fallowers masu yawan gaske, sai yaji ta shiga ransa. Gata dai ƴar yarinya amma akwai kaifin basira da nuna kwazo akan aikinta. Ga mahaifin Mansoor da Mansoor ɗin sun addabama rayuwarsu. Kowane motsinsu yanzu yana a station ɗinsu ne. Azalzalar su kawai suke faman yi akan a gano musu inda Samraah ɗinsu take su dai. Hakama Yaya Musaddiq idan ka kallesa sai ya baka tausayi, rashin dauriya kawai Mansoor ya fisa. Shiko Hafizzullah sai dai kuka. Yayinda jikin Abba ya fara sanyi, sai dai yaƙi yarda ya nuna hakan ga mutane saboda shakkar Mom..



      ⭐❤️⭐❤️⭐❤️⭐❤️⭐



       Faɗa muku yanayin da nake ciki a kwanaki tara ɗin nan da suka gabata sam bazai yiwu ba. Dan koda da kwatance nace zanyi hakan bai zama lallai ku iya fahimtata yanda ya kamata ba. Abinda kawai nake so ku fahimta al'amarin sam bashi da sauƙi. Nayi kuka matuƙa Bily. Irin wanda ni kaina sai da na tabbatar da nayi sa. Sai dai ku sani badan kaina nake yinsa ba. Domin ƴan uwana biyu ne da nasan zasu fi kowa shiga tashin hankali ne. Sai kuma masoyina da ya rage saura kwanaki goma sha uku kacal ya amsa sunan mijina. Dai-dai da daƙiƙa ɗaya ban gaza wajen miƙama UBANGIJI kukana akan ya kuɓutar dani daga wannan ƙangi, ya sa ina da rabon komawa ga dangina. Bani da wani ƙarfin nuna yunƙurina saboda halin rashin lafiya da nake ciki. Ciwon kai da zazzaɓi sun kasa barina. Na kuma gagara faɗama wanda ke zaryar ajiyemin abincina da har yanzu bai taɓa min magana ba, ban kuma taɓa ganin fuskarsa ba. Sai a yau da safe kusan goma da rabi sai gashi ya shigo. Nayi mamakin shigowar tasa saboda ba lokacin kawo min abinci bane, kuma baya shigowa dama sai zai kawo abincin. Amma ganin waya a kunnesa yasa na zuba masa manyan idanuna. Har gabana ya ƙaraso, batare da yamun magana ba ya tsaya ƙiƙam a kaina kamar wani mai gadin gidan kallon kwallo. Wayar dake a kunnensa ya sauke. Batare da yamun magana ba ya ajiyeta a ƙasa gabana. Na ɗago da nufin kallonsa maganar da akai cikin wayar ta katseni. Da sauri na maida kallona akan wayar, wata dattijuwar murya ce da nake ji kamar na taɓa saninta, cikin nuna ƙarfin iko da tabbatar da rashin wasa aka furta.

        “Nasan zuwa yanzu kin fahimci inda kike ba wajen wasan yara bane ba. Ba kuma filin ɗaukar rahoto bane ko dandalin sada zumunta. Baƙya buƙatar wani bayani kam dogo yanzu ƴammata. Sanin wanene ni? Miye dalili? Mi kika aikata duk bana buƙatar ji. Video recording ɗin hannunki kawai nake buƙata, mi zanyi da shi, ko minene alaƙata da shi ba damuwarki bane. Na duba a duk wayoyinki babu kin ciresa a ciki, ya rage naki faɗar inda yake ko wajen wanda yake a bani ke kuma ki kama gabanki. Idan kuma kikace zaki zama mai taurin kai tabbas zaki dawwama a wannan ɗakin tamkar kabarinki, dan ko mutuwa kikai a ciki zamu gina miki kabari mu bizne ki batare da wani mahaluki ya taɓa sanin hakan ba har abada. Kuma zan mallaki video ɗin sannan na ɓatar da duk wani ahalinki daga doron ƙasa. Zaɓi ya rage naki lokaci na tafiya miki dan nasan kina shirin zama amarya”.

       Ni kaina ban san sanda murmushi ya suɓuce min ba. A karan farko na wani ja numfashi mai nauyi tare da sakin wata siririyar dariyar ƙarfin hali. Kaina tsaye na nima na furta,........✍️




_Shin wa kuke tunani ne? Gashi dai Sam-G tace muryar Dattijo, kai nafa ruɗe nima. Amma mu haɗu a comment section ko wani zai canko mana🤔😞_




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments