Breaking News

Tsutsar nama 37


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_




.......Yanzun ma dai barci ne mai nauyi sosai ya sake yin awon gaba dani batare dana gama tantance fuskar mutumin ba. Ban kuma farka ba sai washe gari da rana gatse-gatse. A yanzun ma dai ba farkawar daɗin rai bace ba. Dan still dai ciwon ne ya farkar dani ta yanda har sai da doctor ta sake dawowa. Yanzun kam naga alamun ruɗanin yanayin nawa a fuskarta itama. Dan bayan ta ɗan duddubani fita tayi tana danna waya, da alama magana take son yi da wani...

       Bata wani jima sosai ba ta sake dawowa. Allurar dai ta sake fakar idona tamun, sai dai da alama tamafi ta jiya ƙarfi. Dan ko minti biyu cikakku banyi ba na sake komawa barci, daga haka ban san wainar da ake toyawa ba kuma...


     A ɓangaren Doctor bayan tama Samraah allurar barci ya ɗauketa babu jimawa wanda tai kira a waya ya iso. Kamar yanda ta shawarcesa da kai Samraah asibiti ya amince. Sai dai da kansa ya nuna zai kaisu asibitin data tabbatar masa akwai dukkan tsaron da suke buƙata. Dan ya sanar mata alaƙarsu da yarinyar ta yanda hankalinta zai ɗauka bawai ainahin gaskiyar sato ta ko kwatota ne ma oho musu ba. Ita kuma jin wanda ya saka aikin yasa bata wani damu ko ɗarsa zargi a ranta ba take bata duk wannan kulawar. Dan tun jiya da tasan yana a garin Abujar nan take jin wani farin ciki, tasan kuma a dalilin aikin yarinyar nan zata iya haɗuwa da shi, duk da dai yanayin ciwon yarinyar yana buƙatar aje da ita asibitin da gasken.. 

        Sun isa asibiti batare da wata matsala ba. An kuma yima Samraah dukkan binciken daya dace. Dan har dare suna a asibitin, sai kusan goma  suka gano matsalarta. A take suka haɗo duk abinda zai taimaka mata a matakin farko kafin ai mata abinda ya dace. Gidan suka sake maidota aka saka mata drip kamar yanda ya buƙata, daga haka suka fice aka barta da masu tsaronta.


     Tunda suka shigo katafaren ginannen gidan take jin jina kai da sakin kurmushi. Duk da tasan wannan ba komai bane daga mamallakin gidan. Amma dai tayi mamakin yanda yaron nasa ya bata labarin an ginashi cikin ƙanƙanin lokaci tare da wani ma a Kano. Duk da kuwa tasan yana da gidaje sosai a Abujar nan da basu da adadi ma musamman ga ita da ba kowanne ta sani ba, amma tasan wannan ɗin na musamman ne gaskiya. Har kusan ƙofar falon ya kai kafin yay parking, cikin murmushi yay mata nuni da suje ciki. Babu musu ta ɓalle murfin motar ta fita, sai wani taku take cikin yauƙi da yanga. Tun a takun farko na shigowa falon wani sanyi da ƙamshi mai sauke gajiya suka ratsata. Ta wani shaƙi iska da dogon hancinta ta fesar a slowly. Ko makaho yasan falon ya haɗu tamkar mai shi. A hankali ta ɗan kai dubanta ta gefen damarta da take jin ƙamshinsa yafi yawaita a tanan. Shine kuwa zaune cikin kujera 1sitter da laptop a saman ƙafafunsa daya miƙe saman Centre table. Yanda keyboard ɗin laptop ɗin ke bada sautin ƙara zai tabbatar maka da typing abu yake. Da alama kuma mai matuƙar muhimmanci ne. Dan gaba ɗaya hankalinsa na kan screen ɗin, kuma yana dannawa ne da ɗan yanayin sauri na ƙwarewar sabo da hakan. Ƙananun kaya ne a jikinsa kamar ko yaushe. Dan sune suturar da yafi sakawa sai ko suit kamar dangin yahudu. Sai dai kasancewar wandon nasa kaɗan ya zarta gwiwa ya bama ƙafafunsa damar bayyana samɓal. Har suka kai zaune bai kallesu ba balle ya nuna yasan da shigowarsu. Sai da ya ɓata kusan mintuna shida curr sannan yay magana batare da ya kallesun ba yanzu ma.

         “Any problems?”.

     Ya faɗa a daƙile cikin silent voice ɗinsa. Hayatu ne ya jin jina kai yana mai sake sakama kansa nutsu da gyara tsaiwarsa cikin nuna girmamawa sosai. “Eh to Sir dama dai akan batun yarinyar can ne. Kasan tun jiya na sanar maka abinda ke faruwa na rashin lafiyar da take ciki, har kace Dr Rumaisa tazo ta dubata. To tun dai jiyan tayi duk abinda ya dace amma ba'a dace ba. Ɗazun dai dole tasa mukaje da ita asibiti domin a bincika matsalar ta shine dama muka zo sanar maka dan yan zun ne muke dawo wa...”

          Shiru kamar bazai tanka ba, sai da ya mula dan kasa ya furta, “Uhum ina sauraren ku”.

    Da sauri Doctor Rumaisa tai tsigil ta ce, “Ranka ya daɗe Good evening”.

      Bai amsa mata ba, illa ɗan jinjina kansa da yay kawai alamar amsawar kenan batare da ya kalleta ba kuma. Taji ba daɗi, dan ba haka taso ba. Amma sai ta daure ko za'a dace ta cigaba da faɗin, “Gaskiya yarinyar akwai babbar matsala a tare da ita. Da alama tun kafin yanzu tana fama da pain a duk sanda zatayi prioud, kuma yana mata tsanani. Maybe hakan ne ya jata ta dinga shan maganin hana zuwan prioud ɗin a duk sanda lokacinsa yayi, shine ya haifar da matsalar wannan karon ɗin. Dan sai wahala kawai take sha amma jinin yaƙi ya fita, yanzu dai in sha ALLAHU na mata dukkan abinda ya dace akoda yaushe zai iya fita ɗin, sai kuma ta kiyaye cigaba da shan wancan magungunan inba haka ba zatama kanta illa. Dan a yanzu hakan ma sai an ɗorata akan magunguna masu ƙarfi sosai da zai dai-daita mata komai, sai dai sunada wahalar samu maganin dan sunada tsada gaskiya, ba kowanne pharmacy zaka iya ganinsu anan ba ma”.

      A yanzu ɗin ma dai babu alamar zai amsa dan kamar ma bashi takema bayanin ba. Hakan yasa Hayatu bata amsar dan yasan Maash bazai sake magana ba kuma. “Sir zan ƙarasa komai in sha ALLAH. Dama dai na kawota ne kawai ta maka bayani yanda zakafi fahimta.” daga haka yayma Dr Rumaisa nunin ta miƙe shima yana tashi. Sam ba haka taso ba, dan fuskarta ma ta nuna. Ta kafe Maash da kallo tana mai fatan ya sake cewa wani abu koda bazai ɗago ɗin ya kalleta ba, dan dama ita ta matsama Hayatu akan ya kawota ta masa bayani da kanta. Amma sai bai ko kallonsu ba aikinsa ma ya cigaba dayi kamar yanda suka shigo suka samesa. Sai ka ɗauka ma ya manta da su a falon ne tsabar halin yarfin mutumin nan.

     Suna fita ta kalli Hayatu rai ɓace. “Amma ba haka mukai da kai ba Hayatu?”.

       “To yaya kike so nayi doctor. Kin san dai halin Boss ba sai na sake tisa miki ba. Ba yau ne kika fara masa aiki ba kuma. Shiyyasa naso ma ki bari muyi komai mu gama iya mu kaɗai tunda ba gagara zai yi ba. Tunda kuma shine yasa kizo zai buƙaci ku haɗu kafin mubar garin. Yanzu dai kiyi haƙuri a madadinsa. Kiyi kuma magana da pharmacy ɗin da kikace zasu turo maganungunan nata. Sannan ki bada account number da za'a saka kuɗin.”

        Gaba ɗaya fuskarta ta sauya da tsantsar damuwa da ɓacin rai. Duk da dai tasan zata shaƙi kuɗi a aikin nan, dan ko Hayatu hannunsa a buɗe yake tamkar boss ɗin nashi a wajen ƙyautatawa. Kamar zatayi magana sai kuma dai ta shanye da ƙyar, gaba tai idanunta na cika da hawaye ta buɗe motar da suka zo ta shiga. Murmushi Hayatu dake binta da kallo yayi, acan ƙasan ransa kuma yana jin tausayinta. Dan yasan tamkar ta ɗebo ruwan dafa kanta ne dakon soyayyar wanda soyayyar uwa kawai da familynsa ya sani sama data wata ɗiya mace a wannan rayuwar. Shi kansa har mamaki yake anya ogan nasa nada lafiya kuwa, dan shi dai zai iya rantsewa, bayan abokan huɗɗa dana aiki be taɓa ganin wata mace a gefen ogansa ba da sunan yana mata kallon mace mahaɗin rayuwa ko wani ɓangaren jin daɗin duniya. Shi dai kawai neman kuɗi, ina zaka business ina ka fito business. Abinda kawai ke birgesa da shi neman kuɗi bai taɓa shagaltar da shi bautan ALLAH ba. Ga shi dai nan da zubin tsagerun mutane, amma batun ibada babu wasa.. Motar ya shiga shima, yay mata key suka fice a gidan bayan securitys dake gate ɗin sun buɗe masa. Lallashi da daɗaɗan kalamai ya dinga gayama Doctor Rumaisa, acewarsa ta cigaba da addu'a, idan ALLAH ya ƙaddara Maash mijinta ne sai ya aureta. A hankali ta saki murmushi kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta, shi ko ya girgiza kansa dan shima ya san dai gangan yake faɗa, dan ga wata can ma a Lagos data fita wayewa da komai ana tirƙa-tirƙa bayan na bayan fage da iyayensu suke faman masa tallarsu wasu ko sune da kansu suke masa tallar kansun. Shifa yasha ganin ballagazayen wasu matan na kuka akan Maash ko kwanciya yay dasu idana bazai aurensu ba, amma ko kallonsu bayayi ma balle su samu karɓuwa. Gaskiya kuɗi a mafi yawan lokuta fitinarsu tafi alkairinsu yawa. Shi shaida ne. Dan shi kansa ma da bashi ke da dukiyar ba yana cin azaba balle shi Maash ɗin da kansa. Aure ma da ƙyar akai masa a shekarar data wuce, yanzu haka matar nada ciki, amma kullum cikin faɗa suke akan rashin lokacinsa. inaga kuma matar mai gayya mai aiki da ake fatan ta shigo, ai duk wadda zata zauna da shi a matsayin aure kam sai ta jajirce, ko dai ta dinga binsa duk inda zai je itama taji a jikinta dan yawon ma ba hutu bane, ko kuma ta cigaba da hakuri da abinda ta gani kawai.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments