Breaking News

Tsutsar nama 32


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒕𝒘𝒐_




.......Kusan mintuna biyu ina zabga kuka, kafin na sake jawo jakar da tarkacen ciki dana juye ƙasa duka zuwa gabana. Sake zazzagawa na koma yi kamar wadda ta zautu. Ko abinda keda alaƙa da waya babu a cikin duka wayoyina biyu. Amma na kasa yarda, sai ƙara zazzagawa nake da ɗaɗɗaga kayan dana zazzage kamar wata mai neman barimar ɗan kunne. Sai da dai zuciyata ta tursasani akan babu ɗin da gaske sannan na sake fashewa da kuka tare da yin wurgi da jakar. Haka na kasance a wannan daren babu wata nutsuwa irin ta cikakken mai hankali a tare da ni. Sai dai koda wasa ban mance ambaton UBANGIJINA ba. Gab da asubahi wani wahalallen barci yay awon gaba dani, ban tashi farkawa ba sai kusan bakwai da kwata. A firgice na miƙe na nufi toilet na ɗauro alwala. Bayan nazo na gabatar da salla koda na idar a wajen na cigaba da zama na fara karatun Alkur'ani a hankali jikina duk babu ƙarfi, dan akwai yunwa ma tare dani, jiya gaba ɗaya banci ba ban sha ba. Nafi awa ɗaya da kusan rabi a wajen naji ana ƙoƙarin buɗe ƙofa. A zabure na ɗago daga cusa kaina da nai cikin ƙafafuna dan a haka nake karatun. Kallo ɗaya mai shigowar yamun ya ɗauke kansa, yana sanye da mask baƙi kamar yanda komai na jikinsa ke baƙi, dan hatta hannunsa akwai safar hannu baƙa. Ya kuma toshe idanunsa na baƙin eyeglasses da babu abinda zan iya ganewa ko gani nashi. Irin ledar dake ajiye a ɗakin ce a hannunsa. Batare da ya tankamin ba ya ajiye ya ɗauki ta jiya dako kallonta banyi ba ya nufi hanyar fita abinsa.

      Muryata na rawa nai saurin dakatar dashi ta hanyar faɗin, “Wanene kai? Miyasa kuka kawoni nan? Mi kike buƙata da ga gareni? Wani laifi na muku ko kuɗin fansa kuke nema?”. 

     Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Ina kammala faɗa kuma bai tanka ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sake kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawaye na gangaro min da gudun tsiya. Lallai ina a tsaka mai wuya, gashi bamma san wanda zan iya zarga ba. Dan gaskiyar Mansoor ne. A wannan gaɓar hatta da Baby da MD kai har Mom da Abba kansa ni zasu iya shiga lissafina ma. To amma ni abinda ke damuna waɗan nan mutanen da duk na lissafo idan sunyi hakan gareni duk miye ribarsu? A yanzu ba kaina kawai nake tausayi ba  ƴan uwana da halin da zasu shigane ke matuƙar tada min hankali fiye da komai. Ga Mansoor shima. “Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki ka kuɓutar dani da gaggawa. Kasa kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya a zukatan ƴan uwana da masoyana da ni kaina. Duk wanda bashi da laifi akan wannan al'amarin ya ALLAH ka hanashi shiga wahala. Mai hannu a ciki UBANGIJINA ka hanashi damar cutar dani koda yayi niyyar hakan a gareni”. Zamewa nai a hankali na sake kwanciya ina mai cigaba da karatun Alqur'ani na. A haka barci ɓarawo yay awan gaba dani tunda dama bai isheni ba. Ga kaina na wani kalar masifaffen ciwo.

      Barci nayi sosai, dan ban tashi farkawa ba sai da naji ƙarar an buɗe ƙofa. Firgigit na miƙe kuwa ina murza ido. Mutumin ɗazu ne dai kuma kamar ɗazun fuskar tasa a rufe. Wata ledar abincin ya sake ajiye min da wata babba fara ita kuma yanzu ma ya sake ficeewarsa batare da yamun magana ba ya sake kullenin. Kwata-kwata yanzu ma hawayen nawa sun kasa fitowa. Da alama zuciyar ta fara dakewa. Salloli da nake jiyowa anatayi a masallatai yasa na miƙe a hankali. Jikina sai ciwo yake tako ina. Na tabbatar harda rashin wanka dan ni mutum ce mai son yawan wanka a rayuwa. Kuma ko yaya idan banyi ba sai na dinga jin babu daɗi. Naso na daure kada nayi, kamar yanda nake ƙoƙarin hana kaina cin komai, dan ko ruwa sai a wajen alwala nake ɗan haɗiyarsa. Amma na kasa hakan dan wani ƙyanƙyamin kaina nama fara ji, harma zuciyata na wasi-wasi akan yin salla da su. Ledar kayan na janyo na shiga fiddosu. Dogayen riguna ne har biyar duk marasa nauyi da bazasu takurani ba. Sai hijjab biyu manya. Harda su b&p shidda-shidda. Sai kayan barci har uku da man shafawa da turare. (Ko wanene wannan anyi cikakken ɗan iska ma wlhy. Wato komai anyisa akan shirine, babu kuma alamar zan bar nan ɗin a kusa tunda harda tanadin kayan sakawa). Duk a zuciya nake wannan tunanin. Cikin jin ban aminta da ɗakin ba na ɗauka doguwar riga ɗaya da b&p na shiga toilet. Wanka nayi da ruwa masu ɗumi dan akwai hitter a toilet ɗin. Sai naji jikina ya rage nauyi, hakama zuciyata. Na ɗan ji ƙarfi da nutsuwa har ƙwaƙwalwa ta na iya sarrafa tunani yanda ya kamata. Brush shima nayi na ɗauro alwala na sake fitowa. Banbi takan mai da abinci ba na koma na kwanta a katifar na lumshe idanu kawai ina mai faɗawa duniyar tunani.....


       ✨💞✨💞✨💞✨


    Zuwa safiya labari ya fara karaɗe gari da social media. Abinka da sananniya musamman ma a watanni biyun nan da sunanta yay amsa kuwwa a lungu da saƙo sakamakon abinda ya faru a wajen taron buɗe Companyn Maash da kuma hirar da tai da shi. Ta wani ɓangaren kuma wanda basa harkar yanar gizo sun santa ne a dalilin shirin da take gabatarwa ta hanyar rediyo. Duk wani wanda ke a office ɗinsu hankalinsa a tashe yake. Musamman ma MD da ƴan sanda suka gano shine mutum na ƙarshe daya tura mata text message akan yana son ganinta. Dan haka a ranar Monday ɗin ƴan sandan suka gayyacesa office ɗin su. Gefe kuma gasu Mom suma an tattare zuwa station saboda abinda sukaita faɗa a randa aka kawo lefen Samraah, ga kuma rikicin da suka sake yi a daren bayan mutane sun watse maƙwafta da suka ji komai sun faɗa da sake tabbatar da anyi hakan. ALLAH sarki Mansoor da Musaddiq sai su baka tausayi. Dan kwana ɗaya kacal duk sun fita hayyacinsu. Hafizzullah ma a ranar Monday ɗin ya tsallako karatunsa ya nufo Kano..

       Shigar mahaifin Mansoor a zancen ya saka ƴan sanda sake ɗaukarsa da girma. Dan a yanzu D.c.o ɗin ne ma da kansa yake gudanar da binciken. A yau har Attahir ma Yayan Mansoor ba'a bari a baya ba, dan shima dai yana a station ɗin anata ɗan kai kawo dai akan batun...


      Al'amari kamar wasa akan ɓatan Samraah ƙaramar magana na neman zama babba. Dan ƴan sanda sun matuƙar takurama MD da Baby da Mansoor ya tabbatar da yana zargi. Sannan wani mai shago a anguwarsu ya tabbatar da yaga sanda Samraah ta tare napep ta shiga, dan har gaida shi ma tayi kamar yanda ta saba. Ya kuma tabbatar da zai iya gane napep ɗin dan har number ɗinta da tambarin dake jikinta ya riƙe saboda mai napep ɗin ya jima tsaye a ɗan nesa da shagonsa shi yama yi zaton ko wani yake jira a wajen. Sai can ya maida hankali ga sallamar mutane sai ga Samraah. Lokacin da take gaishesa tabbas ya ɗago ya kalleta yaga tana ƙoƙarin tsaida Napep. Sai dai bai ga mai shirin ɗaukar tata ba har sai da ta shiga ciki. Mai napep ɗin ma yaja sun fara tafiya, ya ɗan zabure da nufin tsaidasu dan hankalinsa yaji bai kwanta ba amma har sun wuce. Sai kawai ya bisu da addu'a tunda bawai yasan gaibu bane, kuma yaga bayan ita akwai wani kamar ma a ciki.

       Bayanin mai shagon nan yayi matuƙar yima ƴan sanda da duk wani masoyin Samraah daɗi. Dan koba komai an fara kama bakin zaren. Sakamakon kamar yanda mai shagon nan ya faɗi tambarin dake jikin napep ɗin nan haka mutanen da aka ajiye wayarta a inda suke suma suka maimaita dan tambari bai kamata a manta da shi ba. Wannan yasa duk wani masoyinta buɗe idonsa tarwai akan lura da shigi da ficin masu napep duk da kuwa kamar banza suke a Kano dan yawa. A ta gefen jami'an tsaro kuwa kai tsaye ofishin shugaban masu kula da ƴan napep suka je. Inda suka bada report akan napep ɗin da mai tuƙata. A take kuma babu ɓata lokaci aka shiga bincikenta. Abinka da komai a tsare a yinin ranar sai da aka gane wanda ke tuƙa napep ɗin. Tuni ƴan sanda suka saka aka cikuykuyosa shi da napep ɗin tasa. Inda wanda suka gani suka tabbatar da ita ɗin ce kuwa. Sai dai basu da tabbacin shine a ciki ko ba shine ba. Amma tabbas dai napep itace.

         Kasancewar dare yayi ba'a wani tuhumi mai napep ba a ranar sai washe gari da Samraah ke cika kwanaki uku kenan. Sai dai me, a yayin tuhumar mai napep yayi rantsuwa ya ƙara kan shi bai san komai ba. Hasalima a ranar napep ɗin ba'a wajensa ma ta kwana ba. Ya bama wani abokinsa da yamma akan zai yi aiki ya ɗan samu nashi har zuwa dare sai ya dawo masa da ita. To bai dawo masan da ita ba sai washe gari kusan takwas dan har sukai faɗa ma saboda ya karya masa alƙawari, ga shi shi kuma yana fita aikin wurine amma ranar yasa ya makara........✍️

    




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments