Breaking News

Tsutsar nama 38


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_




......Har gidansu dake anan Abujar Hayatu ya maida doctor. Koda ya dawo a inda suka barsa nan ya sake samunsa. Yanda yaga fuskarsa tai kicin-kicin sosai ya sashi sake nutsuwa, kamar yaron da yayma mamarsa laifi kafin ya tafi makaranta. Sun kai tsahon minti uku a hakan yana satar kallonsa, shiko yana aikinsa kamar bai san da shigowar tasa ba. Sai can a bazata cikin daƙilalliyar muryar nan tasa dake fita silent ya furta, “Bani black tea”.

      Da sauri Hayatu ya amsa da, “Okay Sir” yana nufar hanyar kitchen. Bai wani jima sosai ba sai gashi da abinda yace masan. Lokacin da yake amsa ya ɗan kallesa, hakan yasa Hayatu saurin rissinar da idanunsa, dan ko motsi ogan nasa yayi yasan abinda yake nufi. Shayinsa ya kai baki ya ɗan kurɓa sau biyu sannan ya sake kallon Hayatun. “Minace maka akan yarinyar nan?”.

            “Sir wlhy ba laifina bane. Kasan tanada shegen naci, nunawa tai ma idan ban kawota inda kake ba a jiya da ciwon yarinyar ya motsa bazata taɓata ba”.

       “Sai akace ita kaɗaice likita kuma?”.

   “Am sorry Sir. Anyi kuskure amma za'a kiyaye in sha ALLAHU”.

   Shiru kamar bazai sake tanka masa ba. Har sai da ya gama shan shayin ya ajiye kofin yana miƙewa sannan ya furta, “A dawo da yarinyar nan gidan”.

           Wani mugun waro idanu Hayatu yayi yana binsa da kallo. Sai dai shi bai ko waiwayo ba har ya gama haye stairs ɗin da zai kaika inda bedroom ɗin sa ya ke. Jagwab Hayatu ya zube a kujera tare da faɗin, “Boss rigimarka tafi ta sojojin yaƙin basasa wlhy. Kai komai idan zuciyarka ta raya maka sai kace ayi baka tuna abinda zai iya zuwa ya dawo. Yarinyar da ake nema ruwa a jallo kawota gidan nan ai haɗari ne, mun ɗakkota da ga Kano jiya ALLAH ya somu mun fito lafiya, yau kuma kace a kawota nan. Mu kuma da muka zo jiya zamu iya wucewa akoda yaushe ya za'ai da ita a gidan nan da ko ƴan aiki duk maza ne?” ya zabga tagumi bayan ya gama sambatunsa babu mai bashi amsa. Sai dai yasan ko giyar wake ya sha bai isa ƙin bin umarnin nan ba kuma. Dole ya miƙe ya tattare kayan daya baza falon ya koma tsaf. Shima ficewar yayi domin duba ɗakin daya dace a saka yarinyar idan sun ɗakkota.....



        💞💥💞💥💞💥💞


    A hankali nake buɗe idanuna da sukai min matuƙar nauyi. Hakama jikina jinsa nake tamkar ba nawa ba dan yayi min jingim. Ga laima ina jina kwance a ciki kamar wadda tai fitsarin kwance. Hannuna na ɗaga da ƙyar nakai inda nake jin laimar na taɓo, da ƙyar na ƙara ɗago hannun domin ganin minene. Duk da dama shi ɗin nai zaton gani sai da gabana ya faɗi, nai wani kalar rumtse ido da ƙarfin gaske ina cije lips ɗina shima da ƙarfi kamar zan huda su. A dai-dai nan naji ana taɓa ƙofar, sake faɗuwa gabana yay, nai ƙoƙarin yunƙurawa dan na tashi zaune amma har an riga an buɗe. Rashin ƙarfin jiki yasa na kasa jawo blanket ɗin dake a gefe, duk da ma wani sashe na zuciyata mamakin ganin kuma a inda nake ya kamani. Dan nan ɗakine mai ɗauke da kayan gado complete, sannan yafi wancan ƙyau fiye da zaton mai zato ma gashi ƙato sosai. 

          Mutumin nan da sukai min allura tare da doctor a daren jiya ne ya fara shigowa. Sangamemen ƙato biye da shi da da ledoji a hannu. Muna haɗa ido da shi na kauda kaina. Shima nasa kan ya kauda, batare da ya sake kallona ba ya furta, “Waɗan nan naki ne zaki iya amfani da su. Bayan su duk ma abinda zaki iya buƙata akwaisa a ɗakin. Likitarki ta gama aikinta, har magungunanki gasu anan ta kawo”. Daga haka ya juya ya fita. Da kallo na bisa zuciyata na wani irin kai-kawo. Kenan dai da gaske mutanen nan ne sukai kidnapping ɗina. Sune kuma suka saka ake bibiyata? Hakan na nufin sun san na ɗauki wannan video recording ɗin dai kamar yanda nai tunani?. (Ya ALLAH ta yaya hakan ta kasance?) Na faɗa a zuciyata, a zahiri kam ina mai runtse idanuna dake cike da nauyi har yanzu. Na kai tsahon mintuna goma ina faman tunani kafin na yunƙura na tashi da ƙyar, dan dama yanayin da jikina ke ciki yasa bance da shi komai ba da ya shigo. Yanda na jiƙa wajen da jini ya bani tsoro sosai, kamar wadda tai ɓarin ciki jama'a, haka dai na daure na sakko, sai dai ganin an saka min abune a inda na kwanta ɗin ba ainahin gadon na ɓata ba na ɗan saki ajiyar zuciya. Abin mai kama da leda-leda katifa-katifa na tattare na ɗauke. Cikin ɗingisa ƙafata dake ciwo na nufi hanyar da nake ƙyautata zaton toilet ne. Shi ɗinne kuwa, sai dai ya tsaru matuƙa, dan da za'a bani zaɓin wajen kwanciya maybe na kawo katifata nan na shimfiɗa, bawai dan yafi ko ina ƙyau ba, kawai dai ya birgeni ne shima. Duk da rashin ƙarfin da nake ji haka nai ƙarfin halin gyara jikina yanda ya kamata, nai wanka da ruwa mai zafi sosai. Sai a lokacin kuma hankalina ke neman tashi tuna bani da pant balle azo ga batun bad, sai dai tuna abinda yace yasa na fito. Ledojin da suka ajiye na shiga buɗewa, ta farko abinci ne, ta biyu kuwa kayan ciye-ciye ne. Sai ta ƙarshe ce ke ɗauke da kayan sawa, a ciki na samu pants da bad ɗin. Duk da naji wani iri da ganin hakan banda damar ƙorafi, ɗauka nai kawai na koma ciki na kimtsa jikina na dawo ɗakin. Kayan na sake buɗewa na ɗauki doguwar riga na saka batare da na damu da sanin sauran abinda ke ciki ba. Bana jin yunwa, dan in har ina a wannan yanayin ban cika son cin abinci ba, sai masifaffen kwaɗayi kamar sabuwar mayya. Dan hankalina duk yana akan naman can dana gani, ko naso basarwa kuma bazan iya hakan ba, garama naci bai nak yanda zan samu ƙarfin sauke musu abinda ke kaina. Zama nai kuwa nacisa sosai har saida naji na ƙoshi, na fiddo magungunan dana gani na duba duk yanda aka tsara shansu suma nasha.

       A yanzu bana buƙatar zaman yin dogon tunani, tunda na fahimci a hannun waɗanda nake saɓanin kwanakin da suka gabata da nake canki canka da rashin tabbas. Yanzu babbar damuwata ahalina. Na tabbata duk inda Yaya Musaddiq da Mansoor suke hankalinsu a matuƙar tashe yake kodan kiran da nai a waya. Amma ina fatan askine yazo gaban goshi, dan nayi alwashin komi mutanen nan zasumin bazan taɓa basu video ɗin nan ba ko faɗa musu a inda zasu samesa, iyaka dai suce nima zasu halaka ni, ban damu ba, dan hakan da zasu yi shine mafi girman kuskure da zai tona asirinsu insha ALLAHU.


        Shan maganin ya ƙara saka min jin daɗin jikina. Sai dai damuwa data kasa ɓoyuwa a kan fuskata. Sai gajiyar zama waje ɗaya daban saba ba. Nida nake yini tsaye kan ƙafafuna ina faman bautar aiki, garama idan office naje akan ɗan samu sassauci tunda shi kusan daga zaune ne. Motsin sake buɗe ƙofa da naji ya sakani tashi daga kwancen da nake cikin kujerar ɗakin, ɗan kwalin abayar naja na rufe kaina zuwa ƙirjina da ƙyau. Dai-dai nan aka ƙarasa shigowa. Mutumin ɗazu ɗinne dai, daga bakin ƙofa ya tsaya yayinda ni kuma nake kallonsa a tsiwace. Dan sai yanzu ne komai ke dawo min game da sanin da nai masa. Tabbas shine yaron mutumin nan mai kama da ƴan daudu ko nace ɗan daba ma ko sara suka oho duk ya cancanta, shine kuma ya kira da PA ɗinsa a ranar wancan taron. Nai saurin kauda kaina ina ƙoƙarin dai-daita fuskata da jikina. Tsahon mintuna kusan biyu ɗakin shiru, kafin cikin son nuna jarumta na furta,

         “Dama kune kukai kidnapping ɗina?”.

      Maimakon bani amsar dana buƙata sai jinai cikin bada umarni ya ce, “Zaku iya shigowa”. Baima ko gama rufe baki ba kuwa garadan samari biyu suka shigo. Ko namiji yaga wannan samudawan dole ya ji tsoro balle ni, amma dai nayi ƙoƙarin dake zuciyata ban bari tsorona ya fito a saman fuska ba. Sai dai faman haɗiyar yawu nake da ƙyar zuciyata na faman kai da kawo a cikin ƙirjina. Umarnin tashi suka bani, bani da ikon yin musu ko dan bindugun dake a hannunsa, ɗaya daga cikinsu ne ya koma ta bayana ya ɗauro ƙyalle a saman idona, zanyi magana ya ce, “Shiii!! Young Lady, inba hakaba harsashi ya rufe miki baki”.

     Yawu na sake haɗiyewa mai kauri, daga haka ban sake magana ba har suka bani umarnin tafiya bayan sun saka min wani abu a hannu na riƙe. Tafiya kawai naji munayi batare dana san ina muke nufa ba, amma dai baka jin hayaniyar komai ko'ina tsitt sai kukan tsuntsaye daga ɗan nesa damu kaɗan. Da ace hannuna babu handcuffs wlhy sai na cire abinda aka rufen fuskar komai ma za'ayi ayi. A haka naji mun shigo wani waje mai shegen sanyi da ƙamshi na musamman. Nanma mun ɗan yi tafiya kafin naji mun tsaya cak a inda ƙafata ta taka wani lallausan abu.........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments