Breaking News

Tsutsar nama 39


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_




......Kamar yanda d.c.o ya nema washe gari an sake kawo masa bayani akan ɗayan daya buƙata. Sai dai abin baƙin ciki shima layin na taƙaitaccen lokaci ne kamar wancan, ba kuma a taɓa kiran wani da shi ba. Nasara ɗaya da suka samu itace na shi wanda yay register ɗin layukan duk mutum ɗaya ne. Kuma a lokaci ɗaya yayisa. Sun saka a nemo musu shi a duk inda yake. Hakama abokin masu napep an samu nasarar cafkosa a safiyar yau. Bayan kamar awa biyu da kawosa police station ɗin aka kaisa office ɗin d.c.o kamar yanda ya buƙata. Sai da ya gama masa kallon tsaf daga sama har ƙasa kafin ya tura masa hoton Samraah dake gabansa. 

      “Kasan wannan?”.

   Ya faɗa kansa tsaye idanunsa ƙyam akan saurayin. Hoton saurayin ya ɗauka ya kalla na kusan sakan talatin, ɗagowa yay ya kalla d.c.o sai kuma ya rissinar da kansa yana ɗan jinjina kai. “Nasanta ranka ya daɗe. Sam-G ake kiranta, tana gabatar da shirin matasa kuma ina ɗaya daga cikin fans nata da shirin baya wuceni ta redio ko shafukanta na sada zumunta  musamman YouTube da ake ɗora shirin, nakan je na kalla videos ɗinta”.

        Kai d.c.o ya jinjina masa da faɗin, “Masha ALLAH. Minene sana'ar ka?”.

     “Direban napep ne yallaɓai”.

  “Kozan iya sanin ranar goma ga watan nan kana ina? Da ga shida na safe har zuwa ƙarfe takwas?”.

    Jimm yay irin na mai son tunano abu. Har kusan minti ɗaya sai kuma ya ɗago yana girgiza kansa. “Na manta yallaɓai. Saboda kwanakin sun ja da yawa”.

      “Uhhm yayi ƙyau” d.c.o ya faɗa yana kallon yaronsa. “Azo da yaran nan su duka”.

   Kai yaron nasa ya jinjina cikin girmamawa. Fita yay babu jimawa sai gashi ya dawo tare da samarin farko da aka fara kamawa. Yanda suke kallon saurayin haka yake kallonsu. Duk da babu duka ko zagi da akai musu zaman waje ɗaya da ɗan karan Dauda yasa duk sunyi wujiga-wujiga dasu....

     “Kasan waɗan nan?”.

   “Eh yallaɓai na sansu, su duka abokaina ne. Tare ma muke harkar napep ɗin ma.”

    “Kace ka manta mi kayi ranar goma ga watan nan da safe ko?”.

   “Eh yallaɓai a gafarceni”.

D.c.o baice dashi komai ba. Sai abokinsa ya kalla ya ce, “Kai tuna masa”.

     Kai tsaye abokin nasa ya ce, “Kazo ɗakinmu ni da ƙanina bayan sallar asuba dan gari ma bai gama haske ba. Kace na baka makulin mashin ɗin Imran zakaje amso saƙo tasha kai taka tayar na gareji dan naka babur ɗin ya samu matsala tun jiya sai barinsa ma kayi ya kwana a gareji kan yau zaka kai musu tayoyi da zasu canja maka. A gaban ƙanina Isa akai komai kuma”.

      Da sauri ya dafe kansa ya ce, “Tabbas anyi haka Salisu. Tabbas abinda ya faɗa gaskiyane yallaɓai, amma a gafarceni inada yawan mantuwa ne wlhy. Na amshi mashin ɗin, abinda nace kuma zanyi naje nayi da shi”.

      “Masha ALLAH haka muke son ji ai dama. Ina ka kai yarinya to? Sannan waye ya sakaka kidnapping ɗinta? Ko raɗin kanka ne kawai?”.

     “Ya salam kidnapping kuma? Ni banyi kidnapping kowaba ranka ya daɗe. Duk wanda ke tare dani kuma yasan wannan ba aikina bane ba inada sana'a. Taya ma kuma na rasa wanda zan ɗauka sai Sam-G”.

      “Ƙarya kake yi, a waccan ranar ba gareji kaje da napep ɗin abokinka ba Yakasai kaje layin gidan su Samraah. Kai zaman jiranta na kusan mintuna talatin da huɗu. Zata iya yiwuwa kasan dama zata fito a lokacin ne. Dan haka tana fitowa da shirin tsaida abin hawa kazo ka ɗauketa. Ka tsaya a dai-dai fita anguwar ta titin bayansu gaba ɗaya. Ka cire wayarta da facemask da eyeglasses ɗinta ka ajiye saboda maybe kana tunanin za'a iya ganeka ko kuma wanda ya saka ka aikinne ya baka umarnin yin hakan. Ɗan saurayi ban kawoka nan dan ka raina min hankalina ba. Amma kana da zaɓi guda biyu. Fitomin da komai a yanda yake dan ka samu sassauci ko cigaba da raina min hankali na saka ka faɗa ta dole wanne ka zaɓa?”.

       Ɗan jimm yay na wasu sakanni, sai kuma ya sauke numfashi da faɗin, “Zan faɗa maka gaskiya yallaɓai.......


   🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟(✧✧)🌟


      Cikin fisgar zaren da suka ɗaure min ido naji sun warwaresa. Har sai da na ɗan ciza lips saboda yanda naji zafi, amma dai na dake ina mai buɗe idanun nawa a hankali, dan zan gama da ogansu ne sannan na dawo kansu shegu masu suffar bakaken aljanun kan kuka. Sosai gabana yay masifar faɗuwa dan kai tsaye idanuna akan mutumin dake zaune cikin kujera yay crossing ƙafafunsa idanunsa a tab.. dake a hannunsa suka sauka. Ga wani daddaɗan ƙamshinsa da ya cika min hanci da gauraye falon gaba ɗaya. Fuskarsa ciɗin-ciɗin kamar bai taɓa sanin abinda ake kira dariya ba ko saƙon wani bala'i ya riskesa a yanzu. yauma akwai kitso a kansa guda biyu rak da suka zanu tamkar an zana a takarda dan zaka rantse ba hannu ya kitsasu ba, sai farin sirrin gilashi da ya zauna masa ɗaram a fuska tamkar an haliccesa da shi ne. Yatsunsa biyu ya ɗan juya, da sauri sangama-sangaman samarin nan da suka rakoni da bindiga duk suka fice aka bar abokin cin mushen nasa kawai. Sai lokacin ya ɗago ya zuba min cat eyes ɗinsa. Kallon ido cikin ido mukaima juna. A take naji ciwon marata na neman dawowa sabo fil, ba shiri nai saurin duƙar da kaina ƙasa zuciyata na wani kalar masifaffen bugu kamar zata faso ƙirjina ta fita. Amma cikin ƙarfin hali na murguɗa masa baki bayan na saukar da idanun.

     Shima janye nasa yay cikin yanayin isa da ƙasaita. “Sit!” ya faɗa a daƙile yana maida kansa ga tab ɗin tasa. Duk da na gane dani yake banyi abinda yace ɗin ba har sai da yaronsa ya sake maimaita min a ɗan tsawace. Ta ƙasan ido na hararesu su duka, kafin na kai zaune saman lallausar kujerar falon, amma sai yaron nasa ya daka min tsawa da mun nuni da wai na zauna ƙasa. (Munafuki ɗan baƙin ciki) na faɗa a raina, a zahiri kam hararsa na sake yi sannan nayi yanda yace na zauna ƙasan carpet ɗin da ko makaho ya laluba yasan ya haɗu. Jikina na ɗan takure a waje ɗaya, na tallafo ƙafafuna duka da hannayena biyu idanuna na kallon carpet ɗin. Sai da kusan mintuna uku suka sake shuɗewa babu alamar zai sake magana, sai kuma a cikin daƙilalliyar muryar nan tasa ya ce, “Wa kike ma aiki a kaina?”.

        Sosai tambayar tai matuƙar bani mamaki, har takai na ɗago na ɗan kallesa. Amma a mamakina bama ni yake kalloba, wasu files ne a hannunsa yan rubutu a ciki ya ajiye tab ɗin yanzu. A hankali na maida kaina na duƙar, nima sai da na kwashe wasu sakanni kafin cikin siririyar muryata da yanayin gafara na bashi amsa, “Ni nafi ƙarfin yima kowa aiki ai, dan ni ma ɗin gayyace”. Shiru baice komai ba, dan haka na cigaba da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa batare da tunanin zasu ji ni ba. (Ni ai nafi ƙarfin aiken wani, sai dai zuwan kai da kai. Dan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE ai. Idan kuma baka san haka ba kaje kayi bincike. Ashe ma matsoraci ne, tunda har baka iya fito na fito sai ta YAƘIN SUNƘURU...)

       Harara yaron nasa ya zuba min. Kafin cikin kakkausar murya ya furta, “Hattara dai ƴammata. Dan ba'a ado da furuci wani lokacin takobin yanka wuyan mai shi yake zama. Nan ba gidan jarida bane, fadar SARKI ce mai cikakken iko kike.”

      Murtanin harar nima na maida masa ƙasa-ƙasa. Sai dai na gagara iya cewa komai saboda yanda ogan nasa ya tsareni da shegun kaifafan idanunsa na maguna. Tsahon lokaci falon shiru, yayinda tuni ya janye idanun ya maida ga abinda yake yi. Sai zuwa can a wani irin daƙile ya furta, “A duk sanda wani ya nema shiga min hanci nakan ji farin ciki da mazantakar fyatosa. Shiyyasa abinda yafi birgeni a duniya sune mutane irinki masu taya business ɗin da bai shafesu ba. Well ba tabbatar miki da ni waye yasa nasa a kawoki nan ba, dan inada tarin ayyuka na kai da kai matuƙa. WAYE YA AIKO KI WAJENA?”.

       Takaicin maganganunsa yasa bamma san sanda na furta, “Umarnin kaina nake bi ni, na kuma faɗa ai”.

     A harzuƙe yaronsa ya katseni da faɗin, “Be careful ƴammata. Walƙiya ba tana nufin ado ne kawai ga sararin samaniya ba. Takan zama gargaɗi ga ma'abota shagala ne. Jirgin ƙasa duk ƙawatuwarsa a hanyarsa kawai yake iya tafiya, saɓanin hakan faɗuwar baƙar tasa zaiyi ta yanda ko kufansa bazai moru ba balle ma'abota shiga cikinsa. Ki dinga bambance tsakanin sama da ƙasa a duk lokacin da kikai tunanin hawa tsani da tunanin taɓa rana ko farin wata. Dan batun wanda zashi sama ya taka leda zance ne kawai irin na masu iya magana.”

       Baki na laɓe tare da watsa masa harara ta ƙasan ido. Cigaba yay da faɗin, “Kina da zaɓi biyu, bada abinda ke hannunki ki koma ki cigaba da rayuwarki cikin salama, ki kuma sakama ranki baki taɓa ganin komai ba a wacan ranar, ko nuna taurin kai ki dawwama anan har ƙarshen numfashinki, kin buƙaci 500m an baki rabinsu, amma ke kin kasa cika naki alƙawarin duk da an tabbatar miki idan kin bada za'a baki sauran 250m ɗin. Ke kin san kuwa dawa kike tare ana?”.

     Yanzu kam sosai na ɗago a razane matuƙa, tare da wurga masa hararesa dan naga yama fi ogan nasa zaƙewa. A kausashe nima na ce, “Lallai baka da hankali. Ni nace ku bani 500m?........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments