Breaking News

Tsutsar nama 41

 *_Typing📲_*










   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_



.....Hakan kuwa akai na tsaya dai-dai motar dake a fake, wanda akace Yayanta ya fito cikin nuna alhini yana min godiya, su biyu suka kamata suka saka a motar, ni sai lokacin ma na lura sun shaƙa mata maganin da yace, amma sai ban kawo komai a raina ba tunda dai dama yace zai saka mata magani. Yayan nata ne ya bani kuɗi masu yawa, nace masa bazan amsa ba ni dan ALLAH nayi, kuma ma ai kuɗin daya bani sun wuce na hakkin aikina. Murmushi kawai yamun ya ajiye kuɗin ya faɗa mota. Daga haka suka wuce suka barni ina kallon kuɗin, wlhy ban san sun yadda wayarta da facemask harda eyeglasses ba. Kuma suma ina ƙyautata zaton basu san sun faɗi ba kuskure kawai aka samu maybe. Suna wucewa nima na wuce, ban kuma san mike faruwa ba sai da yamma nake jin labari, abinda ya tada min hankali shine yanda ake misalta al'amarin yayi dai-dai da abinda ya faru da safe ni da dattijo, washe gari kuma sai naji batun kama Salis dangane da napep ɗinsa. Wlhy iya abinda nasani kenan, amma banda alaƙa da ɗaukar tata nima sai da naji daga baya hankalina ya tashi wlhy. Dan da nasan abinda zasuyi kenan babu yanda zan taimakesu, idan ma naga sunfi ƙarfina zan kira ƴan sanda. Dan ka tambaya kaji munsha irin wannan taimakon, adalilin haka har karyani an taɓayi abokaina gasu nan shaida ne”.

         Shiru d.c.o yay na wasu mintuna kamar mai nazari, sai kuma ya sake kallonsa ya ce, “Zaka iya gane mutumin da saurayi yanzu idan ka gansu?”.

      “Tabbas zan iya ganesu musamman ma dattijon duk da ya saka hirami a kansa ranka ya daɗe”.

    Kai kawai d.c.o ya jinjina batare da ya sake cewa komai ba ya bama yaransa umarnin a maidasu cell. Hakan kayi, bayan an maidasu ya zauna da yaronsa dake kan case ɗin.

    “Ɗan Bakori mika fahimta a zancen yaron nan?”.

   “Ranka ya daɗe al'amarin ne akwai wuyar sha'ani, amma dai kamar akwai ƙamshin gaskiya a zancen nasa. Wani abu dana fahimta shine amfani kawai akai da shi, kuma tabbas in har da gaske bashi da hannu duk waɗanda sukai abun to sun sanshi dan dole sunada kusanci koda ta zaman anguwa ne. Shiyyasa sukai masa wayo da batun iska tunda sun san ƙanwarsa na fuskantar irin matsalar zai fi saurin afkawa. Zancen daya faɗa ya taɓa samun karaya akan taimakon wata yarinya kuwa gaskiya ne. Dan na samu wannan labarin a binciken da nayi tun a farko. Mutanen na shegune suna da wayo, kuma sun shirya komai yanda suke so kafin su tunkaresa. Abu na ƙarshe bana raba ɗayan biyu duk wanda yay aikin nan na jikinta ne, ta sanshi ya santa sosai, dan inba haka ba tayaya suka san zata fito a lokacin tunda ba ranar aiki bace ba?”.

         “Tabbas zancenka na akan hanya ɗan Bakori. A wannan gaɓar dole aikinmu ya ɗan sake komawa baya kaɗan. Wayarta da aka tsinta daga biyar na yammacin ana gobe abin zai faru har washe gari a duba dawa tai waya? Waye yay kiranta? Koya turama saƙo koya turo mata.”

     “Okay Sir, amma naji kamar Yayanta yace da waya biyu take amfani, kuma sun wuce da ɗayar”.

    “Wannan ba damuwa bane, duk da dai ta wani fanin kasancewar wayoyin duka biyu zai fi mana. Amma ɗayar ma zata taimaka mana. Dan kamar yanda yaron nan ta faɗa sam basu san sanda ita wannan wayar ta faɗi ba kuskure aka samu. Itama in sha ALLAHU zamu samu abinda zai taimaka mana ku bincika”.

    Cike da gamsuwa ɗan Bakori ya miƙe tare da yin salute ɗin sa sannan ya fita da sauri....



        💥💫💥💫💥💫💥



    Ɗan taku yake cikin kai-kawo babu alamar rikicewa ko shiga wani yanayi a tare da fuskarsa a bayyane. Sai dai a can ƙasan zuciyarsa auna komai daya fita daga bakin Samraah yake kalma bayan kalma. Tare da ajiye kowanne word a mizanin hankali. A wannan yanayin Hayatu ya samesa. Ganin a yanayin da ogan nasa yake sai ransa ya ƙara ɓaci shima, dan haka a harzuƙe ya ce, “Sir yarinyar nan fa nada ɗan banzan wayo, ga bakinta kamar reza baya mutuwa. Ƙarya take tasan komai tana pretending ne kawai. Ba gashi yaron nan da aka amsheta a wajensa yace itace ta sakashi yay kidnapping ɗinta Dan ta bada ƙafa......”

       Wani irin murmushi Maash daya kafa masa ido ya saki a karo na farko, sai kuma ya girgiza kansa kawai tare da janye idanun ya maida kan ƙyawawan firannin fulawoyi da aka ƙawata wajen da su, baka jin komai sai daddaɗar iskar da suke badawa da ƙamshinsu a wajen. Shiru bashi da niyyar cema Hayatun komai har shi Hayatun ya ƙosa da shirun nasa duk da ba sabon abu bane a wajensa. Dan inma bai gadama ba zai iya sharesa yaƙi cewa komai kuma shikenan amsar tabi ruwa. 

    Sun kai tsahon mintuna uku a haka kafin cikin silent voice ɗinsa a can ƙasan maƙoshi a daƙile ya furta, “Hayat be a man mana. Kullum ina sanar maka ka dinga lissafi akan abubuwa. Amma na fahimci brain naka harkar business kawai take iya ganewa. Mizai hana a duk sanda baka fahimci miya dace akan abu ba ka dinga bashi lokacinsa dan ka fahimta. Ina matuƙar tsoron kada maƙiyan dake bayana suyi amfani da wannan ruɗanin naka da rashin hange wataran su ci nasara akan ka. Yarinyar tanada tsiwa da raini. Sannan harshenta nada kaifi. Zan mata hukunci dai-dai da wautarta. Kuɗina kuma nasan inda suke, zakuma su dawo nan bada jimawa ba batare da rasa ko naira ba a cikinsu. Video kuma dake hannunta muna farautarsa ne mu da su a hannunta, sai dai basu san MAASH ba shashasha bane irinsu. Zan tabbatar musu kuma da hakan, dan a matakin wasan farko da su zan fara buga game ɗin kafin na dawo kanta. Ka siyama Sani ticket a yau ɗin nan ya biyo jirgi zuwa Abuja. Hakama Abubakar ina son ganinsa yau da dare”.

     Daga haka ya juya ciki batare da ko waiwayen Hayatu ba. Da kallo Hayatu ya bisa galala kamar idanunsa zasu zubo. A zuciyarsa ya shiga faɗin, (Idan nace mutumin nan Aljani ne ace ba haka ba. Yanzu dan ALLAH duk wannan zaƙewar da nake dama ni yakema kallon wawa? To wai tsaya ma. Shi abinda ban gane ba anan. Kuɗi dai ni aka saka na turasu a account no.. da mutumin ya turo. Kuma ni da shi mun tabbatar da sabon account ne aka buɗe muna saka kuɗin kuma aka ciresu tare da blocking account ɗin ma gaba ɗaya. To shi tayaya ya bibiya ya gano komai? Mutumin da kullum damuwarsa maida naira ta zama dala. Kai nikam fa na fara tsoron boss ɗina. Ko yanzu ma ji nake zazzaɓi na nemam rufeni, dole ne sai naje asibiti naga likita). Ya ƙare zancen zucin nasa da kai hannu ya taɓa goshinsa da wuyansa kamar wani ƙaramin yaro.

     

     (HAYATU na buƙatar ganin dacta. Likitocin gidan nan ku fito ku bashi agaji🤣😂🙏)



   💞✨💞✨💞✨💞


     A lokacin da ƴan sanda keta nasu ƙoƙarin, a ɓangaren Yaya Musaddiq shima yana can tare da su Kawu Musa da sukazo da ga Gwarzo. Ba wannan ne zuwansu na farko ba. Sun dai sake dawowa ne suji yaya ake ciki duk da suna waya da Musaddiq ɗin akai akai game da al'amarin. Da ƙyar Mum ta yarda ta basu abinci, dan saida ma Abba ya nuna mazantaka yau. Bayan sun gama cin abincinne suka zauna tattauna abinda ya kawosu. Kawu Lurwani ne ya fara magana alamar shi suka wakilta yayi. Sai da ya kalla Abba da Musaddiq sannan ya fara faɗin. “Wato Imamu magana ce mai muhimmanci ta kawomu nan tare da sake jajantama juna akan batun yarinyar nan. Al'amarin nata akwai mamaki da ban tsoro ƙwarai matuƙa. Dan zuwa yanzu dai duk mai hankali ya kamata ya fahimci ba waɗan nan mutanen bane masu cewa a basu kuɗi idan sun kama mutum. Dan da ace hakanne da tuni sunyi maganar kuɗin. Amma gashi yau har kwanaki goma sha uku da rasata babu wani bayani. Hakan na nufin aikin magautane tunda yarinya ce mai farin jinin mutane sakamakon aikinta. Yanzu mu kai tsaye bazamu ce ga wanda yay wannan aika-aikar gareta ba damu ma kammu da ke a cikin tashin hankali. Bamu ce kuma ƴan sanda sun gaza ba, dan suna iya ƙoƙarin su suma. Amma magana ta gaskiya bai kamata muma mu rungume hannu muna jiransu ba.....”

      “To Lurwanu yaya zamuyi idan ba hakan ba. Aikinsu ne ai, sune kawai suke da dabarun bincike, dan a yanzu haka since wanda ya ɗauke ta a napep yana hannunsu ma, sai dai yaƙi amsa laifinsa”. Abbane yay maganar cikin katse Kawu Lurwanu. Kai Kawu Lurwanu ya girgiza, “To ai ban kai ƙarshe ba nima ka katseni Imamu, abinda nake so nace bafa zama zamuyi mu rungume hannaye muna jiransu su kaɗai ba. Kamata yay muma mu saka roƙon ALLAH tako ina. Sai dai kasan mu ɗin ba masu ƙarfi bane, kuma al'amarin yana buƙatar sadaka. Dan haka muka yanke hukuncin dawo da waɗan nan kuɗi na aurenta da aka karɓa, dan dubu ashirin kawai mukaci a ciki aka ajiye tamanin akan idan lokaci yayi zamu ƙara da wasu a rage maka hidima. Kaga kaima saika kawo wani abu daga cikin wanda ke hannunka a haɗa a sai abinci da wasu abubuwa aita sadaka ana addu'a sai kaga anci nasara ALLAH ya bayyanata cikin sauƙi. Dan yarinyar nan kullum kwanakin bikinta sake matsowa sukeyi, dan ma yaron kirki ta samu, kuma danginsa basu da fitina, amma wlhy da wasu ne da yanzu sun fara zame-zame akan al'amarin nan. Amma kaga yaron nan da shi aketa faman faɗi tashi na son ganin an samota har ma da iyayen nasa. Amma yaya ka gani shawara ce?”.

       A ɗan fusace Abba ya ce, “Ni gaskiya babu kuɗin nan yanzu a hannuna. Sai dai idan shi Musaddiq nada su ya aramin idan na samu zan bashi”.

     Kaf falon babu wanda bai ƙwalalo idanu waje dan mamaki ba.......✍️


      _Ai ni kaina idanun nawa a waje. Abba al'amarin ka ya fara ban tsoro da mamaki. Ya rabbi kasa mu rayu da ƴaƴanmu, maraici da banne wlhy a rayuwa😭_.




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

No comments