Breaking News

Kanwar Maza 38


Kamar sokuwa haka ruma ta bi bashir da kallo, daga bisani ta ja wani uban tsaki ta ce “Dan Allah ka daina raina mini hankali, wai komai nawa sai wannan mutumin ya shigo ciki, to wallahi ba shi bane ba, É—ana ne ba shi ne babansa ba”.  Ko cikin gushewar hankali takawa ba zai manta wannan muryar me shegen karaÉ—i da tsiwar tsiya ba. Shi kansa mamaki yake yadda aka yi rumaisa take shigowa cikin rayuwarsa a bazata. Ya É—aga jajayen idanunsa ya na Æ™are mata kallo.

Usman ya ce “Rumaisa, kin ga ki nutsu kin ji, shi a ina ki ka san shi?”

Ta kalli Bashir, sannan ta É—an kalli takawa, ta girgiza kai ta ce “Ni ban san shi ba, ku karÉ“o É—ana ku bani, ba shine babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba”.

Bashir shima ya Æ™arasa gaban rumaisa ya ce “Rumaisa, ba cewa ki ka yi tace miki ita ‘yar turakin kano ba ce? Ta ce miki giwar Galadima ce sirikarta ba, to ai ga giwar Galadima nan, Adam kuma É—anta ne” ruma ta yi shiru ta tafi tunanin abun da ya faru ita da Aisha.

Lokacin da ta kammala bawa Aisha labarin abun da ya faru a tsakaninta da Adam, ta din ga yi mata dariya ta ce “Kamar na san mutumin nan da kike bani labari”.

Rumaisa ta ce “TaÉ“, aikuwa idan É—an uwanku ne sai dai ki yi haÆ™uri dan ba shi da mutunci, bama ki san shi ba anty aisha”.

Aisha ta kalli ruma ta ce “ÆŠan gidan marigayi Galadiman Kano ki ka ce ko?”

“Oho masa, amma dai kamsr haka aka ce”

“Amma da Æ™arfin hali kike ruma, dan Æ™arfin hali babban mutum ki yi masa wannan rashin kunyar?”

Ruma ta taÉ“e baki ta ce “Ai ni Allah kaÉ—ai nake tsoro”

Aisha ta yi murmushi ta ce “To ki yafe masa mana my baby rumaisa” ruma ta daki Æ™asa ta ce “Ai ko shine zai zo gabana ya ce na yafe masa ba zan yafe masa ba, kin ga rashin muntucin da yayi mini, har da ce mini ‘yar talakawa, yanzu da ciki ya fito mini da ya taÉ“a mini nono fa, ina zan saka kaina?”

Tayi dariya ta ce “Ai bai fito É—in ba, kuma gaskiya kar ki yi masa sharri dan kin tsane shi, you are still a baby, ina wani nono a nan banda sharrinki ruma? Ko kwatan nawa ba su kai ba fa, ko ganinsu ba ayi”

Rumaisa ta ce “Wallahi sun fara fitowa, mama ta ce duk wanda ya taÉ“a ciki zai fito mini, kuma korata za su yi daga gidan su, yanzu da ya sa an koreni fa, ni fa bana son ma su fito, idan ba haka ba mama zata hanani yawo ba riga, yanzu ma hanani take yi”

Aisha ta yi dariya ta ce. “gaskiya ki daina zaginsa tun da dai ba a korekin ba, kin yi masa sharri, ina wani abun taÉ“awa a nan” tayi maganar tana sake tuntsirewa ruma da dariya.

Ruma ta ce “Wallahi ya taÉ“a, kuma idan Allah ya sa na bar nan idona idonsa zai gane bashi da wayo, ana i gobe zan zo katsina, yayi mini wanka da kwata a tsakiyar layi, wai har da cewa na yi masa sharri da nace ya taÉ“ani, wai zuwa yayi ya duba ya ga ko akwai wani abu a Æ™irjina ki ji É—an iska fa”

Aisha ta dafe Æ™irji ta ce “Wayyo zuciyata, haba baby rumaisa sunan mijina adam, kar ki sa kishina ya tashi. Amma ni nawa Adam É—in shima yana da zafin zuciya, baya son raini ga miskilanci, amma idan ki ka fahimce shi, mutumin kirki ne, mai son kulawaga iya soyayya, sai dai….” ta É—an yi shiru sai kuma ta ce “Ruma zaki auri Adam?”

Ruma ta waro ido ta ce “wane Adam É—in? Ni da ban yi tsawo na girma ba za ayi mini aure?”.

“Adam da kuke faÉ—a, ki yafe masa ko dan albarkacin yana da sunan mijina”

Ruma ta turÉ“una fuska ta ce “Ai wallahi ko yayanki ne ba zan yafe masa ba, da in auri Wannan gara na mutu ba aure, kuma ni miji kyakkyawa nake so, kuma mai kuÉ—i”

“In dai kuÉ—i ne akwai su ruma, kuma ai kyakykyawa ne”

Rumaisa ta dubeta ta ce “Ba fa mijinki ba, wannan da muke faÉ—a nake gaya miki, mai suffar mugwaye da wata banzar motarsa in sha Allah sai an sace motar ma”.

“In an saceta ma zai sai wata, kuma ya sai miki kema, banda faÉ—an rashin gaskiya ke fa ki ka fara zaginsa a social media, amma tsabar rigimarki kina ta zaginsa, kin ci sa’a da bai É—aureki ba, ko ya sa a zaneki ba”.

“Oho ni dai ban yafe ba”

Tayi ajiyar zuciya ta ce “I love your confidence my dear, you can face the challenges. Jikina na bani wani abu game da ke, zaki iya ruma” tayi maganar tana jan kunatun rumaisa ta ce “Kamar haka mijina yake wasa da kumatuna”.

“Anty Aisha, yake taÉ“aki? Ba a wasa da maza fa” ba ta bawa ruma amsa ba, sai dariya da take yi mata, tana fatan Allah ya tabbatar da abun da take ji game da ruma.

Ranar da zata rasu bayan ta haihu, ta riÆ™e hannun rumaisa ta ce “Baby rumaisa, idan Allah ya sa kin kuÉ“uta, ni ‘yar gidan turakin kano ce, amma kar a nemi mahaifina kai tsaye a nemi sirikata, idan ba zaki iya riÆ™e jaririn nan ba, ki danÆ™a mata shi, Hajiya Binta giwar Galadima, uwar gidan galadiman kano, sirikata ce ita zaki danÆ™awa jaririn nan, É—an ta shine mijina” a lokacin gaba É—aya ruma ta manta da wani adam balle ta kawo shi a lissafi da aisha ta yi zancen galadima.

Ko da ruma ta zo nan a tunaninta sai ta tambayi kanta ‘Kenan da gaske shi ne mijinta?’ a zahiri kuwa ta fashe da kuka ta ce “Wallahi ba shi ne babansa ba, ni ba shi ta ce mini ba” a bata iya tafiya ta fara Æ™oÆ™arin dirowa daga kan gadon tana miÆ™a hannu ta ce “Ni ku bani jaririna, ba É—ansa bane ba, ni ba ta ce mini in bawa kowa ba, ku bani É—ana” mama tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.

Bashir ya miÆ™awa Adam hannu ya ce “Ka ga Adam, kawo yaron nan, gaba É—aya a ruÉ—e take, kamar ba ta hayyacinta ne ma, kawo a bata shi kan muga yadda hali zai yi”.

“Bashir ka haukace ne? Taya ka ke cewa in baka É—ana ka bawa wani?”.

“Wallahi ba É—ansa bane ba, ku bani É—ana” ruma tayi maganar tana kuka.

Bashir ya karÉ“e yaron, ya miÆ™awa rumaisa, ta rungumeshi tana fashewa da kuka ta ce “Cewa ta yi idan ba zan iya riÆ™e shi ba, in bawa giwar Galadima ni ban santa ba ma, ban san a in da take ba, amma ni dai zan iya riÆ™e yarona, ai cewa ta yi ta bar mini shi har abada nice mamansa”. Gaba daya É—akin aka zubawa sarautar Allah ido.

Ammi da tun É—azu take zaune kamar an shukata, ta kasa magana sai tasbihi kawai da take yi, ta tashi sannu a hankali, ta je kusa da rumaisa suka matsa mata ta zauna.
Ta dafa kafaÉ—ar rumaisa idonta fal hawaye ta ce “‘ya ta, nice giwar Galadiman kano mai rasuwa, Adam kuma É—ana ne, shine mahaifin wannan jaririn, kuma mijin Aisha”.

Ruma ta girgiza kai ta ce “A’a wallahi ba shi bane ba, ni fa ba zan bawa kowa ba, ni ta ce ta barwa shi”.

Ammi ta ce “To shikenan, na ji babu mai rabaki da yaronki, Ubangiji Allah ya baku lafiya gaba É—aya, yanzu ki bayar da shi a mayar da shi sashen kula da yara”.

Rumaisa ta girgiza kai ta ce “Ba zan bayar da shi ba, haka kurum ya bishi ya sace shi, da in bashi É—ana gara na koma wurin ‘yan garkuwa da mutanen”.

Huzaifa ya ce “To fa ana wata ga wata”.

Ammi ta ce “To shikenan, rungume shi da kyau, kin ga bacci zai yi kema ki kwanta ki huta” a’a ba zan rufe idona in je ya gudu da shi ba.

MiÆ™ewa Adam yayi jikinsa yana rawa, amma Ammi tayi masa wani irin kallo, tayi masa nuni da ya fita, yayi gaba ya tsaya ya waiwaya yana kallon rumaisa, da jaririnsa da yanzu ya shiga tunanin ina uwarsa? A wane hali kuma take ciki?”.

Suna tafe a hanya babu wanda ya iya cewa komai, sai Bashir da yake yi wa Adam nasiha “Adam dole sai mun bi yarinyar nan a hankali har yanzu a rikice take, kuma a cikin firgici ba Æ™aramar azaba ta sha kan ta fito da yaron nan ba, kaga Yarinya ce Æ™arama ikon Allah ne ya fito da su, dan ita ma ba gama sanin ciwon kanta tayi ba, a sannu zamu bita mu ji a ina ita Aishar take, sai mu zo mu yi shiri”.

Daga Ammi har takawa, babu wanda ya ce wani abu, kowa da abun da yake saƙawa a zuciyarsa, adam bai taɓa tunanin abubuwa su cukurkuɗe masa haka ba.

Suna zuwa gida ammi ta wuce part É—inta, adam ma bai jira bashir ba, ya rufa mata baya.
A falo nusaiba ta tare ta tana tambayarta, “Ammi wai ina ki ka tafi haka, mun dawo daga islamiyya kawai muka tarar ba kya nan, kalli dare har ya fara yi fa” sai dai fuskar ammin ta nuna mata ba lafiya ba. Kan ta yi magana ta ga adam ya shigo ya bi bayan anmi, hakan ya sanya ta sha jinin jikinta.

A É—aki ya tarar da ammi, ta ajiye carbin hannunta da mayafinta, hawaye tuni ya wanke mata fuska.

“Ammi dan Allah ki tsaya ki saurareni, kar ki yi mini haka”.

Ta kalli Adam ta ce “In saurareke ka gaya mini me adam, yanzu a duniya akwai abun da zaka iya É“oye mini? Ta ina zamu kalli duniya mu fara bayanin abun da ya faru? Ta yaya duniya za ta yadda da cewar jaririn nan É—anka ne? Da yaya zaka yi wa turaki bayanin abun da ya samu ‘yar sa, shikenan mun zama masu son kai kenan, idan maganar nan ta yaÉ—u ina zan saka kaina, ina ta Æ™oÆ™arin toshe waccan kafar wannan ta É“ullo, adam kana me garin yaya haka ta faru ka É“oye mini, É—an da ba a san da cikinsa ba kawai mu ce ga É—a meye shaidarmu ba Æ™arya muke yi ba, ina ita Aishan?”

Adam da ya gama rikicewa ya ce “Dan Allah ammi ki fahimce ni, zan yi miki bayani bani da laifi, ba domin na É“oye miki na yi duk abun da na yi ba”

Ammi ta katse shi ta hanyar cewa “To domin ka faranta mini ne? A tunaninka zan yi murna da hakan ne?”.

Ya girgiza kai tare da goge hawaye ya ce “A duniya bani da makusancin da ya fiki, daga ni har aisha, kin san komai Ammi, kamar yadda muke ta neman magani tsawon shekaru huÉ—u, aka dace cikin jikinta ya zauna, bayan É“ari da take ta yi babu Æ™aƙƙautawa a dalilina, cikin nan  babu wanda ya san da shi, bayan ke sai mu, wanda hakan shawarar ki ce, har zuwa lokacin da kika bayar da shawarar ta je Saudiyya wurin É—an uwanki kawu mahadi, ta zauna ta raini cikin a can, idan ya isa haihuwa ta dawo Nigeria, duk dan kaucewa hatsarin da ka iya faruwa da cikin, muka yi nesa da juna ni da ita.
Bayan na kai ta ta yi watanni huɗu, na sake komawa Saudiyya umara, na dubata, na dawo babu daɗewa ta ce mini ita ta gaji da zaman Saudiyya so take ta dawo gida. Ta ce mini wannan kakar ta ta, mariƙiyar mamanta babu lafiya, dan haka ita so take ta dawo ta je ta ganta, kar ta rasu basu gana ba. Gudun ɓacin ranki, ya sanya ta dawo babu wanda ya sani, sai dai a lokacin cikin yayi girma sosai ta sanya rigima a kan lallai sai ta je duba matar, an ce ba ta gane kowa, wankin ƙoda ake yi mata ma. Duk sauƙin kan Aisha, haka ta kafe a kan lallai sai ta je katsina duba matar, a daidai lokacin kuma ni tafiya Abuja ta kamani, bayan tafiyata ta sanya ɗaya daga yarana, masu tsaron lafiyarta ya kai ta katsina. Ta turo mini saƙo a waya tana bani haƙuri a kan ita fa ta tafi, ba zata iya jira na dawo ba, a tsorace take kar kakarta ta mutu. Bayan dawowata daga Abuja, sai samun saƙo na yi, an tsinci gawar yarona da motar, ita kuma ba a san in da take ba, tun da ga wannan lokacin nake ƙoƙarin gano in da take, har zuwa wannan lokaci, daga ni sai Bashir muke ta ƙoƙari, dan ko su Jabir basu sani ba, na san na yi laifi ammi amma ba da gayya na yi ba.

“Adam nika É—ai zan fuskanci wannan bayanin naka, duk mutane sun san da cewa tana Saudiyya, babu wanda ya san ta zo Nigeria haka zalika babu wanda ya san tana da cikin ma, kawai sai mu ce ga É—a to ita tana ina, na gaya maka bana samunta a waya, amma ka yi ta yi mini Æ™arairayi, dama akwai abun da zaka iya É“oye mini Adam? Me zaka cewa Turaki?”.

A raunane Adam ya ce “Ko babu wata cikakkiyar shaida,ni na san da cewa É—ana ne, babu yadda za ayi yarinyar nan ta san wasu abubuwan idan ba gaya mata tayi ba, amma ammi ni yanzu ba abun da mutane zasu ce ne ya dameni ba, samo aisha ne ya dameni, babu wata hujja da nake jira yaron nan nawa ne, ko a fuskarsa kamanni na ne, sannan da kaina zan gayawa turaki komai, duk hukuncin da zai yi mini zan É—auka”.

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce “Zan cigaba da yi maka Addu’a, Allah ya kawo mana mafita, amma yarinyar nan ka bita a hankali dan Allah, in sha Allah yadda jaririn ya kuÉ“uta, ita ma zata kuÉ“uta”.

Adam ya jinjina kai kawai, ya tashi ya fita daga É—akin, su Nusaiba suna falo a tsaye cirko-cirko, adam ya zo ya fice.
Cikin rige-rige suka tafi É—akin Ammi, amma suka tarar ta shiga toilet, ko da ta fito umarni ta basu, na su je su kwanta sai da safe, dan kar su bi diddigin abun da ya faru, sai dai a tsorace take da abun da ka iya faruwa idan zancen nan ya fasu.

A asibiti kuwa, Aliyu ne ya dubi rumaisa ya ce “Ke dai a rayuwarki ba a taÉ“a rasaki da matsala, an samo uban yaro kin ce ba shi ne ubansa ba, sai ki nuna mana waye ubansa?”

Usman ya ce “Ai ko da uban me ki ke yawo, sai an mayar musu da É—an su”

Mama ta ce “Yanzu dai a bar wannan maganar, Allah ya dawo mana da ita, daga dawowarta sai a bari ta sarara kan a hau yi mata faÉ—a, Ali ku je gida haka, kwa sanar da mutane an ganta”

Mai sunan Baba ya ce “Eh amma kar su sanar da Asibitin da take, kar azo a takura mata, ko ayi ta surutu saboda jaririn nan, a bari komai ya daidaita”

Mama ta ce “To hakan ma babu laifi, kar ku gayawa Abubakar a daren nan tun da ba a samu wayarsa ba, ku bari sai da safe kar ya ce zai bsro dutse yanzu”

Usman ya ce “In sha Allah”

Mai sunan Baba ya saka hannu, ya karÉ“i jaririn da ga hannun rumaisa, sai bin sa take da ido, kar ya fita ya bawa Adam yaron, ya Æ™arewa yaron kallo ya ce “Bari na bawa nurses É—in nan, su mayar da shi É—akin da ake kulawa da sh, mama gobe in Allah ya kaimu zan zo mu koma ki ga likitan ki”

Mama ta ce “Ga mara lafiya ni ina zani? Dama rashin lafiya tawa saboda ita ne”

Ya ce “Duk da hakan, yakamata ke sai da safe, ki nutsu ban da gardama da taurin kai ki yi addu’a ki kwanta ki huta”

Kamar ba zata amsa ba sai kuma ta ce “Dan Allah mai sunan Baba kar ka bawa kowa shi, wallahi zan iya rasuwa idan aka rabani da shi” bai ko waiwayo ba ya fice daga É—akin.

Mama ce ga rungumota tana rarrashinta ta ce ‘Ba wani zai bawa ba kin ji, ki yi haÆ™uri É—akin da ake kula d shi zai kai shi” rumaisa ta yi lamo a jikin mama, can ta ce ‘Mama”

Mama ta amsa mata da na’am.

“Ba mafarki nake ba ko, ba zan kuma farkawa na ganni a dajin ba, na ga kun daÉ—e a wannan mafarkin nawa”.

Mama ta shafa bayanta ta ce “Ba mafarki bane ba, duk muna tare da ke”.

“Mama kin ga yadda ki ka rungumenin nan? Haka maman yaron nan take rungumeni tana rarrashina idan na tunaki ina kuka, sarÆ™arta da zobuna ne a cikin É—ankwalin nan, É—an kunnen da ki ka cire a kunnena shi ma nata ne, mama ba zan manta da ita ba” rumaisa ta yi maganar cikin kuka.

“To ya isa, ita ma in sha Allah zata kuÉ“uta cikin amincin Allah” rumaisa ta cigaba da kuka, dan ba wanda ta gayawa aisha ta rasu.

Aliyu suna zuwa unguwarsu, ya wuce gidan su Habiba, lokacin kusan ƙarfe goma na dare, ya aika yaro ya ce yana sallama da Habiba.
Maimakon Habiba sai babarta ta fito tana masifa, wani watsatstsen ne ya zo neman habiba a wannan daren, yar habiban guda nawa take?

Tana ganin Aliyu ta yi sak, ta ce “Ya aka yi ne, ko laifin ta kuma yi maka, ko Æ™anwar ta ka ta kuma duka ka zo rama mata, duk da ance an yi garkuwa da ita”

Ya ce “Ba É—aya, wani abu zan gaya mata”.

“Wani abu ne kenan?”

Aliyu ya ce “Shikenan tun da na ga hankalinki bai kwanta ba”

Sai kuma ta ce “A’a, bari na taso ta” ta koma cikin gida, mintuna uku sai ga habiba ta fito tana mutsutsuka ido.

“Habiba” ya kira sunanta, ta kalleshi ta ce “Yaya Aliyu ina wuni”

“Albishirnki” yayi maganar cikin murmushi.

Ta É—an yi saroro ta ce “Goro”.

“To zaki bani goron nan, Alhamdilillah addu’a ta karÉ“u, rumaisa ta kuÉ“uta yau, tana asibiti ma”

Gigicewa ta yi ta ce “Innalillahi, dan Allah da gaske, dan Allah kar ka ce da wasa kake yi, dan Allah mu je in ganta”.

“No, ba a zuwa wurinta yanzu, ba ta da lafiya, amma zan zo da kaina na kaiki ki ganta”

Hawaye ta fara matsewa tana “Allah sarki Æ™awata, Alhamdilillah, Allah na gode maka”

Ya ce “Maza ki je ki cigaba da baccinki, Sai da safe”

“Dan Allah yaushe zaka zo ka kaini na ganta, gobe?”

“A’a zan zo dai, ki je ki cigaba da baccinki” yayi maganar yana É—aga mata hannu ya tafi.

Ta shiga gida da gudu tana murna.

Adam kuwa yana zuwa É—aki ya zauna ya fashe da kuka kamar yaron goye. Wai matarsa ce ta haihu a daji a hannun ‘yan bindiga, ko a yaya ta haihu oho, ko a wani hali take sanin gaibu sai Allah.

“Why aisha, meyasa ki kasa jira na dawo ki ka tafi? Duk yadda muka tssra rayuwa bayan kin haihu, Æ™arshe a tsinto mini É—ana babu ke, haba aisha kin ga sakamakon rashin jin magana ko, matar da ki ke so ki je ki duba ita bata mutu ba, amma ke kin shiga wahala. Amma bakomai, Allah ya sa kina cikin Æ™oshin lafiya, zan fito da ke ko da zan rasa rayuwata ne!

ƘANWAR ₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143*

Ayshercool
08081012143.

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI’IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA’A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA’IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA’IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni’ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Sannan ga wadanda sokeso jikinsu yayi kyau sosai amma basa son susha supplement to albishirinku muna da kowanne irin mai na gyaran jiki da kuke bukata irinsu lotion, cream, soap, scrubs, face Cream,sun screen, serums concentrate, hair oil, hair cream face mask etc, sannan ga masu fama da matsalar ciwon jiki wadanda kullum sai sunsha magani suke jin dadi ko iyaye ko kakanni, to albishirinku kuma mun kawo muku cream, soap na ciwon jiki masu kyau da inganci wadanda indai kana amfani dasu ka huta shan maganin ciwon jiki da yardar Allah*

*Muna saida duk wasu nau’in supplement Lotion da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*₦500 ne, via 0009450228 Aisha Adam, jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*

No comments