Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 20


MIJIN MALAMA
PAID BOOK
0811923761622
Mutumin dake zaune cikin motarshi ya zame idanunsa daga cikin nata a hankali ya rufe Ido yana jin abin da Latifa Omar ke faÉ—a. “You surprised me, Aliyu” Yana jinta dai bai ce komai ba, Latifa Omar ta Æ™ara cewa “Zuwan bazata har haka? Bayan am not in a dreams, kuma ba dare ba balle na ce?” Aliyu ya buÉ—e idanunsa cikin gajiyawa a gajarce ya ce “To ya na iya? My heart beating so faster” murya bata fita sosai ya Æ™are maganar. Ganin Majeederh na Æ™oÆ™arin shige su bayan daman tare za su fita É—in ya sa ta ce “2 minutes please” Fita tayi da sauri harta isa ga Majeederh tana riÆ™e hannunta ta ce “Me kike Æ™oÆ™arin yi? Bayan kinsan ke nake jira kada ki bari Æ™waÆ™walwarki ta daina aiki ko ta samu matsala sbd tuna-ne-tuna-ne” Kallonta kawai Majeederh ta yi ba tare da ta ce komai ba. “Kizo muje, ya ce hanyar B.u.k É—in zai yi shi ma” Yadda Majeederh ke kallon Latifa Omar yasa ta fahimci kusan dalilin kallo. Murmushi ta yi ta ce “Uhm I knw ur problem Majeederh, kina tsoran what those few people are going to say, right? Ai na faÉ—awa Baba ko waye kuma Abbu ma ya sani you can ask idan baki yarda ba, kawai if you trust me you have to believe” Majeederh da fararen Idanunta wanda suka kuÉ—e kawai ake gani,ta juya su a taushashe ta ce “Ke macace, ita mace sirri ce, sirrinki tsaraicinki ne, ki riÆ™e shi kamar tazugenki” Latifa Omar ta saka dariya mgn É—aya kawai Majeederh za ta yi mai cike da ma’ana da azanci ta ce “Ok zan riÆ™e da hannu bibbiyu, Majeederh sbd ke na ce zai kaimu, nasan Abbu bai baki kuÉ—in mota ba, kuma is like compulsory to you na zuwa karÉ“o form É—in, ki yarda dani in sha Allah nothing will happen as you think” Kafin Majeed ta yi magana ta yi gaba abinta hakanne kawai zai saka ta taho. Ta cikin madubin motar yake Æ™are mata kallo har ta buÉ—e ta shiga sai a lokacin nauyin da zuciyarsa ke masa tun daren jiya ya saki, ciwon kan ya yi nasa waje. A ransa yake mamakin yadda ko kwalli bata sakawa cikin Idanunta. Key ya yi tare da yin reverse kana ya É—auki hanyar da zata kaisa B.u.k new side…. Sun yi nisa sosai babu abin da ke tashi sai maganar Latifa Omar, Aliyu ya É—an ya tsuna fuska yana tunanin yadda abu kamar wasa yake neman zamar mishi gaske, ya ce yana son Latifa Omar amma baya jin aurenta a ran shi duk da furta a baki, ya rufe idanu ya buÉ—e saman kwalta his heart disappointed him. Ya kasa daurewa ya ce “Na zama drivern kurma” Latifa ta ce “Kurma? Yana driver idanunsa rabi da rabi akan madubi ya ce “Ur friend, Jiddatul-khairy” Latifa ta buÉ—e ido kana ta juya ta ce “Malamarmu, Malama Majeederh mijin da zan aura ba sai anja masa aji? Ba gaisuwa” Aliyu-haydar ya ce “Hakan kuma ba halin Malaman Æ™warai bane” Duk tana jin su sai da suka gama surutu da wajan minti biyu suka ji ta ce “I don’t want interfere” Wata É“oyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke lokacin muryarta ta sauka cikin kunnenshi, ba zai iya cewa ko ranar daya fara ganinta ya ji muryarta ba, sbd baya cikin nutsuwarsa ji yake kamar new Aliyu akai a lokacin ba shi Aliyun ba, sai ya ji kamar bai taÉ“a jin murya irin haka ba in his whole life, sanyi, nutsuwa, haÆ™uri da kamalarta duk ta bayyana cikin maganar da tayi ta kalmomin da baza su gaza biyar ba. Suna zuwa cikin B.u.k É—in Majeederh ta fita babu jimawa ta dawo lokaci Aliyu na zaune hannunsa riÆ™e da Swn water yana sha ganin yadda ta yi tsaye ta kasa knocking Glasses É—in motar yasa gently ya saka hannu ya fito daga cikin motar yana zuba hannu a aljihu tare da juyawa ya dinga ganin Students different department suna ta zirga-zirga. Ya kalli Majeederh ya ce “Jiddatul-khairy, you are too…” Da sauri ta É—aga kanta a tunaninta ko yau Allah zai sanya wani namijin ya ce tana da kyau, saÉ“anin Uncle Isma’il da yake cewa tana da kyau da kuma Æ´an-uwanta mata sai ta ji ya yi shiru ya ce “Kin gama ne?” Ta girgiza kai tana addu’a a zuciyarta Aliyu yana son ya Æ™ara jin muryarta ya ce “Mene ya faru? Me bada form É—in ne baya nan ko?” Har ranta ta gaji da magana ga yunwa sosai take ji ga kewar Little da rashin sanin inda yake ta marairaice kamar za ta yi kuka sosai ta ce “Uhm ba nan bane” Aliyu ya ware ido hadda riÆ™e Æ™ugu ya ce “Oh ni Haydar sai aka ce ina?” Batai magana ba har Latifa ta fito daga cikin motar ta ce “Meke faruwa nan?” Aliyu ya yi mata shiru Majeederh ta É—auke kai can ta ce “Murtala way” Murmushi kawai Aliyu ya yi ya ce “Oh Kano state ministry of education, i think Government office?” Ya faÉ—a yana duban Majeederh “To yanzu can zamu kenan? Domin idan muka koma gida ba wannan form É—in mun shiga uku wajan Abbu kwana zai yi yana faÉ—a” Aliyu ya ce “Waye?” Kai tsaye Latifa Omar ta ce “Her father” Sosai ran Majeederh ya É“aci Latifa na son nunawa Aliyu Mahaifinta masifaffe ne ko yana takura musu ta É“ata fuska duk da ba’a ganin yanayin nata. Cikin Aljihu ya saka hannunsa ya ji ba kuÉ—i ya juya yaga babu wani pos a kusa da su, babu cash da sauri ya juya mota tuna cewa kamar ya bar kuÉ—i ciki jiya daya siyi Popcorn 2k ne ya miÆ™awa Latifa ya ce “For transport, ku yi amfani da shi wajan napep ina da shari’a 1:00” Latifa ta ce “Ok bye” Ya girgiza kai kawai jin ko godiya babu bawai kuma damuwa da hakan ya yi ba, Majeederh ya san ba za ta yi magana ba…..
Sun jima cikin haÉ—aÉ—É—en office É—in na commissioner for education É—in, kafin a hankali su ji an shigo duk suka miÆ™e tsaye ya nemi waje ya zauna, magidancin mutumi ya zauna saman kujera, babba ne mai shekaru amma kuÉ—i sun zauna rayuwar daula ga hutu da kwanciyar hankali plus jin daÉ—in rayuwa. Ya amsa gaisuwa ya ce “How can I help you?” Majeederh ta yi Æ™asa da kanta a hankali ta ce “Sunana Majeederh Abdul’aziz Khan, ance na zo na amshi Form na scholarship É—in da akai mana al’Æ™awari ranar Candy da MusabaÆ™a” Ya jinjina kai ya ce “Ok” Kana ya shiga jawo file gefe É—aya kuma yana danna waya ya ce “I, Alhji Aliyu S, Commission for education” Bayan sun amshi form É—in ya haÉ—a su da wani ya yi musu bayani, Sai dare Majeederh ta ci abinci towon masara biyar kuÉ“ewa bushasshiyya bacci É“arawo shi ne ya É—auketa. Washegari babu inda ta fita sbd ciwon kai da zazzaÉ“i tana ta kiran number Akeeth shiru a kashe. 5days left da yamma ranar laraba tana zaune a É—aki tana tunanin hanyar da za ta yi cigiyar Little sai kawai ta yi ta sauke application É—in facebook ta buÉ—e Acct da full name É—inta Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, ta saka photon Little cikin uniform da rubutu mai tsayi da ma’ana, tausayi da neman taimako. Comment É—in data gani ya É—aga hankalinta zuciyarta tayi nauyi, ta ji kanta na juyawa komai ya yi mata zafi, ta Æ™ara buÉ—e Idanunta akan comment É—in da aka ce mata “Ke aure ya kamata dake, shekaru sun ja” Ta cillar da wayar tana miÆ™ewa tsaye kena kowa ya san bata da aure? Me ya sa ake son goranta mata yin aure ne? Ita zata aurar da kanta ne ko ita za taga namiji ta ce tana son auren shi? Ta Æ™arasa gaban madubi ta shiga kallon kanta Majeederh ba zata iya tantance da gaske tana da kyau ko bata da shi ba, tasan dai ita fara ce ba ruwanta da Powder, kwalli, lipstick kullum fuska a rufe cikin liÆ™ab sai duguwar riga da take sawa ko Æ™aton hijabi. Ko dai gwada fita za ta yi babu wannan abubuwan? Idan ta fita hakan zata samu wanda zai ce yana sonta? Ta yi shiru… Washegari Alhamis bikin Widad ya kama yau za a fara za su yi Arabian night. GabaÉ—aya suna zaune a parlourn gidan Uncle Isma’il, ga Uncle Bello ga Abbu sai Yaya Bilkisu da Innati. Uncle Isma’il ya ce “Na fahimci matsalarka Abdul’aziz, sbd baka da É—a namiji shi ya sa ka É—auki Majeederh kamar namiji? Tunda ita ce babba, duk abinda yake faruwa na sani, kawai zan maka cewa ba ka yi kanka da Æ´arka mai hankali adalci ba, Majeederh does not deserve this Abdul’aziz, idan karatu ne kaima kana iya faÉ—aÉ—a naka kaje ka Æ™aro ilimi, idan ma hakan kake so ta yi why not ka fara yi mata aure first sai karatu ya biyo baya, kaga da mijinta da komai babu wata fargaba, amma Fisabilillahi ka É—auki Majeederh wacce take kan shekarunta na balaga tun daga Nigeriya zuwa Misira? Kasan halin da zata kasance a tsayin shekaru takwas É—in da za ta yi? Yanzu ko namiji ne ka sadaukarwa ilimi shi ba tare da tunanin lafiyarsa ba?” Abbu ya kalli yayan nasa Uncle Isma’il ya ce “Lafiya kuma? Ina tunanin ai akwai kulawa ta makaranta?” Uncle Isma’il ya ce “Ok bari na na fito maka a mutum, idan Majeederh ta buÆ™aci namiji makaranta zata bata? Ko maza zata fara bi? Ka haifi yarinya a cikinka amma You don’t even know abinda ke damunta, da abinda take so ba, Majeederh Allah ne kawai yake kula da ita kuma shi ne ya bata yawon da take da shi, gata Æ´ar fari ga babu kulawar uwa data uba a wajanta” Sai a lokacin Yaya Bilkisu ta ce “Allah na tuba gata dai kyakkyawa amma ai babu mai ganin kyanta bata da kaya sai duguwar riga kamar haihuwar Larabawa, ai Allah ne ya san manufar Fulani da tace ka aurar da ita tun tana 15 amma kaÆ™i, ka ci mana wasiyya Allah ya sanya ta fito da kabari tai maka fatalwa sai ka fahimci tashin hankalin da take ciki” Innati ta zare idanu ta ce “A’a ba amin ba wannan kuma ai fatan tsiya ne meye kuma fatalwa ana zama lafiya abi dai komai a nutse tunda shi ya ce karatun take so ku zuba masa idanu idan yana laifi sai ya yi, duniyar gabaÉ—aya nawa take? Allah na tuna ya rubuta ya ajjiye komai ya faru ya shirya amsa” Uncle Bello ya ce “In sha Allah babu abin da zai faru, da dai ya barta tayi auren shi ne kawai” Abbu ya ce “Aure fa baya bari ayi karatu by the way waye ya ce yana son aurenta na hana?” Duk su ka yi masa shiru haka dai taron ya tashi ba fahimtar juna tsakanin Abbu da Uncle Isma’il da Æ™aninsa Uncle Bello, familyn Khan maza ba su fiya yawa ba mata duk sun fi yawa. Majeederh na parlour ta yi shiru tana kallon yadda Æ´an matan suke shiryawa cikin abayas baÆ™a Ruma jiya Imran ya bata, Raihana ma saurayinta ne ya siya mata, Aaliyyah kuma Majeederh ta siya mata da kuÉ—in albashi. “Anti Jeederh ba zaki ba?” Majeederh ta kalli Ruma ta ce “Eh” Aaliyyah ta ce “Amma me ya sa Anti Jeederh?” Ta yi musu shiru kawai Mami ta ce “Hawwa’u me ya sa baki son shiga cikin Æ´an uwanki ne?” Ta ce “Ba komai” cewar Majeederh tana rufe ido Mami ta ce “To Allah yana kallo na yi nawa yin, Majeederh idan kana da kyau ka Æ™ara da wanka amma dai kuma ta wani É“angaren kina da gsky tunda duk kin girme su sai dai ko Sahar” Aaliyyah ta ce “Kai Sahar É—in ce sa’ar Anti Jeederh? Naga na girmeta da shekara É—aya ma” Mami ta ce “Ji Æ™uruciya to ai duk wanda ya yi aure ya zama sa’anta yanzu hirar da za ayi da Sahar waye zai yi da Majeederh?” Majeederh ta miÆ™e tare da shigewa bedroom É—inta zuciyarta a cunkushe ji take gwarama kawai ta tafi karatun ta huta zuciyarta ta samu salama. Gidan Uncle Isma’il akaiwa decorations ya yi kyau sosai bride mate da friends É—inta sun yi kyau aci make up, ga abokan ango sun kyau yawancin su classic ne masu aji ilimi ga wadata ta iyaye. A hankali Majeederh ta sako Æ™afarta cikin harabar gidan kiÉ—a na tashi zuciyarta sai rawa take for the first time data zo event har haka, wanda kuma bayin kanta bane tabi ragamar zuciyarta akan abinda take jin kamar shi ne daidai, abaya ce mai Æ™aton hannu a jikinta ga faÉ—i da take da shi ta yi mata yawa sbd ramewar da tayi, tayi rolling kanta a hankali ta saka hannu ta zame liÆ™ab É—in fuskarta a karo na farko in her whole life data cire liÆ™ab a gaban maza tafiya ta fara yi zuwa wajan, gabaÉ—aya idanun jama’ar wajan suka dawo kanta duk wanda ya ganta sai ya taÉ“o na kusa da shi ya nuna masa Majeederh daga mazan har matan, ta ci-gaba ta shiga cikin wajan tana zuwa dab da wani matashin mutum tun kafin ta Æ™arasu ya juya da sauri kamar yaga Aljana yabar wajan jiki na rawa……

 

No comments