Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 21


MIJIN MALAMA
Via this number….. 0811923761623
Duk inda ta sanya Æ™afarta sai taga ana matsawa tare da jan jiki baya, Majeederh was Shocked ta yi saurin saka hannunta ta shiga shafa fuskarta ko wani abu ne ya sameta, amma bata ji komai ba, bata iya shiga razani ba sai numfashinta ya fara sauka da Æ™arfi ciwonta ya fara neman tashi, wani saurayi ya dinga kallonta daga nesa ganin attention É—insa yana kanta ya sa ta nufesa duguwar rigar jikinta na neman yarda ita sbd tayi mata yawa sosai. Tana zuwa wajan saurayin taga ya yi saurin rufe idanunsa a fili ya shiga faÉ—in “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, Ya subuhanallahi!” Kalamansa da salatin da yake na neman taimako daga Ubangiji ya Æ™ara firgita Majeederh da jirkita duniyarta idanunta da sukai jajur ta buÉ—e akan saurayin ta ce “Don Allah mene ya samu fuskata? Me ya sa kowa ke kallo na?? Me ya sa maza suke guduna?” Sosai muryarta ta razana shi amma ya dake deep down na zuciyarsa addu’a yake na neman tsari ya dai daure ya ce
“But are you a Baha’i?” Majeederh ta dinga kallonsa ya ce “Ina nufin ke Bahaushiya ce?”
Ta jinjina masa alamar eh ya ce “Ki dai bincika amma duk wanda ya ganki zai ci Aljana ce, kyanki ya yi yawa ni ma dauriya kawai na yi” Yana faÉ—in haka ya bar wajan da sauri jikinsa na rawa. “Aljana??” Majeederh ta tambayi kanta tana nuna kanta da yatsa a fili ta ce “Is this really happens to her?” Ta zube saman kujera tare da dafe kanta “Wai meke faruwa? Ni ce Majeederh ko wata new Majeederh? Ko dai gaske Aljana ce, Innalillahi” da Æ™yar ta iya jan jiki tare da É—aukan liÆ™ab ta mayar a fuskarta tana fita Aliyu ya shigo wajan shi kansa bai san mene ya kawo shi ba….. GabaÉ—aya suna zaune a parlour Hajia ta gyara zama speaking calmly ba faÉ—a ta ce “Sannu fa, ai zata aikata duk me aka ce ta yi bana doubting” Hajiya Rahmerh ta ce “I don’t think so, amma dai ta ce komai zai daidai In sha Allah” Hajia ta girgiza Æ™afa kawai hankalinta yana ga Aliyu-haydar da har yanzu ba taga shigowar shi ba. Anti Biba mai bin Hajiya Rahmerh ta ce “Ni wai ina Autanki ne Hajia? Babu shi ba Almustapha?” Kafin ta yi magana Aliyu ya shigo muryarsa mai É—auke da damuwa ta É—an baiyana a parlour. Daga Mahaifiyarsa Hajia har Æ™annenta Hajiya Rahmerh da Anti Biba suka dubi Aliyu. “Kai lafiya kake? Wannan idanun kamar mai azumin Kaffara?” Ya nemi waje kusa da Hajiya ya ce “Am Good, ya hanya Aunties?” Anti Biba ta ce “Lafiya, lawyer sarkin Æ™arya” Bai ce komai ba ya shafa kansa feeling better ganinsa kusa da Hajiarsa “Aliyu” Aliyu ya kalli Hajiya Rahmerh har sai da gabansa ya faÉ—i ta ce “Aliyu, Aliyu, Aliyu how many times do I call your names?” Ya yi Æ™asa da kansa ta ce “Ok na kira na ji daÉ—in bakina ne ko mene? Eh?” A hankali ya ce “Afuwa” Ta gyara zama ta ce “Kana da gata, kana da kuÉ—i, kana da ilimi ka fara aiki zaka gina kanka to me ka ke jira? What are you waiting for??” Shi dai bai magana ba ta ce “To ka fita daga cikin idanuna, ku biyu kawai Allah ya bawa Hajiya Laylerh ai yana da kyau yanzu zuri’a su fi haka yawa, bari na buÉ—e maka zancan a faifai maganar aure nake maka” Ya yi shiru daman ya san abin da zata ce kenan ya ce “To” ta ce “Ba wannan nake son ji ba, cewa zakai to Hajiya Rahmerh zan yi nan da wata kaza ka gane, ni a kawo maganar ba ga can Æ´ar uwarka ta Æ™are karatunta a London Buhayyerh talk to her ina da tabbacin zata amince maka” Ya cira idanunsa ya kalleta ya ce “She is not strong enough to be my wife, I need someone stronger” Ta ce “Are you kidding me, right?” Ya yi shiru, Hajiya Rahmerh ta shiga faÉ—a ta inda take shiga bata nan take fita ba har tayi masa tas bai ce komai ba. Ya miÆ™e tare da shigewa part É—insa, yana shiga Anti Biba ta bi bayansa ta ce “baka kyauta ba Aliyu” ya riÆ™e kansa ya ce “Goodness, me na yi?” Ta ce “Ba haka ya dace ka bata amsa ba, ana iya yin Æ™arya domin kare kai wannan ya halatta a mazahabar malam Bahaushe, ana iya lashe rai É—aya domin kare rai dubu” ya yi shiru for some seconds ya ce “Kawai sai a haÉ—a aure? Kamar an daina wannan abun an shige Æ™arnin tun tuni” Ta yi Murmushi kawai ya ce “Ina Antin Turkey?” Anti Biba ta ce “Sun sauya sheÆ™a an yi mijinta transfer na wajan aiki” Yana kwanciya tare da rufe idanu ya ce “Zuwa ina?” Ta ce “Ban san Æ™asar da take ba, tana ta complain dai bata so sbd karatun yaranta baya yake dawowa” Ya mirgina ya ce “Tana da gaskiya” Hira su ka yi sama tana lura da yadda Æ™irjinsa ke É—agawa sosai da ramar da ya yi sai ba tayi masa magana ba…. Washegari da safe Innati ta dira gidan Abbu lokacin duk suna karyawa ta dubi Abbu ta ce “Audil azizu saÉ“on Ubangiji kake amma ba zaka gane ba” Da damuwa sosai ya ce “SaÉ“o Innati?”
“A’a, Allah na tuba ai duniyar gajere ce kaje ka yi bance komai ba, amma zaka sha mamaki da izinin Allah ka kuma shirya” Kalaman Innati suka daka Abbu cikin shakku na rashin sanin abinda ya aikata har haka da zai gani? Innati ta kalli Majeederh data raÆ™ube gefe É—aya kamar ba gidan Ubanta ba ta ce
“Babu komai, jarrabawa ce amma ni kaÉ—ai na san abinda idanuna ke gani akan ki Kululu ki yi ta addu’a takanas na zo wajanki tunda na ji ance jirgi zaki hau ki bar duniyar”
“Ƙasar dai ba duniyar ba” Aaliyah ta faÉ—a tana kallon Majeederh wanda ko kunun ta kasa sha. Kamar daga sama kuma su ka ji ta ce “Inna da Aljanu nake kama?” Innati ta zare idanu tana dafe Æ™irji ta ce “Yanzu to mene haka? Ina ruwanki da zancen Aljanu da sanyin safiyar nan don Allah? Allah ya yafe miki” A raunace kamar bata son yin magana ta ce “Na taÉ“a ji kince na tsorataki” Innati ta ce “To bance komai ba, ke kuma kwaÉ—ayayyiya wacce ta sha nonon maita ki ke idan wancan yaron ne zaki gani, abin da naga komai ina kan gani” Ta faÉ—a tana nuna Ruma da hannu ita kuma ta tura baki gaba, ta juya kan Mami ta ce “Ban yi mamaki ba, haihuwar Legas ce ke sai abinda Ubangiji ya Æ™addara za mu gani, duk Æ´an iska ne Legas É—in ai” Abbu dai bai ce komai ba sbd yasan halin mahaifiyarsa kamar wacce take da matsala idan tana abu sai dai kawai su dinga jinta. Majeederh ta yi shiru a É—akinta inda take kwance akan gado sai juyi take, bata san meke damun zuciyarta ba, wacce kullum ke Æ™aryata ta akan zata iya samun wanda zai aureta ya rusa zuwanta Egypt.
Ta juya a hankali tana Æ™anÆ™ame pillow jin tsigar jikinta na tashi wani abu yana mata yawo a jiki, wanda ta kasa sabawa da jinsa a kullum, yanzu ko ta É—auki azumi ma sai ya karye bata san meke kawo wannan abun ba, ta Æ™ara juyawa tana kiran sunan Allah ko zata daina jin abin amma ina, ruwan saman da akayi ya Æ™ara haddasa bayyanar abu a jikinta kamar cin wutar kara. MiÆ™ewa tayi ta nufi toilet tana zuwa ta dinga sheÆ™awa kanta ruwan sanyi a hankali ta durÆ™oshe akan Æ™afafuwanta duk yadda ta kai da haÆ™uri, juriya, da miÆ™a lamura ga Ubangiji sai da ta fashe da wani raunataccen kuka har da shassheÆ™a. Da Æ™yar bacci ya É—auke ta, ta farka da wani irin zazzaÉ“i ta juya tare da kallon Mami dake zaune bakin gado ta zabga uban tagumi ta ce “Kin farka?” Majeederh ta miÆ™e zaune tana mistake idanunta da suka kumbura “Mami”
“Kuka ki ka yi Majeederh?” Ta yi shiru domin bata Æ™arya Mami ta sauke numfashi ta ce “Hawwa’u, kina ji cewa a ranki bana kyautawa ko?” Majeederh couldn’t speak Mami ta ce “Majeederh bani da iko dake, haka kullum mahaifinki yake ce mini, shi ya sa na tattara komai na ja bakina nai shiru, to na ce me? Ina tofa tawa zai Æ™ullace ni, mun sha samun saÉ“ani da shi akan ki amma ya ce ba ruwana Æ´arsa ce ke ba wani ya haifa masa ke ba, hatta tafiyarki ba a son raina ba dana faÉ—a masa gasky cewa ya yi zan yi ta igiyar aurena, ni kam mene ya yi mini zafi? Ƙatuwa dani ina shirin kai Æ´a É—aki na samu jika da yawon zawarci?” Ta ja numfashi ta sauke ta ce “Allah yana gani na fara gajiya yana neman shafa mini baÆ™in fenti” Murmushi kawai Majeederh ta yi ta ce “Ba komai”
“Da gaske babu?” Ta jinjina kai ta ce “To Allah ya iya mana, ko can É—in kika je kiyi ta addu’a, ki riÆ™e mutumcinki har zuwa shekaru takwas É—in” Kanta a Æ™asa ta ce “Na gode” Mami ta miÆ™e tsaye tana cewa “Maza ki tashi ki shirya wani sa’ilin ke kike mai da kanki baya ayi mace ba kwalliyya? Ba kwalli ba powder, fuska kullum a rufe da wata Æ´ar malafar uban duguwar riga, kamar matar mamaci ko wacce aka koro daga Saudiya? Fuska a maiÆ™aci sai farin bala’i kamar an kwara miki man É—anyar gyaÉ—a haba Majeederh? To ai shikenan” ta saka kai ta fice abinta.
Majeederh ta sauke ajjiyar zuciya, wai ta yi kwalliyya? Ai bata da wata sauran dama ta riga ta sallama, ta yarda ta amince domin ta yi ilimi da bautar Ubangiji take raye, ta yarda ita ta rako mata duniya ko me za ta yi a rayuwa ba zai taÉ“a sauya abin da zuciyarta ya yarda da shi ba, ko fata za a sauya mata ba zata taÉ“a samun mijin aure ta yarda za ta yi karatu zata zama cikakkiyar Malamar addinin Musulunci zata fafata da duk wanda zai ja da wata É—iyya mace zata zama jaruma mai yarda da suke abin da Ubangiji ya zo mata da shi, yarda da Æ™addara ta zama feminist. Ta buÉ—e wayarta tare da kunna network ta shiga facebook, abin ya bata mamaki ganin ta samu mabiya da yawa sosai kamar jira ake ta buÉ—e. Ta shiga wajan timeline ta yi rubutu ta ce “ITA MACE, BA BAIWA BA CE, KO A GIDAN MIJI” tana gama rubutawa hannunta na rawa ta yi posting É—insa, Just now amma over 100 comment ta duba sunan wani Bilal-Habib ya ce
“Uhm ke ba aure ba, kuma zai kashewa wasu? Shi aure ne ba bauta ba? To uwarki ne?” Tana gama karanta idanunta ya sauka akan wani da ya rubuta.
“Malama Majeederh ki bari ki fara auren ko? Ai wannan maganar bata yara ba ce” Da sauri ta yi wurgi da wayar bayan ta kashe datar zuciyata na harbawa. Ta daÉ—e kafin ta samu nutsuwa. Mami da maÆ™ociyyarta na zaune suna hira Latifa Omar ta yi sallama ta shigo cikin wani lace mai kyau ta sha kwalliyya ta ce “Ina yini Mami?”
“Lafiya lou Latifa ya Maman taki?” Ta ce “Ta ce a gaisheki, Majeederh fa?” Da hannu ta nuna mata hanyar É—akin Majeederh ta shiga da sallama ta sameta zaune ta ce “Ya naganki zaune ba kyan gani? Kamon ba?” Ta yi shiru idanunta akan waya tana da Research more than 2hrs tana abu É—aya “Amma dai baki isa ki ce ba zaki ba ko? Bikin Widad Æ´ar uwarki ni ma zani balle ke?” Ta ce “Mene amfanin zuwa? Ana zuwa domin farin ciki ni raina ke É“aci Latifa Omar ki bari kawai karatu zan yi” Latifa ta zauna ta ce “Mene ya faru?” In brief ta faÉ—a mata komai, Latifa ta yi jigum ta ce “Kamar wata mujiya, Majeederh anya lafiya?” Majeederh ta yi murmushi ta ce “Lafiya lou, i believed Ubangiji ke komai i trust ni mutum ce ba Aljana ba….

 

No comments