Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 26


MIJIN MALAMA
Paid book
08119237616

ALLAH ya nuna mana ranar Monday Monday Lafiya…. Have a nice weekend29
Da sauri Aliyu ya juya tare da fita daga hall É—in, Alpha ya harÉ—e hannu a Æ™irji zuciyarsa na harbawa, Ajlaal Sultaan kowa numfashi ya sauke yana mai lafewa a bayan matarsa tunani fal a zuciyarsa, kyakkyawan matashin dake zaune kusa da Gwamna ya runtse idanunsa. Tsoro da fargaba ya cika zuciyar ko wanne haifaffen É—an Nijeriya dake zaune a hall É—in. Idanun dubban jama’ar wajan ya sauka akan Majeederh da jikinta ya fara rawa Æ™waÆ™walwarta ta tsaya cak kamar wacce akaiwa formatting. Malaman da suke lura da musabaÆ™ar suka dinga kallon Majeederh cike da mamaki da tu’ajujji tunda ta fara babu gyaran da akai mata, babu shakka mu’ujizarsa Alkur’ani ce ta sauka akanta, hakan ya sa ta mancewa komai. A hankali ta kifa kanta cikin rauni ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Ubangiji ka taimakeni kada na kunyata a idanun Æ´an Æ™asata” Da sauri wani malami ya yi mata alama data É—auki ruwa ta sha, kasa yin musu ta yi ta É—auki ruwan ta sha ta cikin liÆ™ab É—in fuskarta, a daidai lokacin kuma computer ta KaÉ—a wanda yake alamanta mata cewa ta fita daga cikin lokacinta. Jikinta jama’ar wajan duk ya yi sanyi domin kowa ya Æ™addara Majeederh matsayin wacce za ta yi nasara ganin har zuwa zagaye na biyar É—in ba a cita gyara ba, makinta ya fi na kowa saÉ“anin sauran da duk zagaye aci su gyara wajan biyu ko uku. Akai sanarwar tafiya break bayan an dawo za ayi Finally round wanda shi ne zagaye mafi wahala aka umarci gabaÉ—aya É—aliban da suje su sha ruwa su huta.
A sanyaye Majeederh ta tashi juwa na É—aukanta Ƙhulud na ganin haka ta miÆ™e cikin sauri ta Æ™arasa ta ce “Mu je ki huta” Majeederh ta tsorawa Ƙhulud Arzaan idanu kasa magana tayi sai jikin Ƙhulud data faÉ—a ta Æ™anÆ™ame tana sauke numfashi, da ace taga idanun wani ahhali nata da babu shakka ta ji sauÆ™in abinda take ji a zuciya, amma Æ™addara ce haka babu kowa nata a wajan da zata iya raÉ“ar shi ta ji sanyi. “Ba zan iya fa, I alrdy told them”
Ƙhulud ta ce “Zaki iya, kina da cikakken lokaci”
Ta faÉ—a tana rungume Majeederh. Daga gefe suka ji an ce “Daman dai Nijeriya ai ta saba samun failing, bata taÉ“a winning ba ko sau É—aya, babbar matsalar sun É—auki daÆ™iÆ™iya matsayin wacce zata wakilce su” Ya taÉ“e baki ya ce “Goodness, please Maa step down for Juwaira ki barwa Qatar domin baki da ilimin cin gasar Alkur’ani ta duniya, actually baki da shi, baki cancanta ba”
Ba Majeederh ba, hatta Ƙhulud ta girgiza da jin maganar kai tsaye ta fahimci mamallakin muryar ta juya suka haɗa idanu da Ajlaal ta ce
“Kalb, Majeederh ce fa? Ita ce DaÆ™iÆ™iya?? Duk ciki ita kaÉ—ai ce ba aiwa gyara ba, me ya sa?” Ajlaal idanunsa akan Majeederh da kanta ke Æ™asa ya fahimci yadda maganarsa ta yi tasiri a zuciyarsa musamman da yaga jikinta na rawa
“Ita fa, ni muryarta ce ma ta firgitar dani wallahi, karatu sakaka kamar zubar ruwan sama, Asstagafirullah gaskiya Nijeriya akwai saura gashi sun saka hope kuma za su yi failing” Ajlaal Sultaan ya sake faÉ—a yana lumshe idanu. Ƙhulud ta kafe shi da idanu ta kasa fahimta yanayinsa, bata taÉ“a jin ya yi magana mai tsayin haka ba, a rarrabe yake yinta. “Me ta yi maka da zaka jefe ta da wannan maganar Ajlaal Sultaan? Da zaka wulaÆ™anta ta?” Ya watsa hannu irin ko a jikinsa ya ce “I don’t know what comes over me, amma na ji kamar bata yi mini ba, ina bala’in son mace mai tsayawa akan nasara wacce bata yarda da faÉ—uwa ba, Sorry Nigeria” Ya yi gaba
“Meke damun Ajlaal?” Ƙhulud ta furta tana binsa da kallo ganin yadda yake tafiya kamar bai so. Majeederh kasa motsi ta yi maganganun Ajlaal suka zauna daram a zuciyarta tare da yi mata amsa kuwwa! Ta ji jarumta ya zo mata, komai na kanta ya dawo fresh, Ƙhulud za ta yi magana Majeederh ta girgiza kai tana É—an yi murmushi “Babu komai”
Majeederh ta faÉ—a a taushashe tana nufar wani corridor, duk abinda yake faruwa akan idanun Captain Alpha daya jingina yana kuma jin komai deep down na zuciyarsa godiya yakewa Ajlaal yasan Majeederh ta tsani ace bata da ilimi ko a jefata da kalmar _“Kasawa”_ Ya yi murmushi kawai yana É—auke kansa gefe guda. Majeederh ta buÉ—e bottle water mai sanyi ta shanye tas, a hankali ta shiga safa da marwa idanunta rufe, idan ta ja numfashi sai ta sauke. Tana tsaye Wani malami ya ce “Ki nutsu, tunda kin fahimci weakness na ki sai ki kiyaye kallon mutane, mu je lokaci ya yi” Ta jinjina kai har yanzu idanunta rufe yana gaba tana binsa a baya. Cikar da hall É—in ya yi har yafi na baya, kanta a Æ™asa ta nemi wajan zamanta a hankali girgiza cinyarta idanunta rufe. Rabin jama’ar wajan idanunsa yana kanta mamakin yadda sauran É—aliban aka rufesu malamai da jagororin Æ™asar su, ita kuma ba kowa. ÆŠaya bayan É—aya aka fara gabatar da final round babu Æ™asar data tsallake sai da suka sha gyara, gyara kuma na ban mamaki har aka zagayo kan Majeederh. Ta runtse idanu jin computer na gabanta ya yi Æ™ara kafin ta ji computer ta ce. “الله”
“Ma hukumu?” Ma’ana hukuncin kalmar Allahu.
Ta sauke ajjiyar zuciya a taushashe cikin sanyin murya mai daÉ—i ta ce
“Tafkimun laámun ismul jalala” Computer ta nuna blue alamar “Mumtaz” ta yi daidai aka ci-gaba da yi mata tambayoyi na Alkur’ani kafin daga bisani aja mata aya
“Allah taziru waá zirataán uƙƙurrah” Ba sunan sura ba number aya kawai ita ce zatai tunanin wacce surah ce. Ta yi shiru ta rufe Idanunta tare da dunÆ™ule hannu exlty yadda take yi idan tana haddar Alkur’ani.
Ajlaal dake hakimce saman kyakkyawar kujera ya zubawa Majeederh Idanu, haka Aliyu da shigowar shi kenan sai Alpha daya kasa Kallonta, matashin saurayi kuma Æ™anÆ™ame jikinsa ya yi waje guda…. Daga can Æ™asa Nijeriya gabaÉ—aya Khan family ne zaune a babban parlourn gidan Uncle Isma’il, sun tisa plasma a gaba tsoro ya cika zuciyar kowa musamman Abbu. Ba iya Khan family ba duk wani gida idan ka shiga kallon musaÉ“ar suke live, wanda basu da t.v a rediyo suke saurara. Abbu ya saka hannu ya share zufar data gangaro masa, ya kasa zama waje guda ya gama tsara plan É—in yadda zai yi da duk wata kyauta da kuÉ—in da Majeederh ta samu, amma da alama yarinyar baÆ™in ciki take masa yana da tabbacin ta iya mugunta ce kawai. Ba zai iya zama ya ji wannan abun ba ya nufi hanyar fita daga parlourn daidai nan ya ji sautin saukar muryarta a cikin kunnenshi wacce ta wadatu da zallar Æ™ira’a Tajwid mukarijil hurum, ta fitar da komai da karatun Alkur’ani yake buÆ™ata ta saka komai cikin muhallinta. Cak Abbu ya tsaya yana washe baki farin ciki fal zuciyarsa. Uncle Isma’il, Uncle Isma’il Bello, Maman Alpha, Anti, Mami, Aaliyyah, Ruma, Raihana, Widad, Innati… E.t.c suka sanya kabbara.
Wata É“oyayyiyar ajjiyar zuciya Ajlaal Sultaan ya sauke yana tasbihi a ransa, Aliyu ya yi Æ™asa da kansa hall É—in tsit sautin Æ™ira’arta ne kawai yake tashi har computer ta tsayar da ita alamun lokaci ya yi. Lokacin daya shiga cikin kundin dairy É—in Majeederh Abdul’aziz Khan, ta kasa tashi a hankali ta durÆ™oshe a wajan jikinta na É“ari rawa da Æ™yarma wani irin raunataccen kuka ya Æ™wace mata lokacin da alÆ™alai suka tabbatar da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Matsayin wacce ta zama Gwarzuwa a jerin É—alibai sama da 100 wanda yake nufin Nigeria ta Æ™wace kambon tarihi daga hannun Ƙasar Misira wanda sune su kai na É—aya a shekarar data gabata. Shugaban Æ™asar Nijeriya riÆ™e kai ya yi ashe kafin ya sauka da rabon a teniwarsa uwa Nigeria zata amsa wannan kambon? Sauran gwamnoni suka miÆ™e lokaci guda hadda gwamnan Kano suka shiga É—aga hannu da kabbara, da sarkin Misira dana Saudiyya Sarki Sultaan suka nufi inda Majeederh Abdul’aziz Khan take durÆ™oshe, Zaytoon ta saka hannu ta É—agota tare da jawota ta rungume tana cewa
“Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar ma sha Allah” Majeederh daman waje take nema domin ta kasa believing na nasarar data samu, ta Æ™anÆ™ame Zaytoon tana sakin wani mahaukacin kuka, She just wished that her parents were here to see her suga nasarar data samu, musamman Abbu burinsa ya fara cika. Ƴan jaridu gidan t.v da rediyo sukai kan Majeederh É—aukarta suke ta ko’ina, lokacin da aka É—auki wata farar hula ta silver aka saka mata tare da É—aukan wani abu mai kama da Award na zallar tagulla aka bata wanda ya biyo ta hannun Sarki Sultaan, yin duniya ta cire liÆ™ab É—in taÆ™i haka aka dinga yi mata photo wanda kai tsaye ake watsa su a duniya, wasu mahaukatan kuÉ—i aka bata wanda ita kanta ba zata ce ga adadin su domin hankalinta baya kai tunaninta yana ga mahaifinta. Aka rataya mata sarÆ™a gold daga nan aka dinga mata kyauta wannan gwamna ya ce ya bata kaza wannan ya ce ya bata kaza, Shugaban Æ™asar Nijeriya har yanzu kasa tantance me zai bata matsayin kyauta, duk abinda ya yi tunani sai yaga ya yi kaÉ—an. Kyautar kujerar Umara data hajji aka bata sarkin Makka ya Æ™ara bata kyautar kujerar hajji. Kana aka dinga photo lokacin da aka sanya mata albarka bata san mene ya faru ba, Majeederh ta samu kanta da wani irin jin girma wani abu mai girma ya hau kanta daga nan taro ya watse sai walimar da za ayi da daddare. Ƙhulud ta rungume Majeederh tana kuka murmushi kawai Majeederh ta yi tare da bubbuga bayanta a hankali ta ce “Ina mijinki?”
“Yana wajan takawa” cewar Ƙhulud, Majeederh ta ce “Rakani” Da sauri Ƙhulud ta kama hannun Majeederh suka isa wajan Ajlaal na tsaya rungume da Zaytoon da yake tsokanarta Majeederh ta tsaya kanta a Æ™asa Zaytoon ta ce
“Ba dai ita ce wacce kike bani labari ba?”
“…. Ita ce Grandma”
“Ma sha Allah, na yi farin ciki ina alfahari dake da Æ™asarku” Murmushi Majeederh ta yi ta ce “Na gode Mama” Zaytoon ta ce “Laa, wacce irin Mama bayan zan iya jika dake?” Ta yi murmushi kawai Ajlaal dai yana lafe da bayan Zaytoon ya kasa Kallon Majeederh ya ji ta ce “Thank you”
“For?” Ajlaal ya tambaya yana gyara tsaiwa ta ce “Kai ne ka Æ™arfafa mini qiwwa na kasa mance kalmar DaÆ™iÆ™iya” Ajlaal ya É—an shafa gemunsa ya ce “Congratulations”
Yana faÉ—in hakan ya bar wajan. Bayan sun fito tana Æ™oÆ™arin shiga mota domin komawa gidansu ta ji ance “Hawwa’u”
Cak ta tsaya ta kasa tuna inda ta ji muryar ta juya, yana tsaye hannunsa zube cikin Aljihu sanye da wani tissue É—in farin yadi Æ™al da shi ta yi murmushi ta ce “Aliyu”
Ya yi jim domin bai É—auka ta san sunan shi ba ya ce “Congratulations Hawwa’u ko wani zai nuna mini farin ciki ina tunanin bayan Abbu ne” Kafin Majeederh ta yi magana aka ce “A sbd kai ne wa?” Majeederh ta ware idanu ganin Captain Alpha bakinta na rawa ta ce “Yaya?” Ya ware mata idanu ya ce “Me kike? Yana da kyau ki huta” Ta ce “Ayya yau ai bana iya bacci, Aliyu baka da lafiya?” Aliyu dai bai ce komai ba sai kafeta da idanu da yake ya ce “Congratulations once again, take this matsayin nawa gift É—in” Ya dubi hannunsa ta box ne É—an Æ™arami ta ce “No thank you, hakan ma ma gode sosai” Calmly ya taka har inda take ya ce “Please, ki amsa kamar yadda kika amshi ta kowa” Tana Æ™oÆ™arin amsa Alpha ya karÉ“a ya ce “Mun gode, let’s go” Majeederh bata ji daÉ—i ba amma haka ta daure ta ce “Jazakallah-bil khair, ina Latifa Omar? Kun yi aure hala?” Ta faÉ—a cikin muryarta wacce ta juye bai amsata ba ya juya kawai tare da barin wajan. Majeederh ta shiga mota Alpha ya shiga baya kusa da ita, driver ya ja suna tafe ya buÉ—e box É—in wani É—an Æ™aramin ring ne mai kyau sosai, sai wani farin tissue da akai rubuta cikin good handwritten a hankali ya fara karantawa da sauri kuma ya tura tissue É—in cikin aljihu ya maida ring É—in yana tafe baki. Har Magriba Majeederh na tare da yayanta Alpha sosai tayi farin ciki, har akai walima. Ƙarfe 12 na dare ta buÉ—e wayarta message kamar hauka musamman daga wajan Aaliyah da Anti cikin sauri ta dinga dubawa ko za taga na Abbu domin tasan he’s the first person da zai cnrgt nata amma har ta gama dubawa babu nasa jikinta ya yi sanyi a hankali ta danna number Abbu ringing É—in farko ya É—aga ta ce “Assalamu alaiyka Ya Abbu” Abbu ya ce “Majeederh na ji labarin irin kuÉ—aÉ—en da kika samu, da na yi lissafi sun haura miliyan 20 banda kujerar makkan ” Sosai abin ya bata mamaki ta É—auka zai farin ciki ya sanya mata albarka kan nasarar data samu amma sai ta ji babu batun hakan a bakinsa maganar kuÉ—i kawai yake? Ta yi murmushi mai ciwo ta ce “Ban san nawa bane Abbu, amma dai da yawa” Abbu ya ce “To da kyau ai tuni na lissafa, a hakanma banda kuÉ—in albashinki” Ta jinjina kai idanunta cike da hawaye wanda ya fara sakkowa saman fuskarta ta ce “Abbu ka shirya tafiya aikin hajji, ni ma zani Uncle Isma’il da Mami su je Umara” Abbu ya yi zumbur ya miÆ™e daga zaune ta cikin wayar ya ce “Ashe Majeederh baki da hankali baki da wayo?” Muryarta na rawa sosai ta ce “Me na yi Abbu? Ka yi haÆ™uri don Allah” Ya ce “Daga ni harke har su Uncle Isma’il É—in da ita Asaben babu mai zuwa ko nan da airport balle aikin hajji, siyar da su za ayi a haÉ—e kan kuÉ—in tas” Majeederh ta ware Idanu while hawaye na zuba a fuskarta ta rufe bakinta ta kasa cewa komai “Hawwa’u?” Muryarta na rawa ta ce “Na’am Abbu?” Ya ce “Kuka zaki akan na ce haka? Shikenan riÆ™e kuÉ—aÉ—enki” Da sauri ta girgiza kai tana zubewa saman gwiwoyinta jikinta na rawa ta ce “Ka yafe mini Abbu wlh ba kuka nake ba, idan kukanne ma na farin ciki nake, na bar maka kuÉ—in halak makal ko biyar ba zan É—auka ba, amma don girman Allah Abbu ko kai É—aya ne ka je aikin hajjin idan ya so sai a siyar da sauran”
Abbu ya girgiza kai ya ce
“A’a ai tas za a siyar da su, nan gaba sai ki sama mini kuÉ—in da zan je aikin hajjin hakan ya fi ko?” Ta jinjina kanta ita gabaÉ—aya ba ruwanta da kuÉ—in ba shi take buÆ™ata ba burinta kawai ta ji ya ce “Majeederh Allah ya yi miki Albarka” Wannan kalmar ita kawai take buÆ™atar ji, babu uwar da zata sanya mata albarka uban kuma bai damu ba. Abbu ya ce “To sai anjima aci gaba da Æ™oÆ™arin adana kuÉ—i banda É“arnatarwa” Kafin ta yi magana ya kashe wayar, sakin wayar ta yi tare da durÆ™oshewa ta shiga rera kuka kamar ranta zai fita tana buÆ™atar sanya albarka ko sau É—aya ne idanunta ya kumbura sosai da Æ™yar ta iya kiran Uncle Isma’il ya yi mata addu’a haka Uncle Bello ta kira Anti da Mama kana ta kira Mami sai Aaliyyah ji tayi duniyar ta yi mata zafi komai ya jirkice mata bacci ya Æ™auracewa idanunta…… Majeederh ta tattara komai ta ajjiye waje guda karatu take sosai, shaÆ™uwa sukai sosai da Ƙhulud Arzaan Ajlaal kuma basu taÉ“a magana ba tun ranar, duk wata sai ta turawa Abbu kuÉ—i bata san me yake da su ba, Majeederh kullum cikin azumi take ta rame sai É—an jiki fatarta ya goge sosai, zamanta da Ƙhulud ya Æ™ara sawa ta zama wayayyiya sosai rashin magana ya ninka nata, tun a lokacin da Abbu ya ja mata kunne ta cire batun aure a ranta, tun tana sha’awar yi har ta fice mata a rai, ta sanyawa ranta ba zata taÉ“a yin aure ba, duba da cewa tun a lokacin babu wanda ya Æ™ara cewa yana sonta, a shekarar Æ™arshe ta zanna jarrabawa mai kyau ta samu first class tayi farin ciki sosai ta zama cikakkiyar Malamar addinin Muslunci ga tarin magoya baya da take da shi a facebook ta fara faÉ—akarwa akan maza da mata kamar yadda taga Fauziyya d sulaiman tana yi….

No comments