Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 32


BOOK 1 PAGE 31*
MIJIN MALAMA
LITTAFIN KUÆŠI NE WANDA YAKE SO YA YI MAGANA 08119237616

Ina godiya bisa ta’aziyyar da akai mini ta babban rashin da na yi na wan mahaifina Alhaji Musa Zakari sheka ( Dagacin sheka) Na gode sosai Allah yabar zumunci marubuta da yawa wasu ma ban san su ba, sun nuna mini kara Æ™warai makaranta ina alfahari daku kune silar kai ni inda nake kune kuke goya mini baya ta hanyar siyan littafaina, ina fatan ba zaku gajiya ba32
Janta ya yi har tsakiyar main parlour yana zuwa ya saki hannunta yana binta da wani irin kallo kafin ya ce “Baki da hankali?” Ta buÉ—e idanu wanda sukai jajir ta ce “Me na yi?” Da idanu ya dubi shigar dake jikinta da kuma kallon fuskarta dake buÉ—e, itama tayi saurin kallon kanta tana É—an marairaice fuska zuciyarta duk babu daÉ—i ta kasa cewa komai sbd yadda Æ™irjinta ke É—agawa ga zafin da idanunta suke mata duk ta sushe su. Ya gyara tsaiwa yana harÉ—e hannu a Æ™irji shi ma nasa idanun sun yi ja sbd abubuwan da suke masa yawo a zuciya can Æ™asa ya ce “Kuma da gaske fita zaki haka? Tsirara?”
“…. Tsirara!?” Ta faÉ—a da sauri cike da tsoro, Alpha ya haÉ—e fuska ya ce “Mene marabar dambe da faÉ—a?” Majeederh ta yi shiru domin ita sam tunaninta baya nan wajan, zuciyarta ta KaÉ—aita da maganganun Abbu, lura da yanayinta ya sa Alpha bai Æ™ara magana ba ya bi ta gefenta ya shige ya zauna saman kujera yana harÉ—e Æ™afafuwan. Majeederh ta shige part É—inta not too long ta dawo sanye da rolling na vail a kanta, ta nemi waje saman kujera ta zauna, shiru ya biyo baya can ta ce “Ina yini?”
“Lafiya” Ya bata amsa a taÆ™aice. Majeederh ta yi Æ™asa da kanta cikin sanyin murya ta ce “Ance an maka Æ™arin girma congratulations” Alpha ya ce “Uhm” Yana É—an kaÉ—a Æ™afa kafin babu wasa idanunsa ya kira sunanta ya ce “Majeederh!” Ta yi shiru.
“Zabiya?” Ta kwaÉ“e fuska tunda bata son sunan ya É—an shafa kai daman He just wants to tease her. Ta miÆ™e zata bar parlourn ya ce
“No, please” Ta zauna kamar zatai kuka ta ce “Tun ina Æ™arama kake ce mini Zabiya Yaya, ni ban so idan kai ma da Aljanar nake maka kama to”
“Stop it Majeederh!” Ya furta a tsawa ce, domin ji ya yi kamar ta caka masa nashi a Æ™ahon zuciya, ya girgiza kai ya ce “Sorry”
Ta yi shiru speaking calmly ya ce “Sannu da dawowa Æ™asa Nigeria, yanzu sai me?” Kanta a Æ™asa tana wasa da yatsun hannunta ta ce “Sai abin da Abbu ya ce” Alpha ya watsa hannu ya ce “Kina sane da problem É—inki, komai zaki ki fara tuna aure first” Kunya ta kama Majeederh sai yanzu take dana sanin sanar masa da matsalarta, kuma yanzu da baya ai ba É—aya bane tuni Ubangiji ya ye mata “Kina ji?” Ta ce “Aiki zan nema” Da wani irin sauri ya ce “Aiki?” Ta É—aga kai ya ce “Shi ma Abbu ne?” Tayi shiru cike da tausayawa ya ce “Am sorry, zan masa magana ya fara bari kiyi aure” Wani irin abu ne mai É—aci ya tsayawa Majeederh a maÆ™oshi ta runtse Idanunta tuni ta ji rauninta na son bayyana muryarta na rawa amma ta dake domin tayi al’Æ™awarin ko hawan jini zai sameta, ko zuciyarta ce zata buga ta mutu nan take ta daina yin kuka ta sauke ajjiyar zuciya ta ce “Idan ya amince nayi auren wa zai aureni?” Alpha ya zura mata manyan idanunsa ya ce “Kamarya? kina nufin tsayin shekarun da ki kai a Egypt baki saurayi ba?” A hankali Majeederh ta girgiza kai ta ce “Even friend ban ba, shekaruna ashirin da takwas 28 ban taÉ“a yin saurayi ba idan ka É—auke Imran shi ma ya guje ni ba tare da sanin dalili ba, baÆ™in jini ne dani Yaya na zama mujiya a idanun mazan duniya, hatta soyayyar Æ™uruciya ban san ya take ba, ban san daÉ—in soyayya da wahalar cikinta ba, ko saurayin da zai zo ya yaudareni ban taÉ“a yi ba, balle wanda zai ji muradin aurena a zuciyarsa….,”
Ta yi shiru sbd numfashinta dake fisga kaÉ—an kaÉ—an kafin ta ce “Duk son da maza suke wa farar mace, duguwa mai kyan fuska nawa ya tashi a banza, mummunar mace wada ta fini farin jini, to idan ban yi aiki ba me zan Yaya? Shi ma Abbu fahimtar hakan ce ta sanya ya zaÉ“a mini wannan rayuwar kuma ina farin ciki da ita” Duk rashin imanin Alpha kasancewar shi Soja, wanda yaga masifu da yawa ya kashe rayuka da yawa amma a yanzu a gaban Majeederh sai dai zuciyarsa ta karye ya miÆ™e tsaye ya shiga kaiwa da komowa yana bugawa hannayensa waje guda kafin cikin sauri ya tsaya a gaban Majeederh ya ce “Majee ki minin wani al’Æ™awari, do me a favor please” Ta kasa kallonsa ya kai hannu zai riÆ™e nata tayi saurin janye nata tana É—an yi murmushi ta ce “Na maka”
Ya ja baya ganin bata son ya taÉ“a jikinta, numfashinsa na sauka ya ce “Kiyi accepting duk wani abu dana yanke miki muddin ba cutarwa bane, ki yarda ba zan cuceki ba Majee” Ta ce “Me zakai?” Ya bata amsa ya ce “Zaki ji, ki amince first” Ta jinjina kanta bai Æ™ara cewa komai ba, ya fice daga part É—in ya shige part É—in Abbu ita kuma ta nufi Kitchen ta fara haÉ—a dinner harta gama ta shige part É—inta ba taga fitowar Alpha ba….

Washegari ya kama weekend ne, Aaliyah na zaune a parlour watching Ds t.v lokacin 10:10 na safiyar Saturday jin ana sallama ya sanya Aaliyah É—ago kanta tana amsawa da faÉ—in “Wasalamu Alaiki, Anti Latifa” Latifa ta zauna tana cewa “Ashe fa yau weekend da tuni kina school” Aaliyah ta yi murmushi ta ce “Ina kwana?” Ta amsa da “Lafiya lou” Sukai shiru can Latifa ta ce “A level nawa kike ne yanzu?”
“… 200″ Aaliyah Said, tana É—an buÉ—e Idanunta akan series É—in _My heart knows_ da take kallo a zee wrld. “All The best little sister, ina Malama?” Aaliyah ta nuna mata hanyar kitchen da hannu ta ce “She’s in the kitchen” Lura da hankalin Aaliyah nakan series ya sanya Latifa miÆ™ewa ta nufi hanyar kitchen É—in tana zuwa ta samu Majeederh tsaye gaban sink tana wanke hannunta tayi dariya ta ce “Sannu da aiki Madam koko” Majeederh ta É—an yi murmushi ta ce
“Uhm” Latifa ta ce “Gasky am lucky na samu abinda nake so”
“… Kike so? Ko ya ke so?”
Latifa ta ce “Shi wa?”
Majeederh ta watsa mata harara tana É—auke plate É—in data wanke ta ce “Nasan ciki ne dake”
Latifa ta ce “A’a ba ciki ba, baya ne dani” Ta faÉ—a tana tofar da yawo a bakin kitchen É—in har sai dai Majeederh ta runtse idanu a É“oye.
“Ni dai zuba mini breakfast yunwa na ke ji” Da mamaki Majeederh ta ce “Idan na baki mijinki fa?” Latifa ta jima tana kallon Majeederh can ta ce “Na yi fa, idan ni nayi bana iya ci sai na kwaÉ—ayi” Bata ce mata komai ba, ta haÉ—a mata breakfast fal cikin warmer hadda kunun gyaÉ—a mai kyau, tana bata tayi godiya ta fita a hanya taci karo da Raihan tana shigowa cikin compound É—in a haÉ—aÉ—É—iyar motar ta, bata kulata ba ta fita tare da shigewa nata gate gidan… Lokacin da Raihana ta shiga gidan duk suna parlour suna breakfast ta cire mayafinta tare da ajjiye hand bag É—inta tana zama saman dining ta ce “Ki ce nazo a daidai” Aaliyah bata ce komai ba haka ma Majeederh, sai da Raihana ta kai abinci bakinta ta ce “Majeederh ba gaisuwa?” Da sauri Aaliyah ta ce “Wakike so ta gaisheki Anti Raihana?” Kai tsaye ta ce “Majeederh?” Baki buÉ—e Aaliyah ta juya ta kalli Majeederh kana ta kalli Raihana ta ce “Anti Jeederh ce zata gaisheki? Bama ke ki gaidata ba?” Raihana ta ce “Ai ni ya dace ta gaisar” Aaliyah da ranta ya fara É“aci ta ce “A sbd kin haifeta? Shekaru nawa Anti Jeederh ta baki?” Raihana ta saki dariya hadda buga dining É—in dake gabanta ta ce “Ji banza wake ta Æ™ama da shekaru? Ai tunda nayi aure to yanzu ni ce gaba da ita, bayan nayi aure haihuwa zan yi Kinga durÆ™osawa wada ba gajiyawa bane ko? Ai aure shi ne martabar ko wacce mace, kiyi Æ™oÆ™ari ki aure sai mu iya haÉ—a kafaÉ—a dake”
Aaliyah ta miÆ™e tsaye itama tana sakin dariya ta ce “hehehe, matar na tuba bata rasa miji aure, ai dake da Anti Jeederh da ke kwaryar sama ce take dokan ta Æ™asa, mene marabarki da ita? Sunan kinyi aure amma kullum kina hanyar barbaÉ—a na zuwa gida ana Æ™arar da albarkar aure akan titi, Anti Jeederh da izinin Ubangiji ba zatai auren barbaÉ—a irin naki ba, zata auri miji wanda yake kishinta yake sonta wanda zai jure duk wani Æ™alubale nata wanda zai sota fiye da yadda take son shi zatai aure inda aka san darajarta, ba zata taÉ“a auren wanda zai sallamawa duniya matarsa ba” Aaliyah ta riÆ™e Æ™ugu ta ce “Mema kika ce haihuwa? Ai sai dai kici ki haifi kashi ba dai É—an mutum ba, domin juma’ar da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta….,”
Hannu Raihana takai zata kifawa Aaliyah mari tayi saurin ja baya, Raihana na huci ta ce “Zan yi maganinki dan uwarki idan ni sa’arki ce” Aaliyah ta zare idanu ta ce “Ni na isa na haÉ—a kaina da uwar mata mai aure? Wlh wani ya kalleki sai ya É—auka kin yi shekaru 20 da aure duk kin rakwaÉ“e kamar tsohuwar mota” Wani baÆ™in ciki ya turnike Raihana ta ce “Ni kike faÉ—awa haka?” Sai a lokacin Majeederh ta tashi ta zabgawa Aaliyah mari ta ce “Ya zama Æ™arshe” Aaliyah saka kuka sosai ta ce “Na gaji Anti Jeederh na gaji da abinda suke miki, su basu da aiki sai gorin aure? Kamar ke zaki aurar da kanki sun manta komai lokaci ne? Ita Anti Raihana da take yin É“ari ta taÉ“a zama ta tambayi kanta me yasa cikin baya zama? Da aure da haihuwa da arziÆ™i duka na Allah ne, wani jinkirin alheri ne kuma da aure irin nasu wallahi gwara mutum bai aure ba, mata nawa suke aure amma baya zuwa ko’ina auren ke mutuwa” Majeederh na Æ™oÆ™arin yin magana suka ji gyaran murya a tare suka juya Alpha ne tsaye hannunsa harÉ—e a Æ™irji fuskar nan kamar an aika masa da saÆ™on mutuwa, yana sanye cikin wani jeans da Racing jersey ya saka p.cap a kansa sai Æ™amshi yake. GabaÉ—aya sukai shiru jikin Aaliyah da Raihana ya É—auki rawa musamman Aaliyah domin tasan Alpha baya son raini da rashin kunya ga babba bakinta na rawa ta ce “Ya…yaya A.b don Allah….,”
Hannu ya É—aga mata, idanunsa akan Raihana ya ce “Ke dan kan uwarki Majeederh sa’arki ce?” Raihana ta yi shiru ya Æ™ara sakar mata tsawa ya ce “Shegiya munafuk za kici ubanki daga ke har mijin da kike tunanin kin aura wanda yasa kikewa wata gori akan haka, duk sanda na Æ™ara ganin Æ™afarki a gidan nan without any reason wlh sai na kusa karya ki” Ya nuna mata Æ™ofa ya ce “Bar nan wajan kafin na karyaki na karya banza, shi ma mijin naki bashi da tunani bai san ciwonki bane” Ganin ta juya zata shige part É—in Mami yasa ya nufeta ta kwasa a guje tana kurma ihu ta faÉ—a part É—in Mami, tsayawa ya yi yana shirin komawa kan Aaliyah yaga wayam babu ita sai Majeederh dake tsaye. Bai ce mata komai ba ya juya zuwa part É—in Abbu. Mami ta kalli Raihana dake haki duk tayi wujiga-wujiga ta ce “To shi haka ake bai ji ta bakin kowa ba sai ya hau faÉ—a?” Raihana ta ce “Shi daman baya son mu ai, ya fi son Anti Jeederh da Aaliyah he’s so selfish” Mami ta ce “To ai shi ba Allah bane, kuma ke matar aure ce yana dokanki Shari’a ba zata barsa ba, yabar ganin shi soja ne wlh garÆ™ame shi za ai a bayan canter” Raihana tayi shiru Mami ta kalleta ta ce “Kema bana son rashin ta ido, ina ke ina zabgawa Majeederh wannan maganganun? Kar na kuma ji balle ki ja mini zagi” Raihana ta tura baki Mami ta Æ™ara cewa “Yau kuma me ya kawo ki?” Ta ce “Jiya da daddare ya dawo, ya kuma da asubar fari a haÉ—a kayansa wai wani aiki ke ya taso masa” Mami ta zabga tagumi ta ce “Shi kuma Æ™addararsa kenan tafiye-tafiye? Wai aikin me yake ne?” Raihana ta ce “Ni ban sani ba” Ta ce “To Allah ya kyauta”…… Kwana biyar kullum sai Alpha ya zo wajan Abbu ba tare da sanin meke kawosa ba, da yamma liÆ™is Anti ta shigo gidan Æ´arta Sona bayan sun gaisa da Mami ta ce “Ina Majeederh?” Mami ta ce “Ta leÆ™a gidan Latifa daga nan ance sun fita” Kafin Anti tayi magana Majeederh ta shigo bakinta É—auke da sallama Anti ta amsa “Daga ina kike?” Majeederh ta ce “Mami gidan Latifa” Cikin faÉ—a Mami ta ce “Ji munafukar Æ™arya ba ance kun fita ba?” Majeederh ta ce “Oh na rakata asibiti na sameta tana ta amai ne ashe É“ari za tai” Mami ta ce “Au ciki ne da ita?” A hankali ta ce “Eh” Mami ta Æ™ara cewa “Yanzu ya É“are cikin?” Nan ma Majeederh ta ce “Eh” Mami ta jinjina kai ta ce “Ikon Allah, wannan É“arinta na uku kenan, mahaifarta ce bata da Æ™auri ina zato” Babu wanda ya yi magana tsakanin Anti da Majeederh, Mami ta gyara zama ta ce “To me Likitoci suka ce kuma” sai a lokacin Anti ta ce “Haba Asabe wannan tambayoyi kashi da kashi ita yanzu Majeederh me zata ce?” Mami ta É—an yi murmushi, Anti ta ce “Daman abin alheri ya same mu” Mami ta ce “Ma sha Allah” Anti ta kalli Majeederh kana ta ce “Alpha ne yake son Majeederh yana son ya aureta” Da wani irin Shock mai kama da mamaki Mami ta ce “Shi Alpha É—in? Kuma Abbu ya amince?” Anti ta ce “Shi ne ma ya saka ranar auren ai” Da wani irin Scorned expression Mami ta ce “Ikon Allah bani da labari Allah ya sanya albarka” Majeederh ta yi shiru She couldn’t say a word sai bin Anti da idanu take. “Majeederh kin amincewa da yayanki kuma É—an-uwanki Alpha? Kin aminci ya zama mijinki?” Buri Majeederh ta auri wanda ya san kima darajar ta, wannan yasa take yawan kallon Alpha matsayin crush É—inta take jin inama ya aureta? Ganin bashi da interested akanta yasa bata taÉ“a sanyawa ranta ba, Majeederh ta tsinci kanta cikin tashin hankali sbd babban burinta ta zama matar A.b Alpha Bello, It’s her dream tun sanda ta buÉ—e idanu ta gansa yana kula da ita, She can’t afford to lose him, her life will be incomplete without him, She’s felling scared and restless me yasa take jin tsoro?… “Majeederh”
Anti ta kira sunanta. Ta É—an kalleta kana ta sunkuyar da kanta Æ™asa ta ce “Kina son auren Alpha?” Majeederh ta ce “Anti ai zaÉ“i ba nawa bane kamar taimakona ya yi” Anti tayi shiru sai kuma ta ce “Shikenan jeki Allah yasa haka ne alheri a rayuwarki” MiÆ™ewa tayi ta shige bedroom amma deep down na zuwarta mamaki take anya shi yace zai aureta? Mai yasa bai fara neman Soyayyarta ba? “Ke da za a taimakawa ina ruwanki da neman soyayya?” zuciyarta ta bata amsa.

Da daddare bayan Majeederh ta gama dinner tayi sallar Magriba tana zaune tana azkar wayarta ya yi ringing ganin sunan Alpha yasa gabanta faÉ—uwa har kiran ya katse bata É—auka ba, wani kiran ya sake shigowa ta yi bismillah ta É—auka a hankali ta ji ya sauke ajjiyar zuciya ya ce “Me kike?” A hankali ta ce “Azkar” Ya yi jim ya ce “Shi ne baki picking kiran farko?” Ta É—an marairaice ta ce “Kayi haÆ™uri” Ya share maganar ya ce “Majeederh” Ya kira sunanta ta kasa amsawa ya ce “Wannan shi ne hukuncin dana yanke mana, ina fatan banwa rayuwarki Shisshigi ba, idan kuma baki so na baki son aure let me know first” Ta yi shiru Ya ce “Kina son Aurena? Majee?” Da sauri ta kashe wayar tana rufe Idanunta kamar yana gabanta, daga can É“angaren murmushi Alpha ya yi kana ya kashe wayar ya shiga Parlourn Mahaifiyarsa zaune ya sameta ya ce “Sannu da dare Mama” ta É—aga masa hannu ta ce “Ya isa” Tana faÉ—in hakan ta miÆ™e tare da ficewa daga parlourn…… Ciki sati gudu wata muguwar shaÆ™uwa ta wanzu tsakanin General Alpha Bello da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Tana jinsa har cikin zuciyarta gashi da masifaffen kishi, Anti ta kira mai gyara aka shiga yiwa Amarya Majeederh wani mahaukacin gyara, sosai Alpha yake kashe kuÉ—i har kawo lokacin ko hannu Majeederh ta hana ya riÆ™e mata….. Ana saura kwana É—aya É—aurin aure tun safe aka haÉ—a Family meeting gidan Uncle Isma’il an cika sosai yara da manya maza da mata, Alpha ne kawai babu a wajan can Uncle Bello ya É—akko wayarsa ya kira shi yana É—agawa ya ce “Wanne irin iskanci ne haka? Mu zamu zauna zaman jiranka?” Muryarsa can Æ™asa Ya ce “Am sorry” Uncle Bello ya kashe kiran babu jimawa ya shigo kansa a Æ™asa ya zauna can kujera, aka buÉ—e taro da addu’a Uncle Isma’il ya ce “Ma sha Allah, a gobe In sha Allah muna da É—aurin auren da zai kafa tarihi a Khan family” Cikin sauri Alpha ya ce “Auren wa za’a É—aura Uncle?” GabaÉ—aya aka kallesa cike da mamaki Uncle Isma’il ya kasa bashi amsa, Alpha ya ce “Me ya sa kowa ke kallona? Why are you staring at the?” Anti ta ce “Gidanku General Aurenka mana” Ya ware idanu ya ce “Aurena kuma Anti? Dawa?” Ta ce “Da Majeederh” Ya Æ™ara waro idanu ya ce “Wacce Majeederh? Ni zan yi aure kuma Majeederh zan aura?” Innati ta ce “Ji wawa dilla kuyi abinda ya kawo ku” Uncle Isma’il ya kwaso katin É—aurin auren ya ce “Gashi nan It’s too late ka bawa friends É—inka” Alpha ya kwashi katin da Shock ya dinga bin sunansa da idanu da kuma na Majeederh ya É—ago kansa ya ce “Ke ni na ce zan aureki? Wai meke faruwa ne?” Uncle Bello ya miÆ™e ya zabgawa Alpha ya Æ™ara zabga masa ya ce “Bana son hauka, lokacin da kazo da maganar aurenta kwana bakwai daga shige uban waye ya yi maganar ba kai ba?” Alpha ya girgiza kai ya ce “Wallahi Abba ni ban taÉ“a cewa ina sonta ba, ni me zai saka na aureta Æ™anwata ce fa?” Innati ta ce “To da sauÆ™i tunda ba nono É—aya kuka sha ba” Alpha ya ce “Uncle,Abba this is misunderstanding wlh ni bance zan auri Majeederh ba infact ina da wacce nake so kuma gobe zan kawota ku ganta don Allah kada ku aura mini Majeederh…….

No comments