Breaking News

Mijin Malama Book 1 Page 33


*BOOK 1 PAGE 32*
*MIJIN MALAMA*
_littafina na kuÉ—i idan kina so ki biya ki karanta…. 08119237616 ko yayane kada ki karanta free without my permission please siyan littafinmu shi ne nuna soyayya a garemuï«‚_

*Ƙaddarar mace abace mai wahala musamman Æ™addarar za dinga maka gori da ita, ana ganin kamar ganganci ne ko kuma kai ka É—orawa kanka ba yin Allah bane凉 Yadda da Æ™addara shi ne cikar imanin mutum, Ubangiji bai baka abu ba hakan na nufin abin nan ba alheri bane a gareka da rayuwarka, Æ™addara na tafiya da lokaci shi kuma lokaci ne abu ne da baya jira, hakan na nufi ita kanta Æ™addarar ba tabbatacciyya bace, akwai lokacin da zai zo ta zama tarihi… Wani jinkirin alheri, rasa abu baya nufin rasa rayuwarmu hakan wata dama ce da Ubangiji ya baka wajan gane laifinka da kuskurenka, wasu suna sakaci da addu’a, wasu kuma rashin biyayya ga iyaye, wasu kuma ruÉ—in Æ™awaye, wasu kuma Æ™addarar ce dai…. Idan aka haÉ—a zamu fahimci gabaÉ—aya lokacin kowa ne bai ba, da zarar lokaci ya yi komai zai zama shuÉ—aÉ—É—en, cimma manufa bashi iyawa ma, cimma nasara da tsayawa akan ra’ayinki shi ne cikakken mutum.  NO MAN IS THE MAN WITHOUT A WOMAN﫰落*33
Murya na rawa ya ce “Don Allah ku tausaya mini wallahi ban taÉ“a son ta ba, balle na ce zan aureta, why should I? Allah kuka aura mini ita mutuwa zan yi mana son ta, bana Æ™aunarta, kada ayi mini auren dole” Ya faÉ—a His voice was shaking. Yanayin yadda kowa ke binsa da kallon mamaki ya sanya shi Æ™arasawa gaban Uncle Isma’il ya ce “Kun sai dai ni ba mahaukaci bane? Balle ayi mini uzurin taÉ“in hankali, I don’t know what is going to happen to me, I don’t know when this happened…..,” Tass! Mama ta É—auke Alpha da mari, without letten him to recover ta Æ™ara sauke masa wani wanda ya sanya shi yin baya sai kuma ya dawo ya tsaya da Æ™afafuwan shi dafe da kuncinsa tayi pointing É—insa da yatsa ta ce. “Idan Æ™wayar ku ta sojoji ta faÉ—a maka ba daidai ba, ko allurar da ake muku to gabaÉ—aya haukanka ya zama na banza a nan, kayi kaÉ—an kayi tsararo bamu haifi É—an da zai juyamu ko ya raina mana hankali ba, We are your parents, you are the child we gave birth to, we have the power to pass the sentence on you….” Mama ta ja Æ™wafa ta ce “Let make it clearly for you, idan harni na É—auki cikinka wata tara, na haifeka na baka nono na, naci kashi da fitsarinka wallahi wallahi ko zaka mutu ka farko sai ka auri Majeederh aurenka da ita a gobe babu fashi” Ta faÉ—a Sounding very angry. “…. Mam….”
Alpha’s Expression softened slightly as he looked at her ya juya ya kalli Majeederh wanda take zaune kamar anda sata, bata ko motsi sbd tsananin tashin hankali ruÉ—u da fargaba, da kuma tu’ajujjin abinda yake shirin faruwa da ita, An fasa aurenta? Kuma ranar É—aya kasance saura kwana É—aya a É—aura? Ko dai ba ita jin ake nufi ba? Fizgota da Alpha ya yi ya sanya ta dawo daga hayyacinta ta dinga kallonsa kamar zautacciyya a hargitse ya ce “Kiji tsoran Allah Majeederh ki faÉ—a musu gaskiya, tunda nake na taÉ“a cewa ina son ki? Yaushe na sameki nace zan aureki kada ki bari a cutar dani ina da wacce nake so” Majeederh ta girgiza kanta tana jan jikinta baya Æ™irjinta na É—agawa sama tana dafe saitin zuciyarta ta ce “Me ya sa zaka zaÉ“i tuzartani a lokacin dana saka rai da samun Æ´anci kamar ko wacce mace? Me ya sa zaka samun son abin dana fidda rai da samun shi? Me ya sa ka dawo da kwaÉ—ayin kasancewa É—aya daga cikin matan da zamu martabar aure bayan kasan ba haka bane? Me na yi maka a rayuwa daka nemi É—aukan fansa ta hanyar da zuciya ba zata iya É—auka ba? Me ya sa Æ™addara zata juya ta zo mini ta hanyar da ba zan iya jure mata ba?…” Ta girgiza kanta duk wannan abun jikinta Æ™yarma da É“ari yake kamar mai shirin yin jijjiga ta zube a Æ™asa saman Æ™afafuwanta tare da rarrafawa ta riÆ™e Æ™afar Alpha ta ce “Ko a lissafin Æ™addara ban taÉ“a lissafa zuwan wannan Æ™addarar ba, ka tausaya mini ka aureni kuma aure zaÉ“in zuciyarka, zan zauna da kai a haka koda baka so na, koda zan zama Æ´ar aiki a cikin gidanka dakai da matarka, wallahi ba zan iya jure wannan Æ™addarar ba fasa aurena da zakai daidai yake da tsayawar numfashina” Majeederh ta Æ™ara Æ™anÆ™ame Æ™afafuwan Alpha ta ce “Tunda na buÉ—e idanu naga kana damuwa da duk wata damuwata naji babu wanda ya dace dani sama dakai, zuciyata ta Æ™auna ce ka Yaya, Æ™auna mara algus ina sonka zan zauna da kai komai wahala, Æ™unci, damuwa,takura ka rufa mini asiri kamar yadda Allah ya rufa maka kada ka muzanta ni kada ka sanya na sama abar kwatance a dangi da kuma unguwa ka dubi girman Allah ka amince da aurena wallahi da bakinka kazo mini da maganar da……,”
“Stop it, stop!” Alpha ya faÉ—a yana janye Æ™afarsa daga gareta ya ce “Wallahi ba zan iya aurenki ba, baki mini komai but i can’t be your husband, i don’t love you anymore ki barni na aure wacce nake so ni ko zan takura miki ba zan iya aurenki ba ni ma kiyi mini wannan rufin asirin” Ya faÉ—a yana riÆ™e kansa da hannu bibbiyu.
Majeederh ta kallesa irin kallon ka rusa mini rayuwata kafin ta ce
“What have i done to deserve this from you?? Wallahi ina sonka ni” Aaliyah ce ta tashi tare da Æ™arasawa wajan Majeederh ta ce “Anti Jeederh ki barsa Allah zai kawo miki naki rabon, ya yi haka ne domin ya kunyata ya sanya Æ™addararki ta Æ™ara tsamari” Majeederh ta girgizawa Æ™anwata kai ta ce “No Aaliyah ba zan iya jure gorin aure a wannan lokacin ba” Kuka sosai Aaliyah take kamar ranta zai fita, tana tausayawa halin da yayarta take ciki. Anti girgiza Æ™afa kawai take lokaci zuwa lokaci take jan Æ™wafa, Abbu tunda aka fara maganar ya sunkuyar da kansa Æ™asa baka iya gane yanayin da yake ciki, wai Æ´ar cikinsa take durÆ™oshe tana roÆ™an wani ya aureta? Me ya yi mata da zata nemi tuzarta shi har haka? Mami ta yi jigum idan ranta ya yi dubu to ya yi tsatsa ya lalace, kana ganin yadda idanunta ya yi jajur zaka san zuciyarta a kusa take. Uncle Isma’il kallon Alpha kawai yake, Uncle Bello ya dubi É—an nashi ya rasa me zai ce masa he really disappointed him. Innati zare idanu tayi kana ta ce
“Komai yana da lokacin, lokacin bayyanar hakan ne ya yi kada ku damu, gaggawa aikin shaiÉ—an nasan za rina ansaci zanin mahaukaciya na jima da ganin wannan rana” Ganin babu wanda ya Æ™ara cewa komai ya sa Uncle Bello É—aukan wayarsa ringing É—in farko aka É—auka cikin sauri ya ce “Liman kayi haÆ™uri an samu matsala a invitation card É—in nan, É—aurin auren Æ™arfe 9:00 na safe sai a sanar a masallaci” A gigice Alpha ya kalli mahaifinsa ya ce “Abba me na yi maka da baka son farin cikina? Wallahi kuka aura mini Majeederh zan kashe kaina” Wani Mahaukacin mari Uncle Bello ya sauke Alpha kafin ya dawo hayyacinsa Mama ta Æ™ara sauke masa wani, ganin haka yasa Widad fashewa da kuka sosai ganin yadda ake marin yayan nata Uncle Bello ya nuna Alpha da hannu ya ce “General Ajzan-Alpha Bello Khan wallahi yau ko da gawarka ne sai an É—aura aurenka da Hawwa’u” Alpha ya juya ya kalli Majeederh ya dawo ya dawo ya kalli Uncle Bello muryarsa bata fita ya ce “Sai a É—aura da gawar tawa”
Yana faÉ—in haka ya fice daga cikin parlourn, Majeederh ta miÆ™e zata bi bayansa sai a lokacin Anti ta ce “Kada ki kuskura ki bi bayan wanda bashi da imani” Uncle Isma’il ya miÆ™e da hanzari ya ce “Kada Alpha ya cutar da kansa fa?” A takaice Uncle Bello ya ce “Rabo dashi daidai nake da zamaninsa, he really disappointed me ya nuna bashi da biyya ban isa da shi ba” Kafin kowa ya yi magana aka ji faÉ—uwar abu gabaÉ—aya suka juya Majeederh ta faÉ—i babu numfashi a Æ™irjinta…..

Duk da kiran asubar da ake bai sanya É—aya daga cikinsu ya motsa ba, ko wanne ka kalli fuskarsa za kaga tashin hankali musamman Dattijan mazan. Uncle Isma’il ya saka hannu ya sharce zufar data gangaro masa yana cire hular kansa ya ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un!” Ya juya ya dubi Uncle Bello daya kasa cewa komai idanunsa ya yi jajur ya kalli Mama dake rusa kuka sosai ya ce “Wai mene ya faru mai zafi har haka da yaron nan zai mana wannan cin mutunci?” Mama ta share hawayenta ta ce “Idan ni na haifi Alpha da cikina to wallahi…..,” “A’a please” Anti ta tare ta da sauri wanda ya hana Mama Æ™arasa faÉ—in abinda tayi niyya. Uncle Bello ya É—ago kansa ya ce “ÆŠan cikina? ÆŠan dana haifa Isma’ila?” Uncle Isma’il ya sauke numfashi ya ce “Dole akwai wani abu, yadda Alpha ya birkice kamar Mahaukaci sabon kamo zaka san something is fishy?” Jinjina kai kawai Mama take kafin suyi magana motar Abbu ta shigo cikin compound É—in gidan Uncle Bello wanda aka baza rumfuna na É—aurin aure, Abbu ya jima cikin motarsa kafin ya buÉ—e ya fito da sauri Mami ta fito tana mara masa baya, tun a balcony kafin su Æ™arasa Æ™ofar parlour suka fara jiyo kukan Mama, Mami kamar zata kifa haka ta bangaje Abbu ta shige “Ba dai an fasa auren ba?” Abinda Mami ta faÉ—a kenan tana binsu da idanu, Abbu ya shigo tare da jingina da jikin bango can ya ce “Isma’ila, Bello na ji kira cikin gaggawa gashi ina Æ™oÆ™arin rasa sallar asuba?” Uncle Isma’il ya miÆ™awa Abbu white paper ya ce “Read, karanta” Har Abbu yaÆ™i amsa sai kuma ya saka hannu ya karÉ“a tare da buÉ—ewa hannunsa na rawa idanunsa ya sauka akan handwritten É—in Alpha da yake cewa….

DEAR PARENTS.
_Bani da baki ko kalmar da zan muku bayani wajan fahimtar daku abinda nake nufi, amma na zaɓa mana hanya mai sauƙi da warware ƙullin da yake ƙoƙarin raba zumunci, ban kashe kaina ba, ban kuma zauna a cikinku na ɓata muku sunan family ba, more especially mahaifina, kayi mini komai a rayuwata ta duniya har kawo lokacin da nayi wayo na girma na mallaki hankalin kai na, Ina son Majeederh a matsayinta na ƴar uwata wacce jinina da nata suke yawo a jijiyoyin ko wannenmu, amma bana sonta ta aure bana ƙaunar zama da ita, akwai yarinyar da nake so a duk sanda kuka amince mini zan gabatar muku da ita a matsayin matar da zan aura kuma sirikar ku._
_Naso karɓarta matsayin mata kuma nayi muku biyayya, amma wallahi zuciyata ta kasa yarda da wannan ƙudirin idan na auri Majeederh ba zan iya sauke hakƙin aurenta akai na, zanta cutar da ita, zata zama bora a cikin gidana, zan wulaƙanta ta, wulaƙanci da human rights za su iya hukantani, zan muzantata, muzancin da babu macen da aka taɓa yiwa irinsa, zata zama baiwa a cikin gida, irin bayin da ba a samun su a yanzu sai ƙarnin baya irin bayin gidan sarauta ɗin nan, zata zama almajira a cikin gidan mijinta, To idan zan iya aikata mata duk wannan gwara ban aureta ba, nima ina mata fatan samun rayuwa mai ƴan-ci, ina gudun na tashi da ɓari ɗaya a shanye rana gobe ƙiyama_
_Babban Dalilia na rashin aurenta shi ne, Ni mashayi ne, ni mazinaci ne Majeederh bata dace da mutum mara tsafta kamar ni ba, ku yafe mini don girman Allah, kuji tausayina kada ku aibata ni, zan dawo duk sanda kuka yarje mini idan kuma mutuwata ta riskeni ina roÆ™an kuyi mini addu’a da samun dacewar Ubangiji!_

~G.A.B Alpha~

Abbu ya É—auke numfashi lokacin da idanunsa ya sauka akan kalma ta karshe, date da time. A sanyaye ya ce “Yaushe ya tafi?” Mama ta ce
“Ya tafi ko ya gudu? Wallahi Æ™arya Alpha yake baya Shaye-shaye, duk mutum bai hali irin wannan baya zama inda yake, ya tsani zin kamar yadda ya tsani fitar hawayena” Anti ta ce
“Me ya sa zaiwa kansa irin wannan tabon to?” Uncle Isma’il ya ce “That’s what i was thinking too” Wayar Abbu ce tayi Æ™ara ya ce “Ina zuwa” fita ya yi yana É—aga kiran ya É—an yi shiru sai kuma ya ce “Thank you, na gode sosai” Ya kashe wayar kana ya dawo. “Yanzu mene abin yi?” Uncle Bello ya miÆ™e ya ce “Ku san hanyar daza ku bi ku kwantar da hankalin Majeederh, ita nake tausayawa wallahi da ina da wani yaron bayan shi da a yanzu ba sai anjima ba zan É—aura masa aure da ita, Allah ne shaidata, Alpha kuma sam ba zan masa baki ba, amma zan ga illar bijrewa iyaye nasa kalar godiyar kyautatawar da mukai masa kenan” Yana faÉ—in haka ya fita gabaÉ—aya mazan fita sukai domin gabatar da sallar Asuba zuciyoyinsu babu daÉ—i. Mami ta kasa cewa komai domin ta girgiza da al’amarin, wani irin baÆ™on al’amari ne wannan? Only God knows! Bayan Anti tayi sallar Asuba bata jira mijinta ba ta nemi napep zuwa gida…
Wajejen huÉ—u na rana ta fara buÉ—e Idanunta da Æ™yar, wanda sukai mata nauyi har lokacin drip ne manne a hannunta, ta juya kaÉ—an sbd ciwon da É“arin kanta yake mata ga wani dishi dishi da take gani kamar mai hawan jini, da sauri kuma ta buÉ—e idanun tare da yin shiru tana Æ™oÆ™arin tina mene ya kwantar da ita ciwo haka? Duk Æ™oÆ™arinta na son ganin bata kwanta ba? “Sannu Anti Jeederh” Aka faÉ—a daga can gefe, ta juya suka haÉ—a idanu da Aaliyah da kuma Sona É—iyar Anti ta ce “Ƙarfe nawa?” A sanyaye Aaliyyah ta ce “HuÉ—u da kusan minti goma” Majeederh tai shiru sai kuma ta ce “HuÉ—u?”
“….Ai an kwana har yamma tayi, don baki da lafiya ne” Majeederh ta ce “Kina nufin kwana na É—aya kwance?” Ta bata amsa da “Eh” Daidai nan Anti ta buÉ—e Æ™ofa ta shigo tana kallonsu ta ce “Yaushe ta tashi?” Sona ta ce “Yanzu Anti” Anti ta ce “Sannu Hawwa’u” Ta É—an yi murmushi tare da yin shiru a hankali kuma ta ce “Shikenan na zama matar Yaya? Ni ma nayi aure an É—aura mini aure da Yayana General Alpha ko Anti? Allah na gode maka za a daina yi mini gorin aure ni ma nayi aure Æ™addarata ta zo Æ™arshe….

*Mijin Malama it’s a paid book….. Subscribe before you Read邏*

No comments