Breaking News

Mijin Malama Book 2 Page 45


Majeederh bata san lokacin data hantsilo daga kan gadon ba, tana ture kan Khalil, jikinta na rawa sai a lokacin ne take jin duk wata soyayyar shi matsayin É—an uwa yana ratsa jinin jiki da tsokarta. Ta kasa magana sai kallon Maman Alpha take da wani firgitaccen tashin hankali, wanda ya kasa É“oyuwa daga zuciyarta, gabaÉ—aya zuciyar buÉ—ewa take a hankali ta shiga aikinta a gaggauce. Ƙirjinta tana jin kamar an É—ora mata dutsen dala da Gwauron Dutse saboda yadda take fusgar numfashi da Æ™yar, Æ™waÆ™walwarta na buÉ—e a gaggauce tana amsar saÆ™on, cikin yanayi na firgici da hali na gigita da manta kai. Khalil ya zura farar tattausar Muslimi thobe jallabiya É—insa, ta bi jikinsa ta kwanta kasancewar jikinsa ya buÉ—e ya Æ™ara cikar da zati da haibar shi ya Æ™ara bayyana a fili yadda maÉ—aukakan jama’a zasu gani su fasalta yanda kamalar ta kwanta a fuskarsa. Gashin kansa duk a barbaje baya son ya yi cutting É—insa gashi bai je saloon ba, ya É—an juya sai yaga wani Æ™aramin white ribbon siriri ya É—auka ya tattare gashin ya É—aure ya sauka a wuyansa, duk ya cuccure kamar Indomie, ya É—auki p.cap ya É—ora a saman kan shi, babu abinda kake iya gani sai jajayen laÉ“É“ansa masu kauri da taushi, sun É—an jiÆ™e da damshin yawun Jee, sai fararen Idanunsa da suke jiÆ™aƙƙu kamar wanda hawaye ya kwanta a cikinsu, sun yi wani laushi a lumshe irin yanayinnan na kasala, asalin blue eyes É—insa da ba kowa ke lura dasu ba ya fiddo saboda yadda ya É—an buÉ—e idanun yana gyara zaman agogon Rolex akan wrist É—in shi, yanayin suffar Khalil ta cikakkun baÆ™aÆ™en Æ´an America É—in nan ne, a fusge kuma laushin fatarsa da É—an duhunta kamar ta Æ´an Etopia ko Mali, Khalil
baÆ™i ne sosai irin dark-skinned É—in nan wacce har Shinning take, amma kana kallonsa kasan cewa hutu da jin daÉ—i sun zauna masa, saboda yadda dark-skinn É—insa tai fresh gwanin sha’awa _His elegant black skin_ sai sheÆ™i take cikin light blue É—in hasken da yake É—akin six-packs É—insa a bayyane ya bubbuÉ—e ta cikin jallabiya É—in, ga Round face wacce saje da gemu suka yi covering É—insa,sexy eyes masu fitinannan É—aukan hankali, ko namiji shakkar idanun yake balle mace, ba ruwansa da kowa amma wanda ya shiga inuwar shi a nan yake sanin asalin haukan Khalil, yana da rauni akan mata,baya son cin amana, Æ™arya, da munafurci.

“Mu..mu..mutuwa?” Ya furta a rarrabe kamar bagware, yana fiddo idanunsa waje cike da razani, yama rasa cikakke kuma ainahin kalaman da zai amfani dasu wajen yiwa Maman Alpha magana É—in. Majeederh ta kama hannun Maman Alpha ta ce “Ya..yaya..? Daman bai dawo ba gida ba? Karki ce mini ya mutu” Maman Alpha ta kama hannun Majeederh ta riÆ™e cikin nata idanunta na zubar da wasu azababbun hawaye wanda yake da cin zuciya ta ce “Ko wanne bawa mai rai a nan duniya, al’amarinsa na wanzuwa ne bisa tsarin Ubangiji, Alpha ya rayu a cikin uwa mai kyakkyawar zuciya na tsayin wata tara da kwanaki, tun kafin zuwan shi duniya Ubangiji maÉ—aukakin sarki ya zartar da ikon shi akan yadda rayuwarsa zata kasance a duniya” Ta sauke ajiyar zuciya tana Æ™asa da kanta, Khalil duk baya fahimtar wannan farsafar zancan, mai wahalar fahimta azancin maganar na kalaman da akai amfani dasu sun dunÆ™ule a kansa ne. A hankali Maman Alpha ta sake cewa.

“To me zamu ce da Ubangiji banda godiya ga ni’imar shi? Daman wanda bai godewa ni’imar Allah ba to zai godewa azabar shi, Alpha ya jawa kansa, tun a haihuwar Bilal yaci ace jirkitacciyyar Æ™waÆ™walwar shi mai wassafa masa muggan abubuwa wanda zasu gurÉ“ata goben shi, fahimtar shi Zuleehart kyauta daga Allah ce, kuma ita ce ni’ima a gare shi, ni, ke, Khalil, Alpha kowa na duniya yana rayuwa a cikinta bisa yardar Allah, kowa na rayuwa da kalar tashi Æ™addarar, wacce Ubangiji ya samar da ita tun kafin zuwanmu duniya, hakan rubutacce ne, kuma halataccen rubutu ne akan allon da ba zaiyi Æ™arya ba, hannun da ba zai rubutu ba daidai ba, zuciyar da bazata cutar ba, kyakkyawan rubutu ne kamar rubutun tawada a jikin dutse wanda baya goguwa balle ya zama shuÉ—aÉ—É—e, barin Alpha garin nan, aurenki da Khalil, dawowar Alpha, mutuwar khalil, aurenki da Alpha, dawowar Khalil a matsayin rayayye gabaÉ—aya yana zane jikin Lauhul Mahfouz, wata Æ™addarar mune muke janta, wasu siya musu akayi, i believed cewa General ba alheri bane ga duniyarki shi yasa abinda ya faru, bai wakana ba sai ana ranar aurenku” A kiÉ—ime Majeederh na damÆ™e hannun Maman Alpha muryarta na sarÆ™ewa da Æ™yar da iya cewa.
“Fahimtar dani meke faruwa? Ina jin kamar na yi ba daidai ba!” Maman Alpha ta ce “Majeederh alfarma nake nema, amma kafin nan kizo muje hospital É—in” Majeederh ta juya ta kalli Khalil bai kalleta ba, ya É—auki key d’in motarsa wanda alama ne ya kewa majeederh ta shirya, doguwar riga ta saka ta É—auki mayafi tayi rolling, wani fitinannen kallo Khalil ya yi mata ba tare da ya ce komai ba yana É—aukan Alhassan, wajan wardrobe ta nufa ta É—auki hijab har Æ™asa ta saka, ta nufi wajan Al’hussain a É—an hankali ya ce “Madam, ur niÆ™ab” Tayi jim domin bai taÉ“a nuna sha’awa akan niÆ™ab ba, ta É—an hargitsa kayanta ta É—auka ta saka, ya dinga kallonta from head to toe kafin ya nufi waje ta É—auki Al’hussain dake kusan lokaci É—aya yaran suke bacci, suka jero gwanin sha’awa suka samu Maman Alpha a motarta, gabaÉ—aya suka kwantar da yaran a baya da wani irin gudu Khalil ke jan motar har tsoro ta ji, ta manta komai nasa a gaggauce yake yinsa, kuma ya saba da tseren mota tun sanda suke kasawa da Æ´an sanda. Lokaci kaÉ—an suka Æ™arasa shiga cikin hospital É—in kai tsaye kuma Emergency, a reception suka samu Yaya Bilkisu dasu Widad da Du’a su nata kuka, jikin Majeederh ya yi sanyi zuciyarta ta karaya, Uncle Bello ya kalli matarsa ya ce “And who gave you the permission? Me kike Æ™oÆ™arin yi?”
“Ni uwa ce, zuciyata ba zata É—auki halin da É—ana yake ciki ba, zan nema masa abinda kai ka kasa nema masa bayan kana da ikon yin haka” Uncle Bello ya ce “Idan taÆ™amar shi É—an uwanta ne kin manta ya suke da mijin nata? Ko kema son zuciyarki zaki gwada ne?” Maman Alpha ta cillawa Uncle Bello dairy ta ce “Ka duba, General shi ne ya sakawa Majeederh suna tun ranar da aka haifeta, babarta Fulani tayi Supporting nasa, ya nemi ta bashi Majeederh zai kula da ita, a nan Fulani ke cewa ba kulawar Majeederh ta bashi ba, har duniya ta naÉ—e ta mallaka masa Majeederh, ta bashi ita matsayin matar aure ya yi mata wannan alfamar, ya amshi batunta wanda ita ta kasa gane ribar tasa ce, sai dai ashe kashin dankali ne, General yana jin zai sadaukar da komai wajen ganin ya auri Majeederh ya cika mafarkin Fulani, da al’Æ™awari na muradin zuciyarsa” Ta goge hawayen fuskarta ta ce “Kun kasa fahimta, nima a bincike na gano hakan gabaÉ—aya bedroom É—in shi pictures d’inta ne tana Æ™arama har zuwa girma, ba wanda ya taÉ“a faÉ—awa hakan wanda dalilin hakan akai masa asiri, after all these things he did, didn’t he deserve to be Majeederh’s husband?”

“Idan mutuwa gaskiya ce, hisabi wajibi ne, haka nan Soyayya ma gaskiya ce Ubangiji ke samar da ita a zuÆ™anta bayinsa, ba tare da sani ko tambayar su ba” Khalil dai kallonta kawai yake a hankali ya É—auki wayarsa dake ringing shiru ya yi a hankali yana Æ™asa da murya ya ce “Ko Latifa ne, arrest her directly ku kai ta prison” Yana faÉ—in hakan ya kashe wayar ganin Maman Alpha ta ja hannun Majeederh zuwa room É—in da Alpha ke ciki ya miÆ™e tsaye walking slowly ya bi bayansu, rashin sanin abinda zai iya faruwa ya saka Uncle Isma’il da Uncle Bello da Yaya Bilkisu suka rufa musu baya. Cak Majeederh ta tsaya ganin gabaÉ—aya jikin General maÆ™ale da na’ura musamman Æ™irjinsa, cikin bakinsa ga oxygen ta hancinsa, sai wani green É—in yadi da aka ja masa zuwa wajan cibiyar shi babu inda yake motsi a jikinsa kamar matacce, Maman Alpha ta juya ta kalli Majeederh sai kuma ta zube akan Æ™afafuwanta tana riÆ™e Æ™afar Majeederh ta ce “Alfarma nake nema a wajanki Majeederh, ba don na taÉ“a taimakonku a rayuwa ba, ba dan na wahalta miki ba, ba don na kasance cikin zuciyarku ba, yadda Ubangiji ya bayyana miki gaskiya akan Latifa da Hajiya Luba, yadda Ubangiji ya dawo da hankalin mahaifinki, yadda Ubangiji ya sadaki da dangin mahaifiyarki, kiji tausayina,kiji tausayin halin da É—an uwanki yake ciki, ki duba girman Allah, kaÉ—aitar shi da buyawarsa ki sadaukar da soyayyar Ibrahim wa Alpha…” A gigice Khalil ya kalli Maman Alpha sai kuma ya cire p.cap É—in kansa, tare da zare ribbon É—in ya girgiza kansa gabaÉ—aya sumar ta wargatse ta rufe fuskarsa, a hankali ya yi kneeling down a gaban Maman Alpha shi ma ya dafa Æ™afarta ya ce “I love you Maa, and i also respect you, ke uwa ce kina fahimta, ni i don’t know how to explain yadda Ƴar madara take a raina, ki yi tunani idan na rasata ya Ummie na zata shiga? I love my wife ku barni da ita nayi rayuwar farin ciki don Allah…,” Kafin ya sauke Maman Alpha ta damÆ™e hannun Khalil tana kuka kamar ranta zai fita ta ce “Don Allah don Annabi Ibrahim, ba danni ba saboda girman da Soyayyar da kake ma Ummie ka barwa É—ana Majeederh bari na har abada….

No comments