Breaking News

Cheaters Club 1

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(...Babban goro sai Magogin Æ™arfe...)_ 



#ROMANCE


#FICTION

#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER

#FRIENDS TURN ENEMIES.

#GAY/SODOMY

#REVENGE


BY

 _SURAYYAHMS_



 _AIDA BEUTY SALOON AND LOUNGE._ 

    9:30a:m.

 _Lekki epe expressway lagos state, nigeria._ 


Gidan kwalliyar Aida Beauty being one of the Best Beauty luxury spa a garin lagos yasaka yau ta amshi Bakontar Latest Bride in town wato sananniyar matashiyar nan HALISA MANSA wanda aka fi sani da _Halsy queen_ Da kuma kyawawan Hamshakan ayarin kawayenta da suka mugun shaƙuwa da junansu wanda a kullum zaka gansu tare sam basa rabuwa da juna.


Deir friendship is like no oda bakasafai ake samun irinshi ba,tamkar yan uwan jini haka suke dan sun mugun shaƙuwa da junansu,kawance ne irin na mutu ka raba takalmin kaxa ke wanzuwa a tsakaninsu tun tashuwarsu adacan.


yau wata rana ce ta musammn agaresu na tsananin murna da farinciki wanda bazai iya misaltuwa agaresu ba.


Daga yanayin hasken annurin dake kwanciyar akan fuskar kowacce acikinsu zaka san cewa ayau lallai suna cikin yanayin tsananin farinciki da nishadi, kowacce ka duba cikin su bazaka iya mata kallo daya ka dauke kanka cikin sauki ba, sun sha tsadadden yadinsu cool royal blue silk material daya kame dirin jikinsu, soft indonesian silk material ne da aka kera musushi a companyn babban designer nan zuhair murad domin wann ranan, tun daga style kayansu har ixuwa kan duk wani accerories da suka saka na wengers luxury diamond ne,duk wani classy designs najikinsu iri daya ne kama daga kan high heels shoes,clutches, watches, bracelets,har style na dinkinsu iri daya ne, kwalliyarsu wanda ya kasance mai tsananin kyau da tsada wadda shine ya kara fitar da tsabar kyan kowacce acikinsu,murmushin nan nasu mai sanyi tare da daukar numfashin duk wani me kallo suke sakarwa juna.


hamshakin Group din nasu kwata kwata su biyar ne, kyawawan mata ne classy and matured babu kamshin yaranta a jikinsu ko kadan، they are ladies in der late 20s and early 30s,body game nasu ajin farko dan kamar su suka zabi kansu domin kuwa kowacce cikinsu tanada irin kalar tsarin kyau na musamman da Allah ya zuba mata.


 _Halisa Roberts mansa_ wato halisa mansa ko halsy queen ita caramel colour ce tsiriyace mai jiki irinna models dogaye masu shape sosai,Sai _Amina Ali talba_ ana ce mata meenal talba farace sol doguwa Mai matsakaicin tsayi da jiki, _shema'u usman marafa_  da ake ce mata shema marafa, full option ce tana da wani irin diri mai daukar hankli amma blck beauty ne wacce bata bukatar wani make up a fuskarta kwata kwata cos of her natural beauty,sai _Hadiza umar maitaima_ a.k.a Dije meitama, ita kuma irin kim kardashian skin din nan ne gareta, farinta na yan gayu ne sabida make up surgery datayi wa sassan jikinta to make it look soo perfect, she is flawless and neat, tattali iya tattali, kana kallonta kaga creame de la creame high level woman with class, sai kuma _victoria williams Baltimore_ wato vicky, siffar jikinta irin na black americans ne babu abunda babu ajikin nata na diri da kuma tsarin halittar fuska vicky tana da dogon gashi dayake zuba har gadon bayanta yake kwanciya dan haka bata taÉ“a saka kari ko wani attachement ba.



mutum uku cikinsu musulmai biyu cikinsu christians amma bazaka gane hakan akan lkci ba sabida mode of life dinsu da character dinsu gaba daya iri daya ne, kusan kominsu atare suke gudanawarwa,izuwa yanxu acikin su kowacce tay aure wacce ta rage din kenan Halisa wacce ake kkrin daurin aurenta ayau,shiyasa ayau din sukejin kamar suyi fifika dan tsananin farinciki.


yau suka rufe kofa kirif sun dawo complte group of power Housewives Kamar yadda suke kiran kansu.


Daga cikin hadadden spa na Aida beauty dayaji komi da komi na zamani evrything was decorated in Wedding colour theme na halisa sabida su mata ne masu azaban son kyale kyalen duniya da uwa uba kwalliya na kece reni,favourite colour na amarya halisa Royal blue And gold ne، dan haka ko ta ina an kawata spa din dashi with touch of white ballons here nd der akasa suna boucing.


Oda flying ballons da stickers na weding all over the wall and floor na spa din,yau ranar tasu ce dan haka suka kama services din spa din gabaki daya,yau kwata kwata baza'ayi attending kowa ba saisu, Ata gaban mirror inda Amarya ke zaune daga saman sa har kasa golden glitters da stickers ne an rubutu _"Happy married life mrs sweetboy"_ an ma halisar wani irin kywalliya mai daukar nunfashi shi ba heavy ba shima light ba idanunta an kawata shi in dark smoky style an bishi da golden glitters that make her shine

,white luxury weding gown nata mai tsananin shape ya baje ta kasa yacinye rabin inda zasu saka kafafunsu akasa sai qamshin turaren Creed aventus hade da lattafa feminine dake tashi ajikinta,she is sitting pretty like a queen sabida halisa asalin kyakkwar mace ce, ita ba fara ba ita ba baka ba, skin colour nata dinta smooth caramel ne wato tsakanin madara da da chokolate colour mai wani irin sulɓi da sheki, tsiririyace doguwa mai cikakken shape din kugu kalar siffar mahaifyarta datakasance yar kasar somalia, shakikiya kuma Aminiyar Amarya wacce sukafi shakuwa wato amina MEENAL TALBA itace a tsaye kusa a tare da ita tadan dafa kafadunta fuskansu cike da wani rin kyatattcen murmushi ayayin da suke kallon irin azaban kyaun da sukayi yau ata cikin mirrorn dake gabansu bayan angana tsantsara musu kwalliya dataci dubbunan kudade.



Kusan wanda halisan zata aura badai nitsuwa da hankli ba, wanda shi yasaka suke cema mata sweetboy irin mazan nan ne da basuda matsala basuda hayaniya komi tace mishi zaiyi duk abunda tacemai ya bari kuma baya mata musu zai bari. Baishan giya baya bin mata, kai hatta kallon ball bayayi,shide daga aikinsa sai gidansa kusan duk cikin kawayen nan biyar babu wanda peaceful rayuwar gayen halisa baya basu mamaki.


Wajajen karfe 9 na safe lokacin Hankalin sauran kawayen naga kan wayoyinsu, wasu na waya,wasuna lura da wasu abubuwan dake gudana daga wajen da za'ayi events.


Banda scrolling chat din whatsap babu abunda amarya halisa takeyi, dan ixuwa yanzu ta karanci sakon ango to be  din nata da sukayi na karshe yafi dubu. Last seen dinsa was yestade at 8pm lkcin da suka kammala maganan akan weding gown dinta da zata saka yau.


Evrything she did was based on his choice. kalar tsananin Soyayyar da suka nunawa junansu kwanakin ki was soo sweet and amazing dan tamkar baza su ga wann ranan ba haka sukata zumudi, Ta tura masa hotunan ta yafi guda goma a dm dinsa, Saidai rashin ganinsa online tun jiya da kashe wayarsa da yayi yana bala'in saka mata damuwa acikin ranta sosai.


Ganin yadda ta kafe last text dinshi da ido yasaka meenal ta kwace wayar ta ajeshi akan table tana dada gyara nata zaman hair dress dinta tana dan murmushi, ahnkli halisa ta dago kai suka hade ido da magana abakinta wanda batagai ga furtawa ba meenal ta girgiza mata kai akan karta soma cusa wani abu aranta yau ranar farin cikine bana bakin ciki ba.


Halisa batace komi ba ta dan lumshe ido aranta tana tunowa da zancen hadiza tun kafin su iso wajen make up din ayau, tun jiya wajajen takwas har iyanxu bata sake jin duriyar angon nata ba. Wann yanayin bai taɓa faruwa da ita ba dan iya shakuwa sun shaku dashi sosai tasan kusan duk wani motsin sa, she was tensed, musmmn ma da Hadixa tayi tunanin hala ba lafiya ba, but meenal and the rest of the friends sunce karsu spoiling vibes din wann special ranan musmmn ma da suka san zach baxai yi wani abu marar kyau ma halisa a wann ranar ba.


Da wann tunanin hakan ta bude lumsashun idonta ahankli tanamai sauke ajiyan zuciya a asirce.


Hadiza dake lura da yanayin ta asace ta miƙe ta fita daga bisani vicky tabi bayanta da waya ahannun ta cikin sauri ta sauka akan step kafin vicky ta cimmata harta kai gaban parking lots taja ta tsaya jin kirjinta na bugawa da sauri.


Kallo daya zaka mata kasan cewa Bakaramin tsoro take jiwa kawarta halisa ba,in har ace yau wani abu mummuna zai same halisa toh babu shakku ko tantama dukansu ne zasu ji tsananin ciwon abun aransu kasancewarta wacce tafi kowa shan wahala da rayuwarta acikin su. 


yau aranar daya kasance na farin ciki, halisa data fi kowa shan gwagwarmayar rayuwa acikinsu zata aure mutumin nan kwalli daya a duniya datake matukar darajawa da kauna, they all pray that nothing goes wrong, dan duk wani abunda zai same halisa a wann ranar toh bakaramin girgizasu zaiyi gabaki dayansu ba.


Tana tsaka da wann tunani aranta Jim kadan sai ga vickyn ta iso itama wayarta take dannawa, koda ta karaso wajen hadiza batace komi ba ta cigaba da danna wayar a dan gaggauce dan ta dedeta mood dinta. Wani lamba vicky taketa kira da alaman ana danna mata busy.


Fuskarta a matukar dore ta yarfa hannu muryanta kamar na wanda zatay kuka snn tace meye ke faruwa ne For god sake?..ta fada tana kikkifta eye lashes dinta akan hadiza acikin yanayin kufula sosai.


Hadiza batace komi ba taja sautin hmmmm acikin ranta, Sake dialling lambar vicky tay for the 5th time taga wai ur call have been fowarded nan ta dago kai ta kalle hadiza akaro na biyu dake tsaye ajikin motar ta tay shoru ta naÉ—e hannayenta cikin wani irin yanayi.


Karantar yanayin hadizar tay snn ta sauke Ajiyar xuciya tace Dije nifa kaina ya kulle ynxu kam..like what the hell is  happening..meyasa  abokan ango da ayarinsa suke kashe mana waya?

What about the venue? "Anya auren nan zai yu yau kuwa?.Evrything is just unfinished..oh my god...it feels like kamar mukadaine kawai muke ta shirin xuwa wajen dorin auren nan..even the pastor tun safe yake min korafi cewa side din ango basu kirashi ba so shi bai dau hidiman namu da wani muhimmanci ba..wai babu wani shiri daga wajensu..bawani motsi.. itakanta halisa bai kirata ba tun jiya, and this is nine clk for god sake!! Auren da za'a dorasa 10am?? I invited my own ppl fa what the hell is all this..


Hadiza ta lumshe ido ta bude ranta nadan susa tuna itama abunda ke damunta aranta kenan, cikin jan numfashi mai karfi dake tahowa da wani irin feeling na tsoro da jimami,ahankli tace toh ya zamuyi just stop complaining Vicky bana ma son hunch dinmu ya soma zamowa gaskiya, im going crzy already...

kinasani inajin kamr tunani na akan rashin yuwar auren nan gaskiya ne..just stop okay...

Kidena ma daga muryanki kar wani ya jiyomu lets just calm down for now.


shiru vickyn tay ayanayin damuwa sai bata kara cewa komi ba tay dan tagumi,itama duk ta daga hanklinta, ganin haka yasaka hadiza ta dafa kafadunta ahankli tanamai cewa "cmon vicky chill mana..lets be hopeful..nifa tun safe nakeji ajikina auren nan akwai matsala, cos it feels odd ace ansamu silence dayawa haka daga wajen ango,bai taba mata haka ba, tun jiyafa shikenan babu shi babu labarinsa, and

neither his family nor his friend call to confirm the venue, nothing...amma tunda already Meenal tace karmu dagawa halisa hankali da maganan nan Lets just be positive dat he will show up in the church kamar yadda tace din

..even i dont feel good about the whole thing.


Tana gama rufe baki sukaji motsin taku akansu kusan atare suka daga idanunsa sama suna kallon paveway din, ahnkli vicky ta sauke ajiyan zuciya ganin shema'u ne take saukowa walking majestically holding her silky flowing gown dayake nan royal blue dake duk iri dayane kayan jikinsun tana takowa ahnkli tana juya hadadden dirinta cikin kamewa sosai.


Tun kan ta karaso kasa take kallon yanayinsu na damuwa sosai ranta ya bata cewa da akwai wani abu dayake gudana,wa idanunsun ta kurawa ido daga nan tana karantar yanayinsu tanamai cewa "...Babes is evrything alright.?.


Shiru suka mata, ta kuma cewa..."ya naganku kunyi tsamo tsamo?..


Murmushin dole suka kirkiro kusan atare sukace mata" yeah all good...babu komi fa.


Nan take vicky ta maida hankalinta kan wayarta da sauri tana cewa ohh ni yar Adam yau an hadani da aiki pastorn nan akwai nacin tsiya sai kace bazamu iso ba. Daga haka ta sabule ta koma gefe can tana dan danne dannen wayarta just to avoid futher conversations dan tasan shema'u tafi shakuwa sosai da hadiza.


Ahnkli Shema ta dauke kai akan vicky duk dama ta gane metake ciki snn tay murmushi ta dube hadiza ganin tay shiru itama..


murmushi tay cikin basarwa snn ta sauke ajiyan xuciya,"huhhh i just cant wait to see my beautiful halisa walking down the aisle. Fadin hakan datayi cikin kwanciyar hankli da neman jin baki yasaka hadiza yin murmushi, a mugun kame shemau Ta juyo hadaddun idanunta da sukaji wani irin cat eye make up a kisinance kuma ahankli ta dube hadiza snn tace kawata dije, Did u see that coming kuwa???


Da kyar Hadiza ta hadiye shaukin maganan a wuyarta snn ta murmusa sosai itama a kisinance jikin jin baki, murya kasa kasa tace "yeah,why not?..i feel dat too, cos after all,our halisa girl derseve to be sooo happy. ..wai Me sukeyi aciki ne ynzu? Did he  call..


Cikin tabe baki Shema tace uhmm uhm not yet.


Hadixa tay rau da ido

Tace Ohhh god,and i Hope she is fine dai...


Atakaice Shema tace "Meenal tana tare da ita.


 Hadiza tace 

"Good point..


Dan jim tay snn ta kuma cewa "so,.. mune zamukaita church din witou the presnce of the groom and his family and friends? Shema I dont get..the waiting is bcming much. Tun 8 aka kammala kwalliya muna jiransu amma sai shiru.


Cikin katse Shema'u tace i think we shud just do that,..we are independant ladies we shud wait for no one,.


 ba bata lkci hadixa ta gyada kai tace yeah ure ryt.. as long as halisa will be happy lets all do dis for her sake..


shemau ta gyada kai snn ta juya tay hannu ma vicky akan ta karaso. 


Vicky Tana karasowa suka mata bayani snn suka hauro sama cikin beauty palor din inda suka same halisa xaune akasa cikin ballons dinta sun kewayeta kamar princess fuskarta cikin wani irin yanayi mai ragwabarwa.


Irin murmushin nan ne mai cike da damuwa da jin alaman wani abu zai faru da ita yau, marar kyau aranar aurenta akan fuskarta..


she is already in stress and anxiety, tana ji aranta da ajikinta cewa shirun zach yau din bana lafya ba, meenal ce zaune agefenta ta tsuguna tare da dafa kafadunta tana sauraron ta hawaye na sauka akan fuskarta ahankli itama. Dan sosai halisan ta fara bata tausayi.


Babu abunda halisar take tunowa face yadda take tsananin son "zach" wato mijin nata da zata aura.


Zach yana da matukar muhimmaci arayuwarta da zuciyarta tuna yadda ya amsheta cikin rayuwarsa da zuciya daya wanda a tarihi bata taba samun namiji daya sota haka ba. A she gets from men was the used and abused portion.


Halisa ta rasa iyayenta ne tun tana yar shekara bakwai a duniya، babanta dan nigeria ne idoma man from benue state her dad was a  Half muslim half christian man sam baida alqibla arayuwarsa,ranar da dare haka yasha giya mota ya bugesa ya rasu, mum dinta kuma somalian ce daga kasar somalia aikin yar jarida ne ya kawota nigeria hartay aure, ta rasu ne da cutar cancer wanda ya kasance gado ne a familynsu (genetic disease inheridetory) tunda ta rasu no one ever knew her familys where about a somalia. 


Halisa ta rage ita daya batada wani madafa gatanan yar karama.


kanin mahaifinta daya amsheta yake rike da ita shikuma talla yake dora mata aka, daga nan ya soma cusata cikin harkar karuwanci tun tana yar karamar domin ta kawo masa kudade tukuna yake bata dan abincin da zata saka abaki da wajen kwana cikin kwancyar hnkli.. duk sanda bata amince maza sun latsata ta kawo masa kudade ba toh zata sha tsinannen duka awajensa shida matarsa da ake cewa mama G, snn ajibga mata wanki cikin dare wanda harta kammalashi suna zaginta haka zata kwana tana zubar hawaye. Iya abu me kyau da kawunta ya mata arayuwa shine daya sakata a makarntar gwamanti tana karatu.


In the process na wann harkan datakeyi na saida jiki ta kawo kudi She got pregnant while she was 16yrs old, adan dole ta cire cikin sabida batasan na waye ba, tanaa cikin kuncin hakan uncle din nata ya dawo gida abuge ya sha giya sai yay raping dinta, tunda yaji dadin gindinta shikenan sai ya maida abun sara, duk sanda tay talla ta dawo memakon ya bugeta sai kawai yajawo ta daki ya rufe kofa ya danneta yay iyayinsa batare da sanin matarsa ba.


daga bisani ta kuma yin wani cikin wanda yana da tabbacin nashine amma gudun abun kunya yasakata agaba ta zubar aranar haka suka taru suka mata duka shida matarsa suka kirata kariya kuma karuwa, cikin burga da son rufa ma kansa asiri sai ya koreta yace mata bazai iya riketa ba, halisa na kukan kunci da baqin ciki ta tuhumesa akan yaji tsoron Allah akan lamarinta amma baiji tausayinta ba,alkcin rayuwa yy ma halisa zafi da tsanani, bayan nan tay yawo kwaroro kwaroro tana neman nakanta, da wahala da dadi duk seta nema take samun na sawa abaki, bbu kazamin rayuwar da batayi dan ta ceto kanta daga mutuwa da yunwa ba,dan har sata tayi dan taci abinci ahaka kuma ta cigaba da karatunta. until one day she get to live with her childhood friend meenal ita meenal din yar masu shine sosai mahaifinta Alhaji Ali talba ya rasu ya bar mata gadon arxiki mai uban yawa itakuma mahaifyarta ce kawai araye mai suna hajiya nadiya tana kulawa da ita cikin tsannanin so da uban gata, da ita halisa ta soma gamuwa dan haka babu wani sirrin rayuwar halisa da meenal bata sani ba, da temakon meenal din dana sauran kawayen nan nata rayuwarta ya dawo dede tay karatun gaba da scndry a makarnta me kyau itama sosai. 


Zamanta tare da meenal agida daya bai saka tay relying akan arxikinsu ba sam, halisa tana da zucyar nema, dan haka she become a self made millonaire ayayin da ta hadu da saurayinta zach wanda yazo mata as her business mentor.


Sun fara soyyayarsu ne ata hanyar neman aikin yi,she was his client, sabida halisa ta saba da shige shige kyaunta yasaka take samu karbuwa sosai, tay modeling, tay coaching a gym, tay marketing ma kamfanoni dayawa har tazo ta samu aiki a wani construction company tana tallata musu aikinsu dan susamu hannun jaruka masu tsoka, dan sosai ta iya jan hanklin clients da bayananta,  tun da zach yaganta yaji ta mugun kwanta masa arai yake kuma iya bakin kkrinsa wajen share mata hanyar arziki shine ya dora ta akan hanyar business ya kuma kare mata mutuncinta mysmmn daya lura cewa halisaa tafi damuwa wajen neman nakanta  tana da zubin mata masu kamun kai bata son harka da mazan banza sam.


Zach irin masu kudin nan ne wanda arayuwarsu basu san talauci ba. Baida damuwa sam, he is cool, baida hayaniya, a perfect describtion of a husband material.


She love him soo much with all her heart tana kuma bashi girmamawa mai yawa aranta dake bai taba yunkurin neman jikinta ba kmr sauran maza. 


Ko kadan bataji wani abu aranta akansa na fushi waidan bai nemeta ayau aranar aurensu ba, banda mummunan tsoron kar ace wani abune ya sameshi awani waje babu abunda yake gigita mata kwakwalwa. She trust zach with all her heart and her life. Yadda take musu bayanin irin soyayyar daya nuna mata mai tsafta mai cike da mutuntuwa yakasa duka jikinsu yay sanyi sosai.


Hadixa datafi kowa jan baya akan hidimar itace ta karaso cikin sauri ta rungume halisan sosai yanayin jimantawa tanamai bata karfin gwiwa akan lamarin musammn da sukaga tafara tsorata da tunanin ko wani abune yaje sameshi ata wani waje shiyasa bai nemeta ba.


Hannunsu rike da juna ita da hadiza suna kallon cikin idon juna dayake cike da hawayen kaunar junansu da sukeyi, murya a sanyaye dije tafara share mata tears dinta itama ranta cime da tsoron tanacewa am so sorry mendy, bawai ina kin abun bane i just dont want anything to hurt u today my friend, hawaye sosaai ya sauka akan fuskan hadiza ayayin datake maganan.. Muryanta na rawa Tace. Halisa i cant bear to see u in pain, you have faced so much cruelty in ur life,u struggled alot...we all cant see u in any sort of pain ..This is ur weding day.. ranar farin cikin kine bana kuka ba.


Cikin wata ragwabbiyar murmushi data kufcewa halisan abazata tace " please dont worry about me..Am more worried about zach.."nagode muku kawayena,nasan kun damu dani sosai but i promise u dija، Zach won't hurt me..he will neva.. i swear. Sede in wani abu ne ya sameshi mukaji shiru..im sure he is happy to see this day.. its our dream to see this day im sure of it.


Hawayen hadiza ya sauka na tausayin kawarta, su meenal ma dik jikinsu yay sanyi, ahankli hadizan ta rungumeta tace shikenan halisa we all belive u..

Shiyasa muka yanke hkuncin cewa zamu kaiki venue din aurenki dakanmu..we shudnt wait for anyone..


Murmushi halisa tay jin sunce mata hakan, sosai suka rungume junansu sauran kawayen suna kallonsu suna murmushi kowa jiikinsa yay sanyi sosai.


Cikin katsesu vicky tace enough girls lets take our bride to the church is almost time.


Wooohh wooh shema'u tafara rawa tana jujjuyawa nan da nan tay sparking wajen suka tafa da vicky taf taf suna ihun suna halisan suna dan dariya mai cike da nishadi dansu warware mood dinsu sosai atake suka dawo dede.


Nan da nan kuwa suka miƙe cikin sake kimtsa kansu kowacce ta dawo dede da murmushi akan fuskarta nan dukansu suka gewaye amarya halisa dataci kyau ma fitar hankali suna bata princess treatment..


Meenal ce rike da jelar gown dinta, hadiza na fetsa mata turare shema da vickey suka leading way ixuwa kan tsadadun motocin su dake parke a waje.....

#SURAYYAHMS

*SHARE PLEASE*

FOLLOW ME ON WATTPAD @ 

SURAYYAHMS


Ko chat me 

08060712446 




Surayyahms on romance

No comments