Breaking News

Wata karuwa 1-2

1-2

*_MAFARI_*
Hanisa ke Hanisa wato yauma saikin jamin asarar da kika saba ko nikam narasa irin ki kullum aita maimaita miki mgn É—aya


doÉ—É—iyar Æ™waÆ™walwa irin ta kifi to wlh yau ki tabbatar idan kika dawomin da kwantai na Shinkafar nan saina nakasaki Yayarki Hasina yanzu haka ta kusa dawowa amma ke kinanan kina iskanci” fuuuu Baba Indo ta zari buta ta shige bayi Wata matashiyar Budurwa ta fito daga É—aki sanye da riga da zani na atamfa kyakkyawa Chocolate me matsakaicin tsayi me dirararren jiki.
ÆŠaukar bahon Shinkafar tayi ta É—ora akanta ta nufi Æ™ofa tana cewa “Na fita Baba Indo Bata saurareta ba dama kuma bataji a ranta zata kulata ba ta fice a gidan ta tsari É—an sahu ta hau tace masa yan taya zai kaita. Suna tafe tana kalle²nta suka isa gurin ta zaro kuÉ—insa ta basa ta É—auki kayanta ta Æ™arasa yan abincin ta zauna a gurbinta.
Can nesa da ita ta hango Hasina tanata danna waya ta miÆ™e da sauri ta isa gabanta ta tsugunna tace “Yaya Hasina Ina kika samu waya?” ÆŠagowa tayi ta kalleta tayi mata dariya tace “Sai yanzu kika fito Ni abincina har ya Æ™are” buÉ—e bohon abincin tayi taganshi jingim ko taÉ“ashi baayi ba ta É—ago da sauri ta dubeta tace “ai Bama ki fara taÉ“awa ba” yatsina fuska Hasina tayi tace “Eh ban taÉ“a ba jira nake azo a bani kuÉ—insa ki bari kema idan yazo zance ya haÉ—a ya biya da naki”

 

Zaro manyan idanunta tayi tace “Waye shi Yaya Hasina?” Rufe mata baki tayi lkcn da wani matashin saurayi kyakkyawa yake nufosu Hasina ta nunawa Hanisa shi fari tas dogo me dirararren jiki faffaÉ—an gaske yana sanye da Æ™ananun kaya da suka amshi jikinsa sosai. Ajiyar zuciya Hanisa ta sauke lkcn da idanunta ya sarÆ™e cikin nasa tayi saurin janye nata kanta na sarawa gabanta na faÉ—uwa ta miÆ™e zatabar gurin Hasina ta riÆ™o hannunta tace “Ta Baba Ina zaki?” Dubanta tayi ta dubi matashin daya tsaya akansu yanata zuba Æ™amshi tace “Zan koma gurin abinci na”
Sake riÆ™e hannunta tayi tace “Wannan da kike ganinsa sunansa Abdul-Ahad Anace masa Abdu zan baki lbrnsa sai munje gda yanzu dai ki tsaya mu samu almajiri muyi musu sadakar abincina da naki duk yace zai biya” sake dubansa Hanisa tayi tace “akan me Yaya Hasina nifa kinsan banason juye haka kawai kina ganin Ladidi da Tabawa daga juyen nan aka juyesu fita ma ta gagaresu saboda sunyo shegu nikam a’a abarmin nawa zan siyar banson san zuciya…..”

 

 

No comments