Breaking News

Ameenatou 7


 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#Arewabooks@Mamuhgee

#ZafafaBiyar




7

*_ASHNA BEAUTY SKINCARE_*

Free class free class 

 Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku




********

Iyayen Aleena sunada wani irin qyanqyami da kabilanci ga Wanda basu sani ba Sam duk da suna kallan su mamman din a matsayin family na Mr Jaden sedai Sam Sam Basu aminta da mamman ba duk da Shima fari ne sosai kaman Omar Kuma kyakkyawa daya kusa ma yafi Omar din kyau amma dai hankalinsu yafi Kwanciya dari bisa dari akan Omar dasuke ganin kaman a taredasu ya taso duk da basusan yarinyartasa ba Amma ai a tinaninsu a hannun Mr Jaden ya taso Kuma dansa ne Daya haifa acan.


Aleena a zuciyarta mam kaman yanda yanzu ake kiransa ya kwanta mata dari bisa dari sbd yakai duk mataki da tsarin datakeson namiji yakai mata,

Yanada kyau sosai da wayewan da baya shakka ko tsoron kowa,

Hakama yanada class Wanda taku ne Daya iya abinsa tinda ya samu kansa sabuwar duniyar datafi wadda suka fito,.yanada ilimi da dukiyar kansa da bazai taba damuwa da tata dukiyar ba hakama ya Bata tabbacin shine zai tattaro ya dawo qasar da zama bazai taba daukanta zuwa koina ba Dan haka taji Hakan ya mata.


Omar Bai taba tinanin akwai Kokuma wata manufa zata shigo cikin maganar auren mamman da Aleena ba dan haka yafi kowa farin ciki

Su kansa su mum dinsa sunyi farin ciki daga baya Daya nuna musu Yanason su nuna farin cikinsu da Hakan.


Ansha fitina da damuwa sosai akan iyayen Aleena su amince Amma suka qi musamman mahaifinta Sam Sam Bai amince ba.


Har Aleena ta cire Rai sai kwatsam Dad din nata aka wayi gari ya mutu a dakinsa kwance Yana Yana bacci.


Sun shiga tashin hankali sosai sbd Aleena na tsananin son Dad dinta fiyeda mum din shiyasa ma ta hakura da maganar auren mamman bawai Dan shekarunta basu Kai tayi abinda ranta yakeso ba sai dan Dad din kawai.


Jadens family sun shiga tashin hankali da firgicin mutuwar Mr Harris sbd kusancinsu da zamtowansu family friends tin tsawon lokaci me tsayin gaske.


Omar dasu mamman sun shiga damuwa sosai sosai Dan haka Omar ma yaji Yana sake son auren Aleena da mamman Dan ta samu musulunta ita da mum dinta kafin Suma su rasa wannan damar kaman Mr Harris.


Shi kansa mamman yasan yanzu Kam Babu wata shamaki da zata shiga tsakaninsa da auren Aleena musamman yanzu da nauyin komai na kamfanin Dad dinta da uban dukiyarsa zasu dawo kanta.


Mutuwar Mr Harris ya taba Aleena da mum dinta sosai musamman mum din da Bata sake lafiya ba 

Ba Bata lokaci Aleena ta sake amincewa mamman sbd tsananin kulawansa da tattalin dayake nuna musu ita da mum dinta.


Sunyi register na aurensu da komai hakama auren musilunci suka fara yi wedding dinner Daya sukai bayan daurin auren da kwana Daya anan

Duniya ta sake sheda auren nasu Wanda da yawa manyan mutane da respected families Dake tareda su kusa da nesa duk sun samu halartowa.


Babban sa'ar da mamman yasake tsintar rayuwarsa a ciki shine gabatar dashi da Mum din Aleena tayi ga abokanan huldansu na business da sauransu,

Da yawa ta gabatar dashi take ya nutsu ya fara samarwa kansa matsayin da suna a cikin manya ta hanyar nuna nutsuwa da tinani tareda sanin ya kamata harma da bayyanarda tsananin kauna da son dayakewa Aleena da mahaifiyarta da yanzu shine zai tsaya musu.


Da yawan mutane sun yaba dashi Dan take take aka ringa recognizing nasa shida lameenu Wanda yake gabatarwa a matsayin Dan uwansa Kuma abokin tasa huldar.


Omar Baya buqatan gabatancin kowa sbd shi din sananne ne a cikinsu tini Kuma duk yanda suka yaba dasu mamman Omar ne a ransu da idanuwansu fiyedasu.



***Bayan auren mamman da Aleena ya nutsu ya duba ya karanta da kyau yaga duk inda yake tinanin dukiyar Aleena abin ya wuce Nan Dan haka ya sake iya takunsa Dan kuwa son dayake nuna mata tini ya qarasa gamawa da ita da mum dinta take suka Dorasu akan dukiyarsu sbd ita Aleena batada time sbd karatunta na likitanci da saura kadan ta kammala.


Lameenu ya koma Nigeria sbd gudanar musu da ayyukansu na can Kuma Shima Yana komawa Babu Bata lokaci yayi aure Wanda daga mamman har Omar sun halarta angama sun dawo.


Bayan dawowarsu ba jimawa Aleena ta fara aiki a Special Care hospital din data Gina me tsarin Daya dauki kudi masu yawan gaske da hankalin mutane tareda zuba qwararrin doctors da qwararrin nurses da ma'aikata.


Fara aikinta yayi daidai da bayyanar ciki a tareda ita Wanda ya Saka mahaifiyarta da ita murna sosai kamar me

Sedai duk murnarsu basukai ko Rabin ta mamman ba da Daman haihuwar yake Jira dukiya ta tabbata tasa Dan kuwa abinda zata Haifa shine zai gaje dukiyar to Kuma ai shine uban abinda zai Haifa din.


Omar yabar Poland Yana UK gurin qaro ilimi akan harkar business sosai Wanda Shima acan ya Hadu da tasa matar yar asalin kasar Jamaica tin Yana can suka Kai karshe sedai shikam a Jamaica din sukaje Akai aurensu Kuma kowa ya samu halarta hadda Aleena da mum dinta duk da auren musulmai ne sun halarta.


Bayan auren daga Omar din har Nur dinsa a UK suke sbd itama karatun takeyi Amma ita yanzu ne ma ta fara a matakin farko take.


Lameenu na Nigeria,

Mamman na Poland

Omar na UK,

Haka kowannensu yake gudanar da rayuwarsa bisa tsari da yanda yake Sonta Dan kuwa kowa takai masa iya iyakar yanda yakeson.


Haihuwar Aleena ce ta sake hadasu guri Daya sbd farin ciki Mai tsananin gasken da suka samu rayuwarsu a ciki da karuwar seelahs,


Duk wani Wanda yake Hulda ko yasan seelahs Saida ya sheda farin ciki me tsananin gaske da sukeyi da samun haihuwar farko a cikinsu Kuma Allah a Karan farko Saiya albarkace su da samun 'yan biyu duka Maza.


Mam Bai taba dauka ma zaiji irin farin ciki da tsananin kaunar yayan fiyeda komaiba Saida aka haifosu ya rungumesu jajaye dasu kaman wasu taurari.


Mum din Aleena har hawayen farin ciki ta ringa yi tsabar murna kusan tata dukiyar mallaka musu ita tayi a matsayin will dinta idan ta mutu a Basu 60% na dukiyarta sauran 30 a bawa Aleena din.


Wannan will din ba qaramin dadi yayiwa mam ba Dan haka soyayyar 'yayansa ta ninku a ransa Dan kuwa ya tabbatarda sune mukullin arzikinsa mara adadin dabai samu riqewaba sai yanzu,

Sune sa'arsa Daya Dade Yana jira ta shiga hannunsa,

A yanzu Daya samesu yasan dukiyar Aleena tasa ce itama tinda ta mahaifiyarta ta zama tasa burinsa Daya ne ya rage a rayuwarsa shine mallakar dukiyar Omar wadda duk abinda zai mallaka idan ba ita suka mallaka ba bayajin zai iya numfashi me dadi.

#MAMUH#

#AMEENATOU

#LIFE

#ROM

#JJS

#THE SEELAHS



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

 _Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments