Breaking News

Ameenatou 8


 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#Arewabooks@Mamuhgee

#ZafafaBiyar


8

ASHNA BEAUTY SKINCARE 

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku


*********

Bayan haihuwar Aleena Omar yasake yiwa mam magana sosai akan musuluntarta Amma Sam mam Baya wani takurawa ko damuwa da maganar sbd ganin yakeyi duk lokacinda taso zata iya musuluntar tinda dai shi yasan yayansa musulmai zasu tashi a hannunsa.


MUHAMMAD HAROON HASSAN SEELAH da MUHAMMAD JAMAAL HUSAIN SEELAH shine sunan da 'yayan sukaci Wanda daga Aleena har mum dinta Babu Wanda ya musawa sunan kawai dai suna kiransu da Haroon and Jamaal wani lokacin Kuma little seelahs.


Jamaal da Haroon identical twins ne da ko farcensu baka iya banbancewa bare wani abu nasu,

Kamanninsu sunyi mummunan yawan da dole ake banbance musu kalan tufafin sakawansu Dan gane waye Jamaal waye Haroon.

sun taso cikin tsananin kulawa da gata tareda asalin rayuwar da ake kira luxurious life,

Sun taso a cikakkun halfcase Dan kuwa kana kallansu zakasan baturiya da baqar fata ne suka Hadu suka haifesu sedai Allah yayi musu arzikin tserewa dauko gashi irin na mahaifiyarsu hakama hasken Basu wani dauko nata ba na Dad dinsu ne sedai sun fisa haske sosai duk da mam seelah ya Dade da komawa tamkar baturen a harkar rayuwarsa gabaki Daya.


Omar ya dawo Poland inda yake riqe da komai yanxu na nasu dukiyar da kamfanin sbd Dad dinsa ya huta Dan haka yanzu kwata kwata Mr Jaden ya aje aiki sbd manyanci hutawa kawai yakeyi a gida shida mum din Omar ne akan komai Kuma kaman yanda kowa yasani yake Gani Omar Jaden seelah ya wuce ajin su mam ta bangaren ratsawan ilimi da qwarewa a aiki ga class din ma ba Daya ba.


Sun tashi daga inda suke sbd dawowansa kwata kwata da matarsa Dan haka sun koma wani Sabon mansion din daban da suke rayuwa a ciki shida iyayen nasa da matarsa wadda har lokacin Allah Bai Basu haihuwa ba.


Jamaal suna cika 17 years a duniya kakarsu Dake tsananin sonsu fiyeda komai da kowa ta rasu bayan ta musulunta a hannun jamaal wanda shine yafi kusanci da ita sosai fiyeda kowa a gidan nasu Kuma itace tafi ganesu fiyeda kowa a family duk da halayensu sosai suketa banbanta Dana juna tin suna fara tasowa,

Raayoyinsu suna Dan banbanta Amma dai halayensu shine abinda Kai tsaye ya banbance Jamaal daban Haroon daban.


Rasuwar Granny ya Saka Dr Aleena shida damuwa sosai harta koma koyaushe tana gida sbd a bayan Sam batada time na gidanta da 'yayanta mum dince ke kulawa dasu tana nuna musu kauna kaman ta hadiyesu.


Rasuwarta duk wani hali na mam ya fara fitowa Wanda yafara bawa Dr Aleena mamaki me tsananin gaske Dan kuwa Kai tsaye ya nuna mata Nigeria zasu tattara su koma gabaki dayansu.


Da farko ta dauka ba da gaske yake ba Amma daga baya ya rufe idonsa da Babu Imani ko Daya a ciki ya Bata zabi ko ta bisu ko ya dauke yayansa ya tafi dasu yabarta.


Bata taba Shiga tsoro da tashin hankali ba rayuwarta irin wannan sai a wannan lokacin.


Omar tafara nema ta sanar masa komai yayiwa mam din magana Amma Sam mam Bai yadda ba daga karshe ma rashin fahimtar akansu yaso qarewa Dan haka ya fita a zancen.


Su jamaal Basu San meyake faruwa ba sbd karatu sukeyi sosai basa wani zama gida musamman jamaal da shine yake karatun medicine kaman mum dinsu Haroon ma yaso medicine din Amma Yana Shan wuyar karatu ba kaman Jamaal ba sai mum dinsa ta sakashi karantar law.


Duk yanda Dr Aleena taso riqe yayanta abin gagara Yayi gashi batason tayi kararsa sbd tana tsananin son mijinta Dan haka ta Yanke shawarar binsa Amma ba zaman can dindin ba zata dawo Poland tanayi tana Dan Kai masa ziyara itada yayanta.


Da zasu koma kwata kwata Nigeria din dukiyar su Jamaal ta Dade da shiga hannunsa Dan haka tata dinma da yawanta sun kwashe sun taho da ita kusan 70% sun baro 30% a Poland din.


A Lagos suka Bude sabon Babin rayuwar masu hannu da Mai a makeken mansion gidansa Dake manne Dana lameenu hakama na Omar na manne da nasa Shikuma sbd tin suna can suka Aiko da kudaden da aka zube masu tarin yawa aka Gina musu shi a anguwar security dinta kadai zai baka nutsuwa da Kwanciyar hankalin da duke me kudi yake buqata.


Matar lameenu ta haihu yayanta har so biyu duk mata ta Haifa Fadeela seelah da Aysha seelah.


Daga anguwar har cikin mansion din da suke rayuwa a cikinsa Babu abinda ya banbanta Dana rayuwar luxury da suka baro a Poland Dan haka su Jamaal Basu wani samu damuwa ba hakama mum dinsu ba laifi taji she's ok sedai hidimominta na can data baro tanajin damuwarsu musamman asibitinta Data karbu tana cikin manyan asibitocin Poland din.


Anan din ma lafiyayyar tsadaddiyar asibiti Alh mam seelah ya budewa Dr Aleena me tsadan gaske aka zuba doctors da kwararrin ma'aikata tafara aiki ahankali ahankali harta fara sabawa tafara sakewa.


Su Jamaal kuwa Basu wani jimaba suka koma Poland makaranta Amma Basu wani jima ba Haroon yafara shiga damuwa da hadda su ciwo sbd baitaba rayuwa Babu iyayensu ba 

Kai tsaye Dad dinsu ya dawo dashi Nigeria karatun sbd Daman yafisonsu a kusa dashi.


Jamaal tin farko shine Wanda yafi Jin mahaifiyarsu a ransa fiyeda Dad dinsu sbd tausayin datake basa sosai kan rashin hutun datake samu ga tinda granny dinsu ta rasu mum din ta sake shiga damuwa gashi Dad yakaita Nigeria bataso sbd Bata sababa Dan haka koyaushe mum dinsa itace a gaba cikin ransa kafin dad.


Tinda Haroon ya dawo Nigeria hankalinsa ya kwanta sbd Yana tareda iyayensa,.ita Kuma mum dinsu bataso Hakan ba ko kadan Dan haka ta sake shiga damuwa sosai sosai Dan har gobe batada shiri ko niyar zaman tabbata a Nigeria musamman data fara fahimtar dukiyar Alh Mam din sake babbaka takeyi sosai fiyeda tinani sbd mummunan business din dasuke gudanarwa a bayan fagen business din gasken da akasan sunayi Dan kuwa suna cikin wainda sunansu yafara yaduwa Yana karadewa sbd kudinsu Dake magana.


A nata tsarin data yankewa kanta dukiyar ma bar masa zatayi gaba Daya ta tattara ta komawarta kasarta ta riqe 'danta Daya tinda shi Haroon sosai yanzu yaketa samun shaquwa da Dad dinsa fiyeda Jamaal Wanda shikuma acan wata irin kauna Mai karfi da shaquwa ce take shiga tsakaninsa da Dad Omar Wanda haryanxu Bai samu haihuwa ba.


***Shekaru sun Dan Kara ja Dan kusan Haroon Dake Nigeria karatunsa yafara Nisa Wanda Dad dinsa ke tsananin alfahari dashi Dan kuwa kusan a matakin dayake Kai yafara sanin huldodin Dad dinsa da Dad lameenu Wanda duk da basa Ashalawa a yanzu Amma suna cikin masu fada a cikinta Dan kuwa Babu huldar da zaa kulla a gama a Ashalawa batareda saninsu ba ko kasonsu,

A matsayi da matakin da suka Kai jini da rayukan da suka kawosu matsayin bazasu kirgu ba Dan haka Allah yake sake musu talalan yanda sukeso suke samu Dan a jere da layin masu kudin gaske idan zaa ambata Seelahs na Daya daga Yan farko farko.


Sunada money and power fiyeda yanda ake zato,

Sunada tarin girma da mutunci a idanuwan mutane sbd suna cikin masu bugun gaba su Bada tallafi da taimako duk lokacinda zaa buqaci Hakan sbd son sake samun matsayi da mutunci a idanuwan mutane talakawa da manyan mutane.


Duk tarin daruruwan arzikin da Allah yayi musu haryanxu Omar ne a gabansu Dan kuwa takowanne bangaren haryanxu shine a gaba kafin su,

Baya Nigeria Amma yanada tarin dukiya da kadarori da suna a Nigeria musamman haryanxu dayake tareda Aron da Ahmed Yan amanar da suka zama tamkar wasu Yan uwansa na jinin musamman Shima nasa dangin suka koma sirkin Muslims da ahlulkitabi Dan zuriar mr Jaden gaba dayansu sun Dade da amsarsa a matsayin nasu kaman yanda Shima Jamaal nasu familyn yake a sirke.

#MAMUH#

#JAMAAL JEEY SEELAH

#DEEP

#HAROON SEELAH

#LOVE

#CRAZINESS

#ZAFIN KAI

#AMEENATOU


ASHNA BEAUTY SKINCARE 

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku


*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments