Breaking News

Ameenatou 9


 *_AMEENATOU_*

_Mamuhgee_

#Arewabooks@Mamuhgee

#ZafafaBiyar


9

ASHNA BEAUTY SKINCARE 

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku


**********

Kwatsam labarin rasuwar Mum din Dad Omar ta riski familyn seelahs Dake Nigeria dole suka tattara suka tafi gaisuwa da Alh Lameenu seelah da matarsa harma da yayansa sai Alh Mam da Dr Aleena wadda batada niyar dawowa matiqar ta tafin.


Haroon seelah Bai samu Daman binsu ba sbd tarin karatun Dake gabansa,

Duk yanda mum dinsu taso ya aje karatun ya bisu su tafi tare ya qarasa acan Sam Bai aminta da Hakan ba Dan a rayuwarsa Babu wanda yakeson burgewa da son sakawa farin ciki irin mahaifinsa hakam shi kansa Dad Yana son dansa ya riqa sosai ya qware a harkar sharia Dan tsayawa ga duk abinda ya shafi ahalinsu.


Dr Aleena tin kafin ta tafi Kai tsaye ta sanar da Mam idan ta tafi bazata dawo ba Kai tsaye Shima ya Bata zabin idan ta tafi zai rabu da ita

Ba musu ta aminta da Hakan tinda tasan 'danta Daya Yana acan tareda ita Dan haka ta amince a ranar da zasu tafi ya saketa suna Isa can kasar ma suka shigar da divorce dinsu take Akai komai aka gama batareda yayansu sun sani ba hakama Kai tsaye Bata buqaci komai na sakin da ake bayarwa ba a kasarsu ta yafe masa 

Dukiyarta datake hannunsa tabar masa akan ya kulawa yayanta sbd bataga alaman zai Bata ba Dan kwata kwata Babu sunanta akan komai na dukiyar duka ya cire ya mallake.


Jamaal ne kadai yasan iyayen nasa sun rabu Haroon Bai saniba Dan haka Jamaal sosai yaji tausayin mahaifiyarsa yaci gaba da Bata kulawa Dan tashiga damuwa sosai batada kowa sai shi din a yanzu sai Omar Daya zama tamkar yayanta.


Har sukai kwanakinsu suka gama suka tafi Dad din Baya wani samun Daman ganin Jamaal sbd Jamaal din dayaji Baya buqatan ganinsa sbd abinda yayiwa mum din,

Shi Dan Kai tsaye ne zai iya Jin tsanar Dad din Dan haka ya zabi nesanta kansa dashi a Dan lokacin kafin ya sauko.


Bayan rasuwar mamma kaman yanda Omar ke Kiran Mrs Jaden sosai yake kulawa da Dad dinsa shida matarsa Nur sbd tsufa da manyanci Daya rufesa sosai,

Ko shekara baa rufaba da rasuwar mamma Dad din Shima ya rasu bayan sun mallakawa Omar komai nasu ya gaji wata irin sabuwar dukiya me yawan gaske shi kadai take hankalinsu mamman yayi mummunan tashi abinda suke jima suna dannewa ya taso Dan haka gaba Daya idanuwansu da zuciyoyinsu suka koma kan OMAR JEEDEN SEELAH Wanda shi a nasa bangaren Akoda yaushe yanzu cikin baqin ciki da kuncin rashin MASOYAnsa na asalin gaske yakeyi kasim seelah da iyayen riqonsa da suka daukesa tamkar Dan cikinsu da suka Haifa.


******Bayan abubuwa sun lafa komai ya zama daidai,kowa ya fuskanci rayuwarsa ciki kuwa harda Dr Aleena wadda hasken idaniyarta,Rabin ranta datake jinsa tsakiyar zuciyarta fiyeda komai da kowa 'danta JAMAAL MAM SEELAH ya tsaya cak a kan rayuwarta Bai bari damuwa ko wani qunci ya lalata rayuwarta ba Saida ya tabbatarda da koma asalin Dr Aleena seelah dinta ta dawo rayuwarta ta da mace me qwazo da aji da wayewa tareda sanin ya kamata da burgewa harma da kokari akan aikinta ta bangare Daya Kuma ga sauran dukiyarta datake kulawa sosai da ita tana sake fadada business dinta dukiyarta na qaruwa sbd tanada connections da dama sosai.


Jamaal shine karfin gwiwanta Kuma kuzarin datake karfafa kanta tana komawa babbar macen Daya kamata sbd Sam Bai yarda yaga rauni a tareda ita ba,

Dan shi din kwata kwata ba mutum ne Mai yadda Wani ya takaka ba Koda kuwa Yana sama dakai ne Dan Yana girmama sanin darajar Kai fiyeda komai.


Jamaal shine ya Dora mahaifiyarsa a turban hasken musiluncin da mahaifansu ya kasa dorata duk tsawon shekaru zaman auren da sukai har sai da yayanta sukai wayo Jamaal ya musuluntar da ita itada mahaifiyarta da Shikenan mahaifiyarta zata mutu ahlulkitabinta.


Tana son danta Haroon sosai kaman yanda takeson Jamaal Amma matsayin Jamaal daban yake Dana kowa aranta Kuma daga Dad din har Haroon sun San da Hakan sedai Shima Dad din yafi qawa zucin Jamaal sbd tsananin zafin kansa Dan Yana kaunarsa akan Hakan fiyeda komai,

Jamaal dinsa Baya daukan reni ko kadan sabanin Haroon da karatun sheriar da yakeyi duk ya Sanyaya zuciyarsa ya koma Yana kallan komai akan tsari na sharia Dan tsoron aikatawa Dan gudun sabawa sharia.


Duk Dad keson Jamaal kusa dashi Hakan Baya samuwa sedai ya kawo musu ziyara a ya Dan yi watanni ya koma Amma Sam Baya iya rabuwa da mahaifiyarsa Dan itace abinda yafi komai so a duniya fiyeda koma da kowa Dan haka itama mum din Bata fargaban zuwansa Dan tasan zai dawo mata.



****Dad Omar Jaden seelah ya dawo Nigeria da zama a karo na farko tin bayan barinta sedai yazo yayi ziyara yayi Hutu ko wani lalurar ya koma Amma wannan Karan ya dawo ne sbd nacin Yan uwansu su mamma da lameenu Da suka matsu su hade guri Daya da Dan uwansu Rabin jikinsu,


Dawowansa Nigeria ya Sakasu samun wata irin nutsuwa da Kwanciyar hankalin da Basu taba samuba tinda suka rabu dashi se yanzu Daya dawo gasu gashi ahali Daya zuria Daya.


Duniyar duk Wanda yasan seelahs gabaki Daya da iyalinsu Basu taba sanin su ukun ba uwa Daya Uba Daya suke ba sbd tare aka Sansu tare ake jinsu hakama suna Daya da suke amfani dashi hakama dukkaninsu Babu Wanda ya taba fadawa wani ko Yan jarida masu fira dasu abu Daya suke fada musu su din Yan uwane da jini Daya yake yawo a jikinsu.


Kaman mansions dinsu suke a jere haka securities dinsu kusan duk Daya ne Kuma dawowan Alh Omar Jaden seelah ya Saka aka sake samun securities na gidansa daban shi Amma na gidan lameenu da Mam Daya ne.


Tareda Jamaal ya dawo Nigeria Dan haka Jamaal din a gidansa yake zaune tareda shi sbd Mom Nur Bata biyaosa ba tana can itama aikinta datakeyi acan Bata saki ba shi Kuma Bai takurata ba.


Alh Mam ya sake aure tini ya auri matar wani abokin huldansu Daya rasu anan Lagos wadda suke kira da Mum Atee asalin sunanta Atika.



***Tinda Alh Omar ya dawo Nigeria kullum busy yake daga shi har su Ahmed da Aron da yanzu bawai masu aikinsa bane Suma sun zama kaman abokanan aikinsa Dan ya Basu matsayi me kyau Dan haka Sam basa zama sai sunga sun gama daidaita komai nasa anan Nigeria din yafara huldodinsa kaman kowa.


Da farko su Alh Lameenu sun masa tayin su hade dukiyarsu kaman yanda ta Mam da lameenu din take Amma sbd akwai dukiyar dayake son warewa mahaifiyar kasim da haryanxu tana Raye sai yace su datakata tukuna.


Hakan da yayi ba qaramin kular dasu yayi musamman lameenu

Dan haka ko sati biyu baa rufa ba da maganar aka bugawa Alh Omar din waya cewan innar kasimu ta rasu gidanta datake ciki Wanda Omar din ya Gina mata a kauyen na alfarma da Kwanciyar hankali kawai cikin dare akaga ya kama da wuta Dan haka gawarta ma kurmus aka samu.


Ya shiga tashin hankali da mamaki sosai da Jin wannan mummunan labarin sbd baifi sati ba da yayi magana da ita a waya duk da ta tsufa sosai.


A ranar ya shirya suka bi jirgin shi da JAMAAL da Baba Ahmed zuwa gombe.


Sai dare suka Isa

Suna sauka motocin da aka tanada suna jiransa da securities suka kama hanyar kauyen da sai sunyi kusan kwana da wuni Basu Isa ba Dan gaba Daya yayi Nisan da kaman ma baa Nigeria suke ba can asalin asalinsu Wanda ake Kiran kauyen da suna Kartako.



Tafiya sosai sukai tareda jigata Amma dai dole sai je yayi jana'izan inna Dan kuwa itace uwar Data rage masa a duniya Kuma ta tafi tabarsa kaman yanda kasim ya tafi ya barta.


Koda suka Isa Jamaal duk karfin halinda amai ya ringa yi sbd Bai taba wannan wahalan ba duk da ga AC ga komai a mota Amma dai ya gaji matiqar gaske baima taba zuwa irin wainnan gurarenba ko a waya kuwa Bai taba ganinsu ba bare Dan dayasan hakane da Bazai ce zai taho tareda Dad Omar din ba.


Isowarsa ya Saka mutane taruwa anata tururuwar gaidashi kaman zasu masa sujjada sbd girmamawa Dan kaf kauyen Babu Wanda baisan Omar seelah ba,

Seelah Daya kwalli Daya daya rage Mai tinawa da asalinsa tareda taimkawa kowa Dake kauyen,

Shi kadai seelah din Daya rage musu tin daga kan iyayensu har sauran da tini suka mance da kauyen.


A taqaice ma dai shi kadai suka sani a yanzu.


Anyi jana'izan tin kafin isowarsa Dan haka addua kawai akayi ya zauna ya tattauna da manyan kauyen sosai wainda duk suke a bushe kaman Kara,

Kowa ka kalla a kauyen kaman kazo karkarar aljanu haka suke duk sun bushe duk da Yana tallafawa sosai Dan kaman shine yake ciyar da kauyen gabaki Daya.


Inna duka rayuwarta Yaya biyu ta Haifa,

Kasim da indo wadda take aure a kauyen kusa dasu harda 'yayanta biyu Maza sai kanwar mijinta AMEENAH datake riqo Dan haka ya buqaci ganinsu.


Koda aka aika Kiranta tazo tana ganinsa ta fashe da kuka Dan shine Dan uwanta itama Daya daya rage mata.

#MAMUH#

#JAMAAL JEEY SEELAH

#DEEP

#HAROON SEELAH

#LOVE

#CRAZINESS

#ZAFIN KAI

#AMEENATOU


ASHNA BEAUTY SKINCARE 

Free class free class  

Assalamu alaikum yar uwa kina neman inda zaki koyi sanaa wadda zaki dugara dakanki Ashna skincare and more tazu muku da garabasa ta musamman inda zata kawu muku yanda ake hada wannan abubuwan kyauta 

Carwash 

Airfreshner 

Liquid soap 

Gamasu nemana hanyar shiga zaku nemeta ta wannan number kamar haka whatsapp only 09031383058

Karku Bari wannan damar ta wuceku


*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

No comments