Breaking News

Diddigar Kaya 1


 DIDDIGAR ƘAYA...

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


                      *Shafi Na ÆŠaya*


*PAID BOOK*


ÆŠANÆŠANO


**WANNAN KARO COMMENTS ÆŠINKU NA DA MATUKAR MUHIMMANCI SOSSAI***


Idanunta da gabaɗaya suka jeme suka kumbure suntum har suka sauya mata kamanni ta sake saukewa kan agogon ɗakin karo na ba adadi, hasken dake ratsowa daga window ɗin ya bata damar kallon lokacin, karfe 12:30 na dare yunƙurawa tayi ta miƙe zaune tana jin kanta na mata wani irin nauyi kaman an ɗaura mata dutsen dala.


Idanunta ta kai kan handbag ɗinta cikin tsananin nazari da damuwa kan ta janyoshi ta zaro wani farin gora ta gimtse cikin hannunta, ɗakin su ta bi da Kallo, ɗakin dake ɗauke da rabi da kwata daga cikin tarihin rayuwarta, duk cikin waenda suke kwance babu wacce zata ce sun yi kusa kusa duk en uwan nesa ne waenda suka zo bukin nan da bata taɓa hasashen yiwuwarsa ba seda taga wankin hula na shirin kai ta dare, kai tsaye zata iya cewa biyar daga cikin ahalinta na ɗakin suna wurin mahaifiyarsu da itama tun zancen ya tashi basu da sukuni.


Ƴar uwarta kuma da suke ciki ɗaya ta ƙaura wa sashen sbd rashin son hayaniyarta, cikin dauriya ta miƙe tsaye jiri na shirin yar da ita, a saɗaɗe ta nufi kofa ta buɗe ta fice, babu kowa a tsakar gidan sede tana iya kallon haske daga sashen mahaifinta alamun idanunshi biyu har yanzu, hannunta har rawa yake wurin cire sakatar ƙaramin gate na sashen nasu ta fice tsakar babban gidan nasu dake ɗauke da sashuka masu ɗan dama.


Chan baya inda haske be cika yawa ba ta je ta tsaya idanunta zube bisa farin robar da aka rubuta sniper da zanen ƙwari a jiki, hawaye masu tsananin zafi ne suka saukar mata maganganun mahaifinta na ƙarshe gareta masu kaifi da ƙuna na amsa kuwwa a kunnuwanta kaman yanzu yake yin su...


"Fauziyya ban san cewa kin tabbata marar kunya fitsararra ba seda kika tsaya gaban su jadda da yaya kina ikirarin kashe kanki saboda abinda yake gata ze miki, kina Tunanin ko wasu iyaye ne zasu yardar ma ɗan su auren mace irinki? Ko ni.. (Ya nuna kanshi da hannu) da Farhan ze zo min da zancen auren mace me makamancin halayenki Fauziyya ina miki rantsuwa ba zan amintar mishi ba, in har kin haifu don Allah ki kashe kan naki in aka ɗaura, jaliha marar tunani.. Daga sadda kika kashe kanki daga sannan ni kuma na zare duk wata alaqa tsakanina dake, zan tsinewa gawarki tun kan a binneki, wanka da sallah ba de a gidana ba don ba zan taɓa yiwa kafira Adu'a ba, kaman yadda kika san hukuncin duk wadda ya kashe kanshi ya mutu kafiri... Don Allah karki faasa, fice ki bani wuri...!"


Kuka take yi sossai tana jin yadda zuciyarta ke mata ciwo, meyasa kowa ya gagara fahimtarta? Meyasa se ita? Hannayenta na rawa ta buɗe roban sniper ɗin ta nufi bakinta, duka jikinta na mugun rawa gwara ta mutu ta bar musu duniyan da wannan bakin cikin, motsin da taji a bayanta yasa tayi saurin juyowa se idanunsu suka sarƙe cikin na juna.


Hannunshi zube cikin wandon Fararen pajamas dake jikinshi masu sulbi da suka fitar da kirarsa na kakkarfan namiji me zaati da charisma, idanunshi masu kaifi ya fara saukewa kan hannunta kan ya É—ago ya tsura mata su na mintuna ya É—aukesu tare da jan tsiririn tsaki, cikin takunshi na zaratan maza ya nufo ta har kaman ze goge ta kan ya É—an ja kuta yace cikin muryarsa me rikitar da mata..


"Mutuwa se ta fi miki sauƙi da aurena! Rayuwar ƙabari se ta fi miki jin daaɗi idan kika mutu kafira da irin rayuwar da na tanadar miki muddin kika sake aka shafa Adu'ar aurena dake! Faizan be yi zina ba da yardar Allah ba ze taɓa auren mazinaciya ba, ki saka wannan a bayan thick lunatic skull na ki..."

Yana kai nan ya tsirtar da miyau ya wuce abunshi ba tare da ko waiwaye ba.


Fitinan da Fatima ta dasa mishi kaÉ—ai ya ishe shi, idan ta mutu se ya fi kowa farin ciki wallahi, ihunta yaji hakan kuma be saka shi waiwayawa ba har ya shige sashen samarin gidan inda nan É—akin shi yake tun kan yayi aure har yanzu.


A kan gwiwowinta ta zube tana kuka me cin zuciya wani irin jarababbiyar kaddara ce wannan? Wadda ake yi mata murnan samun shi kenan a matsayin miji? Wadda shine ya zama duk wani silar taɓarɓarewar farin cikinta, idan da be tsoma kanshi cikin tsarin rayuwarta ba da duk hakan bata faru ba..


Da sauri ta sake kai roban bakinta tana shirin apawa taji an yi chilli da robar, da sauri ta ɗago se taji sauƙan mari bisa fuskanta dake suntume already.


"Fauziyya??? Innalillahi wainna ilahi rajiun..!"

Ko bata É—ago ba ta san jadda ce daga muryar, fusgo ta tayi suka zagaya zuwa kofan sashenta suka shiga, tsallake mutanen dake parlorn suka yi suka wuce kofar É—akin Fauza dake sashen wadda shima mutanen su na Maiduguri ne ciki suka shiga É—akin jaddar, kan gado ta ajiye ta tace 


"Fauziyya kina da hankali kuwa? Meyasa kike shirin kashemu tun kwanakin mu be ƙare ba? Ki bar mu muji da abu ɗaya mana! Kin kuwa san hukuncin ki daga sadda kika aikata abunda kika aikata kuwa? Wuta fa! Kin kuwa san menene dawwama a wuta na har Abada? Haba Fauziyya! Ina iliminki? Wani bala'i ne yafi na jefa kai ga halaka? Akan auren ɗan uwanki saboda laifin da ke kika janyo?"


Cikin kuka sossai take girgiza kai hannayenta gabaÉ—aya a kanta duniyar gabaÉ—aya yayi mata zafi ji take kaman an rufe ta ne a cikin kurkuku me cike da tsananin duhu da zafi, bata iya magana ba Jaddah ta sake cewa


"ba don naji ihun ki na fita ba da yanzu ba wannan maganan ake ba Fauziyya waye ya kawo miki wannan abu? Taya ya zo hannunki?"


Seda ta daka mata tsawa kan ta faÉ—a cikin dasashiyar muryarta..


"Sakinah!"


"Yanzu waennan ƙawayen arziki kenan Fauziyya?"

Sassauta muryarta tayi tace 


"Fauziyya duk abubuwan nan da suke faruwa ki saka a Ranki Allah ne ya tsara hakan ba wai yin mu ba, ina me tabbatar miki kuma Faizan shine alkhairinki in har kinga an É—aura auren nan to tun farko rubutacce ne daga sama! Wlh idan na ganki cikin wannan hali hankalina tashi yake"


Tana girgiza kai saboda babu wadda ze iya hango abunda take hangowa ta fara cewa 

"Meyasa se Faizan? Meyasa Jaddah? Don Allah ki taimakeni Jadda, aure fa ba wai ana yinshi don gobe a fito bane a'a, ana so in ka yi shi ku kasance abadan abada har se mutuwa ta raba, taya kuke hango min farin ciki da zama na har abada daga Maƙiyi na wadda burinshi ko da yaushe ya ga hawaye bisa idanuna? Mutumin da be taɓa ƙaunata ko da na second guda ba, Jaddah idan kuka hana ni mutuwa tabbas zan gudu!"


Bakinta ta buge cikin faÉ—a tace 

"Haba Fauziyya ke kam meyasa kike da taurin kai ne Haka? Auren nan se an ɗaura tunda har iyayenku sun riga sun zartar, tun farko wa ya janyo? A tarbiyarki ban taɓa Tunanin zaki aikata abunda kika aikata ba, gwara ki sakawa zuciyarki salama ki amshi wannan aure don ko gawarki ne na yarda a kai gidan Faizan da irin watsewar da zaki zauna ki mana, kuma babu uban da ze amince da aurenki in har yayi bincike akanki gwara tun wuri mu rufawa kanmu asiri, daga yanzu in kara ganinki ko da a kofar ɗakin nan ne ki gani..."


Tana kai nan ta hau gado ta kwanta tare da kashe wuta, anan Fauza ta cigaba da zama lokaci lokaci tana share hawaye zuciyarta baƙi kirin har bata san sadda bacci ya sureta ba kanta bakin gado tana zaune daga ƙasa.


Sam bata san an yi asuba ba don Jaddah bata tashe ta ba sanin bata sallah, don seda babanta yayi mata har gwajin ciki da HIV kan ya saduda da hana Faizan aurenta Dukda iyayenshi basu damu da duk wannan ba.


Hayaniyar da take ji daga tsakar gidan da salati ya sakata farkawa Sam bata so tashi ba amma jin hayaniyar kaman tayi yawa ne ya sakata mikewa tana yamutsa fuskanta da ya jeme ya rame saboda tashin hankali ta nufi waje, a iyakar sanin ta in har kaji ana hayaniya a gidan Baba Prof to da Fauziyya ne yau kuma to me ke faruwa?


Daga kofar gate na Jaddah ta ja ta tsaya tana kallon matan dake tsakar gidan wasu kuma sun fi yawa a kofar sashensu, tana shirin Juyawa don bata ga abunda ake ba se ta hangi tahowarsa da Fatima a hannu gabaÉ—ayanshi a rikice kana ganin fuskanshi ka san al'amarin dake nufo shi baya kaunar ta ko na miskala zarratin, da ta kura idanu se taga kaman jini ne ke gangara daga jikin Fatimar alamu wannan cikin ma da ya kwallafawa rai ya tafi.


Baki ta taɓe tana jin burbushin farin ciki a zuciyarta, ko yaya shima ya shiga cikin baƙin ciki kaman yadda take ciki, tana shirin Juyawa ta koma taji wata daga cikin en uwansu na cewa

"khaihh na tausayawa yarinyar nan, kishiya ba karamar abu bace a wannan zamani bare ma irin kishiyar da kuka tashi tare matsayin ya da kanwa, iyayenku mata kuma suna auren miji guda"


ÆŠayar wacce Æ´ar uwar Mahaifiyar Fatiman ce tace 

"wannan kam son zuciya ne karara daga gani ai cusa mishi Amaryar aka yi don yadda take ta bore ya nuna komai, Allah sarki Fatima ciki na kusan biyar kenan shima be zauna ba sanadiyar wannan kadararren auren!"


Juyawa tayi ta koma tana mamakin kanta, for the first time kenan da aka yiwa Fauxa Abu ta É—auke kai ta wuce, lallai abunda ya dameta ya dameta.


A kan gadon Jaddah ta sake yin masauki tare da tsunduma komar Tunaninta da ta san babu ranar gamawa, É—agowa tayi jin alamun shigowar mutum.


"Ya Fadeelah!"

Ta kira sunan kawai kan ta maida idanunta ƙasa, babbar yayarta ce itace babba mace a ɗakin su, bata da wani shaƙuwa ko kusanci da kowa a gidan bayan Jaddah da Fa'iza wacce ta san a yanzu ko giyar wake fa'iza ta sha bazata zo kusa da ita ba.


karasowa Fadeelah tayi ta zauna gefenta tare da rike hannunta tace

"Fauxa! Kin ga yadda kika koma kuwa? Wannan anya fauxa ce kuwa? Wannan Fauzan da na sani bata taɓa zama na minti biyu shiru ba tare da ta nemi maganar wani ko faɗar wani ba? Fauxa nata ne..!"


ÆŠago kai tayi tana dan É“ata fuska tace 

"A'a yaya Fadeelah banda É—an banza"


Dariya Fadeelah ta saki ita kuma fauza ta É—an yi murmushi duk sun tuna sadda suke tare kirarinta kenan 'Fauxa kowa naki banda É—an banza' ta kan faÉ—i hakan da proud musamman idan Fatima na kusa se gashi kaddarar Allah ya HaÉ—a su zama inuwa É—aya a matsayin kishiyoyi.


"Bazaki tambayeni yaushe na zo ba? Ko ina yara?"


ÆŠago idanu ta sake yi ta kalleta cikin gajiyawa tace 

"Yaya stop been nice please ba haka muke ba"


Rike hannunta tayi tace 

"I know, yanzu ina so mu fi haka.. Fauziyya ke yarinya ce har yanzu gashi Allah ya jarabceki da auren wadda kika ɗauka a matsayin Maƙiyi gabaɗaya rayuwarki ya kuma Haɗa ki da wacce tun shigowarta gidan nan matsayin agola baku taɓa kaunar juna ba a matsayin kishiya, ba Yola Zaku zauna ba bare ace akwai idanun Jaddah ko Ammi da mammi Abuja Zaku inda daga ku se ku you really need a guardian, please Fauxa ki girma and let me be a good sister I've supposed to be tun farko"


Hawaye masu zafi ne suka saukar mata tana kallon Fadeelah tace 

"Ya Fadeelah kema kin yarda in hakura in zauna da Maƙiyina bayan kin san cewa duk mun tsani juna? Hakanan matarshi ko na minti biyu shiri be taɓa shiga tsakaninmu ba? Yaya Fadeelah wallahi wallahi ban taɓa aikata zina ba, meyasa kowa ze min wannan shedar alhali duk sharrin Faizan ne?"


Fadeelah ta sake rike hannunta tace 

"Fauziyya kiyi Adu'a kinji? Ki sasaautawa ranki ki É—auka cewa wannan aure shine alkhairinki kuma aljannarki karki manta abunda babba ya hango yaro fa baze hangonshi ba ko da kuwa ya hau dutse, yanzu iyayenmu duka fushi suke daku especially ma ke da kike da taurin zuciya, Fatima ta zama abar tausayi tunda tana chan kwance ta rasa cikin da ta kwallafawa rai"


Tace 

"ya fadeela duk cikin munafurcinta ne, ni a duniya Ban taɓa ganin munafuki irin Fatima ba!"


Dafe kai Fadeela tayi, Fauza ta kau da kanta, Fadyaa ce ta shigo itama suka haÉ—u Suka yi ta nusar da ita, É—an banzar taurin kai ne da ita kaman arnan fari, ga kafiyar tsiya da kyar suka samu tayi wanka ta ci wani abu, Fadyaa ta fice ta barsu da fadeela tana ta kokarin cigaba da bata shawarwari.


Walimar da za'a yi ranan har an yi niyyar fasawa Baba prof yace ayi tunda an yi gayyata, duk a Tunanin Faizan za'a fasa auren nan a gobe ganin abunda ya faru kuma har a yammacin da aka yi waliman Da seda mammi ta sa baki kan Amaryar ta fito Fatima na kwance a asibiti, Bayan ta farka tayi ta mishi kuka likitoci suka tabbatar mishi da jininta yayi mugun hawa duk abunda ya É—aga mata hankali haka yayi kokarin kau dashi.


Da takardar ya dawo gida a Tunanin hakan ze zame mishi wata madafa wurin gujewa wannan kadararren aure sede hasashen shi be zama gaskiya ba, a washegarin da safe jama'a masu tarin yawa daga mabanbanta garuruwa ciki harda sarakuna da Æ´an siyasa tare da manyan malaman Æ™asa suka shaida auren 

"FAIZAN IBRAHIM KAKA DA AMARYARSA FAUZIYYA SULAIMAN KAKA" kan sadaki dubu É—ari uku lakadan ba ajalan ba.


Sanarwan yayi daidai da tsayuwar bugun zuƙata masu yawa sede waenda suka bayyana a fili mutum uku ne, Chak numfashin Fauza ya ɗauke ta yanke jiki ta faɗi dama tun safiyar ranar kuka take, Faizan dake zaune kaman mutum mutumi yaji wani duhu ya rufeshi tsana da kyamar auren na ƙara lulluɓe shi.


Fatima da take daga cikin mota dawowar su kenan daga asibiti da mahaifiyarta ta fashe da wani matsanancin kuka me taɓa zuciya, lallai An zalunce ta kuma an ci amanar ta an nuna mata ita ɗin ba jinin GIDAN F ba ce, har Abada bazata manta wannan ba kuma tabbas an taɓa wutsiyar damisar da take bacci cikin matsanancin yunwa...


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

No comments