Breaking News

Diddigar Kaya 4


 DIDDIGAR ƘAYA 

   (Mai Wuyar Tsincewa)


بسم لله الرحمن الرحيم 


FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)


ADABI WRITERS ASSOCIATION 


Marubuciyar:

*Zuhraa*

*Hamrah*

*Igiyar Rayuwa*

*Noor Iman*

*Ruwan Sama..*

*Lelewal*

*GAMON JINI paid*

*Kowa Ya ga zabuwa..*

And Now..

*Diddigar ƙaya... Paid*


                 *Shafi Na huɗu*


*PAID BOOK*


ƊANƊANO


**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA🥰❤️**


Da wani kalar sauri ta amsa tana me miƙewa tace 

"Na'am Alhaji! Sannu da dawowa"


Be amsa ba se idanu da ya zuba mata, duk cikin yaranshi itace yake jinta na karshe a cikin zuciyar shi, Allah ya gani babu yadda ya iya ne yake zaune da ita amma ya gaji iya gajiya da halayyarta babu randa za'a wayi gari a yini ba'a kirashi kan case ɗin Fauxa ba, a gida babu irin rashin kunyar da baya ji da kunnuwanshi tana yiwa yayyun ta, duk gidan babu wadda baya girmama na gaba dashi se Fauxa, dokarsu kuwa ba a bakin komai yake ba a gareta.


"Ki je Baba Prof na kiranki"


Daga haka yayi gaba sbd saƙo ne Yayan nashi ya bashi Idan ya shigo ya tura ta, mikewa tayi da hijab ɗinta dogo har ƙasa kaman ta Allah ta fice, harabar gidan tar kaman rana har ta isa babban parlorn na Baba prof dake gefe da shiga kofan sashen nashi da na matanshi, akwai hanya da ze kaika ɗakunan baccinshi kuma akwai wadda ze kaika cikin gidan nashi ta cikin parlorn.


Da sallama ta shiga, babban parlor ne me ɗauke da kujerun alfarma, carpet ne me taushi da tsananin kyau malale bisa parlorn duk girman parlorn Seda ya ɗauke tsab, ga kujerun alfarma na asalin royals, chan gefe shelf ne na littatafai har ba zasu kirgu ba.


A tsakiyar kujera ta ganshi zaune yana nazarin wani littafi, ta karasa kusa da kafafunshi ta zube tace 


"Barka da dare baba"


Ya kalleta kan yace 

"yauwa Fauziyya"


Fuskanshi ba alamun wasa yace 

"me ya hana ki zuwa Islamiyya yau?"


Wuri wuri ta fara yi da idanu cikin in ina tace

"baba... Am dama.. Dama tunda na dawo makaranta ne na fara ciwon ciki shiyasa ban je ba"


Yace 

"kin san Allah yayi mana hani da karya? Ya kuma kwaɗaita mana riƙe gaskiya a kowanni hali? Karki kasance cikin makaryata sbd daga furucinki zan iya cewa kai tsaye ba gaskiya kike faɗi ba, me yasa baki son karatu daga na boko har na Arabi?"


Kanta dake kasa ta girgiza tana forming hawaye tace

"kayi hakuri"


Yace

"na haƙura, na san ki da tsanar karya hakan yasa farar ɗaya na gane ki, Fauziyya karatu na da wani irin muhimmanci a rayuwarmu daga boko har arabi, barin ma arabi da ya zama dole wajibi a garemu mu nema, duk girmanka da tsufanka dole ne ka cigaba da neman ilimi sbd shi ze zama haske a rayuwar duniyarka da lahirarka, Allah SWT yace ku sanni kafin ku bauta mini idan har baku sanni ba to ta yaya Zaku bauta mini? Haka kuma Ayar farko da ta fara sauka da Kalmar 'Iqra' ta fara to meyasa bazaki dage wurin gyara gobenki ba?"


Nasiha ya cigaba da yi mata da misali da ayoyi da hadisai masu magana akan neman ilimi musamman Addini, tana shiru bayan ya gama ya sallameta ta miƙe ta fice ba wai don ta ɗauki ko abu guda da yace a cikin nasihohin shin ba.


Ya kamata ku san wani gida ne haka? 

Wannan gida da mutane suka mata laƙabi kala kala wasu su ce 

"GIDAN F" dalili kuwa duka yaran da suke cikin wannan gida sunansu daga F ya fara.


Wasu su ce 

"GIDAN PROF KAKA" dalili kuwa babu wadda be san waye PROF Ibrahim KAKA ba a faɗin Nijeriya da ma kasashen ketare.

 Dalilinshi ne ya sanya gabaɗaya unguwan tasu ta tashi daga ainihin sunanta ta koma 

"UNGUWAN ƳAN BORNO"


Wannan unguwa na kafe ne a tsakiyar garin Yola na Adamawa state, zagaye yake da barebari Albarkacin dattijon arziki Baba Prof, asalin su ƴan garin Maiduguri ne na jahar Borno, daga uwa har uba barebari ne, a garin Borno Zulaikha wacce yara suke mata laƙabi da Jaddah ta haife su, su biyu ne rak wurin Mahaifinsu Abubakar Kaka, Baba prof wadda Asalin sunanshi Ibrahim Abubakar kaka da kuma ƙaninshi Sulaiman Abubakar Kaka.


Mahaifinsu mutum ne me nagarta kuma babban malami a jahar Borno, karatu da karantarwa gadon su ne sbd abunda suka taso suka samu Mahaifinsu da shi kenan, a wurinshi suka fara karatu na addini ya basu ilimi me nagarta musamman ibarahim da kullum karfe biyun dare haka ze tashe shi ya makala mishi redio yana sauraran karatuttukan malamai tun yana gyangyaɗi yana farkawa har ya dawo daga baya idan ze kwanta da kanshi ze cewa Mahaifinsu idan lokacin karatu yayi a tashe shi fa kar a manta.


Wani irin buɗewa kwakwalwanshi tayi da Alqur'ani wadda har ya iya qira'o'i da riwayoyi iri iri, a tsakanin ya shiga boko wadda be hana shi yin karatun shi ba, duba da iyayensu girma ya fara kama su gashi shine ɗan su na fari dayake Jaddah tana yawan haihuwa ne suna komawa, haka ta cigaba ko da bayan ta haifi Ibrahim ya tsaya.


Shi kaɗai ya buɗi ido ya gani a gidan hakan yasa ya ci alwashin gadar Mahaifinshi, wadda karantawar tashi wata rana yake fata ta zama sadakatul jariya ga Mahaifinshi, yana da shekaru goma sha biyu ya haddace Alqur'ani, hadda marar gargada bare kame kame, be dena karatun littatafai ba har ya shiga jss3 anan ne Jadda ta sake haihuwa bayan shekaru masu yawa inda ta haifi Sulaiman.


Shekarar su uku da Sulaiman ya samu scholarship sbd irin kwazo da ilimin shi da ya baza ko ina a cikin garin na Borno, har wasu state ɗin da idan be je musabaqa ba to ze je su debate, quiz, spelling bee da sauransu be kuma taɓa ɗaukan na biyu ba.


Madina yayiwa tsinke inda ya dage ya maida hankali yayi degree ɗinshi na farko har kuma lokacin be dena neman ilimin addini ba, bayan shekaru huɗu ya dawo Nijeria.


Alhamdulillah be bar iyayenshi haka ba ko da yake chan, ko da ya dawo ya cigaba da taimaka musu da karfinshi, yayinda Sulaiman ya fi maida hankali a boko Dukda dae ba laifi shima yana da iya nashi karatun na addini sede ba kaman Ibrahim ba.


A haka ya koma Madina yayo masters fannin kasuwanci, bayan ya dawo ya tafi America yayi degree ɗinshi na uku fannin halayya, anan ne ya dawo Nijeria lokacin Mahaifinsu na cikin hali na ciwo Sulaiman yana jami'a.


Wasa wasa Dr Ibrahim KAKA ya zama sananne a harkar musulunci, karantarwa da da'awa babu inda kafafunshi basu taka ba a Nijeriya, wani wurin har jifa suke sha, ruwa, rana, zafi, iska duk ya ƙare a kansu amma basu karaya ba.


A haka Allah ubangiji ya karɓi ran Mahaifinsu yana me alfahari da kaɗan da Allah ya bashi masu albarka sede kuma da takaicin rashin ganin auren Ibrahim sbd har lokacin be maida hankali kan mace ba, ina ka fito karatu ina zaka karantarwa, me kaci karatu, me ka sha karatu haka Ibrahim yake.


Sulaiman na Bautar ƙasa a Adamawa aka fara hare haren boko haram tashin farko kuma da matukar zafin su hakan yasa Sulaiman ya nemi Yayanshi Ibrahim da ya riga ya zame mishi uba sbd irin respect da yake bashi ya wuce na wa, akan su zo yola da Jaddah tunda apartment da shi baba prof ɗin ya kama mishi me girma ne.


Be ƙi ba haka suka dawo cikin garin Yola wadda ya kasance dawowar kenan, wasa wasa Ibrahim yayi wani irin kafuwa sbd mutum ne me zafin nema Sam baya kwanciya kawai yaji daaɗi, a tafiyan su wani kauye ne na mayo belwa ya samo Aisha(Mammi) gani ɗaya ya mata yaji nan duniya itace macen da ta dace dashi ko da ya dawo kan yayi magana Sulaiman ya tare shi da zancen ya samu mata, shima nan ya faɗa musu yayi mata farin ciki wurin jadda harda hawaye.


fili babba ya saya ya samu architecture ya tsara mishi yadda yake so gidansu ya kasance na dindin din kuɗi ya zube aka soma aiki, wata uku aka gama komai sashe uku ne se masallaci da islamiyya babba daga jikin gidan, a lokacin aka yi bukin su.


Yadda faɗan boko haram ke tsamari a Maiduguri yasa yake ta sayan kananun Gidaje a unguwan yana saka ƴan uwa da abokan arziki kusan almost rabin unguwan shi ya mallaka musu Gidajen su kuma in har ya kiraka akan ka dawo yola to wannan gida naka ne halak malak.


Wani irin buɗi yake samu sbd alkhairanshi dake da matukar yawa, basu shekara biyu da Mammi ba ta haifi Yaron su na farko da ya ci suna FAIZAN(Genorous/Me karamci ko kuma beneficence wato me aikata mai kyau), bayan wata uku da haihuwar Faizan ruqayya(Matar Sulaiman) itama ta haihu ta samu ɗiya mace wacce ta ci sunan Fadeelah(Virtuous wato tagari).


Ba'a rufa shekara ba Aka sake baiwa Baba prof mata Hussaina daga Wani kauye na jalingo da ake kira Sunkani, itama Fulani ce ba'a ɓata lokaci ba aka yi bukin nasu, shekaranta ɗaya Mammi kaman yadda Faizan ke kira ta sake haihuwar ɗa namiji Faahim(me ilimi or mai fahimta).


Ammi itama ta sake haihuwar Falaq(Ketowar Alfijir), Anan hankalin Ruqayya ya soma tashi, dama wani irin zama suke yi marar daaɗi da Maa wadda musabbabin abun Ruqayya ce, tunda ta saka kafa gidan ta fahimci nisan dake tsakanin Ibrahim da Sulaiman kaman nisan dake tsakanin sama da ƙasa ne, wai ba haka aka so ba kanin miji yafi miji kyau.


Bata kara shiga tunani ba seda taga irin girmamawar Sulaiman ga Ibrahim kai tsaye zaka iya cewa matsayin mahaifi ya bashi don ko ratar dake tsakaninsu rata ne me girma, randa ta haihu kuwa taga Sulaiman ya ɗauki yarinyar musamman ya kaiwa Ibrahim shi ya mata huɗuba ya sa mata suna alhali ta riga ta faɗawa Sulaiman sunan da take so a sawa yarinyar, ba karamin rikici suka yi ba akan sunan Fadeelah sede Sulaiman ya fi karfinta haka ta bari, sede daga ranar maganan arziki ita da Mammi babu dama chan sama sama ne, se kuma gashi Mammi na jera maza Ita kuma tana jera mata alhali Ibrahim da Sulaiman basu bambanta dukiyar su ba.


Zaman doya da manja ake yi a gidan har Amaryar baba prof itama ta haihu ta samu mace, Falusha(Haske).


Bayan haihuwan Falusha Baba prof yayi tafiya Maiduguri inda ya dawo da Auren Zainab, ba karamin rikici aka yi da Hussaina ba kan ta saduda, Mammi kam fatan alkhairi kawai tayi mishi, a lokacin ma tana da tsohon ciki inda ta haifi Fahad(Damisa) ba'a ɗau lokaci ba Ammi ta sake haihuwan Fadyaa(sadaukarwa).


Hussaina da yaran suke kira Maami ta sake haifan Farrah(Florence nau'in haske), har lokacin zainab bata haihu ba, Baba prof ya karo aure cikin ƴan gudun Hijira Sakinah itama barebari ce usul, a tare suka fara haihuwa da Zainab wacce su Faizan ke kira Umma, ita ta samu Faraj(cure, waraka kenan) yayinda sakina ta samu Farzan(me wayau).


Daga nan dukkansu basu sake haihuwa ba seda aka ɗau lokaci Ammi kuwa ta haifi maza biyu a tsakani Farhan(farin ciki) da Faris (horseman).


A lokacin Baba prof ya kara sashe a gefe da masallaci sbd matasan yaran da suka fara tasowa, Mammi ta sake haihuwar  Farida(ta musamman ko lu'ulu'u me daraja) daga nan har yau bata sake haihuwa ba.

Bayan nan Sakinah (umma) ta sake haihuwan Farhuddeen(farin cikin addini).

Sulaiman ya ƙara aure inda ya auri sumayya ta zo gidan da ƴarta Fatima, sumayya sun haihu tare da Ammi(ruqayya), Ammi ta haifi Fauza (triumphant wato nasara) yayinda sumayya ta haifi fa'iza (Gain, wato samu).


Bayan su Fauxa, sumayya ta kara yara uku Fadiyah(me kyau), Fakiha(fruits) se Faazila(gaskiya) su kenan yaran gidan karan katakap.


Mammi na da huɗu Faizan, Faahim, Fahad da farida.

Maami na da biyu Falusha da Farrah.

Umma na da guda biyu Faraj da Farhuddeen.

Daada na da guda ɗaya Farzan.

Gabaɗaya yaran na Baba prof guda 9 ne Allah ya bashi.


Se Alhaji wato Sulaiman.

Ammi na da shidda Fadeelah, Falaq, Fadyaa, Farhan, Faris se Fauxa.

Aunty Amarya na da huɗu Fa'iza, fadhiya,Fakiha da Faazila.

Gaɓadaya yaranshi 10.


Gidan na da wani irin dokoki ne wadda duk tsari na addini ne, yaran kuwa akwai matukar shakuwa, tausayi da kauna irin ta ƴan uwantaka a tsakaninsu Baba prof baya wasa da tarbiyar su ko na miskala zarratin, duk kuma abunda ze shimfiɗa hannu bibbiyu Alhaji ke karɓa.


Ya ƙara samun wani girma ne a unguwan sbd yadda baya banbance ƴaƴanshi da na dangin shi Dukda ba komai yake da iko akai ba sede fa ya san duka yaran don dole a islamiyya ɗinshi zasu yi karatu kuma shi da kanshi yake koyar dasu sbd dumbin falala dake cikin koyarwa da yara addini babban sadaqatul jariya ce wacce bata gushewa har se me wannan ilimi ya gushe idan kuma akwai wadda ya koya daga wurin ɗaya haka ze yi ta gudana har illa ma shaa Allah.


Wannan al'ada itace zaɓarwa yara abokan zama masu nagarta, kawai ze kira ka a waya akan Zaku yi baƙo ze zo wurin wacce kaza, ko kuma wane kaza na gidan ka yaje wurin wacce kaza na gidan wane, a haka ya Haɗa wani irin bond me girma tsakanin kaɓilarsu ta barebari da suke nan unguwar, kuma duk zaɓin shi suna alfahari dashi sbd baya taɓa zaɓin banza.


Mata da mazan gidanshi kan yi karatu har matakin degree ma idan har maneminki be fito ba, sbd ya san muhimmancin karatu ya kuma san karatu wani makami ne da zaka barwa yaro wadda ba ze taɓa tagayyara ba hakan ne dalilin da ya sa ko maneminki ya fito baki fara makarantar gaba da jami'a ba dole akwai yarjejeniyar ci gaban karatun ki don gudun halin rayuwa. 


Faizan pilot ne wato matuƙin jirgi wadda aka fi sani da Captain Faizan matashi me jini a jika, kyaun fuska da na hali, ilimi both Islamic and western, his father's favorite, the first born to the house of F, har yau Allah be yi yayi aure ba kaman ba Baba prof ne ya haife shi ba.


Fadeelah tana auren wani businessman suna zama a Australia with kids.


Faahim Navy ne, an aura mishi Fadyaa suna da ƴaƴa biyu. Auren da saida aka kai ruwa rana da Ammi ta saduda. 


Falaq har yau bata yi aure ba sbd rashin lafiya da take fama dashi.


Fahad na aiki da inland revenue with a wife and a kid.


Farida tayi aure some months ago with a costume officer suna zaune Lagos.


Falusha and Farrah duk tare aka yi aurensu su biyun duk suna yola suna auren ma'aikatan Gomnati.


Faraj, Farhan da Farzan duk suna final year of their studies a Apti American University mabanbantan courses.


Farhuddeen da Faris suna SS3 


Fatima na SS2 


Fauxa da fa'iza na SS1


Fadhiya js1, Fakiha pri5 and Faazila pri3.


Tou readers ya kuka ji GIDAN F? A tunaninku duk wani haɗin kai da kaunar juna da zaman lumana dake wakana a wannan gida me cike da addini me ɗaurewa ne har abada? Sheɗan ze iya barin ɗaurewar wannan haɗin kan da kaunar kuwa? Akwai wasu abubuwan da ban sa cikin tarihin gidan ba a hankali a hankali Zaku fahimta in shaa Allah, mu je zuwa🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️.


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne.. 

Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin 

09039206763 

Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               🖤Gureenjoh🖤

No comments